Wani hantsi ina shiri zan tafi makaranta,maman su Ahmad ta kira ni a waya ta ce in zo tana kira na, na tashi na tafi.A bedroom ɗinta na same ta sai da na gaishe ta da tambayar ina su Ahmad sai ta faɗa min dalilin kiran wai kayan da Najib ya bani ban taɓa sanyawa ba suna ajiye in sanya ba daɗi ya min kyauta na ƙi sanyawa.
Yanzu in wuce bathroom ta haɗa min ruwa in yi wanka in yi kwalliya.
Ba don raina ya so ba na ce to na wuce bathroom. . .