Yamma liƙis muka shiga Dukku gidan Iya na kwatanta ma direban. Da muka isa suka sauke kayan na samu Iya cikin halin jinya sosai, don mun rabu da waya da na tambayi Inna keso matar babana ce min ta yi wayar Iyar ta lalace. Na amshi jinyarta da ma Inna keso da ƙanwarta su ke yin karɓa karɓa.
Babana wannan karon ma ya ji bakin cikin mutuwar aurena har ya so ya ɗau zafi da ni sai da na ba shi takardar sakin ya ga abin da Hassan ya ce sai ya bar wa Allah ya yi. . .