Skip to content
Part 24 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Bayan sun koma ne, ya sami har Yunusa ya kawo masa abinci, ya karɓi nasa ya wuce wani wuri ya zauna shiru ba tare da ya iya ci ba. Shi kaɗai yasan abin da ke damunsa. Ji ya yi andafa kafaɗarsa ya juyo yana kallonta. Ta fahimci babu abin da Mu’azzam yake buƙata a yanzu da ya wuce kwantar masa da hankali. Da hannunta ta ɗibo abincin ta kai masa baki. Ya jima yana kallon hannun kafin ya buɗe bakin ta zuba masa. Idanunsa suka yi jazir, babu wanda ya faɗo masa a rai sai mahaifinsa. Har da girmansa bai daina ɗibo abinci yana sa masa a baki ba. Gwaggo ma ta faɗo masa a rai.

“Nasan duk duniya babu wanda kake so sama da Gwaggo.”

Husna ta yi maganar tana dubansa, kamar wata babbar mace. Ko da yake a yanzu kallon babbar mace yake yi mata.

“Duk duniya babu wanda nake so sama da mahaifina. Gwaggo ya zama dole insota saboda uwa ce. Maganar a sata a sahun waɗanda nake so kamar cin fuskar iyaye mata ne. Ina son mahaifina Husna. Gwaggo bata taɓa baki labarin shaƙuwana da Abba ba?”

Duƙar da kanta ƙasa ta yi tana dogon nazari sannan ta ce,

“Allah ya jiƙan Abba.”

Bai amsa ba sai dubanta da yake yi. Abincin ta tura masa a gaba alamun ya ci gaba da ci, tana ƙoƙarin tashi ya dakatar da ita

“Me kike son tambayata?”

“Dalilin da yasa ka auri Salima.”

Ta bashi amsa tana mai dubansa.

“Na auri Salima a dalilin mahaifina.”

Bata sake cewa komai ba ta zura masa ido yadda yake cin abincin kamar magani.

Bayan Isha’i ya hura masu wuta suna zaune suna shan ɗumi. Ba hira suke yi ba, kowa da abin da ya dame shi.

“Kina son sanin dalilin shigowata cikin wannan rayuwar ko?”

Da sauri ta ce,

“Eh don Allah ka gaya min ko zan iya barci.”

Wutan ya kafe da idanu sannan ya ce,

“Kamar yadda na gaya maki ne, na shaƙu da Abba fiye da tunaninki. Tun ina ƙarami Allah ya yi min baiwa a fannin kwamfuta. Babu wanda bai san shaharata a wannan fanni ba. Akwai uban gidan mahaifina Alhaji Mu’azu. Sau tari Abba yakan ɗaukeni ya kaini gidan saboda yanayin shaƙuwarsa da mai gidan.

“Hatta kayan makarantana Abba ke wanke min, ya ɗauki soyayyar duniya ya ɗorata akaina. Haka kawai bansan dalili ba aka sace Abba bayan ya tabbatar mana da ya daina aiki da Alhaji Mu’azu. Mun shiga tashin hankali a dalilin sace Abba. Bayan sun gaya mana kuɗin fansarsa muka nemo rabin kuɗin suka ce ni zan kai. Kinsan me ya faru?”

Ya tambayeta yana dubanta ta cikin hasken wutan da ya kunna masu. Girgiza kanta ta yi, don haka ya ci gaba da cewa,

“Gaban mahaifina suka ɗaukeni suka kaini wanda bansan a ina yake ba. Bayan sun fice sun barni daga ni sai shi, na dube shi sosai duk ya rame ya fita hayyacinsa. Zai fara magana na hango Camera da aka saita mana don haka na je na cire na dawo cikin tashin hankalin nake tambayar mahaifina ko waɗannan mutanan su waye?

“Abba yana kuka irin wanda ban taɓa ganin wani babba ya yi ba, ya gaya min yana cikin matsala. Kuka yake yi yana ce min intaimake shi intaimake shi inraba shi da wurin nan, suna azabtar da shi. Na dube shi sosai nace su waye? Ya bani amsa da Alhaji Mu’azu ne da koma Alhaji Saleh. Sun kawo shi nan ne akan ya yi masu taurin kai akan dole sai ya bayar da ni, sun sanyani a cikin ƙungiyar matsafa, saboda antabbatar masu komai nasa hannuna sai sun sami albarkar abun.

“Na girgiza kai nace Abba bai kamata kasha wahala a sanadiyyata ba, ka fito kaje wurin Gwaggo tana da buƙatarka ni abarni anan. Abba ya dubeni cikin kulawa ya ce min, muddin ina son ya bar wurin nan sai naje na ɗauko wani zobe da ke cikin ɗakin Alhaji Mu’azu wanda muddin na ɗauko na ƙona babu makawa asirin Alhaji Mu’azu zai tonu kuma duk waɗanda ya kama a cikin gidan nan za su sami dama su fito.

“Hankalina ya yi matuƙar tashi jin cewar har sun tsaface mahaifina. Kuma yana cikin azaban ciwo, yana kuka yana ce min intaimake shi. Haka aka fitar da ni daga gidan idona a rufe. Na kasa gayawa Gwaggo yadda muka yi, na fara neman taimakon hukumomi da su taimaka min, amma abin mamaki kowa na tunkara zai ya ce ba zai iya ba.”

Mu’azzam ya yi shiru idanunsa suka cika da ruwan hawaye. Ya duƙar da kansa yana jin kamar a yanzu ne komai ke faruwa. Bata yi magana ba, shima kuma bai nemi ta yi maganar ba, ya ci gaba da cewa,

“Kwatsam aka aiko mana da ankashe mahaifina. Nayi kuka kamar raina zai fita, na tsani komai na tsani kowa. Har na kwanta matsananciyar jinya, wanda Gwaggo tasha baƙar wahala akaina.

“Bayan na sami lafiya ne. Aka sake ɗaukeni anan aka kaini ga mahaifina. Farin ciki ya sa na mance da duk wani abu da ke damuna. Na tabbata ko a haka suka barni sun sanya min farin ciki mara yankewa. Sai dai mahaifina ya yi baƙi ya zama wani iri. Ba lallai wanda bai sanshi sosai ba ya gane shi. Buɗan bakinsa sai cewa yake yanzu ba zan taimake shi ba? Basa bashi abinci sai garin kwaki, shima cokali biyar zai yi su ɗauke. Ya roƙe su su kyale shi amma sun ƙi. Yanzu ina raye zan barshi yasha wahala? Maganganun mahaifina sun karyar min da guiwa. Roƙonsa kawai nake yi ya yafe min zan yi ko menene dan ya fito.

“Anan na sami Alhaji Mu’azu ina roƙonsa Allah da Annabi da ya taimaka min ya saki mahaifina Ni ya kamani. Ya nuna min yadda mahaifina ya jawo masa asara, shima sai ya rama abin da ya yi masa. Da na dame shi da magiya, sai ya sa min doka.”

Anan kuma ya yi shiru. Husna ta gigice jin Abba yana raye ta ce cikin rawar murya,

“Dokan me?”

Bai dubeta ba ya ci gaba da cewa,

“Doka ya samin sai na kasance ɗaya daga cikin masu kisan kai, sai na kasance mai sace mutane. Abin da dai na fahimta yana son ya ɓatawa mahaifina suna, ya ɗorani akan gurɓatacciyar hanya ta yadda ko ya saki mahaifina ba zai iya tona masa asiri ba.

“Na roƙi a maidoni wurin mahaifina, na gaya masa komai. Kallona kawai ya dinga yi da idanunsa suna zubar da hawaye. Yana girgiza kai, sai dai ya kasa cewa komai.

“Wallahi a ranar yadda naga rana haka naga dare. Na kasa rintsawa. Na roƙi mutuwata da ganin mahaifina a cikin ƙuncin rayuwa. A lokacin naci alwashin ko ta wani hali sai na fitar da mahaifina. Na ce masu na amince amma sai sunyi alƙawarin za su dinga ba mahaifina abinci mai kyau. Anan suka nuna min sun amince. Na kuma roƙe su su bari inkammala Makarantana daga nan sai inyi wa Gwaggo ƙarya inkoma Kaduna gaba ɗaya. Duk sun amince min.

“Bayan na kammala karatuna na sami kwali, sannan na cewa Gwaggo na sami aikin banki. Ban yarda sun bani masauƙi ba, nayi amfani da kuɗin da Gwaggo ta haɗa min na kama haya. Akwai abokina da muka yi karatu tare ya tabbatar min zai sama min aiki a kamfanin mahaifinsa.

“Cikin hukuncin Allah suka bani babban matsayi , kuma suka sameni da jajircewa hakan yasa na shiga ran mahaifinsa. Duk labarin nan da nake baki a kullum idan naje barci sai na kasa yin hakan saboda tashin hankali.

“A ranar da aka kaini gidan da zai zama gidanmu a daji, suka kafa min dokokinsu. Suka ce kuma ni zan shirya yadda za aje wani wuri a ɗebi kuɗi. Don haka wata yarinya tana tafiya na saceta na kawo masu. Babu wanda bai zageni ba akan me za su samu akan yarinyar.

“Abin da basu sani ba, na sami abokina Mansur na gaya masa ina buƙatan aron kuɗi saboda zan fara wasu kasuwanci. Ya ce min nawa nake buƙata nace miliyan ashirin. Ya ɗibi kuɗaɗen nan ya bani ba tare da anyi rubutu ba. Da wannan kuɗi na haɗa baki da wani a matsayin iyayen yarinyar har aka kawo mana miliyan biyar.

“A lokacin Oga Saleh ya jinjina min ya kuma ce lallai za aje da ni. Muka saki yarinya bayan ta gaya min zata iya gane gidansu.

“Husna nasha baƙar wahala a wurin mutanan nan, ban taɓa cin ko ƙwandalarsu ba, idan ni na haɗa yadda za ayi a sace wani, ana sace shi zan biya kuɗin kuma insake su. Watarana ma bana biyan kuɗin Oga Saleh zai dawo ya sami na sake su.

“Duk da Allah ya ɗora masa sona, hakan baya hanashi ɗaukar mataki idan na yi ba daidai ba. Ni kuma gaba ɗaya na raina shi kasancewar ina da zafin zuciya.

“Nasha dawowa inroƙe su su rabu da mahaifina tunda nayi masu duk abin da suke so, amma sai suke nuna min lokaci bai yi ba. Husna sun yi min katanga da mahaifina. Iyayen matana sun nuna min za su iya amso min mahaifina idan na auri ‘ya’yansu. An tabbatar min da mace zata iya zuwa cikin gidan ta ɗauko wannan zoben, har aka haɗa ni da Salima. Wanda wani Abokina ne ya gaya min. Amma abin tashin hankali Salima kawai dabara ta yi ta aureni ta kuma hanani sakat.

“Husna na zama mahaukaci na zama zararre akan mahaifina. Yana can yana shan wahala. Nasha kwana a ƙasa saboda kawai na tuna mahaifina yana can cikin rashin gata. Allah ya ɗaukaka duk wani abu da nake yi, na sami dukiya amma na banza, tunda basu yi min rana ba.

“Sunsha su fito titi da ni, akan sace-sace ban taɓa kai hannuna na cutar da wani ba, amma nasha taimakon mutanan da suka faɗa tarkonsu, ina ganin hakan yasa suke sake nesantani da su. Tunda ance duk abin da muke yi suna iya ganin komai.

“A yanzu burikana biyu ne, na farko inshiga gidan Alhaji Mu’azu inɗauko zoben nan, na biyu inga mahaifina ya fito yana kusa da Gwaggo yana dariya.

“Gwaggo ta ɗauki fushi da ni, ba tare da ta tsaya ta fahimci saboda mahaifina nake cikin abin da take tunani ba. Bindiga aka ɗora akaina hakan yasa Gwaggo ta ce ta amince in aikata luwaɗi a gaban idanunta, da dai taga gawan ɗanta. Don Allah ni menene laifina dan ina neman mafita akan fitowan nawa farin cikin?

“Na tabbata ko waye zai aikata ko da tsafi ne muddin za a ƙyale masa iyaye. Da nazo ina yi masu barazanar barinsu sai cewa suka yi za su gayawa Gwaggo koni waye.

“Kin ga kenan sun ɗaureni da yawa. Wallahi Husna ban taɓa cin kuɗin haram ɗin su ba, nasan dai tabbas na saita masu hanya ta hanyar kwamfuta suka shiga gidan wasu manyan mutane. Shi ne laifin da nake addu’ar Allah ya yafe min. Idan na tuna hakan ina shiga tashin hankali. Amma nafi shiga tashin hankali ne idan na tuna mahaifina. Ina kallon ƙwayar idanunsa a lokacin da yake kuka yana roƙon infitaf dashi daga wurin da yake. A yanzu ina jin zan iya amincewa ko mutum inkashe muddin za su sakar min mahaifina. Ina yawan mafarkinsa yana roƙon taimakona cikin zubar da hawaye.”

Husna ta sharce hawayenta tana dubansa,

“Abbanmu zai dawo garemu insha Allah ba tare da kayi ko ɗaya daga cikin abubuwan da suke buƙata ba. Kuma ka daina cewa suna iya ganin komai. Da suna ganin komai da sun fahimci baka tare da su. Suna yin amfani da basirarka ce wajen biyan nasu buƙatun. Gwaggo bata yi kuskure ba a irin hukuncin da ta yanke domin kuwa bata san gaibu ba. Na fahimci ka ɓoye mata ne gudun sanyata a damuwa. Sai dai damuwar da Gwaggo take ciki akan rashin Abba da ace tasan yana raye ina ganin zata fi samun sauƙin ciwon da ke cikin zuciyarta. Babu ranar da gari zai waye rana ta faɗi Gwaggo bata yi hirar Abba ba.

“Waye Alhaji Mu’azu? Ka zo mu natsu ka gaya min komai akansa da kuma gidansa ni zan shiga zan ɗauko zoben, sannan ka ɗaukowa Gwaggo farin cikinta. Kai ma kuma ka ɗaukowa kanka farin cikin da ka rasa shekaru masu yawa.

“Kuma ya kamata ka gane yaudararka suke yi, tunda gashi sun haɗaka da ‘yan sanda. Hakan ke nunin basu da ninyar sakin Abba har abada. Da alama suna son su yi amfani da shi ne wajen cikar burinsu. Kafin gobe zamu yi nazarin yadda zamu shiga gidan, da kuma irin matsayin da zanje masu.

“Nasan damuwa ce tasa har ka amince ka gayawa iyayen matanka biyu har suke tunanin sunsan hanyar fitar da Abba, sun yi hakanne kawai domin suma su cimma wata nasara tasu. Ba zan jinkirta ba, gobe zan isa ga Alhaji Mu’azu insha Allahu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mu’azzam 23Mu’azzam 25 >>

1 thought on “Mu’azzam 24”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×