Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Muradin Rai by Zainab Muhammad Chubado

A Shekarar 2019 wanda yay daidai da 28 December na wannan shekarar. Gudu ya ke rungume da qaramin yaro wanda baze wuce shekaru bakwai zuwa takwas ba, gudu yake bilhaqqi da gaskiya wanda daga kallon farko zaka fahimci cewar gudun ceton ransa dana ɗan dake hannunsa yake yi. ko ina ya samu jefa qafarsa kawai yakeyi a cikin qungurmin dajin wanda ke cikeda tarin bishiyu, bakajin sautin komai iface na nishin sa gamida qarar busassun ganyayyakin da yake takawa sabida yanayin bazarar da ake ciki a wannan lokacin.

Can daga bayansa haniniyar dowa kai ce ke tashi gamida ihun mahaya kan dokin wanda suka nufoshi a sukwane kuma suke da muradin kama wannan matashi wanda baze wuce shekaru 35 ba.

Ganin da su kai wankin hula na shirin kaisu ga dare ne yasa ɗaya daga cikin mahaya kan dokin ya zaro bindigar dake saqale a bayan wandonsa ya saita wannan matashin dake gudun tsira da rayuwarsa cikin baqin zafin nama ya sakar masa harbi a gefan hannunsa na dama, take matashin ya kurma wani uban ihu wanda yasa sumammen yaron dake hannunsa ya farka tareda kafe matashin dake riqe dashi da manyan fararen idanunsa waɗanda suke farare dasu tas tamkar bana namiji ba.

Azabar harbince tasa matashin ya fara qoqarin sakin yaron amma kuma se yaron ya qanqame wuyan rigarsa qyam tare da runtse idanunsa a lokacin daya saddaqar da cewar tabbas rabuwarsu tazo koda kuwa basu shiryawa hakan ba.

Burki yaja a lokacin da suka iso gabar wani babban dutse wanda ke fitar da ruwa daga tsakiyarsa, da kyar yake iya ɗaga qafafunsa wanda ke cikin wata farar safa wadda sabida  wahala ta koma nau’in wata kalar daban, gabaɗaya qarfinsa ya gama qarewa amma sabida baqin naci gamida wutar Muradin dake cin zuciyarsa  yasa har  wannan lokacin be yanke qauna ba akan cewar zasu iya cigaba da rayuwa ba.

A haka ya samu wani guri daga jikin dutsen ya kwantar da yaron tareda bubbuga kumatunsa Alamar ya buɗe idanunsa, a hankali yaron ke buɗe idanunsa harya gama buɗesu tas akan hannun matashin wanda keta zubarda jini tamkar an buɗe bakin fanfo, lokaci guda kuma ya zabura ya qanqame matashin tareda fashewa da wani irin kuka ya ce, “Banaso wani abu ya sameka Dady idan har wani abu ya faru da kai a sanadina har abada zanyi dana sani!”

Zare shi daga cikinsa yayi lokaci guda kuma wasu zafafan hawaye suka keto masa sannan ya dubi ɗan nasa cike da soyayya irinta ɗa da kuma mahaifi ya ce,

“Lokaci ya yi HATEEM dole ne mu rabu a wannan ranar muddin kana so ka sake ganina da raina a tare da gangar jikina, don haka ka saurareni da kyau Hateem. Nasan shekarunka sunyi karanci su fahimci abinda nake son sanar dakai, duk rintsi duk wuya kada kayi wasa da shan maganin ka!”

Matashin ya faɗa a lokacin da ya ke mika masa wata karamar jaka dake rataye a bayansa. hawayene suka sake zubowa Hateem a karona biyu sannan ya buɗe baki dayar yace ” idan ka tafi kabarni a nan Dady waze dinga kula dani idan ciwona ya tashi?

Haniniyar dawakai suka ji a dabda su alamar mahaya kan dawakan na dabda riskar inda suke lokaci guda kuma suka juya a tare suna masu kafe ƙofar kogon dutsen da idanu cike da tsoro. Cikin  sauri matashin ya janye yaron daga gabansa zuwa bayansa lokaci guda kuma ya fuskanci yaron ya ce,

“Ka saurareni da kyau Hateem a kwai wata qaramar waya a cikin jakar nan lallai karkayi wasa da ita idan har Allah ya nufa na tsira da rayuwata to da ita zanyi amfani wajen gano inda ka ke.”

Kuka sosai Hateem yake yi tare da kara kankame rigar mahaifin nasa dake hannunsa ya ce,

“Kayi min alkwari cewar zaka dawo gareni a raye ba tare da wani abu mara kyau ya faru da kai ba!”

Idanunsa a kafe bisa fuskar kakkyawan yaron ya ce,

“I promise you zan dawo gareka no matter what if I survive insha Allah!”

Daga haka be sake kallin yaron ba ya miqe da hanzari ya bar gurin yana me qara hanzarinsa akan na farko, a haka yayta ratsawa ta cikin lingu da sakon duhuwar dajin yana gudu jirin jini na ɗibarsa, a haka ya yanke jiki ya faɗi a dedai gaɓar wani babban ruwa me tafiya  cikin kankanin lokaci igiyar ruwan ta samu nasarar jansa tai gaba dashi wanda hakan  yay daidai da rufewar idanunsa.

*****

Kaduna State (Unguwar Malali Gambia Road)

Babban gida ne na Alfarma wanda aka kawatashi da tsarin gini na farin dutse, gida ne wanda ya amsa sunansa gida irin na manyan masu hannu da shuni wanda hannunsu ke cutar gadon bayansu, komai na cikin gidan qirace ta musamman wanda akayo odar sa daga kasashen ketare wanda ya kasance mallakar babban ɗan kasuwar nan wanda duniya ke ji dashi a fanin kasuwanci, a zahiri cikakken ɗan kasuwa ya ke inda a baɗili kuma ya kasance cikakken tantirin ɗan fasaqaurin safarar miyagun qwayoyin da suke ɗauke da wani sinadari me ɗauke da wata ɓoyayyiyar cuta.

Alhaji Kasim Banazir kenan mamallakin Companyn sarrafa magungunan ciwon zuciya dana koda, wanda ya kasance kaf kasar nan babu kamarsa a wannan fagen.

Duk irin tarin dukiyar da Alhaji Kasim Banazir ke da shi ƴa ɗaya tilo Allah ya bashi wadda yake matikar so kamar ransa, Suna kiranta Nooreyn.

Ko kaɗan baya son abinda ze taɓa masa lafiyarta koda kuwa meye shi, idan nooreyn bata da lafiya ko kuma tana cikin yanayi na rashin walwala ko ɓacin rai gabaki ɗaya yanayinsa shima sauyawa yake yi, shiyasa yake matikar kiyaye dukkan abinda ze taɓaasa ita.

A hankali take sakkowa daga stairs cikin takunta na isa da kasaita, sanye take cikin wani pink ɗin wando wanda yay masifar matse ta kamar zai yage, inda rigar jikinta ta kasance very short ta tsaya mata da dai tsukakken cikkinta wanda hakan ya bawa fatar cikinta damar fitowa kaɗan, gashin kanta a baje ya ke bisa doron dogon wuyanta wanda ya sauka bisa cikakken qirjinta, fuskarta a zagaye take wadda ke ɗauke da dogon hancinta gamida manyan fararen idanunta, bakinta yanada ɗan tudu kaɗan wanda hakan ya qara baiyan zallar kyan da take dashi.

Tana gama sakkowa daga sters ɗin ta wani tsaya tanabin daining ɗin da aka cika da abinci iri-iri,  tsaki taɗanja kaɗan sannan  Ta nufi side ɗin dadyn ta wato Alhaji Qasim Banazir.

Tun kafin ta shiga wayarta dake hannunta ta ɗauki ruri don haka ta wani yatsina fuska tare da jan siririn tsaki ta ɗaga ba tare da tayi magana ba.

Katse wayar ta yi sannan ta saki murmushin daya kara fallasa madarar kyan da take tashi ta juya da sauri zuwa side ɗinta, a gaggauce ta buɗe drower ɗinta wadda ta kasance zallar p-caps ɗinta ne a ciki ta ɗauki wata me launin kalar light pink ta saka akan bajajjen gashin kanta ba tare da ta ɗora wata riga akai ba ko mayafi ta nufi shoe Rack ɗin ta ta ɗakko wani haɗaɗɗen takaimi irin me kaiwa har wuyan kafa ta saka. Wanda ya kasance same colour with p-cap din dake kanta sanan ta fita da sauri har tana haɗa steps ɗin wajen sauka.

Koda wasa bata bi takan mom ɗinta da ke part ɗinta ba ta nufi jibgegiyar motar ta kirar ford ta buɗe ta shiga tare da murza mata key.  Tana kokarin barin gurin ta ji,  An ce, “Noorey”

Ɗagowa ta yi da fararen idanunta tana kallon back sit ɗin motar ta cikin mirrorn dake manne a jikin glass ɗin motar ta gaba ba tare da taja motar ba, Ajiyar zuciya ta sauke me karfin gaske wadda ke baiyana irin yanayin tsoron da ta shiga.

Tsaki ta ɗan ja kaɗan tare da watsa masa harara ta ce, ” what are you doing in my car without my permission Saleym?”

Matashin data kira da Saleym wanda ke kwance bisa back sit na motar yay murmushi ya ce,

“I just want to see you Nooreyn thats why I’m here, I’m definitely sure za ki fito at this time shiyasa na shigo gidan ba tare da kowa ya sani ba.”

har lokacin daya kai karshe a maganarsa she’s still staring at him, rintse idanunta ta yi da karfi sannan ta sake buɗe su akan Saleym tana wani male baki kamar wadda ke shirin sakin kuka, siririn tsaki ta saki sannan ta murzawa motar key ta nufi get da gudun gaske kamar zata tashi sama.

Sabi da sanin halinta da Masu tsaron gidan sukai ba shiri kowa ya tsaya a inda yake inda shi kuma get ɗin aka wangale matashi ta fice. Tana fita titin da ze kaita Governor Road ta jefar kan motar cikin mintuna kaɗan ta isa inda take so ta je shi dai Saleym yana makale a bayan motar yana faman dannar waya.

burki ta matsa me karfin gaske wanda yasa wayar da ke hannun Saleym ta suɓuce inda shi kuma kansa ya faɗo kan kafaɗunta.  Dariya ta qyalqyale masa da ita har tana tafa hannu inda shi kuma Saleym ya kafe dogayen fararen haqoranta da kallo batareda qiftaa ba.

Kunnensa tasa hannu ta kama tare da murdawa da karfi ta ce, “Wannan shine hukuncinka na shigar min mota ba tare da izini na ba.”

“Eyyah Nooreyn nimafa kina min haka jiya ma fa haka kika min don na rama shine zaki min mugunta ko?”

Zata yi magana kenan ya bige hannunta tare da ɗaukar wayarsa ya ɓalle murfin motar ya fito yana ɗariya.

Itama fitowa tayi tana murmushi sannan tasa motar lock tare da sunkuyawa tana gyara zaman igiyar takalminta.

Kafeta da ido Saleym ya yi a ransa yana jinjina kyawu gami da tsarin kyan surar da Nooreyn  take da shi,  babu abinda ya fi komai ɗaukar hankalinsa a tare da ita kamar hips ɗinta daya fito ya buɗe a jikin wandon dake jikinta, a hankali idanunsa suka sauka bisa wuyan cikinta wanda yake a kwance flat dashi ya wani irin tsuke tamkar babu wani abincinci dake samun gurbin zama a cikinkata sabida yanda yake a lafe, kasancewar rigar da ke jikinta karamace sosai ne ya bawa cibiyarta damar fitowa tunda dama rigar bata arziki ba ce.

Tana ɗagowa ta wani baza gashin kanta wanda ya kara bajewa bisa doron wuyanta har zuwa kan cikakken kirjinta sannan ta sake gyara zaman p-cap ɗin da ke kanta ta kalli Saleym ta ce, “Heeeyyy ya dai?”

Murmushi ya fuzgo dakyar ya ce, “You look so pretty Nooreyn!”

Dariya ta yi tare da cuno masa pink lips ɗinta ta ce, “Uya muje ko.”

Suna shirin shiga makeken gidan dake gabansu wata matashiyar yarinya ta fito a cikin wata zabgegiyar benz baka wadda baza ta wuce sa’ar Nooryan din ba, kasa ta yi da glass ɗin motar ta ce,

“Nooreyn long time no see?”

Murmushin gefan baki Noor ta yi ta ce, “Wallahi kuwa but ya naga kin fito kuma?”

“Eh wallahi aiba a nan zamu yi ba a can River Kaduna ne.”

Zaro ido Noor ta yi ta ce,

“Kina nufin duk faɗin garin Kaduna babu inda ya yi muku se bakin wannan ruwan me tafiya a lokacin kuna da ake yawan yin ruwan sama?”

Matashiyar yarinyar ta ce, “Eh mana ke dai kawai muje karmu ɓata lokaci duk su Aventika suna can nasan an fara shagali.” Noor ta ce, “Amma Ekram why se a nan za’ayi?”

Zata sake magana kenan Saleym ya dafa kafaɗunta ya ce, “Kinga Noor muje kawai karmu ɓata lokaci insha Allah babu abinda ze faru mara daɗi se alkhairi.”

Kama hannunta ya yi suka koma mota ita kuma Ekram ta yi gaba su kuma suna binta wanda Saleym ne a yanzu yake jan motar har suka isa inda ake gabatar da shagalin nishaɗin nasu duk karshen wata.

Tunda suka je gurin Saleym ke gaisawa da mutane inda itakuma Noor take rike da hannunsa, duk wanda kagani a gurin taron to ubansa ya ci kuma ya tara shiyasa duk wadda na kalli fatarta senaga kamar mudubi sabida shekin jin daɗi,  amma sai dai abin takaicin kaf matan dake gurin babu wadda tayi shigar arziki  dukkansu shigar baiyana tsaraici sukai, a hakan ma wai gara Noor tunda wandonta dogo ne rigarta kuma ta ɗan sauka daidai saman cibiyarta.

Ana kan ganiyar tikar rawa ne wayar dake hannun Noor ta ɗauki ruri tana neman agaji, yatsina fuka tayi tana kallon screen ɗin. Sunan Popsy ta gani yana yawo a saman screen na wayan, fita ta yi daga gurin tana takawa a hankali harta ɗanyi nisa da gurin da kiɗan ke tashi sannan ta amsa wayar cike da kaunar mahaifin na ta.

Hira suka dan tattauna har suka kammala ta kashe wayar tana murmushi, har a zuciyarta take jin son mahaifinna ta yana ratsa ta, a hankali take jin karar tafiyar ruwan da ke ɗan nesa da ita.

A nitse take ɗaga sawun qafarta cikin nutsuwa gami da salonta wanda idan har baka santa ba seka rantse cewar yanga take yi  harta kai bakin ruwan tana kallo,  wata irin iskace mai sanyi gami da wata sihirtacciyar ni’ima me daɗin gaske suka shiga ratsa duk wata gaba dake jikinta, a hankali ta zauna bisa wani karamin dutse wanda seda ta tabbatar da kafuwarsa a gurin sannan ta zauna tare da zare dogon takalmin fatar dake  ɗaure a qafarta, a ɗan tsora ce ta zura duka qafafuwanta a ciki tana wasa kaɗa ruwan a hankali nan take murmushi ya baiyana a saman fuskata. ta jima tana hakan kamar daga sama taji wani Abu ya daki qafarta, a matikar firgice ta janye kafarta na dama kafin tajanye na hagun taji kamar abu ya sarke kafar…… Ihu ta kwallah lokaci guda kuma tayi baya zata faɗi cike da kiɗima gamida firgici ta fara kokarin  janye kafarta.

Duk wani kokarin ta a wannan lokacin be wuce na ta zaro kafarta daga cikin ruwan ba, amma kuma fir se hakan taki yuwuwa mata sabida yanda belt ɗin ɗake ɗaure bisa gefan qirjinsa na dama ta naɗe mata kafa, wani irin karfi ne yazo mata lokaci guda wanda yake ta’allake dason ganin ta raba kafarta na hakun da belt ɗin ya ɗaure.

Tana jawo kafar waje taga mutum yana bin kafar kamar takarda sabida yanda mutum ke rage nauyi a cikin ruwa, zaro idanu Nooreyn  ta yi sabida tsabar tashin hankalin da take ciki. Gaba ɗaya se tsoron nata ya ninka na farko sabida arbar data yi da mutum a irin wannan yanayin da bata taɓa zato ko tsammani ba!

A zahiri ihu take son yi amma kuma ta kasa yin hakan sabida tsabar kaɗuwar data yi, gabaɗaya ilahirin jikinta Rawa yakeyi wanda hakan ke faruwa duk a sanadin yanayin data samu kanta a ciki.

Kasancewar ruwan babban ruwa ne kuma me tafiya yasa bata sha wahala wajen kara kaimin janye kyakkyawar kafarta daga jikinsa ba, haka kuma duk iya kokarinta na takalli fuskar mutumin seta samu kanta da kasayin hakan dole tasa ta fara kokarin barin gurin a matigar kiɗi me.

Tsayawa ta yi cak lokacin data ɗan fara takawa kaɗan zuwa nesa da bakin ruwan zuciyata na wani irin racing, take taji wani irin tausayin mutumin ya samu gurbi a cikin kaso tamanin na zuciyarta wanda hakan yay mata tasiri sosai a duk wata kafar jinin da ke gudana a sassan jikinta.

Komawa ta yi da sauri gurin tare da zube gwiwoyinta duka biyu a kasa, lokaci guda kuma ta kai hannunta saitin kirjinsa a ɗan tsorace, ji tayi jikin nasa sanyi karara kamar tana taɓa jikin kankara, a ɗan hanzarce ta sake kai hannunta daidai mahaɗar babbar jijiyar dake kai sako zuwaga kwakwa, nan da nan kuwa ta fara feeling ɗin yanda jijiyar ke bugawa kaɗan-kaɗan  alamar akwai sauran numfashi a tredas hi.

Hular kanta ta zare tare da sanya hannayenta biyu cikin gaggawa ta naɗe gashin kanta sosai ta yanda sam baze takura mata ba, mikewa ta yi da hanzari har tana haɗawa da gudu ta koma inda Saleym yay parking motanta ɗazun,  gaba ɗaya aɗan rikice take musamman yanda taga jikin mutumin duk ciwo alamun sai da ya sha bakar wahala kafin ya iso inda take,  wani karamin box na ga ta ɗauka wanda na ga anyiwa alama da jan fenti kaɗan hakanne ya bani tabbacin cewar akwatin bada taimakon gaggawa ce, da sauri take gudanar da komai fiye da farko, sannan ta juya don komawa inda tabar mutumin a kwance bisa gabar ruwan inda ta barshi.

Ajiye akwatin ta yi da sauri sannan ta buɗe ta ta fara fito da abubuwan da za tai amfani da su, wani karamin kwanon silver ta fara fitowa da shi sannan almakashi audiga da kuma askar feɗa da kuma wani blue ɗin ruwa a cikin wata karamar roba me murfi.

Buɗe ruwan robar ta yi sannan ta zuba a cikin silver wadda ke ɗauke da almakashi da kuma askar data fito da su sannan ta sanyawa hannunta safar hannu irin wadda ma’aikatan lafiya suke amfani da ita, tashin farko gefan hannunsa na dama ta fara yankawa daidai saitin inda harbin bindigar ya same shi, take jini ya fara fita alamar da sauran rai a tare da shi.

Ta jima tana fama sannan ta samu nasarar cire harsashinta ɗinke gurin ta ɗaure, ajiyar zuciya ta sauke mai ɗan nauyi sannan tasa hannunta ɗaya a saman goshinsa donta tabbatar da abinda take son ganowa a tare da shi, cire hannun ta yi tare da zare safar hannun da ta saka ɗin ta fara kokarin kwashe kayan da tai amfani da su ta mayar cikin madedaiciyar akwatin. Wani siririn tsaki ta ɗan ja a lokacin data kalli haɗaɗɗen agogon fatar da ke ɗaure a tsintsiyar hannunta. 

A ɗan hanzare ta zaro wayar da ke jikin aljihun matsatsen wandon da ke jikinta ta fara kokarin kiran wata lamba, ta ɗan jima tana wayan sannan ta katse  da ga yanayin data ke magana a wayar zaka fahimci a cikin ujila takeyinta,  nan da nan cikin mintunan da ba zasu gaza 10ba sai ga wata zabgegiyar motar ambulance me ɗauke da hatimin Q/B special hospital ta danno kai zuwa gurin gadan-gadan.

Cikin mintunan da baza su gaza biyar ba wasu malaman asbiti maza suka fito da wani siririn gado wanda ya fi kamada na musamman suka ɗorashi bisa kai, a hanzarce suke gudanar da komai sannan suka fara kokarin shiga motar, har sun ta da motar ta dakatar da su daidai lokacin da take ware gashin kanta ya baje a gadon bayan ta har zuwa kan tudun cikakken kirjinta,  cike da kasaita take takawa harta isa inda Malaman asbitin suke takar da ta ɗauka tare da zarar biron gaban rigar ɗaya daga cikin malaman asibitin da ke sanye cikin farin uniform ta ɗanyi rubutu kaɗan wanda baze wuce tsayin layi uku ba ta mika musu, tare ɗa faɗin “make sure kunyi masa wannan alurar sannan kuma lallai ku tabbatar an saka masa jinin da zeyi dedai da nasa, kuma ku bashi kulawa ta musamman.

Cike da girmamawa  suka amsa da to ranki ya daɗe. Akwatin ta ɗauka tabar gurin cikin takunta na isa gami da yarda da kanta ta nufin inda ake gudanar da shagalin mazaunanta na wani irin juyawa,  sannan suma suka tashi motar da hanzari suka nufi tsadadden asbitin  dake cikin tsakiyar unguwar Rimi.

Tana zuwa gurin bata nufi ko ina ba se inda Saleym ya ke zaune ta ce, “pleases my car key!”

Yana shirin magana kenan ta dakatar da shi ta hanyar faɗin, “please Saleym!”

Be ce mata komai ba ya mika mata ta juya da sauri tabar gurin kamar walkiya, da ido kawai Saleym kebinta ganin da yay tana shirin ɓace masa ne yasa yay hanzarin bin bayanta, tana kokarin shiga motar ya rike mata hannu, ya ce “Noor lafiya kuwa na ga duk kin sauya?  Koda…” “Please Saleym I have an emergency patient in the hospital so pls let me go bani da time ɗin ɓatawa.”

Ajiyar zuciya ya sauke sabida jin abinda ta ce ko bakomai ai hankalinsa yanzu kam ya kwanta, yana sakinta taja murfin motar ta rufe tare da murza mata key tabar harabar gurin at 360.

*****

A hankali yaron ke tafiya duk lips ɗinsa sun bushe sabida tsabar kishin ruwan da ke addabarsa, amma sabida bakin na ci sam yaki jefar da karamar jakar goyon da ke hannunsa,  kamar daga sama ya ji wani abu ya sarke masa kafafu nan take ya kwalla kara tare da zubewa kasa sumamme!

Please comment and like

3 thoughts on “Muradin Rai 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×