Na zauna ina share gumin da ya tsattsafo min a goshi.
Na ce wannan shi zai sa zaman gidan nan ya fita a raina.
Anan Zainab ta zo ta same ni muka karya na gama suyar muka tafi ɗaki nan ma hira muka yi ta yi tana bani labarin Sunusi ya kira ta yana roƙon ta ba shi lambata, na ce "Ba ki dai ba shi ba ko? Ta ce "Ban ba shi ba, in ba shi hauka ake? Madam Khadijah ma yau za a yi baƙo, na ga Baba Talatu za ta fara soye soye." Muka yi. . .