Skip to content
Part 35 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Tana zaune ta yi tagumi tana kallonsa. Sai a lokacin ya farka, shima ita ya zubawa idanu. Da ɗayan hannun ya ya fitota, da sauri ta ƙarasa tana kallonsa idanunta cike da hawaye. Kwantar da ita ya yi a gefen kafaɗansa yana jin wani irin tausayinta yana ratsa shi.

“Kada kiyi kuka kinji? Na warware babu abin da ke damuna.”

Bata iya cewa komai ba sai gyaɗa kan da ta yi, tana jin sanyi yana shiga kowane ƙofa da ke buɗe a jikinta. Ba zata iya kintata girman son da take yi masa ba.

A can gida kuwa Salima bata san me ake yi ba, da ta fito tana tambayar bata ga M.Y ba kai tsaye Gwaggo ta ce yana asibiti baida lafiya. Ga mamakinta ko a jikinta sai ma komawa ciki da ta yi abunta.

Da yamma aka sallamo shi, Gwaggo ta haɗa jiƙe-jiƙenta ta bashi yasha. A ranar yaso Gwaggo ta bashi matarsa amma fir ta hana. Sai da ta tabbatar da ya dawo hayyacinsa sannan ta miƙa masa biro da takarda ta ce ya sakar mata ‘ya. Abba yana kallonsu bai ce komai ba. M.Y ya gigice ya shiga ruɗani, duk irin soyayyar da yake gani a idanun Gwaggo akansa a yau bai ga ko ɗaya ba.

Gaba ɗaya sai M.Y ya fita hayyacinsa, ya zama abin tausayi. Ita kanta Salima ta kasa gane kansa. Abba kuwa ganin ɗansa ya susuce yasa ya haɗa Gwaggo da Husna da M.Y ya dubi Gwaggo ya ce,

“Hafsatu ki ba yaron nan matarsa su koma gida.”

Wani sanyi ya ratsa shi. Husna ta ɗago da sauri ta dubi Abba. Shima idanunsa akanta ya ce,

“Husna bakya son komawa ne? Gaya min idan baki son komawa babu wanda zai yi maki dole.”

Ko da wasa ba zata iya duban idanun Abba ta ce bata son ɗansa ba, bare kuma tana sonsa damuwa ce kawai ta yi mata yawa.

“Zan bashi matarsa amma da sharaɗi.”

Duk suka zuba mata ido.

“Muddin na sake ganin Husna cikin ƙunci ba saki ɗaya zai yi mata ba, saki uku ras! Nake buƙata.”

Da sauri ya jinjina kai,

“Na yi alƙawari insha Allahu zan bata kulawa.”

Babu wani sakin fuska washe gari Gwaggo ta shirya Husna suka tattara suka tafi. Salima kuwa ta ɗauki alƙawarin rusa duk wani farin cikin gidan.

A zaman da Husna ta yi da Gwaggo ta koya mata kissa iri-iri don haka ta riƙe su sosai.

Suna isowa Husna ta tsala wanka ta sanya riga da wando da suka fiddo dukka surorinta ta gyara gashinta tana wani ƙamshi irin na Maiduguri.

Sai da ta jima tana kallon madubi sannan ta yi murmushi ta ce,

“Salima kin gama naki wasan yanzu lokacina ne.”

A falo ta same shi, shi da Salima suna kallo. Gaba ɗaya suka bita da kallo kowannensu mamakinta yake yi. Tana ƙarasowa ta zauna kusa da shi tana murmushi,

“Kallo kuke yi ne?”

Ta yi tambayar cikin wata murya mai cike da kissa. Babu wanda ya iya bata amsa, domin kuwa M.Y ya gigice babu abin da yake buƙata sama da rungumeta.

Husna ta zauna sosai ta yadda suke gogan juna ta yi magana cikin marerecewa,

“Uncle ka ga ɗazu bayana kaman wani abu ya cijeni sai zafi yake yi min.

Hannunsa ya zura a bayan yana magana cikin shaƙewan murya,

“Sannu kinji? Muga bayan.”

Hannun ta ciro daga bayanta tana girgiza kai,

“Ya ɗan rage zafin.”

M.Y ya ɓata rai,

“Banason wasa da lafiya.”

Ta miƙe tsaye tana tafiya kamar wata tarwaɗa ta yi hanyar ɗakinta. Shi kuwa ya miƙe yana cewa,

“Muje ingani idan bai bari ba sai akaiki asibiti.”

Gaba ɗaya ya mance da Allah ya halicci wata Salima a wurin. Ita kuwa Salima sai duk ta susuce ta tashi fuuu ta shige ɗakinta. Ta kasa tsaye ta kasa zaune. Ta dai san ta riga ta kashe gabansa ta yadda ba zai iya yin komai da ita ba, to me ya sa ya shiga ya daɗe? Ko dai abun ya karye ne? Da sauri ta tashi ta nufi bakin ƙofar Husna ta cusa kunnenta domin ta ji abin da suke yi.

Cikin duniyanci irin na Husna ta dinga wani irin kuka mai hargitsa wanda ake yi wa, tana cewa,

“Uncle nidai na gaji. Uncle ka bari.”

Salima ta haukace ta shiga ɗakinta tana hauka tana zagi. A lokacin ta ciro asirin da aka ce kada ta fiddo shi idan ba haka ba gabansa da ta kashe zai tashi. Ta fasa ƙoƙon tana cewa duk ƙarya ne ita za a yaudara aci mata kuɗi?

Cikin ikon Allah M.Y ya ji shi lafiya lau, wanda hakan yasa ya ƙara kaimi. Daga shi har Husna sun gamsu, sun gamsar da junansu irin abin da basu taɓa yi ba. Ya gigice ya zama zautacce akanta. Ya ƙara fahimtar bambancin Husna da sauran mata.

Duk da sun sami natsuwa amma M.Y bai daina sumbatanta yana sa mata albarka ba. Kafe shi ta yi da idanunta, a hankali ta kai bakinta saman laɓɓansa ta ɗan sumbace shi,

“Ba zan gaji da nanata maka kalman ina sonka ba.”

Shima ita yake kallo a hankali ya ce

“A kullum kika furta min wannan kalman sukan zama abokin hirana a duk sanda na fita wani wuri. Sun kasance masu yi min rakiya suna faranta min fiye da ayi min kyautan kuɗi.”

(Gareku matan aure, don Allah kada wai dan anyi aure a sami daman gutsure soyayya. Soyayya ta fi daɗi bayan anzama miji da mata. Ki zama mai gayawa miji kina sonsa Walh ko bai nuna maki Komai ba, zaki zauna a zuciyarsa. Wannan wani sirri ne da mata da yawa suka raina shi.)

Tare suka shiga wanka suka yi ta farin ciki kamar basu taɓa sanin wani abu wai ita damuwa ba. Bayan sun fito ya jawo masu bargo bayan ya hanata sanya komai suka rungume juna suna gogan fatan juna cikin wani irin nishaɗi.

Can cikin dare ya ji tana shafa shi a hankali. Ya ɗan buɗe ido ya yi magana cikin raɗa,

“Ya dai baby?”

Ta sake shige masa ta haɗa ƙafafunsu wuri guda ta yi masa raɗa, wanda ni kaina bansan me ta gaya masa ba, na dai fahimci maganar tana da girma domin farin ciki ne ya cika masa zuciya. A lokacin suka sake afkawa wata duniya.

Sai ƙarfe goma sha ɗaya na safiya suka fito kowanne yana ƙamshi kamar sabbin aure. Sun sami mai aiki ta jere masu komai, don haka suka zazzauna ta zuba masa sannan ta zuba nata. Har ya fara ci ta hango fitowar Salima. Don haka ta tashi ta zauna a cinyarsa ta nuna masa bakinsa. Ya fahimci naman da yake taunawa take buƙata. Ya haɗa fuskarsu wuri guda tasa bakinta cikin nasa ta amshe naman. Bata ƙyale shi ba sai da ta tabbatar ta tada hankalinsa a cikin salon kiss ɗin da ya koya mata.

Salima ta yi kukan kura ta yo kan Husna, abin da bata sani ba Husna a ankare take don haka ta tashi tana ƙoƙarin komawa mazauninta. M.Y ya yi saurin riƙe hannunta fuskarsa kamar anyi gobara,

“Me kike shirin aikatawa?”

“So nake in hallakata sannan kaima inhallakaka.”

Zaro idanunsa ya yi sosai,

“Me muka yi maki?”

Kawai sai ta fashe da kuka tana ƙoƙarin ƙwace kanta. Husna ta yi murmushi. Ta yi alƙawarin babu boka babu malam, amma sai Salima ta raina kanta, sai ta rama duk irin baƙin cikin da ta ƙunsa mata.

Anan Husna ta tafi ta barsu ta shige ɗakinta ta rufe. Da ƙyar ya iya shawo kanta, taso ya biyota ɗakinta amma ya nuna mata ba zai yiwu ba sauri yake yi.

Bayan ya fita ne tunanin Husna ya cika masa zuciya, daren su na jiya yaƙi gogewa daga zuciyarsa. Gashi babu waya a hannunta. Dole ya tattara ya dawo gidan. Ƙamshi kawai ke tashi na haɗaɗdun girke-girken Husna, ga kuma wani ƙamshi na turaren wutan ɗaki. A falon ya zauna yana riƙe da kansa alamun ya gaji. Hannunta ya ji a fuskarsa ta rufe masa idanu. Ya saki tattausan murmushi ya ce,

“Wannan hannun ba zai taɓa ɓace min ba. Oya zo ki bani labarin kewata da kika yi yau, dan nasha wahala da babu ke a gefena.”

Zagayo da ita ya yi ta zauna a ƙafafunsa tana dariya. Maɓallin rigarsa ta shiga cirewa tana cewa,

“Ni banyi wani kewa ba.”

Ya sake jawota sosai ya manneta a jikinsa ya shiga bata fake kiss sai kuma ta yi lakwas. Ya yi murmushi ya lakaci hancinta,

“Ga amsata na samu.”

Wanka ya fara yi sannan ya yi zaman cin abinci. Har lokacin babu Salima babu dalilinta. Sai can dare ta fito tana cika tana batsewa. Husna ta katse zaman ta hanyar cewa tana jin barci. Shima ya tashi yabi bayanta.

Salima ta zama kamar mahaukaciya, gashi kullum bokanta gaya mata ƙarya yake yi. Zuciyarta gaya mata take kawai ta kashe Husna ko zata fi samun natsuwa.

Washegari Husna tana shirya M.Y ta ce,

“Yau zaka koma ɗakin Salima sai kuma bayan kwana biyu.”

Ya yi murmushi ya ce,

“Wasa kike yi.”

Bata ce komai ba ta raka shi har mota ta ce,

“Allah ya tsare min kai. Ɗawainiyan da kake yi da mu kuma Allah ya biyaka.”

Ya ware idanu ya ce,

“Ɗawainiyar me nake yi ni kuwa?”

Tana murmushi ta bashi amsa,

“Ko ciyar damu da kake yi ai ɗawainiya ce, wanda ba kowane namiji ne yake iya sauke wannan hakkin ba. Wallahi Uncle samun namiji kamarka sai antona.”

(Anan ma zanja hankalinmu. Dan ciyarwa yana hakki agun namiji ƙarfafa guiwa yana taimaka masa wajen ƙara ƙwazo. Wannan kalaman ma wata dabara ce na sace zuciyar miji.)

Wani sanyi ya tsirga masa. Ya jima yana cefane ayi ta almubazzaranci da su, babu wanda ya taɓa nuna yabawa, bare ace masa ya yi ƙoƙari. Gaba ɗaya ta kashe masa jiki, ya ce,

“Ina godiya babyna. Sai na dawo.”

Yana tafe yana tuna hirar Husna masu daɗi, duk da cike suke da wauta.

Da daddare ta yi wankanta ta yi Sallah ta rufe ƙofarta ta yadda ko key yasa ba zai buɗu ba, ta jawo bargo ta yi addu’a ta shafa.

A cikin barci ta ji bugun ƙofarsa ta yi banza da shi. Hakan yasa ya zuciya ya bar bakin ƙofarta ya shige nasa ɗakin. Bai jima da shiga ba, Salima ta shigo ga dukkan alamu ta shirya ne a matsayinta na wacce ta karɓi girki.

Taku har kullum ‘yar mutan Borno

<< Mu’azzam 34Mu’azzam 36 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×