Skip to content
Part 21 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Oga Saleh ya ƙara so har gaban Gwaggo yana dubanta. 

“Ina son ki zaɓi abu ɗaya. Ko inyanka wannan kafaffen ɗan naki a gabanki, ko kuma ki amince da abin da zan sa shi ya yi… Ina nufin zan bi ɗanki ta baya a yau ɗinnan kuma a yanzu.”

M.Y bai san lokacin da ya damƙi wuyan Saleh ba, kawai yakai masa naushi a baki. Ya ɗaga hannu zai sake kai masa duka yaji anbuga masa wani abu a hannun, hakan yasa ya kasa ko da ɗaga hannun. Husna kuma tuni ta koma gefe tana makyarkyata.

Gwaggo ta rintse idanu tana jin zafin dukan da aka kaiwa M.Y har cikin zuciyarta. M.Y ya yi magana cikin tashin hankali,

“Saleh, ni zan zama ajalinka.”

Gwaggo ta yi magana cikin rawar baki,

“Insha Allahu ba zan ga ranar da ɗana zai aikata irin wannan laifin ba. Ban amince Babban mutum ya aikata mummunan aikin nan ba.”

Saleh ya matso kusa da ita,

“Amma kin amince ke ki bani kanki a matsayin fansar ɗanki?”

M.Y ya rintse ido yana jin wani irin ɗaci

“Saleh! Mahaifiyata ce agabanka.”

“Idan ubanka Yusuf ne a gabana bai dameni ba. Taurin kanka ya jawo maka. M.Y zaka yi biyu babu Walh.”

Gwaggo ta rintse idanu tana jin ba a taɓa wulakantata irin na yau ba. Ƙaran harbi suka ji hakan yasa suka dubi wurin M.Y da sauri. Shi ɗin suka harba a hannu wanda yasa Gwaggo ta fizge da ƙarfi ta nufe shi tana jin jikinta yana rawa,

“Babban mutum kada ka mutu. Don Allah kada ku kashe min shi don Allah. Na amince da dukkan abinda kuke nema muddin zaku bar min shi a raye. Ko me kuke nema ko ni zaku kashe na amince amma ku bar min shi a raye.”

Duk irin zafin da yake ji hakan bai hana shi ware jajayen idanunsa ba yana duban Gwaggo. Bai taɓa tunanin zata furta hakan ba, ko da kuwa gawansa ta gani. Indai kuwa hakane watarana Gwaggo zata iya yafe masa. 

Kafin su sake yin yunƙurin aiwatar da wani abu, sun ji ƙarar bindiga daga waje. Ɗaya daga cikinsu ya shigo ya ce ga ‘yan sanda. 

Da sauri suka yi ta kansu. Gwaggo kuwa tana riƙe da M.Y tana rusa kuka. Sai a lokacin Husna ta ƙaraso inda yake tana duban hannun idanunta sun kumbura saboda kuka. 

Su Salima kuwa idanun nan babu komai sai tsabar tsoro da firgici. ‘Yan sandan suka shigo suka kama M.Y da nufin kai shi asibiti, Gwaggo ta ce ƙafarta ƙafarsu. Don haka har Husna suka shiga mota, su Salima kuma aka barsu da wasu ‘yan sandan don su yi tsaron lafiyarsu. 

Tunda aka shiga da M.Y Husna da Gwaggo suke kuka kaman ance masu ya mutu. 

A ranar basu samu barin asibitin ba, don anriƙe shi ana bashi taimakon gaggawa saboda irin jinin da ya zubar.

Suna nan zaune da misalin ƙarfe goma na safiya, Jamilu ya ƙaraso cikin asibitin hakan yasa su Gwaggo suka ɗan fito domin su basu wuri. 

Gwaggo da Husna suna kusa da windon wanda su M.Y basu sani ba. Hakan yasa Mu’azzam ya dubi Jamilu ya ce,

“Jamilu ka ga abin da Oga Saleh ya yi min ko? Ba zan jira insami lafiya ba, har sai na ɗauki mummunan mataki akansa.”

Jamilu ya rintse idanu ya buɗe cike da danasani,

“M.Y rayuwarmu daga ni har kai tana cikin hatsari. Oga Saleh ya gane cewa ni ne na turo da ‘yan sanda su kawo maka taimako. M.Y tafiyar nan tamu tana gab da tarwatsewa. Kaje ka taimaki mutunin nan da ka gaya min yana can gidan Oga Mu’azu. Kuma don Allah ina son kafin su kasheni ka gaya min wanene shi? Me ya sa duk da kyawawan halayyarka ka faɗa cikin wannan mummunan aikin? Mahaifiyarka ta yarda da kai da yawa, amma ka dubi irin wulakancin da ta samu a sanadiyyarka. M.Y Ka tuba ka daina aikin nan ko da kuwa za su kasheka ɗinne.”

M.Y ya juya da nufin bashi amsa kenan, ya haɗa idanu da Gwaggo cikin kaɗuwa da tashin hankali. Husna tana kusa da ita sai girgiza kai kawai take yi hawaye na bin idanunta. 

Abin da ya ƙara ba Mu’azzam tsoro ganin dukka matansa a tsaye suna dubansa, duba irin na mamaki. Sai dai Salima bata wani razana ba. Saɓanin Bilki da tsoro ya cika zuciyarta.

“Mu’azzam!”

Ta kira sunansa a karo na farko, kuma cikin ketowan zufa da tashin hankali. Da ace ba da kunnuwanta ta ji ba, da sai ta ƙaryata wanda ya zo mata da wannan labarin. 

Sai yanzu wasu abubuwa suka shiga ƙwaƙwalwarta. Sai yanzu ta tuna da irin tambayoyin da Husna take yi mata akan aikin ɗanta. Ta juyo a razane tana duban Husna,

“Ke! Ki gaya min gaskiya. Dama kinsan aikin Mu’azzamu? Gaya min mana!”

Ta daka mata razananniyar tsawa. Bakinta yana kyarma sai dai ta kasa furta komai sai ɗaga kai kawai da ta yi,

Gwaggo ta wanketa da mari ta sake wanketa da mari,

“Ban yi mamakin dan kema kin ci amanata ba, saboda ɗan da na haifa ma bai dubeni a bakin komai ba.”

A hankali ta ƙaraso gabansa tana yi masa kallo kamar wani baƙo.

“Mu’azzamu! Da gaske ne wai ka ci amanar mahaifiyar da ta yarda da kai? Kasan waye Alhaji Saleh?”

Ta damƙi wuyan rigarsa da ƙarfi tana haki kamar wacce ta ci gudu. 

Wayyo rayuwa, ina ma ƙasa zata tsage ya buɗe ya shiga? Ina ma bai zo duniyar ba? Ina ma zai zama ɗan jariri wanda bai san komai ba?

“Gwaggo…”

Zai yi magana sai dai maganar ta kakare ne a lokacin da ya fahimci idanun mahaifiyarsa ya kakkafe. Jamilu ya yi saurin tallabota. Shi kansa M.Y sai da ya riƙeta sannan ya ji azaba a hannun, amma duk da hakan bai saketa ba. 

Husna ta kwasa da gudu ta kira likitoci. Ganin ba shi bane yasa suka ɗauketa suka ce ayi maza aje a yanka mata kati. 

Cikin gaggawa likitoci suka rufu akanta domin ceto rayuwarta. M.Y kuwa tuni ya ji ya sami lafiya. Da ‘yan sanda suka so su ɗauki bayanansa ya nuna masu su yi haƙuri mahaifiyarsa babu lafiya zai zo ofishin. 

A karo na farko tausayin M.Y ya tsirga cikin zuciyar Husna. A take zuciyarta take sanar da ita akwai wani mahimmin abu da yasa shi aikata irin wannan laifi. Ya zama dole tasan menene wannan dalilin kafin ta yanke masa hukunci.

Sai wajen ƙarfe uku na rana ta farka tana wani sumbatu. Tun tana magana ba aji har suka fara fahimtar abin da take cewa,

“Me na yi maka? Me zan cewa Allah akan amanar da ya bani? Ka yaudareni Mu’azzam… A yanzu ina danasanin haihuwarka. Ba zan taɓa yafe maka ba, ba zan yafe ba. Ka bani takardar Husna kaje ka ci gaba da rayuwarka. Muddin ka taɓa ciyar da ni da dukiyar haram, sai Allah ya saka min.”

Haka ta yi ta sumbatu hawaye na sauka a idanunta. Zuciyar Gwaggo ta yi nauyi da yawa. Likitocin sun ji tsoro sun yi tunanin ba zata kai yamma bata mutu ba. Gaba ɗaya kowa ya zubawa sarautar Allah idanu. 

Ji ya yi duniyar ta yi masa baƙinƙirin. Babu yadda ba ayi ba ya koma ya kwanta ya ƙi amincewa. A yanzu babu wanda yake da buƙatan gani ya ɗauki mataki sama da Saleh. 

Kwanan Gwaggo biyar a asibiti kafin ta ɗan sami sauƙi tana iya buɗe idanu tana iya tashi da kanta. Da taimakon Allah da taimakon Addu’ar da Husna take yi mata. Bayan ansallame su akayi juyin duniya ta zo su koma gidan M.Y ta ce ko gawanta aka kai bata yafe ba. 

Ta jawo hannun Husna da nufin su tafi Husna ta girgiza mata kai alamun ba zata je ba. Likitan ya biyota da haɗin bakin M.Y ya ce mata idan bata son taimakon kowa ta amince shi ya taimaka mata indai ta yarda da shi. Babu musu ta juya zata bi bayan likitan ta waiwayo ta dubi M.Y da Husna ta ce,

“Kije ga ki ga shi nan. Kai kuma kada ka sake tunawa da ni Hafsatu a matsayin uwa. Ban taɓa haihuwa ba.”

Ta juya tana sharar hawaye. Husna ta fashe da kuka, bata son ta tafi ta bar M.Y har sai ta ji dalilinsa na aikata munanan ayyukan nan. Suna kallo Gwaggo ta shiga motar Daktan tana sharar ƙwalla. 

A hanya ta dubi likitan kamar zautacciya ta ce,

“Kada ka ga laifina, na bashi tarbiyya na nuna masa hanyar tsoron Allah, na hane shi da taɓa haram. Yau ɗana ya tona min asiri.”

Ta rushe da kuka mai taɓa zuciya. Salim dai sai haƙuri yake bata yana nuna mata jarabawa ce. 

Jiki babu ƙwari suka koma gida kowa da abin da yake tunani. Har dare ya yi babu mai walwala. Husna da M.Y suna zaune su biyu a falo shiru. 

A lokacin suka ji alamun guduwan mutane, daga bisani suka ji ana taɓa ƙofar. M.Y ya tashi ya ce,

“Waye?”

Cikin numfarfashi ma mallakin Muryar ya ce,

“Ni ne Jamilu buɗe min.”

Da sauri ya buɗe masa ya faɗo a jikinsa. Idanun M.Y suka kawo ruwa. Duk wanda ya ga Jamilu sai ya yi masa kuka. Yana riƙe da ƙirjinsa da yake ta zubar da jini ya ce,

“M.Y. Kayi haƙuri da dukkan ƙaddararka. Ni tawa ta ƙare. Kuma ka tashi a yanzu ka gudu, idan ba haka ba, ‘yan sanda za su kama ka. Ga wannan.”

Ya bashi wata waya, wanda abinda M.Y bai sani ba, wayar tana recording ɗin har maganar da suke yi,

“Ka riƙe wayar nan da kyau bayan komai ya lafa ka cika burinka na shiga gidan Mu’azu sai ka damƙawa ‘yan sanda zai taimaka maka. Sun kasheni ne saboda na kira ‘yan sanda su zo su taimakeka. Yanzu za su cewa ‘yan sanda kai ka kasheni. Ruwa zan sha ruwa.”

Husna cikin kuka ta tashi da sauri ta miƙo ruwa M.Y ya fara bashi. Sai dai bai yi kurɓa uku ba ya amsa kiran Ubangiji. M.y ya dinga girgiza shi yana kiran sunansa amma ina… Ya rungume shi a jikinsa yana jin wani irin zuciya yana cinsa. 

Da sauri ya tashi ya wuce ɗakinsa ya ɗauko bindiga. Ko zai shiga hannun hukuma sai burinsa ya cika, ba zai taɓa bari a kama shi a yanzu ba. 

Yana ƙoƙarin ficewa Husna ta riƙo hannunsa tana kuka. 

“Zan bika.”

Ya girgiza kai ya shafi fuskarta cike da damuwa,

“Kiyi haƙuri ki kula da kanki zan dawo insha Allahu.”

Ta girgiza kai,

“Duk inda zaka je zan bika.”

Da sauri ya fice ta bi bayansa yana gudu tana binsa a baya. Da ya ga da gaske take ya daka mata tsawa, amma ko a jikinta. Dole ya kamo hannunta da ɗayan hannunsa mai lafiyar suka yi ta gudu, suna isa bakin titi suka hau napep. Sai da suka yi tafiya mai nisa wurin riga irin na Fulani, ya sauka ya biya mai napep ɗin. Cikin dajin kawai suka nausa suna gudu da iya ƙarfin su.

Taku ‘yar mutan Borno.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mu’azzam 20Mu’azzam 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×