Khairy na kwance akan gado daga ita sai gajeren wandon Zameer, tana danna waya tare da ƙyaƙyacewa da dariya. Kamar daga sama taga Ridayya ta faɗo cikin ɗakin tana huci kamar wata mahaukaciya, jiri sai neman ka da ita yake neman yi amma ta turje.
Tsirarar wuƙar ta nunawa Khairy tana nufar wuyanta da ita, idanunta jajur hawayen baƙin ciki na zuba daga cikin idanunta, na tsananin kishi da soyayyar Zameer, imagining take ita cikin ya tabbata yana da kusanci da Zameer, to; a cikin biyu za a yi ɗaya, ko dai ta kashe Khairy ko kuma ta kashe kanta ta huta.
“Kar ki mini ihu a ɗakin nan, daga ni sai ke ba ki da wani mataimaki” Ridayya ta furta tana sake nunawa Khairy wuƙar. Ganin haka yasa Khairy rikicewa tsoro ya ɗarsu a zuciyarta. Bakinta na rawa da ɓari ta ce “Na shiga uku me na yi miki da zafi haka Anty Ridayya? Me ya sa kika tsane ni?”
“Riƙe kalamanki marasa daraja a wajena Khairy, ba na buƙatar duk wasu shaci faɗi naki, idan yau ki kaga ban kashe ki ba, to wallahi gaskiya kika faɗa mini”.
Ganin al’amarin Ridayya da gaske ne domin ta fara ƙoƙarin fita daga hayyacinta, maganganun fitar da kansu kawai suke ba tare data shirya ba ta ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Kisa kuma? Kashe ni za ki yi, me na yi miki kina cikin hankalinki kowa?” Ridayya ta yi dariya sosai duk da cewa bakinta a waskace yake, fuskar ta tattare saboda ƙona ta da Zameer ya yi, muninta ya sake bayyana ƙarara idan ka kalli fuskar Ridayya ba za ka so ka sake kallo ba.
Ridayya ta ce “idan na yi miki lahani, na saɓa miki kamanni tare da ji miki rauni na kashe ki za ki gane ban haɗa hanya da dawanau ba balle a laƙaba mini sunan mahaukaciya, Khairiyya ki faɗa mini cikin waye a jikinki, mene ya haɗaki zama da ɗakin mijina bayan ga naki can? Ina dalilin sanya sutturar mijina bayan ta haramta a gare ki, gajeren wandonsa, tsaraicinsa ne” Lallai daman an ce; mai haƙuri bai iya fushi da tara mutum ba.
Khairy ta rikice ta rasa da wanne kalamai za ta yi amfani da su wajan shimfiɗa ƙaryar da za ta tseratar da ita, daga haukan Ridayya domin ta gama tattarawa tare da azata a gurbin sabbin masu taɓin hankali.
“Ci…ci…ciki kuma? Ni mene haɗina da ciki? Wallahi….,” Kafin ta ƙarasa maganar Ridayya ta sauke mata wuƙa a gefen hannunta, nan take wajan ya dare jini ya fara zuba. Khairy ta zunduma ihu tare da faɗin.
“Wayyo Allah, mahaukaciya ce wallahi mahaukaciya ce jama’a a kawo mini ɗauki” Ridayya ta sake sheƙewa da dariya ta ce “Ai na faɗa miki, kashe ki zan yi muddin ba ki faɗa mini cikin waye a jikinki ba”
Suka shiga zagaye ɗakin, Khairy na riƙe da hannunta tana ihu a kawo mata ɗauki, amma tsit kake ji, tamkar malam ya ci shirwa. “Khairiyya kenan ki daina ɗauka ban san me nake ba, na sani ni yarinya ce, you’re smarter than me, tunaninki da nawa ba ɗaya bane ba komai nake ganewa ba idan, idanuna suka makance, wallahi a yau ko za a kashe ni, ko zan tafi gidan yari sai kin faɗa mini gaskiya ko na kashe ki a nan, idan ya so a yi jana’izarmu tare Ubangiji ya yi mana hisabi ya kuma tantance mai gaskiya” Khairiyya na kuka sosai, bawai don Ridayya ta fi ƙarfinta ba, saboda makamin dake hannunta ba a wasa da mai wuƙa.
“Ba ni da ciki, mene zai haɗani da ciki kuma? Ki yi mini rai ni gidanki ma zan zo na tattara na bar miki, idan hakan zai zama farin giki a gare ki, da nutsuwar zuciyarki”
“Hehehe ki je ina? Ai ni dake mai ƙarfi yau shi zai ƙwaci kansa lashakka, ki bar gidan Ridayya matar mijin Zameer ban miki lahani ba? Ai ƙarya kike, Har ka tuna mini, an ce da mahaukaci ba ka duka, har ke ce kike cire kaya a gaban mijina ko? To bari na cire miki nono ɗaya sai naga gobe me za ki nuna” A gigice Khairiyya ta ce “Na shiga uku wallahi kin haukace, banda haka ni da nake ƙanwar miji meye na ɗora zargin naki akai na?” Ridayya ta ware idanu ta ce, “Au, ba rami mene ya kawo rami? Kin ji na ambata zargi? Haka tara, in ji kishiyar mai mageduwa, ai shi ɗa na kowa ne, ƙanwar miji ai ƙanwa ce, dole na ba ki tarbiyya saboda gudun bakin jama’a”.
Khairy ta ce “Don Allah ki barni na fita, na je gidanmu babu wani ciki a jikina” Ridayya ta ce, “kin san Allah, wallahi ba zan barki ba, kowa ya yi maka kan kara, yi masa na itace.”
Da gudu Khairy ta juya ta nufi wajan ƙofa ta sunkuya zata buɗe, Ridayya ta sauke mata wuƙar a wuyanta ta ƙara sauke mata a damtsen hannu, Khairy ta gantsare tana kare cikinta don a duniya yanzu ba abinda take so dama da cikinta.
“Jama’a wai ba kowa a gidanne? Zata kashe ni wallahi kashe ni za ta yi matar yayana ta haukace ku kawo mana a gaji” A guje ta buɗe ƙofa ta fita Ridayya ta bita da sauri, daidai nan Zameer na shigowa da Zainaba idanun Ridayya rufe kallon Zameer take tamkar Khairy ce a gabanta.
Yana zuwa ya kifa wata wasu lafiyayyun maruka guda biyu sau biyu a jere ta yi taga-taga zata faɗi ta cake waje guda. Khairy itama wuƙar ta ɗakko ta ce “Wallahi ba ki jimi ciwo a banza ba, ƴar ta’adda kawai” Ridayya ta yi murmushi hawaye na fita daga idanunta bakinta na rawa ta ce
“Haka nake so daman, ko dai ki kashe ni ko kuma na kashe ki” Khairy ta ɗaga wuƙar zata kwaɗawa Ridayya a gigice Zainaba ta hankaɗa Zameer tsakiyarsu daidai nan Khairy ta sauke masa wuƙar a mara, ya fasa ihu yana riƙe gabansa saboda wani azaba daya tsarga masa jini ya fara zuba, ya faɗi ƙasa Khairy ta shiga ɗaki ta rufe ta fara haɗa kayanta.
Ganin Zameer kwance a ƙasa cikin jini ya dawo da Ridayya daga hayyacinta, ta rarrafa ta nufi inda yake ta fara jijjiga shi tana kuka tare da furta
“Ka tashi rayuwata, ka yi mini rai kar ka barni a cikin wannan halin da nake ciki” Zainaba ta ce “Ridayya mene ya sameki a fuska? Gobara kukai ta cinye rabin fuskar ko annoba ce ta faɗa miki? Zameer kuma ina ruwanki da shi, ai bake kika ji masa ciwon ba ki yi ta kan ki kawai” Wani irin kallo Ridayya ta yi wa Zainaba ta ce
“Ki fita daga rayuwata ki barni haka, mene rayuwarki da gidan aurena da mijina kuma? Kin saka mini ido kin takura ni”
“Ridayya ni kike faɗawa haka saboda kina son maso wani? Makauniyar soyayyar da bata da wata riba wajanki, munafukin mijin naki cima zaune wahalalle maƙaryacin” kuka kawai Ridayya take kafin ta ce “Kima siyar da rayuwa take, soyayya kuma bada rayuwa take, ki saurara mini ki bar ni ki tsahirta mini.”
Saukar bulala ta ji ta ko’ina a jikinta, tun yana dukan ta da bulala har ya fara saka ƙafa yana ball da ita tare da taka mata ruwan ciki, daman buta ta ɗauka zata shiga banɗaki ta fasa, azabar bugun mararta da ya yi ta saki kashin wahala a kiɗime take cewa “Na tuba ka yafe mini tausayi ne, don Allah ka da ka kassara mini ɗan cikina” Bai kulata ba, dukanta yake da ko’ina tana ihu da ƙoƙarin guduwa har ta kasa motsi.
Zainaba mutanenta na kusa jikinta ya fara rawa da ɓari ta ƙura wa Zameer idanu kafin ta yi ihu ta zube a ƙasa tana surutai.
“Tsinanne maciyaci, mugu macuci ba za mu barka ba, ka zalunci yarinyar jama’a ka ajiyye karuwa a cikin gidanka ƙarya yake ba ƙanwarsa ba ce zaman cin amana suke bashi da kowa a garin nan” Da sauri Zameer ya ce
“Munafukar banza na ci uwar aljanun” Domin ya ɗauka aljanun ƙarya ta yi. Baban hajjo Usman ya yi sallama Zameer ya ce “Yauwa! Babu matarka babu tawa duk abinda na yi mata zunubinta ya ja mata, ba zata raba mini aure na kasa gane kan matata ba” Usman ya ce, “Ai kowa ya yi na gari kansa, daɗin abin ba a duniya za mu tabbata ba” Yana faɗin haka ya kinkimi matarsa sukai waje, Zameer ya shige banɗaki sosai gabansa da mararsa ke masa ciwo har ɗingi shi yake.
Yana fitowa ya shiga ɗaki ganin Khairy ya yi tana haɗa kayanta da sauri ya ajjiye wayar hannunsa ya nufi inda take, ta yi saurin kauce wa ta ce “Kar ka taɓa ni, kar ka fara” Zameer ya sauke numfashi yana yin ƙasa da murya.
“Haba dear, ki sassauta hukuncin nan” Khairy ta ce “Wato ni ba ƴa bace saboda ina zaman bariki da kai ko? Wallahi idan kaga ba haƙura ka bi mini hakƙina”.
Riƙota ya yi gabaɗaya ya haɗe ta da jikinsa yana sauke mata numfashi a wuya idanunsa a saman kyakkawar fuskarta, a nutse daidai kunnenta ya ce “za ki iya barina ashe?” Ya faɗa yana fesa mata iska a kunne. Jikinta ya saki sai kawai ta fashe da kuka ta ce,
“Ka sauya mini matsayi, ka mayar dani matarka, zan yi istibira’i mu yi aure mu huta da wannan rayuwar na san cewa zaman kishi nake da tsinanniyar matarka mai zubin aljanu”.
Hannu ya sa ya matse bakinta a hankali ya ce, “kar ki mini tsiwa, ke kika bari har tasan da cikin amma nasan me zan yi” daga nan rufe ƙofa sukai abinsu tare da barin Ridayya yashe a ƙasa.
Usman ya ce “Kema Allah ya ƙara ya daɗa, kafirin iyayinki ne ya ja miki wahala” Zainaba na kuka ta ce “Baban hajjo ba zaka gane ba, jin Ridayya nake kamar ƴar’uwata wallahi tausayinta nake ji sosai” Bai ce mata komai ba don baƙin ciki yana jin da shi mai kuɗi ne babu abinda zai hana shi maka Zameer a kotu ko kuma ya kaiwa hisba ƙara. “In sha Allah Zameer sai ya wulaƙanta ba zai taɓa ganin daidai ba, ba kuma zan bar shiga gidan nasa ba”
“Azzalumi ba fa dole sai ya wulaƙanta ba, muddin zai tuba wajan Ubangiji” a fusace ta ce “Banda munafiki irin Zameer wanda shaiɗan ya yi wa fitsari aka”.
Sanyin yamma ne ya dawo da Ridayya daga suman da ta yi, ta motsa kaɗan tare da yin ƙara saboda wani nauyi da hannunta ya yi mata, da ƙyar ta miƙe zaune sai a lokacin ta farga da kashin da ta yi, ta runtse idanunta zuciyarta na zafi da raɗaɗi na rashin mafita da abin yi. Ba zata iya tashi ba don haka ta dinga jan jiki zuwa banɗaki ta wanke jikinta tas, kana ta daddafa ta fito tare da haɗa kai da qwiwa ta shiga sauke ajjiyar zuciya wani irin matsanancin tsoran Zameer ya kamata, haka kurum ta shiga razana ita kaɗai, ga ciki a jikinta, ga duka ga wata kafurar yunwa dake mata barazanar raba mata hanji.
Tunaninta ya tsaya kwakwalwarta ta gaza yin aikin komai da sarrafa wasu kalaman na Zameer. Bata da burin daya shige zuwa gidansu wajan Mami. A hankali ta miƙe ta saci jiki ta fice daga cikin gidan.
Duk inda ta gilma kallonta ake ana nunata, domin kawo yanzu a wannan sabon zamanin da muke ciki ba kowa zai kai Ridayya gidan miji ba, amma a yarda ake kallon nata da yawa sun ɗauka wata dattijuwar ce.
Turus ta yi lokacin da taga gate ɗin gidansu a garƙame, gabanta na faɗuwa wani yaro ta gani, ta ya fito shi da hannu da gudu ya runtuma yana “Wayyo mahaukaciya” Ridayya ta dinga kallon kanta can wata yarinya ta fito daga gidan dake kusa dana su Ridayya, ta ce
“Don Allah masu gidan nan fa?” Yarinya ta kalli Ridayya tana ja da baya ta ce “Sun tafi Rano, sun daɗe da tafiya na ji ana siyar da gidan za a yi”
“Siyar da gida? Rano?”
Ridayya ta maimaita a fili, yarinyar tuni ta juya, zama ta dinga yi a wajan abin mamaki duk wanda suka zo shigewa sai su ajjiye mata kuɗi a gabanta, wani irin hawayen baƙin ciki ya ziraro mata a ƙofar gidansu ake bata sadaƙa? Ganin tana samun kuɗi taƙi tafiya har aka kira magriba, ta rarrafa ta miƙe a hanya ta siyi taliya guda ɗaya, da kayan miya da magi da mai. Tana zuwa ta fassakara itace tare da dafa jallof ɗin taliya ta saka daddawa.
Zameer da Khairy suna ɗaki suka jiyo ƙamshin abinci nan da nan kwaɗayin masu ciki ya addabi Khairy ta ce “Baby matarka ke girki?”
“Ina ta ga kuɗin?” Saboda basu san ta fita ba ta ce “ka duba please wallahi hankalina duk ya tashi” Ya yi murmushi yana cireta a jikinsa ya ce, “idan ma ita ce dole za ta bani ba zata iya cin abinci banci ba, idan ta bani zan kawo miki.”
Yana fita ya samu Ridayya na juye taliyar a faranti daman rabi ta dafa, ya tsaya tare da sassauta murya ya ce “Ridayya mai sona girki kike?” Shiru ta yi masa don magana yanzu sai dole ga zugin fuska ga na hannu da ƙyar take motsa shi.
“Fushi kike dani? Bari na yi sallah na dawo mu yi magana ki jira ji” A hankali ta ce “To” Yana fita ta saka hannu a faranti ta fara cin taliyar ta cinye tas, saboda baƙar yunwa ta suɗe farantin kana ta yi alwala tare da yin Sallah, hannu ta ɗaga ta rasa wacce kalar addu’a za ta yi sai kawai ta yi shiru.
A zaune ta sameta ya ce “Ba dai kin cinye abincin ba?” Ta ce “Wanne abinci?” Ya ce “Wanda kika dafa” ta yi shiru ya sake magana shiru, ji ya yi kamar ya zabga mata mari amma ya daure, “fushinki azaba ce mai raɗaɗi a gare ki wife, zan jure shurin kowa banda naki” Nan ma ta yi shiru. Cike da makirci ya fashe da kuka yana riƙe hannunta ya ce, “saboda Allah ya jarabce ni da son ki, kike wulaƙanta ni Ridayya? Laifi ne don na so ki? Mene laifin zuciyata kar ki hukunta ni ta haka, nikam kar ki mini wannan azabar zan zutu da yawa” Kuka yake sosai ya ce, “I love You Ridha, wallahi ina son ki, ki yafe mini abinda na yi miki jiya”.
“Me ka yi mini?”
Ya ce “ƙona ki da dutse, wallahi lemo aka ba ni na sha ashe akwai ƙwaya a ciki ita ta buge ni, har na ci zarafin matata ƴar aljanna, ba zan taɓa yafewa wanda ya sa na yi shaye-shaye ba” Ta yi murmushi mai ciwo ta ce “Ba komai” Ya rirriƙe hannunta ya ce “Hankalina ya tashi gudun kar ki yi kisan kai a kashe mini ke ya sa na dake ki, ba wai saboda kin jiwa Khairy ciwo ba” Ya sauke murya ƙasa yana tausasa kalami ya ce “Wanne irin miji ne ni? Ridayya ban cancanta da rayuwarki ba ina zaluntarki, ki bari na sawwaƙe miki” Ya faɗa yana bugar cikinta.
“A’a, ka rufa mini asiri ba ni da kowa yanzu sai kai” Ta faɗa tana girgiza masa kai, ya ɓoye dariyarsa ya ce “Me ya sa kike zargin Khairy da ni? Saboda ban taɓa faɗa miki Khairy nada aure ba? Laifina ne ƙanwata Khairy nada aure saɓani suka samu da mijinta shi ne ta nufi gida, a gida aka hanata zama ana ganin laifinta ne, ganin hannunka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka yar ya saka na dawo da ita gidana kafin Allah ya daidaita labarin auren”.
“Kuma ciki bai bayyana ba sai yanzu?” Da sauri ya ce “Kwanciya ya yi, ai kwantawa cikin ya yi amma gobe zan je na same shi zata koma ɗakinta shikenan?” Ta jinjina kai kawai ya ce “A’a ki ce kin yafe mini” Ta ce “Ya shige ba komai ka bata haƙuri” Ya yi sai kuma ya ce “To ɗakko mana abincin muci mai sona” Ta ware idanu ta ce “Bani da abinci,nima bata ishe ni ba” Wata uwar ashariya ya narka Ridayya a zuciyarsa ya fice. Yana fita Khairy ta shigo ta ce “Yanzu kin fahimta ko?”
“Ki yi haƙuri ban ɗauka haka ba, Allah ya daidaita tsakaninku” Khairy ta ce “Wannan turaren naki da maganin matan za ki sammin please” Ridayya ta nuna mata lafiyayyiyar humra ce da kwalacca, tun kafin ta buɗe suka cika ɗakin da ƙamshi ita kanta Khairy ta san humra ɗin ta musamman ce ba a ko’ina ake samun irinta ba, tafiyayyiya ce, sai ka wanke kaya sau nawa ƙamshinta bai fita ba.
Ta duba maganin matan duka ta kwashe ta yi waje Ridayya sam bata damu ba hankalinta ya kwanta bata da matsala da Khairy bata damu da sanin me za ta yi da kayan matan bai tunda ba a gidan miji take ba.
Cikin dare Ridayya ta kasa bacci hannunta ya kumbura, fuskarta sai jini take. Kamar an cillo Zameer haka ya faɗo ta kalle shi ya ce
“Ina buƙatar ki”
“Ba ni da lafiya, marata ciwo take hannuna haka ga fuskata” Rai ɓace ya ce “Nina ɗora miki ciwon? Sanda na biya sadakinki kin faɗa mini ba ki da lafiya ne? Bayan ba uwar tsiyar da kika iya sai dai ki kwanta kamar ruwa? Allah ya ƙara mini haƙuri, ga babu gyara ɗan ƙamshin nan na zamani ɗan farin da mata suke”.
“Dame zan yi kwalliyar? Duk abinda na mallaka wana bawa ina cewa kai ne? Ya kake so na yi wai me ya sa duk ka sauya?” Ya ce “Bai dame ni ba, hakƙina na zo amsa” Mamaki ya cika ta ganin yana rufe fuska da face mask, daman tunda suke irin sumbatar nan ta Zameer bai taɓa yi mata ba, tamkar yana ƙyanƙyamin bakinta “Idan har da yarda ta ce to I’m not in the mood”.
Ƙafa ya saka ya maketa ta faɗi ƙasa kamar mahaukaciya babu tausayi yana ya haike mata babu kulawa ba soyayya, ya yi forcing nata ne tunda bada yardar ta ba, haka ya shaƙe mata wuya tana kakari gabaɗaya bai san me yake ba kamar zai kasheta.
Kuka ta dinga yi ta kasa motsi saboda wahala wuyanta duk shacin yatsunsa saboda shaƙa.
Washegari bayan Zameer ya fice Khairy ta shirya ta fice wajan samarinta. Mai gyara Zainaba ta kira ya duba hannun Ridayya ashe karyata Zameer ya yi tana kuka sosai da muryarta mai sanyin nan kamar shagwaɓa, saboda bata da hargowa sam.
Bayan an gama Ridayya ta kwaɓe fuska ta kasa kallon Zainaba, murmushi kawai Zainaba ta yi ta ce “Alkawari na zo ki cika mini, ki ba ni labarin rayuwarki kafin aure” Ridayya ta lumshe idanunta ba dan ta so ba ta soma bawa Zainaba labarinta kamar haka.