Skip to content
Part 24 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Kowa ya watse aka gyara gidan muka koma rayuwarmu.

Sati guda da tashin bikin na shirya zuwa gidan Zainab, wuni na yi mata har kusan la’asar sai ga Najib shigowa ya yi aka ɗan taɓa hira da shi sai ya dube ni “Na je neman ki Aunty ta ce min kin tafi gidan Zainab shi ne na biyo ki in kai ki gida.” Na kalle shi “Kasuwar fa? Ya ce “Yau Sunday ban dade ba na dawo.”

Suka ɗan taɓa hira da Najib ɗin Zainab da Zainab ɗin ya ce min “Tashi mu tafi.” Ban musa mishi ba na ce “To. Na shiga ciki na shirya na fito suka raka mu har jikin motar.

Muna tafiya muna magana kaɗan-kaɗan har muka kusa zuwa gida sai ya kira sunana ban amsa ba duban shi na yi “Yau kaɗai ki yi min alfarma mu je ki gaida ƙanwar mamana ga layin su nan. Kara duban shi na yi sai na sunkuyar da kaina “Ki daure mu je ina so in gabatar mata ke a matar da zan aura.”

“Amma ban taɓa ji kai ko wani ya yi maganar tana nan ɗin.” Abin da na ce kenan a raina ya kuma kamata in ce mishi sai kuma rashin nazarin da ke damuna kwanakin nan ya sa na yi shiru har ya shiga layin da ya nuna min sabon get ne ya tsaya da ma fentin da ke jikin gidan.

Ya yi horn aka buɗe ya cusa hancin motar ciki ji na yi na yarda da abin da ya ce ganin sabon fenti ne gidan har ga sauran kayan aikin ma’aikata nan ba su kwashe ba.

Wata ƙofa ya shigar da mu da ta sada mu da wani falo ya ce in zauna ya shiga ciki sai sannan gabana ya fara faduwa wane hauka son Najib ya aure ni ya ja min? Idan ba gidan ƙanwar mahaifiyar ta shi ba ne ba fa? Addu’o’i na shiga karantowa sai na ji takun tafiya shi da wata mata suka fito baka ce mai jiki, na dan zamo daga kujerar ina mata Barka da fitowa ta amsa ba yabo ba fallasa Najib ɗin ta umarta ya kawo min lemo yana kawowa ya zauna, ta miƙe ta shiga ciki ya fuskance ni zai min magana ta ƙwala mishi kira ya tashi ya shige ciki gabana na ji ya ci gaba da dokawa da na ji na kasa samun nutsuwa sai na miƙe ƙofar da suka shiga ni ma na bi dogon corridor ne da na yi ta bi a hankali ƙofofi biyu ne wadda na ji magana na tasowa na tsaya na kafa kunne muryarta na fara jiyowa “Duk yammatan da ke yawo garin nan Najib, saboda ba ka da uwar da za ta faɗa maka gaskiya ka rasa wa za ka dauko ma kanka sai bazawara, ni dai ba ni cikin wannan tsarin.”

Cikin marairaicewa na ji ya ce “Waye ya fada miki bazawara ce?

Matar ubanka muka haɗu shekaranjiya ta kai yarta Asibiti, don haka ni na gama magana ba za a yi wannan rashin hankalin da ni ba ko….

Ban tsaya na ƙarasa ji ba na bar jikin ƙofar a hankali, da ja da baya na fara tafiya sai da na kusa ficewa na ɗi ba a guje ina fitowa waje hankalina ya kuma tashi da yadda garin ya haɗe ya yi baƙiƙƙirin da hadari ruwa zai iya saukowa a kowane lokaci, sai dai ban jin zan iya saurarawa a yadda nake jin zuciyata, hanya kawai na kama ko minti biyu ban yi da soma tafiya ba iska ta taso gabaɗaya haɗe da ruwa mai ƙarfi, ban tsaya ba cikin ruwan na cigaba da tafiya na kusa gida na ji alamar mota ina waiwayawa na ga Najib ne na ɓoye jikin wani gida har ya bi wata hanyar sai na gane ni yake nema.

Lokacin da na shiga gida na jiƙe sharkaf tun daga ƙofa na tuɓe kayana kaf sai zane na shiga falon ba kowa na wuce daki na cire zanen na tsane jikina sai na sa wata riga mai kauri don uban sanyin da na ji ya kama ni, na fita na kwashe waɗanda na cire na shanya sannan na leƙa Aunty suna kwance da jaririyarta ta ce cikin ruwan nan Bilkisu? Na ce E ban tsaya ba na koma daki zama na yi shiru cikin tunani dole in dawo cikin nutsuwata ba ta inda muka dace da Najib.

Baba bai amince da maganata da Najib
ba, ya yi mishi mata idan ban yi sa’a ba Maman su Ahmad za ta haɗa ni da yayanta ne da shi ma amfani take so kawai ta yi da ni.

Na fashe da kuka Ni Bilkisu ina rayuwata ta sanya gaba?

Ko da na jiyo motsin ta ban fito falo ba haka na kwana cikin wani yanayi.

Da safe na tashi da matsananciyar mura wadda ta sa dole Maman su Ahmad ta saurara min da aikinta, ina kwance lamo ta shigo ta ce shigowar Najib biyu ya duba kin fito ya ce ya wuce Company ki duba wayarki. Sai sannan na ma tuna da ita na duba ta ta jiƙe sharkaf hakan ya sa ta ɗauke ina son wayar na san ta lalace tun wacce Hassan ya sai min ce,
Na ajiye ta gefe ɗaya.

Ina nan kwance na ji an shigo muryar da na ji ta sa ni yunkurawa na tashi zaune Mami ce ta Abuja ta ƙaraso ta zauna gefen katifar ta kama hannuna “Yarinyata ba lafiya? Na sunkuyar da kaina “Ina kwana Mami, an zo lafiya? “Lafiya lau ɗiyata, Jummai ta ce ba ki da lafiya.”

Na ce “Mura ce Mami.

Ta girgiza kai “Ai ga ma muryarki nan ta dashe, Allah ya ba ki lafiya.”
Na ce “Amin na gode Mami.”

Ta miƙe “Da ma na tambayi mamanku ke ta ce kina nan shi ne na shigo.”

Na ƙara faɗin na gode Mami.
Ta fita ta ja min ƙofar na miƙe ni ma na haɗa ruwa mai zafi na yi wanka na sha magani da Maman su Ahmad ta miƙo min ta ce Najib ya aiko da shi.

Kwanciya na yi na sha barci sai da na tashi na yi sallah ban iya cin komai ba sai hura da na samu a fridge, ina zaune a falo ina shan hurar Najib ya shigo ci gaba da sha na yi har ya zauna “Ya jikin? Na ce “Da sauki.” Ya rufe ido ya buɗe su a kaina”Me ya sa ba ki duba sakon da na turo miki ba?

Ban dube shi ba na ce “Wayar ta dauke.” Me ya same ta? Na ce “Ruwa ta sha.”

“Ok ɗauko min ita in gan ta.” Na tashi a hankali na yi ciki na dawo ɗauke da ita ya dudduba ta sai ya jefa ta aljihu ya dauko tashi ya cire sima siman da ke ciki ya yi goge-goge a ciki sai ya sanya nawa sima-siman a ciki ya miƙo min “Ki yi amfani da wannan, waccan da ma ta daɗe.”

Na ce “Na gode.

Ya ɗauke kai “Ya kike jin jikin? Na ji sauƙi.”
“Me ya sa kika taho cikin ruwa kika bar ni? Ta kaikaice na dube shi ban yi magana ba zai yi magana Maman su Ahmad ta shigo “Alh na kiran ki Bilkisu ta fadi tana buɗe fridge.

Wata faɗuwar gaba ta same ni ba shiri don tunanin me zai sa Baba kira na ni kam na buɗe baki da ƙyar na ce “To.” Na miƙe na shiga daki na sanyo hijab na fito na wuce Najib na fita, kamar munafuka haka nake tafiya har na isa part ɗin Baban na ɗan tsaya kafin dai na yi ƙundumbala na yaye labulan don ƙofar a buɗe take na shiga da sallama yana zaune a daya daga cikin kujerun falon na zube kasa na gaishe shi ya ce “Ya gidan Bilkisu, ba wata damuwa? Na ce “Babu Baba.

Ya ce “Ma sha Allah, abin da ya sa na aika a kira ki Auntyn ku ta same ni da zancen Najib na son ki, Najib kuma yana tare da ɗiyar Alh Idi ɗan sarai mahaifinta ya kira ni ya ce dan wajena na zuwa wurin ɗiyarsa don haka ya ba shi mu zo a yi magana, da na kira Najib ya tabbatar min shi zuwa dai kawai yake, na ce me ya sa ya san ba auren ta zai yi ba yake zuwa wurin ta kuma ita ta ce ma ubanta shi take so, don haka zan je mu yi magana da ubanta aure sai ya aure ta. Auntynku ta fara wasu maganganu da na tsaida ita na faɗa mata Bilkisu dai tawa ce duk gidan nan kuma ba wanda ya kai ni son ta ballantana ya fi ni daga ɗan’uwana ya haifa min ita, kuma bai raye zan fi kowa farin ciki idan da Najib ya cancanci in ba shi auren ki ina miki fatan mijin da zai share miki hawayen wahalhalun da kika sha a baya na zamantakewa ta auratayya so ki cire batun aure ki fuskanci karatu yadda za ki san rayuwa.

Yanzu Khadija wanda ta aura ko da bai da en kai ƙarfin mijin Zainab ba kuɗaɗe na kashe masu yawa na samo mata aiki, mijin Zainab bai yarda ta yi aiki ba ya ce idan Khadija ta fara aikin kudin da za a rika biyan ta zai riƙa ba Zainab ɗin duk wata amma kin ga tana da kwalinta idan buƙatar ta buƙaci aikin ta tashi za ta nema.

Ke ma ina son ki yi karatun da za ki tsaya da ƙafarki, don haka zuwan da kika ga yar’uwata ta yi ita da mijinta ta zo roƙona in ba su ke ita da mijinta wanda shi ma ɗan’uwana ne dukkan su iyayen mu guda shi abokina ne da muka tashi tare, ɗan su daya ne, na ce musu ke amana ce a wuri na, sun ce su ma amanar za su riƙe ki.

A so na zan fi so su zaɓa daga cikin sauran yaran na gidan nan akan ke da kike amana a wuri na sai dai abin da ya sa na amince musu ina so ki yi nisa da Najib ki fuskanci karatun da za ki fara ski je ki kwantar da hankalinki daga Bilki har Abdullahi mutanen kirki ne za ki yi karatun ki a can idan na samu lokaci zan riƙa zuwa ina duba ki, na kuma faɗa musu sai mun je gaban Haj Maryama an nemi iznin ta don da ni da ita muke da ta cewa akan al’amarin ki, gobe idan Allah ya tashe mu lafiya za mu tafi a roƙe ta.

Ki yi ta yi wa kanki addu’a Allah ya haɗa ki da abokin rayuwa na ƙwarai wanda zai rike ki ni ma ina yi miki.”

Ki je ki shirya zuwa safiya in sha Allah za mu tafi.”

Na ce “Na gode Baba. Na mike na fita.

Ba kowa a falon na wuce daki sai dai ina kwanciya ta leƙo ta ce in shiga kitchen in yi farfesu na kaza idan na shiga zan ga naman da ta ware shi zan dafa na ce mata To na tashi na fita wani bakin nama ne da na rasa naman meye ina cikin aikin ta leƙo idan kin gama ki bar shi a tukunyar ki kira ni.

Na amsa mata ta kom ina gamawa na sanar da ita na koma ɗaki har na zauna na ji ina son in dafa baƙin shayi in sa mishi kayan ƙamshi in sha saboda mura da ta riƙe min maƙoshi ta sa kuma ban sha’awar komai ina kawo kaina zan shiga abin da na gani ya sa ni yin baya ina riƙe na numfashina ni dai wani abu da na kasa tantancewa Maman Ahmad ke yi da naman nan, ko da na ji muryarta tana cewa waye nan? Ban tsaya ba daki na shige na zauna na rasa wane irin tunani ma zan yi

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 23Mutum Da Kaddararsa 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×