Skip to content
Part 4 of 4 in the Series Muryar Dalili by Haiman Raees

Mutuwar Fuju’a 

1. Lallai Manzona ya yi gaskiya, kuma da ma shi mai gaskiya ne.

2. Aminu abin gaskatawa, lamarinka gaba ɗaya shiryayye ne.

3. Na yi imani da kai, haƙiƙa kai Annabi ne.

4. Wallahi babu tamkarka, a duniya ko wanene.

5. A wurin Allah nake godiya, mahaliccin kowa da komai.

6. Ka yi mini tarin ni’ima, da ba su faɗo da bakina.

7. Kai ne ɗaya ba wani sarki, ilahu gwani mai hikima.

8. Ka ne ka yi mana rayuwa, sannan ka halitta mana mutuwa.

9. Kai ne ka aiko manzona, ya yi mana gargaɗi akan mutuwa.

10. Girman mulkinka ya buwaya, ya zarce na kowa da kowa.

11. Mutuwar fuju’a ta zo mana, saƙon manzonka ya tabbata.

12. Yau ga shi mun zo zamanin, da mutuwar fuju’a ta yawaita.

13. Ɗauka take dare rana, ba ta ware maza ko mata.

14. Babu ciwo babu rauni, sai dai ka ji yif! mutum ya tafi!

15. Wasu ma suna cikin tafiya, sai dai ka ji tim! Sun faɗi!

16. Wasu kuma abinci suke ci, da zarar ta zo sai su tafi.

17. Ba sallama ko sanarwa, sai dai ka ji yif! Mutum ya tafi.

18. Lallai fa irin wannan lokaci, babu shakka akwai haɗari.

19. Domin fuju’a za ta afko, a kanmu cikin daji ko a gari.

20. Mun shirya ko ba mu shirya ba, kowa ya san za mu tafi.

21. Tashin hankalinta ya dogara ne, da ɓaci ko kyawun aikinmu.

22. A yau aikinmu menene? Cin hanci ya zamo abinci.

23. Nishaɗi kawai da jin daɗi, su ne a gaba ba amana.

24. To kenan gara ko mu tuba, tun kafin ta zo mana dangina.

25. Allahu sarki nake roƙo, ka ji ƙansu dukka iyayena.

26. Haɗa har da kakanni, da ma sauran ‘yan’uwana.

27. Da sauran dukkan muminai, cikin maza ko mata.

 

<< Muryar Dalili 3

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×