Wani ɗaki ta buɗe muka shiga gado ne sai mirror da wardrobe sai kujera guda daya.An gyare shi tsaf yana fitar da ƙamshi.
Ta wuce bathroom ta haɗa min ruwa ta fito ta ce "Mu kwana lafiya."
Na ce "Sannu da kokari, na gode kwarai.Ban shiga wankan ba bisa kujerar na zauna na ciro wayata ganin Zainab online na ce "Mai jego ba ki kwanta ba?
Ta amsa muka ci-gaba da hira har ya Safwan ya shigo ganin bai kalli inda nake zaune ba nasan fushi yake da ni.
Bathroom ya shiga can ya fito. . .