Skip to content
Part 19 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Wani hantsi ina shiri zan tafi makaranta,maman su Ahmad ta kira ni a waya ta ce in zo tana kira na, na tashi na tafi.
A bedroom ɗinta na same ta sai da na gaishe ta da tambayar ina su Ahmad sai ta faɗa min dalilin kiran wai kayan da Najib ya bani ban taɓa sanyawa ba suna ajiye in sanya ba daɗi ya min kyauta na ƙi sanyawa.

Yanzu in wuce bathroom ta haɗa min ruwa in yi wanka in yi kwalliya.

Ba don raina ya so ba na ce to na wuce bathroom ɗin da ta riga ta haɗa ruwa yana ta fitar da ƙamshi, na shiga na yi wanka mai kyau na fito har ina shinshina jikina da ƙamshin da na ji ya ɗauka.

Ta gabatar min da kayan kwalliya na zauna na fara wata hoda da ta bani na muttsuka a fuskata kyan da na ga na yi ya tuna min da uban kuɗin da ta amsa hannun Najib don ta saya min kayan kwalliya, set ɗaya kacal ta bani, ta wutsiyar ido na dubi lace din da ta ajiye min a kan gado, na rasa me wannan mata take nufi da son sai na sanya wannan kaya da za su fito min da tsiraici.

Na gama kwalliyar na zauna shiru sai ga ta ta shigo “Yaya Bilkisu ki sanya kayan mana.”
Na miƙa hannu na ɗauki rigar sai dai na fasa sanyata na ɗauki skirt din na fara daura ɗankwali ta shigo “Ma sha Allah kin yi kyau sosai.” Ni kam kallon kaina kawai nake a mudubi kamar in fashe da kuka yadda saman kirjina duk yake a waje ga skirt din ya zauna min dam “Ki je falo Bilkisu ina zuwa in duba miki mayafi.” Na ce “To.” Na fara takawa kamar mai koyon tafiya ina zuwa tsakiyar falon Najib na shigowa muka haɗa ido sai kawai na nufi kofar fita ta gefen shi na fice har na ɗauki hanya yana kiran sunana sai da na kusa part ɗin Mama na daina jiyo shi.

Ina shiga ɗaki hijab kawai na ciro na sanya ban tsaya canza kayan ba ganin zan yi latti na yi ma Zainab sallama da na fito kuma na yi ma Mama.

Kamar in sanya wa kaina damuwa sai dai na yakice komai na fuskanci karatun da ake mana da muka tashi tare muka fito da Haj Halima ban kai ga shiga motarta ba a inda ta yi parking, na hangi Najib tsaye ya naɗe hannayensa a ƙirji, na saki hannun ƙofar motar da na kama na ce mata “Ya Najib ya zo ki wuce kawai.”

Muka yi sallama na nufi wurin shi “Ba ka je kasuwa ba ya Najib? Na tambaye shi “Na je rashin ganin ki ya sa na kasa zama, me ya sa ba ki jira ni na zo na kai ki ba?

“A’a ya Najib babu nisa ka riƙa tafiya kasuwarka na roƙe ka.”

Ai idan na tashi ban gan ki ba baby akwai matsala, yau kuma kwalliyar nan ta ɗauki hankalina kawai sai kika gudu ba ki bari na gani ba.”

Inda yake na saci kallo kallona yake da wannan mayataccen kallon da na tsana, ban yi magana ba har muka shiga wani siririn layi da ban taɓa sanin akwai shi ba shiru yake ba kowa sai uwar rana da ta ƙwalle. “Ba ki ce komai ba baby.” Ya kuma ja ya tsaya na waiwayo na dube shi sai na juya na ci-gaba da tafiyata, ban san tahowar shi ba sai dai na ji an rungume ni ta baya hannun mutum dumu dumu na yawo a jikina ya kwantar da kanshi saman wuyana.

“Ina fama da kwadayinki da ke galabaitar da ni, me zan ba ki ki yarda da ni?
Da iyakacin ƙarfina na wancakalar da shi “Ba ka da abin bani da zai sa in watsar da mutuncina Najib, a yau zan bar gidanku, zan tattara kayana in bar muku gidan naku kai da wadda ke taimaka maka wajen ganin mutuncina ya fallasa.”

Na wuce shi da sauri duk da bi na da yake yana ba ni baki da haƙuri ban saurare shi ba tafiya kawai nake ina kuma sauraren abin da zuciyata ke gaya min.

Ko gidan ma da na shiga ban nemi kowa ba sallah na yi da na idar kuma na zauna tunanin yadda zan yi in sulale ba tare da kowa ya gan ni ba in bar musu gidansu.

Sai ga Zainab ta shigo ta ce Mama na kira na.
Na miƙe na bi bayanta a bedroom ɗinta na same ta zaune bakin gado na zauna daga nesa a ƙasa na gaishe ta har bakina na rawa ta ce “Me ke faruwa Bilkisu Najib ya zo min da wani zance wai za ki bar gidan nan?

Ban yi magana ba sai kuka da ya zo min na fara kukan da gaske tana cewa in yi shiru in faɗa mata abin da aka yi min ban san da shigowar shi ba sai muryar sa na ji yana cewa.

“Ki bata haƙuri Mama.”

Ba ta yi ƙasa a gwiwa ba hakurin ta soma bani kar in je ko’ina.

Kiran da aka yi mishi a waya da na gane Baba ne ya kira shi da gaugawa ya sa ya bar ɗakin.
Ta ƙara bani haƙuri tare da gargaɗin ko me zai faru kar in sake in je ko’ina, “Kowace mace gidan ubanta shi ne mutuncinta, yanzu kuma ba ki da uban da ya wuce Alh, kika bar gidan nan ba da sanin shi ba ba zai ji daɗi ba, ki tashi ki je ku ci abinci.”

Na share hawayena na miƙe.

Suna zaune a falon na wuce su na hau sama na kwanta na daɗe kwance Zainab ta shigo da abinci ba tare da na cire hijab ɗin ba na sauka muka ci ta fita da kwanonin.

Ni kuma na canza lace din zuwa riga da zane na atamfa, na kwanta kenan suka shigo ita da Khadijah suna hirar su ina tunanin matsalata har sai da suka yi sallar laasar suka fita ni ma na yi na ɗauko wayata, Gwoggo Maryama na kira sai na kira Mamana.

Ƙarfe biyar Zainab ta shigo “Wai ke yau zaman ɗaka kike ji? Murmushin yaƙe na yi mata “To kin san wani abu? Na girgiza mata kai
“Wallahi Sunusi ne ya zo kin san na faɗa miki kullum sai ya kira ni yana roƙon lambarki, rannan da ya zo ba ki fita ba yau sai ya sake salo, tare suka zo da Najib ɗi na sun taru sun ɗaure ni da jijiyar jikina su huɗu duka roƙona suke.

Najib da abokinsa shi ma Sunusin da na shi abokin.

Ki zo mu je ai dai duk nacin shi ba zai dauke ki ba sai kina son shi.”

Na ce mata “To.” Hijab na sanya na zura takalmi muka fito.

Sunusi da abokin shi suna tsaye can kusa da get jikin fulawoyi, Zainab da Najib ɗinta da abokinsa suna ɗan nesa da su.

Yau har Khadijah da ba ta zancen a harabar gidan a falon baƙin Baba take yi yau suna tsaye a harabar gidan.

A irin haka ne aka wangale get ɗin motar Baba ta danno ciki, suka wuce can rumfar adana motocin direba ya fara fitowa ya zagaya ya buɗe Boot yana ciro kaya sai Baban ya fito ya nufi ciki.

Dauda ya iso gaban direban yana kwashe kayan da ya ciro yana kai wa ciki.

Daga inda nake tsaye na tsura wa harabar gidan ido na kare musu kallo, Sunusi da abokinsa kuma suna ta zantukansu na neman shiga har da wa’azinsu shi wannan al’amari tsakanin mu ba haramun ba ne.

Ni dai ban tanka musu ba sai ganin dirar Najib muka yi kanmu kamar an jeho shi, daga shi sai dogon wandon jeans da singlet.

:Wuce ki shiga ciki.”

Ya ce min cikin da ka tsawa, ba dan ina tsoron shi ko shakkar shi ba sai don kar in kunyata shi gaban su na wuce yana kwakkwara musu ƙwaƙƙwarar kashedin su kiyaye ni.

Sai sannan ma na tuna zan yi wa Baba girki don girkin Mama ne.
Na isa kitchen ɗin duk da yamma ta yi.

Da Zainab ta shigo take ba ni labarin yau ya Najib ya sa ta ji kunyar da ba ta taɓa ji ba kaca-kaca ya yi wa su Sunusi ya ce shi ne mai so na kar su kara zuwa gidan nan.

Haɓa kawai na riƙe ina duban ta.

Yau da wayewar gari sai ga Mama ta shigo ɗakinmu abin da ba ta faye yi ba.

Zama ta yi gefen gadon zainab, ta ce in tado mata Khadijah da ke barci na matsa na tashe ta ita kuma da ta fi kusa da Zainab ta tashe ta.
Sai da suka wattsake ta ce Baba ne ya aiko ta ya ce “Jiya ya wuce ku kun cika mishi gida da maza, to ya ba kowacce sati guda ta faɗa ma wanda take so ya zo gida.

Ta maida duban ta gare ni “Bilkisu ya ce min har ke ya ce in tambaye ki in kina da wanda kike so.”

Cikin sauri na ɗaga kai “A’a Mama ni ba ni da kowa, mijin ƙawar Zainab ne ya gan mu tare.”
Ta ce “To da ma ya ce ke kam ya fi miki sha’awar ki huta ki bar batun aure ki ɗan samu karatu.”

Na ce “Ni ma hakan na fi so.”

Ta ce “To.” Ta tashi ta tafi Zainab har da tsalle sai kuma ta janyo wayarta ta yi ma Najib text message. Khadijah dai ba ta ce komai ba.
Ni kuma na sauka ƙasa na yi wa Baba abin karyawa da na gama na zo na yi shirin makaranta Zainab ta ce min idan na dawo za mu fita na ce to.

Ƙarfe uku da rabi muka gama shiri muka bar gidan.

A ƙafa muka taka har zuwa gidan su wata ƙawarta Hanan Aliyu layi uku ne tsakanin su, na su gidan har ya fi na su Zainab girma da tsaruwa.

Tun zuwa na gidan sau ɗaya ta taɓa zuwa wurin Zainab ita Zainab ɗin ma ba ta taɓa zuwa gidan su ba sai fa yau, sai dai suna yawan yin waya.

Muna shiga ita ma a shirye take key kawai ta dauka ta ce mu wuce don mahaifiyarta ma fita.

Wata haɗaɗɗiyar mota ta buɗe ta ce mana mu je.

Sai da ta hau titi ta ce ma Zainab ina muka nufa? Zainab da da ma ta shiga baya ta ce in zauna gaba ta ce “Ga mai kwatancen nan kusa da ke. “Wani iri na ji don ni ban san komai ba.
“Unguwar da Amir yake Billy ina ne?

Da sauri na leƙa baya muka haɗa ido ta ɗaga min gira “Zo mu gano Son ɗinmu yau, wace unguwa yake? Kawai baki na riƙe don na rasa ma me zan ce mata na dai yi ta maza na ce “A kurmin mashi suke.”

Sai da muka shiga unguwar na fara kwatanta mata hanyar gidan zaman da na yi na tsawon shekara biyu a unguwar wuraren ba su ɓace min ba.

Sai ga mu a ƙofar gidan Maman Aminu
A tare mu duka ukun muka fito ina gaba muka shiga gidan.

Ɗakinta cike yake da ya’yanta da jikoki, Abu ita ta fara gane ni cikin mamaki “Bilkisu ke ce kika zama haka?

Maman su kuma ta ce da a hanya ta gan ni sam ba za ta sheda ni ba..Suka yo min ca! Su da surukanta sai Zainab ce ta ce “Ina Amir?
Sai sannan suka farga suka ce a je gidan kawun su a dauko shi Abu ta saɓo shi a kafaɗa duk da uban girman da ya yi shekarun shi bakwai kenan, fes yake ba datti da ma ban yi zaton ganin shi da datti ba sanin Maman ba ta yarda da ƙazanta ba.

Zainab ta janyo shi gabana tana ce mishi ga mamanka sai murna yake don sun ce kodayaushe cikin tambayar Mamansa yake.

Ni na fara miƙewa na ce za mu wuce suka yi ta cewa tun yanzu?

Gaba ɗaya suka rako mu dukan su har Maman.
Zainab ta buɗe mota ta ciro wata leda da ta fito gida da ita ta damƙa ma Amir.

Abu ta tambaye ni lamba ta da inda nake zaune a yanzu na faɗa mata ta ce min za su zo, muka shiga mota muka bar wurin.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 18Mutum Da Kaddararsa 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×