Skip to content
Part 25 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Na rasa wane ma irin tunani zan yi na maganganun da Baba ya yi min ko ko na abin da na ga wannan mata tana aikatawa na ji kunyar kaina na ji kunyar kaina na zargin da na yi wa Baba na ya zaɓi wata ya haɗa ta da Najib sai kuma komawata Abuja nan kam har kuka na yi, ni kuma tawa ƙaddarar kenan daga nan sai can, can kuma ko me zan je in tarar wace rayuwa zan yi da su? Allah ka yanke min wannan al’amari ka ba ni miji inda zan zauna dindindin.

Hawaye suka zubo min sai kuma kamar an tsikare ni na tashi tsaye tunawa da abin da Maman su Ahmad take yi wa za ta ba bakin naman nan ya ci? Waje na yi da sauri na nufi kitchen sai dai ban ga kowa ba na duba kofa a rufe take na koma na kasa kunne kofar bedroom ɗin Maman Ahmad na ji kukan jaririyar ta ƙasa ƙasa na bar jikin ƙofar na koma daki gabana na harbawa kusa da yaran da ke barci na kwanta ina ta juye juye da na gaza barcin sai na yo alwala na yi salloli na yi ma kaina addu’a na kuma yi ma Baba Allah ya kare shi daga sharrin wannan mata.

Sai da dare ya tsala barci ya ɗauke ni wanda ya ja min tashi da ciwon kai dalilin rashin samun isasshen barci ina yin sallah kitchen na faɗa in ɗan samu ko ruwan shayi ne in sha abin da ya ba ni mamaki naman nan na gani a ajiye cikin tukunyar shiru na yi ina nazari in bar mata abin ta da ban san me za ta yi da shi ba ko in yi ƙunar baƙin wake in barar da shi ban yarda na taɓa ba ruwa na sheka mishi na tsiyaye ruwan na zuba naman a leda na ƙulle na jefa dustbin duk abin nan addu’a nake ta yi jikina na rawa.

Na sha Tea a kitchen ɗin na fito na karasa shirina Maman Ahmad ba ta fito ba na fita abu na ban san yadda za ta ƙare da shirin yaranta ba.

Part ɗin Mami na faɗa na yi mata sallama muka fito tare da Mami, mota daya muka shiga ni da ita sai Baba da Daddy ta su daban.
Tafiya mai ƙarfi muka yi don haka ƙarfe tara da rabi mun shiga Malumfashi, da shigar mu Hassan na fara tunawa sai Inna da ya’yanta, kowane hali Hassan yake ciki oho!

Ban san me ya sa Gwoggo Maryama ba ta yi min maganar shi tun dai da ta yi min farkon komawa ta Kaduna.

Maraba mai kyau aka yi wa bakin, Gwoggo ta ita da mijinta.

Ƙarshe har Mami ta shiga falon baban su Bilkisu suna maganar da wannan damar na yi amfani na sheka gidan Rahina ta warke tangaran daga karayar da ta samu, kudi na raba ma yaranta na taho ban wani zauna ba.

Na samu sun gama tattaunawar sai Mami a dakin Gwoggo Maryama tare da Gwoggon suna magana.

Mun yi sallar azahar muka ci abinci sai muka yi sallah muka dauko hanya, ban san wace matsaya aka tsaida ba sai da Allah ya sa muka isa lafiya da zan wuce part ɗin Maman Ahmad Mami ta dafa ni “Ki shirya kayan ki a yau ɗiyata, idan Allah ya tashe mu lafiya da wuri za mu kama hanya.”

Na ce “To Mami.”

A wani irin yanayi na samu Maman Ahmad da na rasa yadda zan fassara shi.

Daki na shige na shiga shirya kayana na kira Zainab mun yi magana na shaida mata komawar da zan yi Abuja murna ta kama yi “Za ki ji daɗin zama da Mami mata ce mai matuƙar kirki, za ta ba ki kulawar da ba ki samu ba ta uwa a rayuwar ki Bilkisu.”

Na ce”Allah ya sa Zainab na gode Allah ya bar zumunci.

Har na kwanta ban fito ba ita ma mai wurin ba ta neme ni ba.

Ina tashi da asuba na yi sallah sai na shiga kitchen Tea na haɗa mana har yaran su Ahmad da za su makaranta na soya ƙwai na kawo musu ina yin wanka na yi musu suka fita inda suke karyawa wayata ta shiga ƙara na dauko ta Gwoggo Maryama ce na gaishe ta ta tambaye ni gajiyar hanya na yi shiru ina sauraren ta, “Bilkisu.” Ta kira sunana sai da na amsa ta cigaba “Jiya nake jin wasu maganganu wurin Haj yar’uwar Alh Kabiru da ke son tafiya da ke, da ma kina samun matsala da wadda kike wurin ta ba ki taɓa faɗa min ba?

Ta ce min tun da ta gan ki ta ji kin burge ta kin shiga ranta, sai kuma da ta kuma dawowa ta samu an mayar da ruƙon ki hannun amaryar Alh, sai ba ta ji daɗi ba don matar halayen ta na ɓoye ba su da kyau amma a zahiri ga wanda bai sani ba zai ce ba wanda ya kai ta kirki.

Ni ma kuma haka na yi ta tunani mata mai kirki a ce iya fuska ne, da gaske Bilkisu haka halin nata yake?

Na ce “Haka ne wallahi Gwoggo.

Ta ce “Allah ya kyauta to, don da tun da kuka taho hankalina ke tashe a falon Alh da aka yi maganar tafiya da ke na amsa ne kawai saboda kunyar Alh Kabiru, amma jin hakan na ji gara a tafi da ke Allah ya sa hakan shi ya fi alheri.

Na ce “Amin Gwoggo.
“Ki kwantar da hankalinki Bilkisu ki yi karatun da Alh Kabiru ke so ki yi, kowane bawa da irin tashi ƙaddarar, in sha Allah za ki ji daɗi gaba.”.
Wasu siraran hawaye da suka taho na share na ce “To Gwoggo.”

Allah ya tsare ki ya duba rayuwar ki a duk inda kika samu kanki ya jikan mahaifinki Bilkisu.”

Na ce “Amin Gwoggo.”

Ta kashe wayar na miƙe na jefa ta a hand Bag Muhammad ya shigo “Aunty za mu tafi lunch box ɗinmu.

Na ce “Jirana ake Muhammad idan na tsaya yi muku zan makara.”

Ya juya na bi shi a baya yana cikin faɗa ma maman shi na shiga ɗakin sai da na gaishe ta na ce mata na fito ta ce “Tun yanzu?

Na ce “E suna jira na.”

Ta faɗi “Allah ya kiyaye hanya. Ina cewa Amin na juya.

Jakata daya na fara dauka na fita na dubi wurin Najib ina mamakin abin da ya hana shi shigowa, a farkon shiga wurin Mama na ajiye jakar na koma kwaso sauran da na shiga ina jin motsin Maman Ahmad a kitchen, ina ɗauke jakar karshe ina faɗi a raina su ma kan su jakunkunan nawa da masu rai ne da sun gane mamallakiyar su ba ta zaune ba ce yau muna nan gobe mun tashi.

Na samu su Mama da Mami suna karyawa na yi ma su Ihsan sallama da za su wuce Sch Asma’u har tana hawaye.

Mama ta ce in sauko mu karya zan noƙe Mami ta miƙo min flate dole na saukan na karya tare da su cikin jin kunya.

Sun tashi don Mami ta shirya na ga ya dace in kira Khadijah in yi mata sallama, ina kiran ta tsiya ta fara min ban zo gidanta ba, na ba ta haƙuri sai na faɗa mata tafiyata Abuja, ita ma dai kamar Zainab yabon Mami ta hau yi ta ce Za ki fi jin daɗi a hannunta Bilkisu. Ta yi min fatan alheri muka aje waya.

Mami ta fito cikin shiri Mama na biye da ita ta ce “To mu je ta.” Suka fita na bi su a baya Baba da Daddy suna jikin mota gidan gaba na zauna kusa da direba, Mami da Daddy suna baya muka dau hanya mota na ta sharara gudu ina kallon hanya cike da tunani kala-kala ban ko rufe idona har muka shiga Abuja gine ginen da muka yi ta wucewa sun matuƙar ƙayatar da ni, a Maitama gidan Daddy yake sojoji ke tsaron gidan kasantuwar shi tsohon soja da ya riga ya yi ritaya.

Wani tunanin na shiga da shigar mu gidan “Nana Bilkisu.” Mami ta kira sunana da ɗan ƙarfi na yi wal da ido na ɗora su a kanta ashe har sun fita “Fito mu je yata. Na sa ƙafata ƙasa na sauko a hankali tana riƙe da hannuna muka shiga ciki.

Wani lafiyayyen daki ta kai ni “Ki yi wanka ki yi sallah sai mu ci abinci Bilkisu.”

Kai na ɗaga mata tare da faɗin “To Mami.”
Ta fita sai ta turo min ƙofar na zauna daɓas bisa gadon na ɗora hannuwana duka bisa goshina tunani barkatai nake ta yi sai hannayen Mami na ji akan nawa hannuwan.

“Meye haka kuma Nana Bilkisu? Ta zauna kusa da ni “Ki yi haƙuri kin ji? Na rabo ki da yan’uwanki na kawo ki wajena, ina so ki ɗauke ni uwa.

Tun ranar da na gan ki na ji kin tsaya min a rai, daga kuma san da na ji ke ɗin ba ki girma tare da mahaifiyarki ba mahaifinki kuma da kika sani Allah ya amshi abun shi ba ki da wa ko ƙane, ga aure ba ki dace ba, tausayinki mai tsanani ya kama ni ban kuma yi tunanin roƙon a bani ke ba sai da na dawo na samu ruƙon ki ya koma hannun jummai ba zan so ta lalata miki tarbiyya ba don na san wace ce jummai, sai kuma Najib da na kula da take taken shi suna cewa son ki yake ɗan dan’uwana ne amma na ji tausayin ki a matsayin ki na mace mai rauni shi ma kuma na san wane irin yaro ne.

Ko me kike bukata ki taho kai tsaye ki same ni kar ki ji ɗar, gidan mu kaɗai ne daga ni sai daddyn Sadauki, Sadauki shi kadai Allah ya ba mu yar ɗiyarsa ke ɗebe mana kewa watan su shida kenan da tafiya kasar Canada wani Team na wasan polo suka kira shi zai buga musu wasa na shekara biyu.

Na gyaɗa kai bayan ta yi shiru cike da gamsuwa da kalaman ta tare da jin son ta kamar yadda take so na domin Allah.

Ta yi murmushi “Yawwa Nanata maza ki yi wanka ki zo mu ci abinci.”

Na miƙe na shiga bathroom da ke cikin ɗakin a gurguje na yi wankan da na fito ban same ta ba sai na yi sallar azahar na ɗan yi kwalliya sama-sama na sanya wata doguwar riga mai kauri na yane kaina da gyalen rigar na fita ina takawa a hankali a dinning area na hango su daddy da Mamin na yi musu Barka da rana ya yafito ni da hannunsa ya ce maza in zo a ci abinci na zauna cikin jin kunya amma suka tasa ni sai da na ci da yawa da muka kare kujerun falon muka koma wani tafkeken hoto na wani kakkarfan matashi bisa doki da kayan wasan polo da kana shigowa shi ke maka maraba na yi ta kallo da ayyana shi ne tilon ɗan Mami da ta kira da Sadauki su Zainab kuma suka kira shi ya Safwan.

Mami na kallon TV daddy karatun jarida, ta ce min in zan kwanta in shiga ɗaki in huta ai kamar jira na miƙe, ina zama bakin gadon wayata ta dauki ƙara na ɗauka bakuwar lamba ce na daga da sallama sai na ji muryar Baba na gaishe shi ya ƙara min nasiha da faɗa min in yi haƙuri. Na yi mishi godiya ina ajiyewa na kwanta bisa gado sai ga kiran Zainab na ɗauka cikin farin ciki mun daɗe sosai har sai da kuɗaɗen wayarta suka ƙare na kira ta muka kare maganar na ajiye ta na gyara kwanciya kiran Najib ya shigo shi kam ɓacin ran shi ya yi ta faɗi kan tafiya da ni kuma shi ne Baba ya tura shi ya bar gari inda ba service ni dai na ce ya yi haƙuri muka ajiye waya ina yi ma kaina addu’a Allah ya sa hakan shi ya fi alheri.

Barci na yi har sai da aka yi sallar laasar Mami ta shigo ta ce in fito mu yi hira mun kasance tare har lokacin kwanciya kafin in yi barci na kira Mamana da na kwana biyu ban samu a waya ba cikin sa’a na same ta da muka yi sallama na kira Gwoggo Maryama.

Da na tashi da safe na so komawa barci amma idon ya ki ba ni haɗin kai sai na janyo wayata whatsapp na shiga can na shagala har tara ta yi na mike na fita. Dakin da Mami ta yi min bayani bedroom ɗinta ne na yi knocking daga ciki ta amsa na shiga kaya na samu tana sanyawa da fara’a ta tare ni ta amsa gaisuwar da nake mata sai na soma gyara dakin duk da cewar da take in bari tukuna har mu yi break fast ban yarda na barin ba gyara mata gado na yi na goge abin da ke buƙatar guga na wanko mata bayi ina fitowa na samu ta kunna turaren wuta mai daɗin ƙamshi wanda har sai da na lumshe ido ita kanta Mamin wani irin kanshi take mai sanyi da ban yi mamaki ba don Zainab ta ce min kusan rayuwar su a Maiduguri suka yi ta zamanin da Daddy ke soja.

Da muka fito an shirya abin karin ta hau sama wurin Daddy suka sauko tare na gaishe shi ya amsa fuska sake tare da tambaya ta yadda na kwana.

Sanya ni suka yi sai da na ci abincin sosai da na gama ban zauna ba cewa na yi zan je in yi wanka, na fito wankan ina gaban kayana zan ciro kayan kwalliya ta Mamin ta shigo na kalli ledojin da ke hannunta ina yi mata sannu ta soma ciro abubuwan da ke ciki tana jerawa kan mirror kayan kwalliya ne da ta gama ta ce.

“A yi kwalliya lafiya.”

Na ce “An gode Mami Allah ya kara girma.” Ta ce “Amin diyata.” Ta fita ta ja min ƙofar.
Doguwar riga ta atamfa na sanya na fita Daddy ya yi min zancen cigaban karatuna ya ce za a sayi Green card don mayar da karatun nawa jami’ar Abuja a maimakon Kasu da na sanya da farko.

Bayan fara raba addmission na samu nasarar samu ana kammala komai da ya dace na fara karatu a Course din da suka ba ni Mass Com.

Har kuma muka kare First semester ban je Kaduna ba ko Malumfashi wurin Gwoggo Maryama.

Zamana da Mami wani irin zama ne da bakina ba zai iya fayyace shi ba, mu’amala take yi da ni mai daɗi irin ta uwa da danta. kyautatawarta a gare ni ta sa dole na saki jiki da ita.

Bikin Najib ya zo min a daidai don lokacin muka samu hutu na second semester na sati guda kacal muka tafi tare da Mami don ɗagawa aka yi da an yi tuni.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 24Mutum Da Kaddararsa 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×