Skip to content
Part 40 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Wajen da muke zuwa da Mami ya kai ni, kitso aka yarfa min da ƙunshi.

Kamar yadda ya ce idan an kusa kammala min in kira shi kiran shin na yi ya zo muka tafi.

Ganin ya kama hanyar gidan Mami daɗi na ji ya kama ni.

Yana ajiye motar masu tsare get suka yo kan mu ganin har da ni suka fara min sannu ya gida? Shi miskilin tunda ya amsa sau daya ya wuce waiwayowa ya yi gani na tare da su ya sa ya ballo min hararar da ta sa na bi shi da sauri.

Afnan ta rugo ta ɗane shi ya cafe ta da ta gan ni kuma sai ta sauka ta zo ta maƙale ni.

Mami ta fito da fara’arta tana min ga ɗiyata ga ɗiyata, shi dai har ya zauna sai da muka zauna na gaishe ta na tambaye ta Daddy ta ce ya fita sannan ya gaishe ta ya ce “Abinci Mami.”

Ta dube ni na daga hannaye sama “Shi ya ce kar in yi Mami in zo mu fita.”

Mai aikinta ta kira ta ce ta kawo abinci da ta kawo ta ajiye gaban shi shinkafa ce jallop da kifi, ya ce “Zo mu ci.”

Kunyar Mami na ji na miƙe zuwa kitchen ɗin sai dai ana zubawa na ji kamshin kifin bai min ba,hura na samu na sha na fito na ce ma Mami zan yi tuwo su tunda na je can su ba su da abin kaɗi.

Ta ce da kin fada sai in ba shi ya kai miki daga kullum sai ya zo.

Kitchen ɗin na koma na ɗaura sanwar miya da na yi amfani da kaza na koma falon Mami na hira da ya Safwan na janyo Afnan tana ba ni labari, sai da aka yi magrib na kada miyar kuka na kaɗa mai daɗi da ake kawo ma Mami na duba suna da manshanu, sai na wuce na yi sallar magrib a dakin Mami don nawa na ji shi a rufe, tuwon Semo na tuƙa na fara tace zoɓo da na dafa na haɗa shi na sanya a fridge sai da na yi Isha’i na haɗa abincin mai yi ma Mami ma tana ta haɗa musu na su na dauko tray na fito na ga Daddy da Mami suna zaune za su fara cin abinci na gaishe shi na je na ajiye tray inda ya Safwan ke zaune yana sana’ar shi ta latsa waya bayan kujerar da yake zaune na tsaya na ce “Ka sauka ka ci abinci.”

Ba tare da ya waiwayo ba ya sanya wayar aljihu ya sauka na zagayo na duka gaban shi na zuba mishi tunanina ba zai ci tuwo ba sai na ga ya fara ci ya ɗago ido ya yi min miskilallen kallon shi “Ke ba za ki ci ba? Na girgiza kai sai ka ƙoshi.” Oya zauna.” Na bata fuska sai sunana na ji Mami ta kira ina tsiyaya mishi zoɓon, na tada kai zan miƙe in je ta ce “Daddy ne ke magana ya ce ba ki taɓa girki kin manta da shi ba.”

Kai na dafe kunya na yi min lulluɓi na dire cup ɗin da na riga na cika shi kuwa ya ɗauka ya kai baki na kama hanyar daki da gudu kan gadon Mami na kwanta rub da ciki na rufe ido kunya na ɗawainiya da ni ya aka yi na yi haka ni da na dafa abu jikina rawa yake in zuba wa Daddy da Mami yau na manta da su zoɓo ma da na zuba musu a kitchen ɗin na manto su.

Ina nan a haka na ji muryar Mami “Tashi ga key ki ɗauki kayanki a dakinki.

Wata kunyar ta ƙara lulluɓe ni ni me cika bakin sati guda zan yi na yi wata guda mulumbuƙui, amma dai hakan
ba zai hana ni ɗibar kayan ba, don ina jin hirar su da Mami tana tambayar shi labarin ginin ya ce ya ɗan tsaya da aikin kwana biyu.

Shi kenan in dawo gidan Mami? A’a ba za a yi haka ba ya Safwan ya koyar da ni karatu mai wahalar bari, yanzu nake jin na yi aure ban kuma son abin da zai nesanta ni da shi ko na kwana ɗaya.

Ina wani ɗan nonnoƙewa na miƙe na buɗe wata drawer da nake zaton nan za ta ajiye key na ɗauka na fita na buɗe dakin na shiga yana nan yadda yake kayan akwatin na buɗe ina nazarin wanda zan ɗauka ya Safwan ya shigo na ɗago na dube shi hannuwan shi ya sanya cikin aljihu yana kallona “Fito ki ci abincin na ce “Daddy fa? Bai magana ba sai fita da ya yi ya dawo kuma tare da mai aikin Mami tana ɗauke da tray abincin tana fita ya ta sa ni sai da na ci na shirya kayan a cikin daya daga cikin akwatunan auren muka fito suna zaune a falo ya ce za mu wuce Mami ta ce in kai mata Afnan daki na saɓa ta a kafaɗa na wuce da ita ina kwantar da ita Mamin ta shigo wata yar jarka fara ta miƙo min ta ce in bude in sha abin da ke cikin ya min daɗi don haka da yawa na sha ta ce “Sanya sauran a hijab da safe ki sha ki sha da rana, zan aiko direba ya kawo miki sauran da na saya miki. Na ce na gode Mami.”

Ta ce “Allah ya shi muku albarka ya albarkaci auren ku.”

Na amsa a zuciya muka fito na yi ma Daddy sallama kuɗi ya ba Mami ya ce ta ba ni ta rako ni har inda motarsa take yana ciki na shiga ya tayar ta koma ciki tunda muka fara tafiya bai yi magana ba sai da muka kusa gida aka kira shi a waya bayan gaisuwa ji na yi ya ce “Zan zo yanzu Aunty.”

Muna isa bai shiga ba daga bakin get ya sauke ni ya ce min yana zuwa na shiga ciki ya juya da motar.

Gidan Auntyn Farha da ke Garki ya wuce kai tsaye ya shiga ciki, a falonta ya same ta zaune suka gaisa aka cika gaban shi da kayan tarbar baki.

Farha na cikin kujera ta lanƙwashe cikin riga da wando bakake na English wear cikin wadanda ta saya da ɗazu tana mishi fara’a.

Fuskantar Auntyn ya yi bai dubi abin da aka cika gaban shi da su ba burin shi ya ji musababbin kiran ta ce “Ɗazu sai ga Farha ta faɗa min ba ta iya barci tana firgita cikin dare ga rabo da ta samu ita mai matsala ya kamata a kula da ita barin ta ta riƙa kwana ita kaɗai kar wani abu ya samu cikin a rasa shi kamar yadda aka rasa waccan.

To kawai ya ce mata za a kiyaye, ba tare da ya fahimci zantukan nata ba.

Ya dubi Farha “Ki taso mu tafi dare ya fara.”
Ciki ta shiga dan siririn gyale ta rufe kanta ba ta ƙara komai kan shigar ta ba cikin masu aikin gidan daya na dauke mata da lodin kayan da ta saya wani kallo ya yi mata “Haka za ki fita? Ta dubi jikin na ta “Ina fita mota zan shiga idan na sauka ma ciki zan shige.”

Bai ƙara magana ba Auntyn da ta zura wa TV ido ya yi wa sai da safe ta waiwayo “Sai da safe Abban Afnan.”

Suka jera da Farha suka bar falon mai aikin na biye da su da kayan har wurin mota.

Sai da suka bar layin ba tare da ya dube ta ba ya ce “Wane maganganu Aunty ke faɗi? Dan jim ta yi sai da ya kuma maimaitawa “Ɗazu da na shiga hospital an duba ni har scanning suka yi min kuma ya result ɗin ya gwada karamin ciki nake da shi.

Duk da son ya’ya da yake sai ya ji ya kasa farin ciki da wannan magana ta Farha bai kuma ce mata komai ba yana dai auna gaskiyar labarin da akasin haka, har suka kai ita kuma sai gwiwarta ta yi sanyi kan dabarar da ta ƙulla karyar cikin za ta sa ta yi salon ta yadda take so ya tarairaye ta har ya manta da wata Bilkisu a gidan duk da bai damu da ita ba ko yanzu hakan zai sa yarinyar ta kama gabanta.

Har gaban part ɗin ya tsaya da motar ta fita ta shiga ciki ya tafi wurin mai gadi sai da ya gama magana da shi ya dawo ya fito da kayan, nata ya fara shiga da su.

Ina zaune a falon bayan ya sauke ni wanka na yi na sanya rigar barci na dawo falon don ganin rashin dacewar in kwanta bai shigo ba.
Sannu na yi wa Aunty Farha wadda tana shiga daki ta fito ta zauna a falon sai ga shi “Sannu da zuwa ya Safwan.” Na ce daga inda nake zaune ya amsa yana ajiyewa Aunty Farha jakar kaya ta ɗauka tana wani murmushi mai kayatarwa sai ta ga ya kuma shigowa da akwati ya turo ta gabana, take annurin fuskarta ya ɗauke na ja abuna na yi musu sai da safe na shige.

Washegari girkina ne ana kuma gama cin abinci Aunty Farha ta mike ta yi daki ni kuma na shiga kitchen zubo mishi farfesun kayan ciki da ya ce in yi mishi na fito muka yi kaciɓis tana zuba ƙamshi ta wuce ni zuwa turaka, na isa gaban shi na ajiye zan tafi daki ya hana ni nan na zauna har lokacin kwanciyar mu ya yi na tafi dakin don na ji haushin shigewar Aunty Farha.

Ina gama shirin barcina ya shigo nan muka kwana sai da fita sallar asuba daga can ya koma dakin shi.

Tun daga ranar ya dawo kwana ɗakina a ranakun girkina ina lura da Aunty Farha da salon da ta dauka na ba ta cin wannan wancan take so, ina zaune ina kallon Iya Larai na wahala mai gidan dai ban ga yana yi kamar wancan ba. Ga shigar ƙananan kaya da ta koma fitar ta kuma sai zan fita makaranta take yi ta kuma dawo kafin in dawo har tambaya ta take yau yaushe za ki dawo idan za ta fita kenan.

Ina cika wata biyu ni da kaina na fahimci ciki ne da ni bayan period da ban yi ba tun zuwa na don ana kawo ni Abuja da aka daura aure na soma fashin sallah sai cikina da ya taso ya yi tauri shi ya fi ba ni mamaki don ciki biyu da na yi a baya ba sa yin girma da wuri ban da wata damuwa komai ci nake ina harkokina sai kifi ne kawai na tsana zuwa lokacin na gaji da zama gidan saboda son ya Safwan mai tsanani da ya yi min dabaibayi ko ya na gan su da Farha sai in ta jin kishi yana kama ni, kullum jiran abin da zai min ko ya yake in riƙe hujja in gudu gidan Mami da tun zuwa na na farko sau biyu ya kara yarda ya je da ni da daddare idan na gudu can sai a yi maganar tarewa ta da ya ma shashantar da ita ko zuwa na da shi ina ji Mami na mishi magana.

To ya ƙi yi min komai tsakanina da shi kullum kyautatawa ce don miskilancin shi na riga na saba da shi shi ba mai son yawan magana ba ce.

Ina cika wata uku alamomin masu ciki duk sun bayyana gare ni na yi narai-narai shi kan shi cikin ya fara turawa duk wasu matsattsun kaya na tattara su na ajiye don ban son a ga cikin shi kan shi mai cikin ban sanar mishi ba.

Ranar da Allah ya tashi bayyana shi
ranar tun safe ina tashi na ji ni ba daidai ba dole da na yi sallah na koma na kwanta ga shi zan shiga makaranta ina kwance zazzaɓi ya ziyarce ni ƙarfe bakwai suka shigo dakin shi da Aunty Farha gani na kwance ita ta tambaye ni lafiya na ce ba ni da lafiya ya ce ta samo min abin da zan ci in sha magani ta fita ya matso ya taɓa jikina jin zafi ya ce tun yaushe ne ban da lafiya me ya sa ban kira shi ba na ce na tashi yanzu na ji ba ni da lafiya ya ce me ya sa na kashe wayata tun da ya dawo masallaci ya kasa komawa barci saboda rashin samun wayata.” Jin alamar tahowa ya sa ya janye daga gare ni Aunty Farha ta shigo Tea ne aka hado ta matso ta ba ni ina shan madara amma yau ina kurɓa sau daya sai zuciyata ta fara tashi na ƙara kurɓa gaba ɗaya cikina ya hautsine na ajiye cup ɗin na faɗa toilet a gigice amai na fara kelayawa kamar zan amaye yan hanjina tun ina yi abinci na zuba har ya koma kakari kawai nake na ɗauraye fuskata na fito na kwanta kan gado Aunty Farha na ta yi min sannu tana ce mashi bari ta dauko wayarta ta kira ƙawarta ta duba ni hannu kawai ya daga mata sai ta fasa tafiyar tana ayyanawa a ranta ko damuwa ai ta haddasa miki ciwo yarinya wata uku kina zaune an kawo ki an jibge miji bai ma san kina nan ba sai dai ki yi ta wahalar mishi girki in Allah ya yarda a haka auren zai gantale waɗanda suka ƙulla shi ba su fahimci komai ba.

Kiran wayar da ya fara ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta lula ta zo ta zauna kusa da ni shi kam yana tsaye bayan gama wayar ya rungume hannaye ko gajiya da tsayuwar ba ya yi ba a jima ba ya fita ya shigo da wani tambayoyi ya yi min daga karshe ya ɗebi jinina ya tafi Aunty Farha ma ta fita ya matso ya tallafo ni yana min sannu muna nan a haka har likitan ya dawo takarda ya ba shi tare da yi mishi murna Madam na dauke da juna biyu fara’ar da ban taɓa gani a fuskar ya Safwan ba na gani kafin ya zame kasa ya yi sujjada ya ɗago suna musabaha da likitan zai wuce aunty Farha da ta ga shigowar likitan ta biyo shi ta ji gargar jin zancen juna biyu da ya yi ya sa ta daskare a inda take har likitan ya raɓa ta gefen ta ya wuce.

Daidai kaina ya ranƙwafo yana gaya min zantukan da suka sa na lumshe ido.

“Me na ji likitan nan ya ce maka Safwan? Aunty Farha ta tambaya da karfi na buɗe ido na kai su gare ta jin yau ta fadi sunan ya Safwan shi kuma ya mike ya fuskance ta tsaye take cikin wani yanayi da ba sai an faɗi maka tashin hankali mai tsanani ya ziyarce ta.
Ya jefa hannuwansa cikin aljihu “Ciki Mami gare ta Farha.”

Ƙirjinta ta dafe idonta waje “Ciki Safwan? Ta riƙa nuna shi tana nuna ni “Ta ya hakan ta kasance ina zaune ? Ta fadi tana dan buga kanta da hannunta kamar wadda ta samu taɓin ƙwaƙwalwa ya yi matuƙar daure fuska.

“Matar tawa za ki tsare ni yadda aka yi na yi mata ciki mts! Ya ja wani ɗan banzan tsaki “Ka cuce ni Safwan a gidan nawa ka kwanta da ita?

Ya kara jan tsaki “Yes yadda na biya sadakinki haka na biya na ta ba na son shirme.”

Ta kwarma ihu “Ni kake faɗa ma matsayin mu ɗaya da wata Safwan?

Ta juya ta fita da gudu!

Ya dawo ya zauna bakin gadon da nake ya sanya hannuna cikin na shi “Me za ki iya ci a kawo miki ki ci ki sha magani?

Na rufe idona na buɗe.

<< Mutum Da Kaddararsa 39Mutum Da Kaddararsa 41 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×