Skip to content
Part 30 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Tana kwance ta ƙudundune a jikinsa shi kuma yana latsa waya ya ɗan dubeta ya ce,

“Baby tashi ki je ki kwanta ina son infita ne.”

Sake ƙudundunewa ta yi sosai ta ce,

“Sanyi nake ji.”

Ya gane sarai abin da take nufi, ta tsani ya ce zai fita ya barta a cikin wannan gida mai girma. 

“To tashi mu tafi tare sai insaukeki a gidan Salim.”

Kamar ƙiftawan ido ta miƙe tana mitsittsike idanu.

“Don Allah da gaske kake yi?”

Ya gyaɗa kai. Har zata shiga ɗaki ya dawo da ita,

“Idan kina son mu fita tare sai kinyi min alƙawarin yanzu zamu je ki cire kunyar nan ki barni inyi son raina.”

Narai-narai ta yi da idanu kamar zata yi kuka. Hakan yasa ya koma ya zauna yana latsa wayarsa. Ƙarasowa ta yi gabansa ta amshe wayar tare da haɗa hannayenta biyu,

“Na yarda amma mu fara zuwa tukun.”

Ya girgiza kai,

“A’a ban yarda ba.”

Kamo hannunsa ta yi suka shiga ɗaki ta ɗan duƙar da kanta ƙasa,

“To gani kayi kayi mu tafi.

Gaba ɗaya ta bashi dariya. Har yanzu da sauran Husna, dan bata san komai ba akan wannan harkar. Duk yadda yake ƙoƙarin koya mata wasu abubuwa kunya ta hanata aiwatarwa.

Ya ɗan sha mur ya ce,

“Cire kayanki da kanki.”

Ta zaro idanu tana girgiza kai alamun ba zata iya ba. Hakan yasa ya kwanta ya kauda kansa. A hankali take raba kanta da kayan jikinta sai dai ta kasa cire bra ɗin, duk ta zama kalar tausayi. Tana ganin zai jiyo ta yi saurin rufe jikinta a cikin bargo.

Murmushi ya yi tare da shigewa bargon ya jawota sosai. Da kansa ya ƙarasa cire komai ya haɗa fuskarsu wuri guda,

“Husna kinsan irin son da nake yi maki kuwa? Ina sonki fiye da yadda nake son kaina. Don Allah ki bani haɗin kai wajen kasancewa da ke a cikin farin ciki don Allah.”

Yadda yake maganar yana mata waiwayi ya hanata furta komai. Sai wani siririn hawaye da ya sauka bisa kuncinta. Za ta so itama bakinta ya buɗe domin ta gaya masa abin da ke cikin zuciyarta. A yadda take jin sonsa za ta iya bayar da rayuwarta domin ceto tasa.

A wannan rana ta sakar masa kanta sosai fiye da yadda ta yi zato. Shi kansa yasha mamakin irin haɗin kan da ya samu. Kullum yarinyar sake rikiɗe masa take yi. Idan yana tare da ita ji yake kamar babu sauran wata mace irinta. 

Tana kwance a gefen kafaɗarta barci take yi irin barcin nan na gajiya. Ya rasa yadda zai yi ya rabata da jikinsa ya samu ya je ya yi wanka. Sumbatarta ya yi a goshi ya ce,

“Ina sonki babyna. Tashi inje inyi wanka.”

Sake maƙale shi ta yi wanda ke nuna alamun ba zata rabu da shi ba. 

A wannan lokacin ne wani sihirtaccen abu ya sami daman shiga jikinsa. Sai dai da alamun a hankali zai dinga aiki. Tunanin Salima ya dawo masa cikin kai. So yake dole sai ya ganta, amma kuma ya ƙi amincewa da abin da zuciyarsa take gaya masa.

Da wannan tunani barci ya yi awon gaba da shi.

Sai wurin la’asar suka farka Husna ta fito wanka tana sanye da hijabinta ya ware idanu ya ce,

“Me ya sa baki tasheni ba? Kinyi min wayo ko? Anjima ki shirya zan rama abin da kika yi min.”

Turo baki ta yi ta ƙaraso ta shafa masa ruwan hannunta a fuska ta ce,

“Ni wai komai na yi laifi ne?”

Tsura mata idanu ya yi yana jin tunaninta yana gauraya da na Salima. Da sauri ya girgiza kansa tare da ƙaƙalo murmushi,

“To mu je ki rakani inyi wankan.”

Da gudu ta yi hanyar waje sai da ta kai bakin ƙofa ta waiwayo ta ce,

“Wallahi a’a na qi wayon.”

Har ta fice bai iya ɗaga ko da ɗan yatsansa ba. Tunani ne fal a cikin ransa. Jiki a mace ya tashi ya yi wanka da alwala. 

Tare suka fita da ita kai tsaye shopping suka je suka yo daga nan suka wuce gidan Salim. Anan ya barta wajen matarsa shi kuma ya wuce wajen Mukhtar. 

Duk yadda yaso su tattauna akan kasuwancinsu abin ya faskara saboda tunani da ya cika masa kai. Haka ya dawo jiki a sanyaye bai sami komawa cikin gidan Dakta Salim ba ya aika aka kirawota suka kama hanya. Ita dai idanu ta zuba masa tana mamakin irin wannan sauyin a lokaci guda.

Bayan sun shigo gida ne ta zauna kusa da shi cike da damuwa ta ce,

“Uncle me ke damunka?”

Yasa hannunsa ya jawota jikinsa sosai ya yi magana cikin son kwantar mata da hankali,

“Baby yaushe zaki cire min sunan Uncle ɗinnan?”

Gaba ɗaya a rikice take don haka ta sake maimaita masa tambayar. Amsa ya bata da baya jin daɗi ne, kansa ke yi masa ciwo. Kansa ta kama ta jero masa addu’o’i sannan ta tofa masa tana sake yi masa sannu.

Gaba ɗaya Husna tausayi take bashi, domin ya karanci tsantsar sonsa a cikin idanunta.

Yau kwana biyu kenan M.Y yana iya bakin ƙoƙarinsa wajen kaucewa irin abin da zuciyarsa take gaya masa.

Suna zaune a falo dukkansu a ƙasa suke Husna ta yi matashin kai da ƙafafunsa, duk sun zubawa t.v ido suna kallon labarai.

Ya dubeta yana lumshe idanu, irin kayan dake sanye a jikinta suna matuƙar yamutsa shi. Hannunsa ya kai ya zura a cikin rigarta. Shiru ta yi tana sauraren irin saƙon da yake aika mata. Tuni idanunta suka sauya suna lullumshewa.

A lokacin aka kwararo sallama ba tare da jiran izini ba aka shigo. Ɗago kai ya yi yana duban waye wannan mai ƙarfin halin? Haka kuma bai cire hannunsa ba.

Ido huɗu suka yi da Salima a lokaci guda wani rikitaccen lamari ya shiga zuciyarsa. Husna ta daddage ta cire hannunsa sannan ta tashi zaune itama gabanta yana tsananta faɗiwa. 

Ba su jira anbasu izinin zama ba suka zauna. Salima tana taunan cingam tana harare-harare tare da ƙure kallonta a kowane ƙusurwa na falon. Bai ce masu kallo ba haka itama Husna bata ce masu komai ba, domin zuciyarta har tafasa take yi,

“Baby kawo masu ruwa mana.”

Cewar M.Y mamaki ya kamata ta yi ta kallonsa tana ganin wasu abubuwa a cikin ƙwayar idanunsa, amma sai ta dake. Ta tashi ta kawo masu ruwa ta dawo ta zuba masu idanu. Bayan sun sha ne suka dubi M.Y cike da kissa Salima ta ce,

“M.Y wurinka muka zo fa, muna son magana da kai.”

Babu musu ya miƙe,

“Muje mu yi maganar.”

Suka tashi gaba ɗaya suka wuce. Husna ta dinga nanata Innalillahi har zuwa ƙarshe. Bata fatan ta nuna wata alama da zata sa ya fahimci wani abu. Suna ficewa ta shiga ɗaki ta yi kuka kamar ranta zai fita. Har bayan isha’i bai shigo ba, a lokacin ta yi kukanta har ta ji babu daɗi daga ƙarshe ta wanke fuska ta shiga kitchen ta ciro tuwo daga frij ta ɗumama masu da miyar sannan ta fito ta zauna tana jan carbi. Babu irin tunanin da bata yi ba, babu abinda zuciyarta bata gaya mata ba.

Yana shigowa da Sallama ya nufi wurinta da sauri. Ɗago fuskarta ya yi yana nazarta daga bisani ya bata fake kiss a laɓɓa sannan ya mayar da kanta kafaɗarsa yana bubbuga bayanta,

“Sorry baby.. Sorry uncle ya yi laifi ko? Ina fita Mukhtar ya kirani su kansu ban tsaya na saurare su ba na wuce. Ki yafe min.”

Ya ƙirƙiro ƙaryar ne saboda ya rasa me zai ce mata, ya rasa irin ƙaryar da ya kamata ya yi domin ya wanke girman laifin da ya yi. Duk irin abin da yake ji hakan baya hana zuciyarsa tunawa da halaccinta. Ita ce dai sanadin dawo masa da farin ciki.

Ita kanta kalamansa sun yi nasarar wanke shi tas! Kasancewar ta yarda da shi fiye da yadda ta yarda da kanta. Ƙanƙame shi ta yi hawaye yana fita daga idanunta,

“Kayi min komai amma kada ka juya min baya.”

Ya gyaɗa kansa yana lallashinta har ya samu ta yi shiru.

Ko da ta gabatar masa da tuwon duk yadda yake son tuwo a yau sai ya ji bakinsa babu daɗi. Wani zuzzurfan tunani ne a cikin zuciyarsa ya rasa ta yadda zai iya kaucewa wannan masifa da ke shirin tunkaro shi. Maganganun Salima suna dawo masa kai, suna cin nasarar tarwatsa duk wani farin cikin da ya samo daga Husna.

Masu karatu mu je zuwa dai.

Taku har kullum ‘yar mutan Borno.

<< Mu’azzam 29Mu’azzam 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×