Skip to content
Part 8 of 36 in the Series Mu'azzam by Fatima Dan Borno

Giwa hospital nan ne babban asibiti kuma mafi kusa, don haka ya garzaya da ita can cikin tashin hankali.

*****

Sannu a hankali ta buɗe idanunta tana kallon ko ina.. Anti Amina ce tsaye akanta, wanda ita kaɗai ta gani, a lokacin ne kuma ta ji murya sama-sama hakan yasa ta waiwaya tana kallon ƙofar ɗakin da zai sadaka da inda take kwance. Gwaggo ce ta shigo a ruɗe idanunta sun yi jazir saboda kuka.

Kai tsaye gadon ta tinkaro tana cewa,

“Innalillahi Wa Innaa ilaihirraji un… Husna! Husna!! Me ya sameki?”

Jikin Mu’azzam har wani rawa yake yi, saboda tashin hankali. Ji yake tunda Allah ya halicce shi bai taɓa shiga damuwa irin ta jiya ba. Ita dai Husna sai idanu take binsu da shi kawai ta kalli wannan ta kalli wancan.

Kabiru ya taso cikin kyarma yana cewa,

“Gwaggo sun yi wa Husna fyaɗe! Sun nakasawa Husna rayuwarta. Masu garkuwa da mutane sun nakasa rayuwar Husna.”

Sai a lokacin Husna ta motsa ƙafafunta, ta ji azaba ya ziyarci kwanyarta. Da tasan buɗe idanunta zai sa ta ji mugayen kalaman nan daga bakin Kabiru da bata buɗe ba. Bata san lokacin da ta daddage ta saki ƙara mai ƙarfi ba. Sai dai gani take ana ƙoƙarin riƙeta, tuni numfashin ya dinga sama yana ƙasa har ya ɗauke.

Ita kuwa Gwaggo tsayawa ta yi cak! Ta kasa gaba ta kasa baya. Ƙafafunta kuwa sai rawa suke yi. Gaba ɗaya Mu’azzam ya ƙarasa zama zararre. Gwaggo so take yi magana, amma wani abu ya riƙe mata ƙirji, dole ta dafe wurin tana numfarfashi.

Mu’azzam ya riƙeta yana girgizata da ƙarfi, amma inaaa… Anan likitocin suka rufu akansu shi dai M.Y da Kabiru sun koma wuri ɗaya a can waje sun yi shiru… Kowa da irin tunanin da yake yi.

Ji yake kamar ya shaƙe Kabiru, sosai yake jin tsanar Kabiru da ya ɗauko Husna ya kuma bari dare ya yi masu ahanya.

Da ba dan yasan halin masu Garkuwa da mutanen ba, da ya ce sun haɗo baki ne kawai saboda aci masa fuska.

Wasu abubuwa suka taru suka tsaya masa a maƙoshi shi kaɗai yasan yadda yake ji… Bakinsa har wani ɗaci yake yi. Rabonsa da abinci kuwa tun jiya da yamma.

Likitan ne ya fito hakan yasa duk suka bi bayansa zuwa Office. Ya ɗan dubi M.Y ya ce,

“Mun shawo kan matsalar. Ita Hajiya hawan jininta ne ya tashi, ya yi mummunar hawa, irin hawan da bamu so. Ita kuma Husna ta razana ne, sai ku guji yin hira akan matsalarta a gaban dukkansu. Yanzu zan rubuta magunguna sai kuje wurin karɓa ku amsa. Allah ya kyauta ya kare gaba.”

Da ƙyar Mu’azzam ya iya furta magana,

“Yanzu ya jikin Mahaifiyata?”

“Da sauƙi kada ka damu, nan da bayan Isha’i insha Allahu za su tashi. Munyi masu allurai ne dan su sami hutu.”

M.Y ya miƙe ya fice ya nemi wuri ya zauna tare da yin tagumi.

Sai bayan sun idar da Sallah sannan suka nufo ɗakin da Gwaggon take. A lokacinne kuma yunwa da jiri suka dirar masa. Babu shiri ya ɗibi ruwan tea da Amina ta kawo ya dinga kurɓa. Baya fahimtar komai a cikin ruwan shayin da ya wuce  ɗaci, amma hakannan yake sha.

Gwaggo ta buɗe idanunta ta kafe M.Y da kallo kamar mai son gano wani abu. Wani irin kunyarta ya kama shi, ya yi saurin duƙar da kai ƙasa yana jin bai cancanci zama ɗa agun Gwaggo ba, mace mai haƙuri, mai ilimi mai addini, sai gashi Allah ya bata wani irin ɗa wanda ko alama basu haɗa hanya da ita ba.

Ya kasa yi mata magana musamman yadda take ta kallonsa, hawaye na zuba a idanunta.

“Babban mutum ba zan taɓa yafewa wanda ya yi wa Husna wannan aikin ba, daga yau zan duƙufa da yi masa addu’a ba zai sake ganin daidai a rayuwarsa ba. Zan ƙarar da dukiyoyina a wurin sadaka da saukan Alqur’ani akan Allah ya tarwatsa rayuwarsa. Husna suka yi wa fyaɗe? Marainiyar Allah? Babu uwa babu uba? Innalillahi Wa Innaa ilaihirraji un… Gara su kashe min ita, da su yi mata tabon da har abada ba zai taɓa gogewa ba.”

Mu’azzam ya ajiye kofin da ke hannunsa ya ƙaraso yana jin zuciyarsa kamar wuta,

“Gwaggo kin ga baki da lafiya ki kwanta ki ƙara samun hutu.”

Girgiza kanta take yi da ƙarfi,

“A’a ku kaini ga Husna,ko duk duniya sun ƙyamaceta ni ba zan taɓa ƙyamatarta ba. Maza muje inga Marainiya. Yau Husna ta tabbata Marainiya tunda har na kasa kula da tarbiyyarta har wasu suka ci galaba akanta. Allah ya isa tsakanina da ko waye ya aikata wannan abu, ba zan taɓa yafe masa ba.”

Tana sumbatu suka nufi ɗakin Husna, bayan ancire mata ƙarin ruwan. Itama Husnan idanunta biyu, tana kallon sama. Ita kaɗai tasan irin tunanin da take yi.

Mu’azzam ta fara hangowa, don haka ta rintse idanunta da ƙarfi tana nuna shi, tana ƙoƙarin zabura ta gudu duk da irin azaban da take ji a ƙasanta. Anan kuma sai duk suka yi cirko-cirko kowa yana mamakin yadda Husna ta zama mahaukaciya. Nurse ɗin ta ƙaraso ta ce wa M.Y ya fita waje, saboda har Dakta namiji ta ƙi bari ya dubata, haka shi kansa Kabiru yanzu ya fita saboda yadda ta gigice tana nuna shi tana ihu, da alamun ta firgita hakan yasa take jin tsoro da tsanar kowane namiji.

M.Y ya girgiza kai kawai ya fice. Sai dai bai yi nisa ba, yana jikin windon ɗakin ta yadda zai iya jin komai da ke faruwa a ciki. Da ace mutum yana iya leƙa zuciyar ɗan uwansa, da tabbas sai an zubarwa M.Y hawaye. Gobara ce ta kama a cikin zuciyarsa wanda yake zaton ita ce sanadiyyar barinsa duniyar gaba ɗaya, domin babu ruwan da zai iya kasheta.

Gwaggo ta ƙaraso Husna ta rungumeta gaba ɗaya suka fasa kuka. Husna tana kuka tana shessheƙa ta ce,

“Gwaggo a daji wani yayi min haka, Gwaggo mutuwa zanyi, zan mutu ki yafe min. Ba zan iya ci gaba da rayuwar ba.”

Gwaggo ta dinga shafar bayanta,

“Ba zaki mutu ba insha Allahu sai kin ga yadda rayuwar wannan bawa zata kasance tun a duniya. Ba zaki mutu ba sai kinji tausayin halin masifa da wanda ya yi maki hakan zai shiga insha Allahu. Ki daina tsoron namiji domin kuwa NAMIJI MUTUM ne kamar kowa, dole da shi zaki yi rayuwa.”

Husna tana girgiza kai tana sake rikicewa da kuka,

“A’a Gwaggo, a yanzu namiji Aljanine a wurina ba mutum ba. Na tsani maza Gwaggo bana son insake rayuwa kusa da wani namiji, zan ƙarashe rayuwata a ɗakinki kusa da ke, dan na tabbata ke ce kaɗai ba zaki taɓa yi min gori ba.”

M.Y ya riƙe kansa da ƙarfi da ke tsananin sara masa. Tabbas idan bai bar wurin nan ba, zuciyarsa zata tarwatse gaba ɗaya. Muryar Salima ya ji tana tambayarsa ya me jikin? Bai ɗago ba, bai kuma ce mata komai ba har suka ƙarasa ciki suka ƙyale shi.

*****

Sati biyu suka kwashe a asibitin cikin wani irin hali mara daɗi. Abinci sai anyi da ƙyar Husna take ci, haka zalika ta rage tsoron da take yi idan taga namiji, amma kuma babu wata magana da ke haɗata da dukkan jinsin maza. Hoton mutumin da ta gani cikin duhun dajin yaƙi ɓace mata. M.Y kuwa duk ya zabge ya zama wani iri, baya magana sosai, haka zalika ya rage fitan da yake yi. Shi kuwa Kabir ya koma can gida akan zai sake dawowa.

Yau aka sallame su, yau ne kuma rana ta farko da Gwaggo ta taɓa taka ƙafafunta a cikin gidan ɗan nata. Duk yadda M.Y yasa a gyara wurare hakan bai sa gidan ya yi fes ba. Gwaggo ta dube shi ta dubi matan cike da mamaki, sai kuma ta ja bakinta ta yi shiru suka ƙarasa ciki. Ɗaki guda aka gyara masu, sai dai ƙatuwar katifa ce a ƙasa babu gado. Husna ta zauna shiru, ciwon abin da ya sameta yaƙi barin zuciyarta ta huta daidai da na minti guda.

Gwaggo ta dubi M.Y ta ce,

“Na ji shiru Kabiru bai dawo ba, ina fatan lafiya.”

Gyaɗa kansa ya yi ya ce,

“Nima na neme shi bana samunsa amma jiya da daddare ya kirani, ya tabbatar min yana tafe da shi da Bappa.”

Gwaggo ta jinjina kai alamun ta gamsu.

A hankali ya bar ɗakin, yana mamakin dalilin da yasa Husna take yawan kallonsa saɓanin da baya da ko idanu bata son su haɗa. Rigingine ya yi yana jin ciwo a zuciyarsa, yana jin shi kansa akwai mutanan da ba zai taɓa yafe masu ba har ya mutu. Rintse idanunsa ya yi yana son ko yayane hawaye su sami sakkowa fili ko zai sami sassaucin abin da yake damunsa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mu’azzam 7Mu’azzam 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×