Skip to content
Part 18 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

A yanzu kam an kai gaɓar da na ma daina firgita da al’amarin shi, abin sai hum da hum wai uwar gulma ta yi cikin shege.”

“Za mu fita ki shaƙata amma don Allah ki bar wannan ƙauyancin kina wani kama jiki.”
Ya cigaba jin na yi shiru ban kuma tsinka mishi ba hammar ƙarya na yi ta jerawa dole ya sallame ni na shiga da ledar zan haye gadon Zainab ta ce “Barii dai in kaiki gadon nan.” Ta kamo ni kamar wata yar yarinya ta kai ni gadon.

Khadijan da ta wuto mu muna zaune da Najib tana kwance ta lulluɓe rabin jikinta ni ma da na kwantan lulluɓa na yi sai dai ni har kai don har yanzu na kasa sabawa da sanyin AC da ko kashe ta ba su cika yi ba.

Wayata da na ga tana haske na janyo saƙo ne ya shigo daga Najib yana roƙo na in kunna data in shiga Whatsapp kamar an ja hannuna sai ga ni ina kunna datar, na bijirewa zuciyata da ke faɗa min in share shi.

Ina shiga Whatsapp ɗin sakon shi ne ya fara shigowa duk da ba saving din lambar na yi ba amma na gane ta shi ce, ina shiga hotunansa da suka shigo na fara budewa.

Ba ƙarya Najib haɗaɗɗen matashi ne da ya jiƙu cikin Naira hotunan an dauke su a mabanbantan wurare da suka fi ƙarfin zuwan mai ƙaramin ƙarfi ko’ina da shiga ta alfarma ga jikin ya amsa ya ci kudi.

Maganganun soyayya ya ci gaba da turo min na ba shi amsar abin da zan iya na ce mishi zan kwanta.

Na daɗe cikin tunani kala kala kafin na samu nasarar barci ya yi awon gaba da ni.

Sai da safe Zainab ta buɗe ledar da ya bani lace ne guda ɗaya sai wata hadaddiyar doguwar riga dukkan su da takalmi da jaka, lace din an mishi dinkin riga da skirt da ya yi matuƙar kyau.

Zainab ta buwaye ni sai na gwada na gwada sun zauna dam a jikina sun fidda komai.
Sai faɗin yadda suka yi min kyau take
Na ce “Amma indai da gaskiya ke ma ban ga kina sanya irin waɗannan ɗinkunan da idan ka motsa kamar za su kece ba.”

Ta ce “To ba mayafi za ki sa ba ?

Na harare ta “Mayafi saman ƙirji duk a waje?
Na tuɓe na kai su cikin kayana na ajiye.

Yau ba shi ya kai ni makaranta ba don Baba ya aike shi Zaria kai wata mota. Da muka tashi na tsaya lesson, na tashi kenan karfe biyu sai ga kiran shi wai wanda ya turo jiya ya mayar da ni an aike shi amma in ɗan jira shi ya dawo zai zo ya kai ni gida. Na ce ya bar shi zan gane, na kashe wayar.

Da ƙyar da lalube na gano gidan makuwa ta biyu ga bala’in rana don haka a gajiye liƙis na yi sallah ko abinci ban tsaya ci ba na kwanta da na tashi kuma na samu saƙon Maman su Ahmad in zo na wuce na tafi.

Cake ta ce in yi mata Allah ya taimake ni na iya shi a ɗan zaman da na yi gidan kawun Hassan, ina cikin aikin har na gama kwabin na soma gasawa na ji muryar Najib ban san me ta ce mishi ba sai ƙamshin turarensa na ji ban waiwayo ba har sai da ya yi magana “Ya ba ki shirya ba? Na kuma gaya miki za mu fita? A raina na ce “E ga mara galihu an kawo maka ka samu ta fita. A fili kuma na ce “Maman su Ahmad ta sanya ni aiki.”

Ya shigo kitchen ɗin gabaɗaya Cake ɗin da na fara cirewa ya ɗauki ɗaya ya kai baki “Ya yi daɗi baby, na faɗa ma Aunty za mu fita ta ce ko bayan kin dawo sai ki cigaba.

Na waiwayo muka haɗa ido ya sha kyau cikin ƙananan kaya na ce “Ni ba inda za ni.”

“Saboda me? Ya tambaya cikin sassauta murya a raina na ce idan ba ni da uwa ai sai in zama uwar kaina.

“Ki yi haƙuri ki zo mu je.” Na ce A’a. Gane ba zan amince ba sai ya fice.

Muryar Maman su Ahmad na ji tana kira na ban tsaya wata wata ba na fito tana zaune kan kujera Najib na kan teburin dinning.

Na zauna ƙasa kan carpet ta ce “Kasa kuma Bilkisu? Na ce “E ya isa.” Ta yi ɗan murmushi “Me ya haɗo ku da Najib kuma Bilkisu? Ya ce za ki yi mishi rakiya, kin ce a’a.”

Na yi shiru ta ƙara maimaita maganarta nan ma na kasa cewa komai “Haba har kaya ya sawo miki musamman, kuma sai ki gwale shi ? Ba a haka karɓi ki je ki shirya ku tafi.”

Sai sannan na lura da ledar kayan da ya kawo min jiya a hannunta, na san Zainab zai sa ta ɗauko mishi.

Tunanin rashin iyaye da shi ne ya jefa ni a wannan gararin ya sa na kifa kaina jikin kujera na fashe da kuka don na san inda gaban uwata nake ba ta tursasa ni fita da ƙato.

Gabaɗayan su suka ruɗe Najib ya sauko daga kan tebur ɗin ya iso gabana ta ce “Meye abun kuka Bilkisu ki yi shiru mu yi magana.” Shirun na yi na ci-gaba da share hawaye ta ce mishi “Wuce za mu yi magana da ita.” Wucewar ya yi sai da ta ji rufe kofar shi ta taso ta kama hannuna muka isa dayan bedroom ɗinta ba wanda na taɓa shiga ba don 3bedroom gare ta, bakin gado ta zaunar da ni sai ta zauna “Meye haka kike yi Bilkisu? Allah ya ba ki tsuntsu daga sama gasasshe ki tsaya wannan sakarcin? Idan ba ki sani ba in karanta miki Najib shi ne da daya da babu wani ɗa kamar shi kasantuwar shi namiji guda kuma babba, an gina shi da dukiya da za ki yi mamakin a shekarunsa ya mallake ta.

Kowa gidan nan yana neman Najib ya zama na shi (Na gane ita da Mama take nufi) ta buɗe ledar da ya kawo min ta ɗaga lace mai matuƙar tsada da aka watsa da ɗinkin zamani “Ina mai tabbatar miki duk yaran gidan nan babu mai zane mai darajar wannan, tashin farko kin samu ina ga kin kwantar da hankalinki ki saki jikinki ki yi duk abin da za ki ƙara riƙe shi duk abin da kika yi mishi dabara kika karɓo kawo su nan in adana miki aurenki ya tashi sai ki ga kin tara abin da ya’yan gidan ma ba a sai musu ba. Kika yi kwalliya da wannan lace ɗin na yi imani ya gan ki cikin shi kiɗimewar da zai yi komai ma ba ki zai yi. Ƙira mai jan hankali aka yi miki ta ja numfashi sai ta ƙara danna wayarta “Najib yawwa ka zo ina jiranka.” Ta kashe wayar “Bari in haɗa miki turarukan wanka da ƙamshin su kaɗai ya shaƙa sai ya sukurkuce ta miƙe ta shiga bathroom ɗin ni kuma hawaye ɓalle min suna gudu kan fuskata jin motsin za ta fito ya sa na yi saurin share fuskata.

Ta fito “Yawwa shigo ki yi wanka ko ba ku fita ba daga magrib ta gabato sai ku yi zancen ku a falona.

Na daga mata kai ta fita dakin na shiga bathroom ɗin na zura wa ruwan da ta tara ido kamar an mintsine ni na yo baya sai na buɗe ƙofar na fito na buɗe ƙofar bedroom ɗin a hankali sai na fita na tsaya jikin labulai na miƙa kunne “Yawwa Najib ka gane ita mace yar rarrashi ce, tana sabawa da kai sai ka yi mamaki, yanzu ka bar ni da hidimar ta wadda za ta sa a ja hankalinta.” Ya ce “Na ɗora miki hidima Aunty ki dai bayar da no acc sai in sanya miki kudin. Da ma na so mu fita ne yau kayana suka iso na buɗe sabon wurin saida kayan kwalliya idan muka je sai su zabar mata waɗanda za su dace da ita.”

“Lallai Najib arziƙi yana ta ƙara haɓaka Allah ya ƙara arziki, shi ne ba a faɗi ba mu ɗan yi bikin taya murna? Ya ce “Ba komai, mama ta sa ni in kai sadaka masallaci sun yi addu’a.
“Shi kenan, sai dai kasan ba za su fi ni sanin kayan gyara ba.”

Ya yi yar dariya “Ai ke ɗin Aunty ta musamman ce, zan sanya miki kudin kamar nawa zan sa?

Kuɗin da na ji ta fadi sai da na riƙe numfashina “Mai tsada ce yarinyar nan mata irin su ba a wasa da lamarin su.” Ta faɗi tana yar dariya

“Bari in je aunty.” Ta ce “To Najib Allah ya shi albarka.”

Da sauri na koma dakin na zauna a ƙasa ba kuma a ɓata lokaci ba ta shigo kaina na kasa ban kuma tayar na dube ta ba “A ya haka Bilkisu ina wankan?

Na ce “Kaina ke ciwo, na ji kuma kamar zazzaɓi zai kama ni.” Ta ce “Subhanallah bari in samo miki magani.” Ta fita ta dawo da ruwa da maganin ta bani na karɓa na sha ta ce “Yi kwanciyarki ki samu ya faɗa.” Na kwanta na juya baya na ci gaba da hawaye ina kaico da wannan ƙaddara tawa, yau kuma ga inda ta kawo ni, rashin gatan iyaye ya sa za a gurbata min rayuwa ta ƙarfi, yaran gidan ba wadda ke fita da wani, amma ni an yo min watsattsen ɗinki da yaran gidan ba su sanyawa in sanya in bi namiji. Wayyo ni Bilkisu. Na dade ina kuka har sai da ciwon kan na gaskiya ya ziyarce ni sai na yi shiru. Jin ana ƙwala kiran sallar magrib ya sa na fito na same ta na ce zan wuce, ta ce ta daura girki ba zan tsaya ta gama in kai ma Najib ba na ce a’a. Ta ce “Shi kenan.”
Na wuce na fice daga part ɗin.

Mama da duka yaranta na samu zaune sama na wuce na yi sallah ina ta rokon Allah a sujjada ta da ya kare ni daga sharrin Najib kar ya samu sa’a a kaina da na idar na zauna hannuna a sama ina ta rokon Allah Ya Allah ka sanya tsoronka a cikin zuciyata fiye da komai na duniya, ya Allah ka buɗe min ƙofofin farin ciki da kwanciyar hankali ka kulle min ƙofofin damuwa da bakin ciki duniya da lahira.

Shigowar Zainab na shafa addu’ar tare da goge hawayen.

Ta ce “Bilkisu.” Na ɗago a sanyaye na dube ta ta jinjina kai “Wai duk saboda ya Najib kike haka, meye aibun ya Najib ɗin da bai cancanci ki so shi ba?

Na ce “Na ce miki yana da aibu ne? Kai ta kada daga haka abin da ya kawo ta ta ɗauka sai ta fice.

Tagumi na yi da hannu biyu ita ma wadda nake raɓa in ji daɗi a gidan ta fara nuna min jin haushi ta kan ɗan’uwanta. “Allah ka dube ni na faɗi ina tashi na hau gado.

Haka na kwana ban ci abinci ba don haka da yunwa na tashi san da na shiga kitchen ko Baba Talatu ban gani ba Tea na fara haɗawa na sha daga tsaye kafin na fara aikin abincin karyawar Baba, da na gama na shirya a babban tray na kai wa Mama ita kuma ta wuce kai wa baban.

Na koma na dauko kunun da na dama na shiga dakinmu na ba Zainab ta yi dariya “Sannu da ƙoƙarin ni ma in ɗa na mai gadon zinare.”

Muka yi dariya tare na ji wani sanyi ganin Zainab ta huce daga haushin da na ga ta ɗauka da ni a daren jiya saboda dan’uwanta.

Tare muka sha kunun sai na yi wanka na shirya zan wuce makaranta na ce “Zan wuce Zainab, don Allah ki ce ya Najib ya hutar da kanshi kai ni, kin ga ina ji jiya mama na ce mishi me ya sa yanzu bai son fita da wuri? Kin ga kar a ji haushi na ace daga zuwa na zan mayar da shi wani iri.”

Yar dariya ta yi “Kin ji ki ke za a tambaya cikin salon soyayya tuni za ki ga ya fahimta.”
Na yi ɗan murmushi “To zan gwada, amma bari in yi mishi text in shaida mishi na wuce.”
Ta ce “Hakan ya yi.”

Sai da ta raka ni har get ta koma na lallaɓa na tafi cikin doguwar riga da dogon hijab.

Hajiya Halimar da muke zama tare har mun soma sabawa sai da ta tambaye ni me ya samu idona da fuskata?

Na ce “Mutuwa aka yi mana wani tsohon kakana.”

Ta yi juyayi tare da mishi addu’o’in samun rahma.

Da muka tashi ma ita ta rage min hanya don mai min lesson ba ta zo ba.

Da yammaci misalin ƙarfe biyar da rabi Najib ya kira ni a waya ya ce yana wurin lilon nan in same shi a wurin.

Ina ajiye wayar na ce ma Zainab ta zo mu je ta gyara kwanciya ta ce “Ke dai kwaskware ki tafi.”

Ban yi komai ba dogon hijab ɗi na na zuba na fita.

Tun ban ƙarasa ba na hango shi zaune ya sha kwalliya ya fito a cikakken handsome wanda yake cikin lokacin shi.

Na yi mishi sallama sai na ɗan bada tazara tsakanin mu na zauna yau na amsa mishi duk maganganun da ya yi min shi kuma ya yi ƙoƙarin kama kanshi bai kawo min maganar shashanci da ya gane ita ke hana ni sakewa da shi.

Ni kuma na gane dole in saurari Najib matsawar ina son zaman gidan ya yi min daɗi.
Abu daya na sani da ba zan lamunta ba in bari ya yi wasa da mutunci na.

Tun daga sannan sai muka fara samun fahimtar juna ni da shi ya daina min maganganun da ba su dace ba da wannan shegen kallon don na ce ban so, duk da ban sa komai tsakanina da shi Baba ba hauka yake ba da zai yarda da yiwuwar aure a tsakani na da shi, akwai tazara da banbanci mai yawa a tsakanin mu.

Duk girkin Mama kuma bana bari Baba ya ci girkin Baba Talatu ni ke yi akai mishi hakan da kuma hidimar da Najib yake yi a part ɗin Mama saboda ni ya sa Maman su Ahmad daura damarar kwato ni in dawo hannunta, don tunaninta janyo ni in koma wurin ta shi zai sa ta samu nasarar janye Najib.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 17Mutum Da Kaddararsa 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×