Skip to content
Part 7 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Yadda Hassan ya ce hakan aka yi muka haɗu a inda ya ce muka lula Kaduna. Hotel ya kama mana muka yi kwana biyu tunda na shiga garin nake tuna ɗana Amir yana cikin garin nan ko a wane hali yake oho, ina tsoron ya rayu a yadda na rayu ina da uwa amma kamar bani da ita ba wata soyayya ko shaƙuwa tsakanin mu saboda rashin zama tare.

Ya kan fita ya yi harkar da ta kai shi idan ya dawo mu fita tare mu ɗan zagaya gari, sai dare mu dawo.Da muka dawo inda ya ɗauke ni nan ya sauke ni na hau nafef na koma gida.

Haka muka yi ta yi idan tafiya ta kama shi za mu yi mahaɗa ya tafi da ni ranar da liƙi ya ɓalle Abuja ya tafi da ni, bayan hotel mai kyau da ya kama ya kuma fita da ni na ga wuraren shaƙatawa kuɗaɗe sosai ya kashe min.

Ana gobe za mu bar garin da daddare,na samu wayar Gwoggo Maryama sai da na gama gaishe ta ta ce “Ɗazu muka haɗu da surukarki take min barkar wai ƙanwar Alh da kika tafi suna.

“Wata irin juyawa na ji cikina ya yi na kasa magana har sai da ta ƙara maimaita maganarta, na yi ƙarfin halin cewa “Wata matar abokinsa ce ta haihu, in ta san gaskiya ba za ta bari in je ba.”

Gwoggo ta ce “To Allah ya kyauta, don na riga na kwafsa muku.” Da sauri na ce “Sai da safe Gwoggo.” Hassan ya ɗago kai daga laptop din da ke gaban shi duk da sanyin ac haka na soma share zufa a raina ina salati.

“Me ya faru? Ya tambaye ni na tashi na isa kusa da shi na ba shi labarin karyarmu da ta ƙare. Ganin yadda na tashi hankalina sai ya nuna min ko a jikinsa ya yi ta gaya min ba abin da zai faru in kwantar da hankalina da muka kwanta ma sha’anin shi ya shiga wanda ya sa marata ta ci-gaba da murɗawa a hankali sai dai ban faɗa mishi ba.

Saboda yanayin tafiyar shi na sammako karfe goma sha ɗaya ya sauke ni a Malumfashi. Kamar kazar da ƙwai ya fashe ma wa na hau nafef zuwa gida gabana na dakan uku-uku a sa’a na shiga don ban samu kowa a tsakar gidan ba na saɗaɗa na buɗe ɗakina na shige.

Komai ban yi a ciki ba kwanciya na yi ina sauraren tsungulawar da marata ke yi, ina nan kwance matar Gambo ta leƙo, gani na kwance ta ce “A’a lafiya masu tafiya aka dawo aka kwanta? Yanzu na fito na ga ƙofarki a buɗe.” Na ce “Na dawo ban jin dadi ne.”

Sai ta shigo sosai “Subhanallahi.” Sai ta shiga yi min sannu wani yamutsawa da cikin ya yi na tashi zaune ta matso kusa da ni sai ta ɓarke da salati “Jini ta ƙafafunki! Cikin faɗuwar gaba na dubi wurin sai ga jini na gudu na sauko ƙasa ina salati, ta fita cikin sauri wai za ta kira Inna to ba su dawo da Innar ba ita kaɗai ta dawo tana ta min sannu sai ga abu ya fado wanda aka gama yi ma halitta tsaf illa watannin shi da ba su kai ba sai dai ba rai.

Na jingina kaina jikin kujera ina mayar da numfashi na ce ta bani wayata gane Inna ba za ta zo ta taimaka min ba na kira Gwoggona don daga inda nake ina jiyo baƙaƙen maganganunta.

“Tsabar jaraba an kanainaye namiji to ina ciki zai zauna? Cikin da ake ta ma zumuɗi an zubar da shi! Kan ka ce me Gwoggona ta iso ita ta ɗaga ni cikin jinin ta kama ni zuwa bayi na yi wanka da ruwan da matar Gambo ta dafa min ta kuma kwashe ta kai min bayi.

Gwoggo ta tattara yaron ta ƙunshe ta kai wa Inna, suka gyara wurin ita da matar Gambo ta haɗa min Tea na sha da ta tabbatar ba ni da wata damuwa ta sallame ni ta tafi gida ta ce za ta turo Bilkisu ta zauna wurina tana taimaka min.

Na kwanta na samu barci Hassan ya kira ni yadda na ji muryarsa na gane ba ƙaramar damuwa yake ciki ba gabaɗaya ma kasa min magana ya yi sai ni ke cewa “Ka yi haƙuri Allah zai bamu wani.

Ina ajiye wayar matar Gambo ta shigo da naman kaza da na bata ta dafa min sai da ta yi min sannu ta zauna “Ai burin mutanen can masu baƙin hali ya cika.” Na dube ta waɗanne mutane kenan?

Ba ta ko numfasa ba ta ce “Su Inna mana, cikin ya ɓare sai su barki ki wataya.Na ce “Uhhm. Ina lumshe idona don wani abu da na ji ya tokare ƙorjina don baƙin cikin rasa abin da ke cikina.

Ko da Hassan ba ya nan to hidima mai yawa yake yi don kullum ɗakina cike yake da mutanen Gwoggo Gwoggon kuma shiri suke ta yi za su ziyarci dakin Allah mai alfarma don sauke faralin aikin Hajji ita da mai gidanta.

Hassan bai samu zuwa ba har sai da na kwana takwas don ya yi tafiya zuwa Ikko. Na warware na yi garas da ni sai dai takurar su Inna da ya’yanta waɗanda kullum suna gida.

Ranar wata Asabar tun safe ina kwance Hassan ya kira ni ya ce in duba hanyarsa yau. Wani daɗi ya lulluɓe ni ɗan barcin da ke idona ya tattara ya gudu na miƙe na fara gyara wurin da na gama na yi wanka na tafi islamiyya sai da na dawo na ɗora girki don ya ce sai yamma zai iso.

Da na kammala na zuba na Inna ban kai ba saboda ya’yanta gabaɗaya suna nan na ba Aliyah ta miƙa mata na zuba wa matar Gambo sai ga Aliyah ta dawo wai abincin da na bayar ba zai ishe su ba, na ɗauki nawa na basu ta tafi sai ga Hajara ta zo ta tsaya a kaina fuska a tamke “Ke an ce ki bada abinci kin bada ɗan wannan.”

Ban ɗago na dube ta ba na ce “Iyakar shi kenan. Cikin sauri ta ce “Wallahi ƙarya kike, na waccan kular fa? Na ɗaga ido na dube ta jin ƙaryata ni da ta yi na dai daure zuciyata na ce “Na Hassan ne.” Ta ja tsaki “To ko shi ya isa ya ce kar a ba Inna, ballantana ke karan kaɗa miya.”

Ta wuce ni ta dauko abincin na ce “Malama ajiye min. Ta ce “Ba saban ba,an samu abin duniya da dai bamu san asalin ungulu ba sai ta ce daga masar take.”

Ta sa kai za ta wuce da abincin na kai hannu na riƙe don na kai ƙololuwa wurin gajiya da wannan cin kashin da suke min, na ce “Ajiye min abincina, in ma zan bayar ba ta rashin sanin girma da ƙima zan bayar ba.”

Ta ja na ja sai ta kaɓe ta faɗi abincin ya watse na dubi yadda ko’ina ya lalace ta wuce ni sai na ji idona ya kawo ruwa na bi bayanta zuwa dakin Inna tana zaune da dukkan ya’yan nata. Na fara faɗi mata abin da Hajara ta yi min buɗar bakinta sai cewa ta yi “Duk abin da ta faɗi akwai ƙarya a ciki? Samun wurin naki har ya kai ki zo ki tsare ni to wanda ya kwaso ki zai zo ya same ni.”

Na fara hawaye na ce “Yanzu Inna duk abin da ta yi min ba ki gani ba? Ta ce “E ban gani ba fita kuma ki bani wuri rashin kunyar ta ishe ni shi kuma zai zo ya same ni.”

Na koma ɗakina sai da na yi kuka mai isa ta sannan na gyara wurin na kuma ɗora wani sabon girkin, ina cikin yi Hassan ya iso ɗakin mahaifiyarsa ya wuce kamar yadda ya saba, har kuma na gama girkin bai fito ba sabon wanka na sake na yi kwalliya, ina cikin daura ɗankwali ya shigo na tare shi da sannu da zuwa sai dai abin mamaki a wurina fuskarsa ba annuri ko kaɗan.

“Me ya sa Bilkisu kike son canza hali, bayan su Hajara yau har Inna kike sa’insa da ita don ta aiko ki bata abinci babu abincin ne da ba za a dafa wani ba? Zan yi magana hawaye suka goce min ya wuce ni ya ɗauki buta, da ya dawo masallacin ma ɗakin Innar ya koma. Na rasa abin da ke min daɗi da abin da aka faɗi mashi kuma ya ɗauka na fita ƙofar ɗakina duk da hatsarin da ke ga zama kan dankari nan ɗin na zauna na yi tagumi da hannu bi biyu idanuwana ƙuri a ƙofar ɗakin Inna labulai da ya ɗaga na hango Hassan na cin abinci ba yau ta fara min haka ba ita da ya’yanta za su zauna sai na yi abinci na basu, amma ranar duk da Hassan zai zo matar nan za ta zage ta yi mishi abinci don dai kar ya ci nawa.

Na gaji da zaman na shiga ɗaki, har na gama abin da nake na kwanta sannan ya shigo, na danne ɓacin raina na gabatar mishi da abinci ya ce ya ƙoshi. Haka muka kwana kowa ransa ba daɗi washegari ya koma.Tun daga nan Inna ba ta ƙara bari mun zauna lafiya ba, kullum cikin kai ƙara ta take ga abin da na yi mata.

Ranar da ba zan taɓa mantawa da ita ba Hassan ya zo ranar kwanan su Gwoggo Maryama biyar ita da mijinta da ɗagawa ƙasa mai tsarki, sai wata ƙanwar mai gidan ce zaune a gidan tana zama da yaran.Tun isowar sa yana ɗakin Inna da ma, ina zaune ƙofar ɗakina ƙanen Inna da suke uwa ɗaya uba ɗaya kawu Isah ya shigo na gaishe shi ya wuce ɗakinta sai ga aminiyarta Inna Ku cinmatu ita ma ta iso .Ba jimawa Aliyah ta zo ta ce min ana kirana a dakin Inna gabana ya ce dum!

Na miƙe da sanyin jiki na shiga ɗaki na sanyo hijab. Daga ƙofa na yi sallama duk suna zazzaune Inna na kuka tana fyace hanci suna ba ta haƙuri na zauna daga bakin ƙofa na rakuɓe aminiyar Inna ta fara magana “Me ke faruwa tsakanin ki da uwar mijinki Bilkisu? Uwar miji ai uwa ce in za ka tozarta taka uwar ina ganin ita ma za ka tozarta ta.”

Gabana ya tsananta bugawa jin zancen shi, Inna ta ƙara tsananta kukanta tana rantsuwar za ta bar min gidan don ta gaji da abin da nake mata. Hassan kuma bai gani. Suka ci-gaba da bata haƙuri da yi wa Hassan faɗan uwa ba a bar wasa ba ce suka sallame ni na tashi na koma ɗakina na yi ta sharɓar kuka, don wannan fitina ta ishe ni. Dare sosai Hassan ya shigo kan cushion a falo ya kwanta gari na wayewa da ya dawo sallar asuba ya miƙo min farar takarda wadda zuwa yanzu ta zame min tauraruwa mai wutsiya.

A ƙasa na zauna daɓas na buɗe takardar wadda ya rubuta ya sake ni saki daya ba dan na mishi wani laifi ba sai don neman samun mas’laha da mahaifiyarsa. Na sanya takardar na rufe fuskata na dafe ta da hannayensa “Ni Bilkisu sai yaushe tsugune za ta ƙare min?Kuka ya ƙwace mun na yi mai isa ta Hassan ya tsaya kaina “Ki yi haƙuri Bilkisu, ba a san raina na rabu da ke ba na yanke wannan hukuncin ne duk da tsananin shi a gare ni don in kwantar wa da mahaifiyata hankali.

Idan komai ya natsa zan zo in mayar da aurena. Na buɗe idona da kyau na kalle shi kafin na galla mishi wata uwar harara “Har abada na haƙura da kai Hassan, yau zan bar garin nan ba za ka kuma ganin ko mai kama da ni ba.”

Da gama faɗin haka na miƙe da ma da hijab a jikina na bar ɗakin cikin sauri, ya biyo ni yana “Ina za ki Bilkisu? Ban saurare shi ba na yi waje ina fita mai mashin na kawowa na tsaida shi na haye ban tashi tuna ban fito da ko sisi ba sai da muka isa tasha yan kamasho suka tare mu suna tambayar ina ne na ce mota nake so zuwa Dukku za ta dauki kaya direban da aka kira shi ya sallami mai mashin don za a bata mishi lokaci.

Muka yi ciniki muka taho ina ta fadi a zuciyata zan bar garin gabaɗaya ba zan kuma komawa gidan Gwoggo Maryama ba da ma rabon aure ya kawo ni kuma ya kare shi kenan zan koma gaban babana in rungumi ƙaddarata.

San da muka isa Hassan na tsaye a ƙofar gida ya rungume hannayensa a ƙirji, kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar da yana cikin matsananciyar damuwa. Na sauka na shiga ciki ya biyo bayana, sai da muka shiga ɗaki ya ce “Wai me kike shirin yi ne mai gadon zinare? Na yi banza da shi na soma tattara kayana sai magiya yake min kar in kwashe kayan in koma gidan Gwoggota zai sa ma mana mafita. Da na gama haɗa iya abin da zan iya na fita na kira direban da yaran motar suka shigo suka fara kwashe kayan.

Mutanen gidan duk sun fito sun tsaya cirko-cirko, na wuce Inna a ƙofar ɗakinta tana ƙoƙarin kunna wuta ban ce mata kanzil ba na wuce ta na isa wurin matar Gambo na yi mata ban kwana kamar ta yi kuka take min addu’a ita mijinta tsaye yake don kamar ma tsoron shi take ji don haka ba ta shiga sabgar su.

San da aka gama kwashe kayan ban ga Hassan ba illa dai kudin kudin da ya ajiye na ɗauka na sanya a jaka na shiga gaba muka dau hanya zuciyata kamar ta babbake don tukuƙin da take min kukan zuci nake ga kaina da ya ɗau ciwo.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 6Mutum Da Kaddararsa 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×