Aure
Duniyar Labaran Haiman 06
Godiya
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin sarki. Tsira da amincinSa su ƙara tabbata ga Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam. Da alayensa da sahabbansa, da jama’ar gidansa, da sauran mutanen kirki daga cikin al’ummarsa baki ɗaya.
Sadaukarwa
Na sadaukar da wannan littafi ga gwanaye kuma fasihan mawaƙan ƙasar Hausa, su ne Aminu Alan Waƙa, Mu’azu Haɗeja, Sa’adu Zungur, Farfesan Waƙa, Nura M. Inuwa, Sani Sabulu, Fati Nijar da kuma Abubakar Sani.
Jinjina Ta Musamman
Ina miƙa jinjina ta musamman ga dukkan malamaina daga kowane fanni na karatu da kuma rayuwa. Allah ya saka da mafificin alheri duniya da lahira. Amin.
Ana Tare
Ina miƙa saƙon gaisuwa ga ɗaukacin membobin ƙungiyar Lafazi Writers Association. Musamman shugabanta Sadik Abubakar, Surayya Ɗahiru, Mukhtar Hussaini, Fauziyya Sani Jibrin, Aseeya Muhammad, Ummu Khamilat, Usaina Salis da duk sauran membobin wannan ƙungiya tamu mai albarka.
Gargadi
Ba a yarda wani, wata ko waɗansu gungun mutane su yi amfani da wani ɓangare ko sashe na wannan littafi ba sai da izinin marubucin a rubuce.
MATASHIYA
A wata duniyar can ta daban, akwai ƙasashe, mutane, dabbobi, addinai da al’adu masu kama da irin namu, suna kuma da zubi irin namu. Ko da yake al’amuran da ke faruwa a cikin wannan duniya sun yi kamanceceniya da irin waɗanda ke faruwa a tamu duniyar, wasu al’amuran sun sha bamban da namu. Akwai labarai masu tarin yawa da suka faru a cikin wannan duniya masu tarin abubuwan al’ajabi da ban mamaki, wataƙila ma mai karatu ya yi tunanin a tashi duniyar suke faruwa, amma a zahiri al’amuran na faruwa ne a wata duniyar can ta daban. A cikin wannan duniyar mai kama da tamu, an yi wani mawaƙi mai hikima da ke cewa…
01.
Da sunan Allahna da ya yo ɓaure
Al-Ƙadiru da ya yi mu ta silar aure
Ya halasta mana ni’imar yin aure
Ya ba mu umurni da mu yo aure
Ya sa zaman rayuwa ya gyaru ta silar aure.
02.
Tsira da aminci su ƙaru ga Manzona
Gwarzona da ya zamo sirrin shiriyarmu
Al-Mustapha gatan iyaye da kakannina
Sannu amintaccen Makka da Madina
Kai ne ka ja hankalinmu akan aure.
03.
Gidan da babu aure ya zama ƙyaure
Da zaman da babu aure gara ɓaure
Zaman samari ba aure sai an jure
Kowace ‘ya mace burinta yana aure
Albarkar Allah ta yawaita cikin aure.
04.
Nutsuwar matasa shi ne su yi aure
Neman ilimi mun san bai hana aure
Neman kuɗi ribarsa a yo aure
Soyayyar gaskiya ribarta tana aure
Masoyan gaskiya burinsu su yo aure.
05.
Kowane Uba yana son ɗansa ya yi aure
Kowace Uwa tana so ɗiyarta ta yi aure
Kowane matashi burinsa ya yo aure
Kowace matashiya muradinta ta yo aure
Jama’ar gari suna son ganin ana ta aure.
07.
Wannan ke tabbatar da kimar aure
Allahu sarkinmu ya darajta mai aure
Manzonmu Aminu ya faɗi girman mai aure
Mutanen duk garinmu suna martaba aure
Addinan duniya kaf na daraja aure.
08.
Babu wata ƙasa da ba ta girmama aure
Babu wani gari ko birni da ba a martaba aure
Babu wata ƙabila da ke ƙyamar aure
Babu wani addini da ya yi hani da aure
Wannan shi ne tabbacin ni’imar aure.
09.
Ko da kana da aure kana iya ƙara aure
Masu mata ɗaya na son ƙara aure
Masu mata biyu an yarda su ƙara aure masu mata uku na da damar ƙara aure
Amma masu mata huɗu sun cike ƙofar aure.
10.
Tun da kowa ka bincika yana son aure
Sai ka ɗauka kowa na iya riƙon aure
Sai ka ɗauka kowa buri nai a riƙe aure
Ka yi tsammanin babu mai shikin aure
To amma yau kisan wulaƙanci ake yi wa aure.
11.
Wani aure a shekara ɗaya an rabu
Wani aure a wata ɗaya ka ji babu
Wani auren cikin sati guda an rabu
Wani ma cikin dare ɗaya an rabu
Shin mi ad dalilin haka ne Malam Habu?
12.
Rashin ƙauna ce ko tilas ne?
Rashin kuɗi ko na abinci ne?
Rashin amana ne ko gaskiya?
Sakarci ne ko kuma rashin lafiya?
Na rasa gane mazan ko matan ne?
13.
A kullum fa jama’a auren ake yi
Kuma kullum mutuwa yake yi
Ga zawarawa birjik bisa layi
Wasu sun kira shi da sauyin yanayi
Wasu kuma sun maishe shi ya yi.
14.
Wasu ƙabilun dai ba sa haka nan
Yawanci cikinmu ake yin haka nan
Mun sa ran saki ya halasta a yi
Amma sai in da dalili ake yi
Dalili mai ƙarfi ke sa a yi.
15.
Mutuwar aure tai yawa mu duba
Niyyarmu da aiyuka mu gyara
Mu sani ibada ce mu duka
Muke yi wa Allah mai duka
Adalci da biyayya mu ɗauka.
16.
Allahu ka kawo mana sauƙi
Matanmu su zauna a ɗaki
Su daina yawon bariki
Da shigar nan ta rashin kirki
Su yi zaman su a gidan aure.