Skip to content
Part 13 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Na zauna ina share gumin da ya tsattsafo min a goshi.

Na ce wannan shi zai sa zaman gidan nan ya fita a raina.

Anan Zainab ta zo ta same ni muka karya na gama suyar muka tafi ɗaki nan ma hira muka yi ta yi tana bani labarin Sunusi ya kira ta yana roƙon ta ba shi lambata, na ce “Ba ki dai ba shi ba ko? Ta ce “Ban ba shi ba, in ba shi hauka ake? Madam Khadijah ma yau za a yi baƙo, na ga Baba Talatu za ta fara soye soye.” Muka yi dariya Khadijar da ke sanya hijab za ta bar ɗakin ba ta tanka ba har ta fice.
Na miƙe “Bari in yi wanka idan ina cikin abin nan duk ƙyanƙyamin kaina nake, ga zafi.”
Ta ce “Sai kin dawo.” Na fito ɗaure da tawul na zauna gaban mirror sai da na yi kwalliya na sanya wasu riga da wando marasa nauyi aka turo ƙofar dakin ban damu ba don tunanin ko yaran gidan ne sai Najib na gani idanuwansa ƙyam akaina, idan na miƙe na san haka zai fi so don haka duƙar da kaina na yi kamar zan yi kuka.
Khadijah ta ce “Ba ka je Company ba? Ya tako zuwa ciki “Na je, kira na masu haɗa gado suka yi. Ku fita za su shigo su ɗaura.
Ta ce “Gadon wa? Ya ce “Gadon ƙawar Zainab.” Ya dora min foam bisa cinya “Ga foam nan ki cike, sai ranar monday za mu je, karatun monday to friday ne.”

Sai kuma ya dubi kan mirror ya dauki wani mai ya daga sai ya mayar “Waɗannan sune kayan kwalliyar yammata kamar ku?

Zainab ta ce “Kai ya Najib na Khadijah fa Baba ya bayar da kuɗi suka sawo, kasan kuma ba a yi mata sayayyar banza. Nawa kuma Najib ya kawo min tsarabar Dubai.”

Ya ja guntun tsaki “Ana miki zancen kayan kwalliyar manyan yara kina wani batu. Ki bari mu fita ku zaɓi kayan kwalliya don bai kamata ki ba babbar yarinya kamar wannan, wannan kayan naku ba sai su bata kyakkyawan skin ɗin nan nata.”

Zainab ta ɗan yi tsalle da ihu sai kuma ta toshe bakinta “Shi ya sa nake son ka bro, kai ɗin ai babban yaro ne.”

Wayarsa da ta yi ƙara ta sa ya juya “Ku yi sauri ku fita za su shigo.” Abin da ya faɗi kenan ya fita da sauri.

Yana fita na miƙe na fara neman hijab ganin fuskata babu walwala Zainab ta ce “Ya ya dai Billy ko cikin ne?

Na ɗan ƙara ɓata fuska “Me ya sa yayan nan naku yake son shigowa ɗakin nan bayan yasan ba ku kaɗai ba ne.” Ta tashi ta dawo kusa da ni “Ni ma wallahi ban jin daɗi, na rasa me ya sa yake hakan, domin dai da baya shigowa.”

Hijab na sanya muka sauko, Mama ba ta nan ta fita unguwa, sai mu kaɗai muka zauna a falon.

Aunty amarya ta kira ni a waya na tafi na bar Zainab.

A kitchen na same ta kamar yadda na yi tunani girki za ta ce mu yi shi ɗin muka yi wanda ya ɗauke mu lokaci mai tsawo, har abincin anan ta sanya ni na ci tare da yaranta su Ahmad da suka dawo makaranta, sai dai ban samu gano ma Zainab abin da take so in gano mata ba wato kalolin magi ta riga ta ɓare su ta zuba a wasu mazubai masu ban sha’awa.
Kiran Zainab da ke ta shigowa wayata yasa na yi ƙarfin halin ce mata zan wuce muka fito tare da yaran.

Na samu Zainab tana ma Khadijah tsiya don baƙon ya zo za ta fita tana fita ta ce min “Ina ta kiran ki ki ga tsalelen gadon ki.”

Na dubi inda gadon yake ba ƙarya kam ya haɗu,girman shi ɗaya da na su Zainab, amma ba a batun kyau. Ta ce “Ya Najib ba ƙaramin ji yake da ke ba.”

Murmushi kawai na yi mata wayarta ta ɗauki ƙara nata Najib ɗin ne ita ma ya zo ta ce in zo mu je na gyara kwanciya na ce “Sai kin dawo.” Ta matsa min na ce “Allah ina daga nan.” Ta gyara fuska ta fesa turare ta tafi.

Tunani na yi ta yi na lissafin rayuwa sai na ji ina son in kira Mamana tunda na zo sau biyu kacal na kira ta.

Mun gaisa da yar hira saboda ba sabawa muka yi da juna ba hira ba ta tsawo tsakanin mu, na ajiye wayar kenan Zainab ta shigo sai ta zauna kusa da ni ta ce “Ki zo mu je Billy Sunusi ke son ganin ki.”

Na yi mata duban mamaki “Da kanki Zainab za ki tura ni wurin mijin ƙawarki? Ni ko ke mu kwatanta abin a kanmu a ka yi mana ya za mu ji? Ta ɗan yi kasaƙe kafin ta ce “Ba za ki gane ba Bilkisu, gayen ya zo ya sanya ni gaba, har Najib da abokin sa suna taya shi roƙona na rasa yadda zan yi ki taimaka mu je na ce yau ne kawai daga yanzu ba ruwana suka ce sun ji.”

Na miƙe cikin sanyin jiki na ɗauko abaya ta kamo hannuna muka bar ɗakin muna tunkarar harabar gidan Najib idona ya fara gani shi da wani yana zaune kan bonet din mota cikin kwalliyar ƙananan kaya. Sai wani sashen kuma Najib ɗin Zainab ne da abokin shi.

Sunusi ne daga kusa da get shi kaɗai.
Wurin su Najib ɗinta ta fara raka ni na gaishe su sai ta raka ni wurin Sunusin, ina tsayuwa ta juya ta tafi.

Ban kalli inda yake ba na dan juya baya na ce mishi “Ina wuni?

Sai ya dawo ya fuskance ni yana haɗe hannuwa “Tuba nake gimbiya idan na yi laifi.”
Na sunkuyar da kaina ƙasa ban yi magana ba.
Maganganu ya yi ta min na bayyana min kaunar da yake min da neman haɗin kaina.

Magrib da ta gabato ya ce in zo mu je get in karɓi saƙo kai na girgiza na ce na gode na juya na kama hanyar komawa ciki.

Najib ɗin Zainab da su ma za su tafi na yi wa sallama. Har mun jera da Zainab zuwa ciki Sunusi ya kira ta a waya, ta tafi na tsaya ina jiran ta har ta dawo ɗauke da ledoji guda biyu “Sunusi da gaske yake Billy. Ga shi ya ce in kawo miki.” Na harari ledojin “Ke dai na lura kin manta da ƙawarki.”

Kafin ta yi magana Najib ɗinsu ya iso gaban mu da alama ranshi a ɓace yake na ƙara sauri na wuce na bar su. Ban tsaya falon Mama ba ɗaki na wuce na cire kayan jikina na faɗa toilet ganin baƙona mai jar mota ya tafi sai na yi wanka na ɗauro alwala don ana ta kiran sallar magrib sai da na idar Zainab ta shigo ta zauna gabana “Wata sabuwa Billy.” Na ɗan buɗe ido “To me ya faru?

“Ke ba fa wani abu bane, ya Najib ne ya aiko ni, ya ce yana son ki.”

Wata faɗuwar gaba ta ziyarce ni ba shiri Ni ba ta garin nan ba yaƙi ya ci kwartuwa.

Na zura mata ido ta hure idon sai ta cigaba “Ya ce ya lura idan ya yi wasa zai yi wa kanshi har an fara kawo hari.”

Na rufe idona na buɗe na ce “Ki faɗa mishi ba zai yiwu ba, da sauri ita ma ta buɗe ido “What? Na miƙe tsaye na haye gadonta na kwanta sannan na ce “Saboda ni ɗin ba budurwa ba ce, na taɓa aure har da ɗa nake da shi koma ba haka ba bana tunanin ya girme ni.”

Kallon mamaki ta bi ni da shi “Na sha tunanin ba ki taɓa aure ba, kuma kike zaune haka daga ba karatu kike ba?

Wayarta ta ɗauki ƙara ta ɗaga “To gani nan ya Najib.”

Abin da ta ce kenan ta tashi ta tafi na bi ta da kallo kafin na rufe idona na faɗa tunani na yi nisa cikin tunanin har ban ji motsin shigowar ta ba sai da ta ɗora hannunta kan hannuna da na ɗora bisa goshi, na buɗe ido muka yi ido biyu “Ki tashi Billy ki ji saƙon ya Najib.”

Ban ƙi ba yunƙurawa na yi na tashi na jingina da bango na miƙe ƙafafuna.

“Na faɗi ma ya Najib saƙon ki kin ce a’a saboda kin taɓa aure har ma kin haihu,kuma ga shi shi ɗin bai wuce sa’ar ki ba.”

Sai ta yi shiru, na bi ta da kallo ta gefen ido ina son jin ta cigaba.

Ta jinjina kai “Ya Najib ya ce yana son ki a haka, shi bai ga alamar wani aure ba ballantana haihuwa a tare da ke.”

Ni ma ɗin na taya shi tunanin hakan, don na yi mamaki wane lusarin ɗa namiji in ba ɗan rakon maza duniya ba, zai samu mace kamar ki kuma ya saki.”

Na kalle ta da mamakin furucin ta har ban san sa’adda maganar ta suɓuce min ba “Hu’um! Lusari shi ne zai same ni kuma ya saki a ganin ki? To abin da ba ki sani ba maza huɗu suka aure ni a cikin tsukakkun shekaru,kuma suka rabu da ni! Wani razanannen kallo ta yi min yayin da ni kuma hawaye suka wanke min fuska.

“Aure huɗu Bilkisu? Lallai na yarda da maganar wasu mata da na ji suna cewa mace mummuna ko me rangwamen kyau, sai ka ga an aure ta an adana ta muddin rai, amma mace mai fasali ko mai tsananin kyau sai ka ga tana ta yawon aure.

Yanzu dube ki yadda Allah ya kyautata halittarki ba namiji ba hatta mace ta dube ki sai ta ji abu biyu, ko dai ƙyashi da hassada don ba ta samu abin da aka cika halittarki da su ba. Ko kuma ta ji da ma ace ita ce.

Akwai wata Class mate ɗi na wallahi yadda kika gan ki haka take, ƙirji a cike kuma tsayayyu ga baya, yadda dai kike da dirin nan, abin da mazan Sch ɗin mu ke ce mata mai gaba mai baya amma na sha mamaki ƙwarai da waɗannan maza duk suka ƙi riƙe ki ko da kuwa cizon su kike yi sun yi wa kansu asara.”

Na share hawaye ta ce “Kar ma ki ƙara faɗin aure huɗu bas su a ɗayan, don ko Baba bai faɗi ma kowa kin taɓa aure ba, ya ce dai zai ɗauko ɗiyar dan’uwan shi ya roƙi matansa har da mu ya ce dukkan mu ya ba amanar ta.

Ba ki ga shi ya sa waccan sarkin ayin take jan ki a jiki don ta burge Baba, ko kuma tana da wata manufa kan yin hakan da take don dai ba ta abu don Allah, har ce ma Baba ta yi in kin zo a bata ke Baba bai magana ba.

Ya Najib ma a ɗayan da na faɗa mishi za mu tsaya, kuma kar ki wani ce ya miki yarinta wa zai dube ku a wannan girman na shi ya matso da shi kusa da ke? 25 yake yanzu shi da Khadijah, ni ce mai 23.”

Ni kuma na ce mata “24 nake.” Ta ce “Kin gani? Na kifa kaina a gadon sai na fashe da kuka, ta dafa bayana “Mene ne Billy? Ko na faɗi wani abu da bai miki daɗi ba? Na girgiza kai ina ci-gaba da kukana “Ina kukan irin ƙaddarata.”

Ta ce “Ki yi haƙuri kowane mutum da ƙaddararsa.” Na ce “Ga yarona tunda baban shi ya karɓe shi har yau ban ƙara jin ɗuriyarsa ba.” Ta ce “A ina yake ? Na ce “Anan garin ne, nan na yi auren farko Babana ya yi ta ƙoƙarin kawo ni gidan ku Allah bai ba shi iko ba har auren ya mace.” Ta ce “Kin bani matuƙar tausayi Bilkisu a wannan yan shekarun naki ace kin yi aure har huɗu da alama ba ƙara ganin rayuwa kika yi ba.”

Na ce “Ba aurarrakin da na yi ba gabaɗaya rayuwata cike take da ƙalubale.”

Ban aune ba sai na ji zuciyata ta amince in bai wa wannan baiwa ta shi labarin rayuwata, na gyara zama tun rabuwar mahaifiyata da mahaifina na soma ganin rayuwa lokacin ina da shekaru takwas da Babana ya dauko ni ya kawo wa matar Babana Inna keso ni.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 12Mutum Da Kaddararsa 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×