Na rasa wane ma irin tunani zan yi na maganganun da Baba ya yi min ko ko na abin da na ga wannan mata tana aikatawa na ji kunyar kaina na ji kunyar kaina na zargin da na yi wa Baba na ya zaɓi wata ya haɗa ta da Najib sai kuma komawata Abuja nan kam har kuka na yi, ni kuma tawa ƙaddarar kenan daga nan sai can, can kuma ko me zan je in tarar wace rayuwa zan yi da su? Allah ka yanke min wannan al'amari ka ba ni miji inda zan zauna dindindin. . .