Skip to content
Part 17 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

A hankali ya sake kai duba gareta, tana nan zaune babu alamun tsoro a idanunta, hasalima idanun sun ƙafe babu ɗigon hawaye a cikinsu.

Mamaki ya ƙara kama shi, ya nufota ya sake ganin rashin tsoro. Bai ce komai ba ya ɗauki wayarta ya fice da sauri. Ba zai taɓa yarda Husna zata aikata hakan ba, dole ya dawo hayyacinsa dole ya yi dogon tunani kafin ya yanke hukunci cikin fushi. Amma kuma ba zai sake barinta zuwa Makaranta ba, domin samarin wannan zamanin babu abin da ba za su iya ba domin ganin sun rushe duk wata tarbiyya da iyaye suke baiwa ‘ya’yansu. Don haka zai sa idanu sosai akanta.

Su Salima kuwa sun sami abin zagi da zunɗe. A yayin da Amina ta rage kawo samari cikin gidan tunda taga asirinta ya kusa tonuwa. Da ace bata yi dabarar tura shi ɗakin Husna ba, babu ko shakka M.Y zai kama su, wanda ta sani sarai idan ita ya kama sai ya yi mata dukan mutuwa, daga ƙarshe ya saketa. Abin da har abada bata fata kenan.

M.Y kuwa ya sake susucewa kasancewar abokin kasuwancinsa da suka zuba maƙudan kuɗaɗe domin samun riba shima ya gudu babu shi babu dalilinsa.

Yana jin kamar ciwon zuciya zai kama shi, sai dai ya sani irin wannan ranar zata zo anan kurkusa. Ya zama dole ya gode Allah, da matsalolin basu taɓa shi ba suke taɓa dukiyoyinsa.

A kwanaki biyu Husna ta rame ta lalace, kasancewar abu biyu da yake damunta. Na farko har yanzu fyaɗen da akayi mata yana taɓa zuciyarta, har gobe idan ta yi addu’a sai ta sanya wanda ya yi mata fyaɗe tana ambatar manyan masifu akansa. Na biyu ƙazafin da akayi mata. Ga shi har yanzu M.Y bai ce komai ba, dan tun ranar bata sake sa shi a idanunta ba. Taso ya hukuntata fiye da shirun da ya yi mata. Ta sani sarai sharrin Amina ne, dan ta ga lokacin da kwarton ya shiga wurin Amina, sai dai kuma waye zai yarda da ita? Gwaggo ce kawai zata iya yarda da ita sai dai babu halin sanar mata da komai.

Littafanta ta ɗauko, sai a lokacin ta zaro wani littafi da wata yarinya ‘yar ajinsu ta bata wai ta karanta tunda ita matar aure ce.

Shafi na biyu a cikin littafin yadda zaka kula da muhallinka ne. Ajiyar zuciya ya ƙwace mata jin marubuciyar ta yi bayanin yadda za ayi wa irin gidan da ya ƙazance da yawa. Cikin ƙwarin guiwa ta miƙe ta fito falon. Babu kowa a gidan hakan yasa ta yi ajiyar zuciya, ta wuce ɓangaren masu aikin gidan. Anan ta kirawo su su dukka ta ce tana son a fitar da komai dake falon a wanke gidan.

Tun safe suka fara ayyukan gidan amma babu wanda ya sami hutu. Komai sai da aka wanke shi aka goge, daman kujerun da kyansu. Komai ma yana da kyau tsabar rashin gyara ne. Sun sha wahala dukkansu kafin suka gama gyaran ko ina, Husna ta umarce su su dafa taliya ta fi sauƙi. Bayan sun ci abinci sun yi Sallah suka koma kitchen.

A takaice dai a ranar har wurin yamma suna gyara, kuma kwalliya ta biya kuɗin sabulu, domin kuwa gidan M.Y ya fito fes! Hatta filawoyin gidan sai da aka aske su aka gyara.

Turarukan wuta suka kunna a ko ina sai ga gida yana wani irin ƙamshi.

Ruwa mai zafi ta watsa wa jikinta sannan ta fito ta ɗauki littafin tana dubawa. Kai tsaye shafin girki ta nufa ta girka abu mai sauƙin ci zuwa Sallar Isha’i ta kammala komai ta ajiye a dinning.

 Sai a lokacin suka dawo, ashe tare da maigidan suka fita. Ba M.Y ba hatta matan sai da suka yi ta kallon gidan cike da sha’awa. Sai dai shi M.Y mamaki yafi yawa a fuskarsa. Salima ta ƙwalawa Saude kira tana tambayarta ko ankira ma’aikata ne aka sauya fasalin falon?

Ta durƙusa ta yi masu bayanin yadda Husna ta tashe su da aiki. Gaba ɗaya kuma sai suka kalli juna. Shi dama M.Y ya kwaso yunwarsa don haka ya nufi inda yaga kuloli yana buɗe girkin ya ji ƙamshi ya dake shi, babu shiru ya hau ci, yana al’ajabin dama Husna ta iya abubuwan nan amma ta bar masa gidan haka? Bayan ya ci ya ƙoshi ya nufi kitchen ɗin da kansa dan ya gani da gaske wannan kitchen ɗin mai tarin shirgi angyara su?

Tas! Ya sami kitchen ɗin, kayan ciki sai ɗaukar idanu suke yi saboda irin wankin da suka sha. Zai iya zama a ƙasa ya ci abincinsa ya tashi. Kitchen ɗin yafi yi masa kama da wanda aka sauya.

Ɗakinsa ya nufa, Salima ta bi bayansa. Ba haka yaso ba, yaso Salima ta wuce ɗakinta shi kuma ya je ya yabawa Husna.

Duban ɗakinsa ya yi yana jin ya kamata shima ta shigo ta yi masa irin gyaran nan.

Bayan ya watsa ruwa ne ya fito yana tsane kansa da tawul. Salima kuwa idanunta sun kaɗa mijinta kawai take buƙata. Dole ya amsa gayyatarta ba don hankalinsa yana kanta ba. Yana gama biyan buƙatunsa ya juya mata baya yana barci.

Salima ta yi shiru tana jin baƙin cikin halin M.Y bai iya tsayawa bayan biyan buƙatarsa ya rungume mace ko kuma ya ɗan kwantar da ita ajikinsa ba. Sai dai yana gamawa ya juya mata baya.

(Idan akwai laifin mazan akwai na matan. Zan waiwayo fannin nan.)

Washegari bayan ya fita, yana dawowa ya je duba kuɗaɗen da ya shigo da su, sai dai suka ce sai ka ɗaukemu a inda ka ajiye mu. Hankalinsa idan ya yi dubu ya tashi dan shi kaɗai yasan me zai yi da kuɗaɗen. Ya tara dukka matan amma banda Husna, yana tambayarsu kowa ya ce bai gani ba. Ya fice yana cewa kafin ya dawo duk wacce tasan ta ɗaukar masa kuɗi ta dawo da su.

Bayan kowa ya koma ɗakinsa Husna ta je har ɗakin Bilki ta ce,

“Anti Bilki ki mayarwa Uncle da kuɗinsa don naga lokacin da kika ɗaukar masa kuɗi.”

Jikin Bilki ya yi sanyi, har Husna ta bar ɗakin bata iya cewa komai ba. Sai dai Husna tana shiga banɗaki Bilki ta shiga ta ajiye kuɗin a ɗakin ta fice da sauri.

  Yana dawowa Bilki ta ce, “Ka bani mamaki da har zaka zo ka titsiye mu akan kuɗinka amma kuma ka tsame ƙanwarka. Bayan da idona na ganta ta shiga ɗakinka ta fito ɗauke da kuɗi. Ya dubeta sosai yana jin ba zai taɓa gazgata abin da take cewa ba.

Ganin har su Salima sun kafeta da ido yasa ta ce,

“Muje idan baka gansu a wurinta ba, na yarda ka sakeni.”

Da sauri ya tashi ya yi hanyar ɗakin Husna, duk suka biyo bayansa. Tana zaune daga ita sai ɗaurin ƙirji tana goge kanta, suka shigo duk sai ta gigice, tana neman hijabinta. Tsurawa ƙirjin idanu ya yi, daga bisani ya yi saurin kauda idanunsa zuwa gefen gadonta. A lokacin yaga jakar kuɗin don haka ya nufa wurin da sauri ya ɗauka tare da zuge zif ɗin ya ciro kuɗi yana dubanta. Shi kallon da yake mata daban, ita kuma sai ta yi suman zaune. Da sauri ta kalli Bilki tana mamakin makircin matan M.Y. wato kowaccen su sai da ta bar mata tabo mai wahalar mantuwa.

“Uncle Wal…” Sai hawaye sharrr!! Ƙazafin Zina, ƙazafin sata wanne ya kamata ta jure? Baƙin ciki yasa ta ɗauki Hijabinta tasa ta dube shi yana tsaye shiru, shi kaɗai yasan irin tunanin da yake yi.

“Idan ni na ɗauki kuɗin nan yanzu zan kama hanya zan tafi Gombe, Allah kasa inmutu a han…”

M.Y ya daka mata tsawan da yasa ta firgice ta sake sa kuka mai ban tausayi.

“Koma waye ya ɗauka tunda naga abin da nake nema don Allah ku ɓace gaba ɗaya bana son ganin kowa. Amma kada ku mance ku dukka huɗun akwai ranar ƙin dillanci. Ke kuma kika sake kika taka ko ƙofar gida sai ranki ya yi mummunan ɓaci.”

Ya fice da kuɗin. Gaba ɗaya ba haka suka so ba, sun so ne ya  wulakantata, sun so ya ci mutuncinta ne. Salima ce kawai ta ci sa’a a cikin makircinta. Ko da yake ita ‘yar gaban goshi ce babu wanda ya isa ya taɓa ta M.Y ya zuba ido.

 *****

Yau asabar, yana jin babu inda zai je don haka ya shiga ɗakin Husna fuskarsa a ɗaure ya ce ta je ta gyara masa ɗaki. Jikinta yana kyarma ta miƙe ta bi bayansa. A karo na farko da ta shiga turakarsa.

Ɗakin ya haɗu babu ƙarya, sai dai kuma tarkace da rashin gyara. Don haka ta cire hijabinta tana gyara tsakaninta da Allah ta wanke toilet ɗin nan, sai ɗaukar ido yake. A lokacin ya sake dawowa, sai dai wannan karon ya rufe ƙofar yadda babu wanda zai iya shigowa.

Tana tsaye ya ƙaraso har inda take yasa hannu ya zagayeta. Nan da nan jikinta ya dinga rawa, babu abubuwan da suke faɗo mata a rai sai ranar da akayi mata fyaɗe. Ta yi ƙoƙarin ture shi da ƙarfinta saboda wani irin firgici da ta shiga, amma hakan ya gagara. Fuskarta ya tallabo ya bata wani saƙo wanda ya tsirga mata tun daga ƙasan ƙafafunta har sama. Hannu ya kai kan dukiyoyin da ya jima yana son sanin yadda suke. Gaba ɗaya suka yi wani irin ajiyar zuciya. A lokacin ne kuma ake bugun ƙofa irin na mahaukata. Tana ƙoƙarin ƙwace kanta ya raɗa mata a kunne,

“Anjima zan ƙarashe baki saƙonnin dukka, kema ki zama cikakkiyar mace.”

Ta kasa amsawa sai sunkuyar da kai ta yi, jikinta gaba ɗaya ya yi sanyi. Wani baƙon lamari ya shiga har zuciyarta ya zagaye ko ina. Zata daɗe bata mance wannan karatun ba. Laɓɓanta da suka yi taushi ta lasa tana son sake kasancewa da shi a irin wannan yanayin. Sai dai ya riga ya makaro domin tuni waninsa ya mayar da ita cikakkiyar mace a cikin dokar daji. Sai dai kawai zata yi farin ciki ne idan hakan ya sake faruwa da ita a karo na biyu cikin natsuwa, kuma a ɗakin Sunnah gidan ɗan uwanta kuma mijinta. Hawaye suka shiga gangaro mata tana gogewa.

Sai da ya daidaita natsuwarsa sannan ya buɗe.  Bilki ya gani tana yi masa wani irin kallo. Salima makira sai cewa ta yi,

“Bilki menene haka wai? Ki bari ya buɗe mana sai mu duba abin da zamu duba a ɗakin ko?”

Bilki ta fizge kanta ta ce,

“Don Allah daina irin wannan halin da kike yi, ki fito ki faɗa abin da ke zuciyarki bai da wuta bai da aljannah. M.Y yanzu da girmanka abubuwan da kake yi ya kamata kenan? Ka ji tsoron Allah. Da rana tsaka zaka shiga ɗakin yarinyar da dukkanmu sai da ka zauna ka gaya mana baka sonta, ba zaka taɓa sonta ba, baka sha’awarta bata da abin da zaka kalla a wurinta kaji sha’awarta bayan kana da kamarmu. Yarinyar da ka tabbatar mana kana son ka yi renonta ne daga ƙarshe ka saketa ita yau kake rufe ƙofa da ita? Yarinyar da kace yaron Office ɗinka zaka haɗa aure da ita yau ita ce kake rawar ƙafa akanta? Ragowar wani? Wacce ta kawo maka kwarto har gida?”

M.Y ya ɗaga hannu cikin zuciya da baƙin cikin munanan kalaman Bilki, da ninyar marinta ta yi saurin kaucewa ta yi ɗakinta da sauri ta sa key. M.Y ya yi shiru domin tabbas duk ya faɗa wa matansa irin waɗannan kalaman, a matsayinsa na munafukin mata. Kuma ya yi hakanne dan ya kwantar masu da hankali su daina mayar da hankali wajen jefe-jefen da suke yi, da kuma wahalar da ita da suke kullum. Duk da bai taɓa kiranta da ragowar wani ba, wannan kuma wani sabon salon sharri ne da suka ƙirƙira domin su dasawa Husna wani sabon ciwo. Sai dai a yanzu yana nadamar furta waɗannan kalmomi domin kuwa ya faɗa cikin tarko mai wahalar fita.

Husna da ta ci-gaba da gyare-gyarenta wanda a lokacin da kalaman Bilki suke fitowa, a lokacinne ta ciro wani abu a bayan gadonsa mai tsananin rikitarwa da ɗaga hankali.

Tunda take ganin masifa bata taɓa ganin irin wanda a yanzu take ciki ba. Jikinta yana karkarwa ga kalaman Bilki kowanne yana tarwatsa ƙirjinta. Wani irin tsanar M.Y ta ji ya lulluɓeta, bata taɓa ƙyamar abu kamar yadda take jin ƙyamar M.Y ba. Taa sulale ƙasa tana jin ƙirjinta yana bugawa da ƙarfin gaske. Tasa hannunta a kunnuwanta ɗayan hannun ta danne ƙirjinta bayan ta yi jifa da abubuwan da ta ciro daga bayan gadonsa. Bata buƙatar yin komai da ya wuce ihu mai ƙarfin gaske. Don haka  ta daddage ta fasa ƙara tana sake maƙalewa a jikin bangon ɗakin.

Ita kuwa Salima tuni ta yi sashenta tana jin farin ciki yana ratsata.

M.Y ya koma ɗakin da sauri jin ihunta, yasan shikenan Bilki ta rusa masa duk wani buri da ya ci akan Husna a daren yau. Jikinsa babu ƙarfi yake ƙoƙarin ɗagota, shi sam bai kula da abubuwan da ke zube agaban Husnan ba. Da sauri ta miƙe cikin rashin tsoro da taurin zuciya ta ce,

“Kada ka kuskura ka taɓa ni da hannunka Mu’azzam Yusuf! Lallai ka haifu, ka burgeni. Ka ci amanar wacce ta yarda da kai, wacce take gaya mana kullum kaine farin cikinta tunda ka kasance mai Gaskiya.”

Ta sharce hawayen da suka yi mata kaca-kaca a fuska tana sake kallonsa ido cikin ido. Gaba ɗaya idanunta sun rufe. Tana jin da zata ga wuƙa sai ta kashe shi ko zata huta ranar ganin Gwaggo cikin matsala.

“Mu’azzam ka fara kashe kanka tun kafin zuwan ranar da zaka kashe mahaifiyar da ta reneka da kulawanta. Yau Gwaggo taso ta tafka kuskure wajen haihuwar abin da zai kashe…”

Ɗauketa ya yi da mari, sai ga jini ta hancinta. Amma ko gezau bata yi ba. Shi a tunaninsa ko ta haukace ne? Ta yaya yarinya ƙarama kamar Husna zata iya tsara kalamai irin wannan? Idan Bilki ta yi magana dan me zata huce akansa?

“Wannan marin da kayi min banji zafinsa ba kamar ranar da ka keta mutuncina, a dokar daji. Ka ɓata min suna, kasa kullum matanka suke zagina suna yi min gori. Ka cuceni Uncle, Ka cuceni ba zan yafe maka ba…”

Ta fashe da kuka. Gaba ɗaya sai ya gigice yana shirin sake ɗora mata tafi, idanunsa suka sauka kan dalilan da yasa Husna take aibata shi da mugayen kalaman da tunda yake ba a taɓa furta masa su ba.

Ta juya da nufin ficewa daga ɗakin tana layi, ta ji muryar Salima tana cewa,

“Gwaggo ke ce kike tafe babu wanda ya san da zuwanki?”

Ba ita ba, shi kansa sai da ya shiga wani irin tashin hankali. Jiri mai ƙarfi ya nemi kwasarsa ya dafa bango. Husna kuwa saboda gigicewa ƙofar kawai ta zubawa idanu.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mu’azzam 16   Mu’azzam 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×