"Tunƙwal! Tunƙwal!!"
Tafisu ke daka a tsakar gidansu. Tana mai tuno ranar da ta bi marrarrabar kasuwa tana tunanin mafitar rayuwa. Yau za a yi wata shida da mutuwar aurenta. Babu yadda ba a bawa maigidanta baki ba a kan ya mayar da ita ya yi ƙememe ya ƙi. Daga ƙarshe ma sai ya bada wani sharaɗi.
"In dai har Tafi tana son ta yi zaman aure a gidana to, fa sai ta bi dokokina. Yaranta ba za su tako su zo gidana ba, ita ma kuma ba za ta taka ta je dangin tsohon mijinta ba. . .