Skip to content
Part 8 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Yamma liƙis muka shiga Dukku gidan Iya na kwatanta ma direban. Da muka isa suka sauke kayan na samu Iya cikin halin jinya sosai, don mun rabu da waya da na tambayi Inna keso matar babana ce min ta yi wayar Iyar ta lalace. Na amshi jinyarta da ma Inna keso da ƙanwarta su ke yin karɓa karɓa.

Babana wannan karon ma ya ji bakin cikin mutuwar aurena har ya so ya ɗau zafi da ni sai da na ba shi takardar sakin ya ga abin da Hassan ya ce sai ya bar wa Allah ya yi min addu’a. Da su Gwoggo Maryama suka dawo aikin hajji ta zo ta yi min faɗa sosai da na taho ban je gidanta ba da za ta tafi ta nemi in shirya mu tafi tare na ce a’a garin ya fita raina.

Babansu Bilkisu ma ya kira babana ya bayyana tsantsan ɓacin ransa yadda ban ɗauke shi uba ba na tsallake gidan shi na taho. Babana ya yi ta ba shi haƙuri, da ya yi min faɗa kan abin da na yin kuka na yi ta yi. Kwanana ashirin Iya ta ce ga garinku nan! Na shiga wani irin tashin hankali na yi kuka irin wanda ban taɓa yi ba.Tana yin bakwai na ce wa babana zan tafi wurin mamana a Taraba State, na kira ta a waya na ce ina tafe.

Wannan ne karo na farko da zan taka inda Mamana take tunda aurenta da babana ya ƙare ta ta tafi ta bar ni. Ban ji daɗin yadda na same ta ba cikin halin rashi ɗakinsu room and parlour ne ga yaransu biyar. Mijinta sam bai maraba da zuwana ba ina ji yana mata faɗa idan sun shiga ɗaki, ni ma ban sake ba dan su ɗin ma wurin ya yi musu kaɗan. Sati ɗaya na yi na yi musu sallama na koma Dukku. Kwanana daya da dawowa matar babana Innakeso ta ce min suna son ɗakinsu dakin iya da na zuba kayan ɗakina za su sa dan haya.

Na kwaso na zube su tsakar gida don kwata-kwata gidan namu ɗakuna uku ne daga na Innakeso room and parlour sai wanda nake zama ƙarami ne shi ƙwarai. Maƙwabciyarmu da ta shigo ta ga kayan zube ta ce in kawo su gidanta, mijinta mai hali ne, gidan nata mai girma ne ƙwarai. Duk kuma san da ta gama girki za ta aiko min da shi abin da take faɗi tausayi nake ba ta da ƙaddarar rayuwar da ta faɗa min. Islamiya na faɗa na riƙe ibada ƙwarai don yadda nake jin zafi a zuciyata ga tunani ga tunanin Amir da ya baibaye ni, ina tuna ko a wane hali yake? Ba don ban son ganin ko me kama da Aminu ba da na je na gano shi, ban son ya rayu yadda na rayu ba tare da ɗimin uwa ba ni da ita ba wata shaƙuwa.

Wata ranar Asabar na fita zuwa islamiya cikin dogon hijab har ƙasa. Islamiyar kaɗai ke fitar da ni daga gida don gulmace-,gulmacen da suka fara yawa a kaina na ban zaman aure, ko da nake da farin jinin manema da na fito, wannan karon tunda na ƙare iddata shiru ce. Na shiga lungu na ji ana “Bilkisu sarauniyar mata.” Kamar ba zan waiwaya ba, na ƙara sauri sai na ji an ƙara faɗi tare da jin ƙamshin turare don har ya cim ma ni, na dubi gefen haguna inda yake ban fasa tafiyata ba.

Maƙwabcinmu ne mijin Maman Kubra da ta ajiye min kayan ɗaki. Na ja ajiyar zuciya “Barka da hantsi sarauniyar mata Bilkisu.” Na ce “Ina kwana baban Kubra? Ya washe baki “Lafiya lau mai gadon zinare. Makaranta za a ne? Na ɗaga kai “Bari in yi rakiya.” Sai na rasa me zan ce mishi haka muka yi ta tafiya yana min hira, ni dai kam ina jin nauyinsa sai da muka kusa da makarantar ya koma.

Haka aka maimaita washegari ina shiga lungu ya biyo ni ya kuma bayyana min shi so na yake kuma da aure, wani irin ruɗani na shiga na ba shi hakuri na ce saboda matarsa ba zan iya auren shi ba ya ce in dan matarsa ba zai rasa ni ba don matuƙar tausayi na da take ji ba za ta ƙi ya aure ni ba. Ni dai na ƙi shi kuma bai fasa biyo ni ba kullum, da zarar na fito. Matar babana da kanta ban san inda ta tsinto labarin ba ta sanya lulluɓinta ta shiga ta faɗa wa Maman Kubra, sai ga mata ta shigo ta yi min tas, matar baban nawa na taya ta tana komawa gida ta sanya aka fito min da kayana aka tule ƙofar gidanmu.

Na yi kuka a ranar kamar raina zai fita.Shi kuma mijin nata yana dawowa ya ga kayana tile a waje ya sa aka kwashe aka kai wani gidan na shi. Tun kuma daga ranar kullum sai ta shigo gidanmu ta yi min tijara sai da mijinta ya ce duk san da ta kuma shigowa matuƙar ba abin arziki zai kawo ta ba to a bakin aurenta.

Hakan ya sa ta bar shigowa sai ta koma leƙowa ta doguwar katangarsu da ban san uwar da take takawa ba tana zagina da aibata ni da kirana da sunan maciyiyar amana. Ranar da ta kai ni ƙarshe tana maƙale jikin katangar tana aiko min da maganganun tozarci na dube ta idona taf da hawaye na ce “Ban so mu yi haka da ke ba maman Kubra, na so saka miki da irin alherin da kika yi min mijinki ki tambaye shi shi yake ta bikin shi na ce ba aure tsakani na da shi saboda ke amma daga kin nuna min ke ba yar halak ba ce zan auri mijin naki in ga abin da za ki.

Goben nan mutuwa kaɗai za ta hana ni faɗi mishi ya fito.Ta shiga kutuntuma min ashar ita kuma Inna keso da ke tsaye ta kama tafa hannaye da faɗin “Ta tabbata kenan dai cin amanar za ki yi?Ko kallon ta ban yi ba na tashi na shiga ɗaki. Washegari da wuri na shirya na fita makaranta ina shiga lungu ya take min baya “Barka da fitowa Bilkisu sarauniyar mata.” Na dubi gefen da yake na sakar mishi wani fari da ya yi matuƙar kiɗima shi “Ina kwana? Na ce ina wani salo da idona ajiyar zuciya mai ƙarfi na ji ya ja “Yaushe za a yi min izni in fara zuwa zance mai gadon zinare? Na kaɗa ido”Duk san da ka shirya ƙofa a buɗe take.”Godiya ya shiga yi min kamar na yi mishi wata gagarumar kyauta.

Ya tura hannu aljihu ya ciro kuɗi ya miƙo min na sa hannu biyu na karɓa saɓanin da da duk magiyar da zai min ban karɓa.In da ya saba bari na yau ma nan ya bar ni ya juya.Dare na yi kuwa sai ga shi a zauren gidanmu. Muna tsaye babana ya zo ya shige mu.Awa daya muka yi na ce zan shiga gida, da na shiga na samu babana da Innakeso suna zaune tsakar gida suna shan iska saboda yanayin zafi da ake ciki.

Zan wuce daki ya sa baki ya kira ni na dawo na tsuguna gefen shi ya ce kamar Alh Buhari na gan ku tare yanzu a waje? Sai da na kalli inda Innakeso ke zaune na ce “E shi ne.” Ya ɗan yi shiru can ya ce “Ya za a yi haka kuma mai gadon zinari? Matarsa tunda aka yi aurenta anan take ana kuma tare.” Na ce “Ya daɗe yana bibiyata baba, ban kuma taɓa kula shi ba saboda ita, kawai tunda aka kai mata labari shi kenan kullum sai ta shigo ta zage ni.”

Cike da mamaki ya ce “Gidan nan take shigowa? Na ce “E baba,sai da ya hana ta sai ta koma leƙowa ta wannan doguwar katangar tasu tana zagina kuma kullum ba fashi, shi ne na ce daga ba mutunci ba ta san shi ba zan aure shi.”Ya jinjina kai “Allah ya yi mana zaɓi na alheri. A zuciyata na ce Amin na tashi na shiga daki na bar Innakeso tana ta surutan wannan ai cin amana ne.

Maman Kubra ba irin haukan da ba ta yi ba don in janye ko mijinta ya janye, amma kamar zuga mu take sadaki kadai na karɓa wani gida da ya gina bene hawa ɗaya a bayan gidan aka shirya min kayana wadanda ya canza min ranar da aka daura aure ranar na tare yan kai ni sai faɗin ma sha Allah suke da ganin tanƙasheshen gidan da kuma dukiyar da aka zuba min. Ana ta min addu’a Allah ya sa mutuwa ce za ta raba.Kowane aure nawa da na shi ƙalubalen shi wannan tun daga daren farko tashi matsalar ta bayyana.

Alh Buhari ya yi iyakar ƙoƙarin ya kusance ni amma abu ya gagara sai ya koma ba namiji ba.Ina fa cikin daula komai shigo min ake da shi illa dai wannan matsalar da ta hana ni sakankancewa in miƙe ƙafa. Lokaci lokaci ina tura wa Mamana kuɗi saboda yana ba ni su. Wannan auren wata uku kacal ya yi wata safiya ya ba ni zungureriyar takarda ya ce ya sawaƙe min, saboda ya sha magani iya sha babu abin da ya canza kuma wurin uwargidansa garas yake .Na baro gidan hankali tashe sai Inna lillahi wa’inna illaihi rajiun Allahumma ajirni fi musibati waklifni khairan minha.”Nake ta maimaitawa, na sha habaici wurin Inna keso da na isa gida.

Babana da ya dawo daga kasuwa ya ji abin da ya faru da ni shiru ya yi bai ce komai ba har washegari na ga bai fito sallar asuba ba na ajiye tsintsiyar da na soma share tsakar gida na isa ƙofar ɗakinsu ina sallama Inna keso ta amsa ta leƙo na gaishe ta sai na ce “Lafiya baba bai fita sallar asuba ba? Ta ce “Da zazzaɓi ya kwana. Wani tsoro da faɗuwar gaba suka yi mini dirar mikiya don ciwon da zai hana babana fita sallah ba ƙarami bane.

Na ce “Zan shiga in duba shi.” Ta kauce na shiga yana kwance idonsa a buɗe na tsugune na gaishe shi da tambayar jikinsa ya ce ya ji sauki ya haɗiyi magani. Na ɗan jima a tsugunnen kafin na fita na koma kan aikina. Ƙarfe sha ɗaya ya fita ya tafi kasuwa amma zuwa Azahar sai ga shi ya dawo zazzaɓin ya rufe shi.Tun daga ranar kullum ya fita zai wahala a tashi kasuwar bai dawo ba.

Ranar da ya cika sati guda har yamma ya kai bai dawo ba ina ta murna, bai shigo ba sai da aka yi sallar magrib ya kira ni na zo na tsuguna ya ce “Ki yi haƙuri Bilkisu da ƙaddarar da ta same ki kowane mutum da ƙaddararsa ina miki fatan samun rayuwar aure mai dorewa kullum addu’ata kenan Allah ya kaiki inda za ki zauna har karshen rayuwarki to ba rabon in gani.”

Jikina ya yi wani irin sanyi na ce “Ka yi Haƙuri baba gobe mu je asibiti.” Ki yi haƙuri, ki yi haƙuri,ki yi haƙuri.Na ce zazzabin ne baba ya girgiza kai na ce “Ina ke maka ciwo? Ya ce “Babu.” Na rasa dalilin da ya sa babana ke bani haƙuri ina nan tsugune har Inna keso ta shigo mishi da tuwo sai dai duk maganar da take mishi ko motsi bai ba, na kamo hannunsa hannun ya koma ganin kiɗimewar da na yi ya sa ta ɗauki lulluɓinta ta fita suka zo da amininsa ya taɓa shi yana Malam Habu shiru sai ya ɗago yana bamu haƙuri na miƙe zan gudu ya ce Inna keso ta ruƙo ni tana riƙe ni na zube ban kara sanin abin da ke faruwa ba na dawo hayyacina na ga haske ko’ina jama’a kewaye da ni take na tuna al’amarin da ya same ni hawaye suka ɓalle min ƙirjina ya min nauyi.

“Shi kenan na rasa babana, yau bangona ya faɗi innalillahi wa’inna illaihi rajiun Allahumma ajirni fi musibati waklifni khairan minha Allah ka zame min bango abin jingina Allah ka shiga lamarina ka zame min gata.”

Jin wadannan lafuzzan da nake yi kowa da ke cikin ɗakin ya fashe da kuka ana faɗin ki yi haƙuri Bilkisu, tabbas yau kin yi rashi. Na lumshe idona hawaye na kwaranya ƙirjina na zafi. Zuwa Azahar Gwoggo Maryama ta zo ita da mai gidanta da yaranta ta ci kuka fuskarta ta yi ƙozai- ƙozai ta rungume ni a jikinta tana kuka tana bani haƙuri.

Zaman makoki aka yi har na kwana bakwai kuma gidan danƙam yake da ɗan adam don yadda bayin Allah ke ta aiko da abinci mata kuma na ta dahuwa.

Ranar uku sai ga dan’uwan babana na Kaduna wanda ya sha bani labari da mahaifiyarsa da ta dan’uwan na shi uwa daya uba daya suke shi ɗan’uwan na shi su hudu duka maza shi ne babba ya so ya kai ni wajen su da ina Kaduna in yi zumunci da iyalansu har barbaɗaɗɗen auren ya gantale Allah bai nufe shi da kai ni ba.

Ya yi gaisuwa ya kawo kuɗaɗe masu kauri ya bayar suka zauna da Gwoggo Maryama suna ta hira ta sanya aka kira ni ta gabatar mishi da ni a matsayin tilon ɗiyar baba da ya haifa da kuma ƙaddarar da ta same ni ta aure aure ya tausaya ƙwarai tare da yi min nasihar in yi hakuri sai da suka yi La’asar suka juya ya ce Gombe za su kwana da safe su yi sammako zuwa Kaduna.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 7Mutum Da Kaddararsa 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×