Washegari daga islamiyya na wuce gidan Gwoggo Maryama, can na wuni tana ta faɗin kyan da na yi Kano ta karɓe ni.
Sai yamma liƙis na koma gida ina isa kwanciya na yi don wata muguwar kasala da ta lulluɓe ni, sai ga wayar Hassan yana tambaya ta dalilin da ya sa ban shaidawa Inna zan wuce unguwa ba ta wuni da yunwa. Jin muryarsa cikin zafi ya sa na kwantar da murya na bayar da haƙuri, bisa tilas kuma na fito na ɗora girkin don kasalar da nake fama da ita har lokacin, ga ɗanɗanon bakina ya canza, girkin da na yi ma ƙamshinsa duk ya buwaye ni.
Ni da kaina nake zargin ciki ne da ni don tun kafin in baro Kano ya kamata in ga al’adata ban gani ba. Haka na yi ta fama ga laulayi da ya dabaibaye ni ga fitinar Inna, duk abin da na yi sai ta kira Hassan ta ce na yi mata kaza shi kuma ya kira ya kama min faɗa.
Rannan na kama mashi kuka don ta ce ban gama abinci da wuri ina barin ta da yunwa. Yana fara min faɗa na fara mashi kuka sai ya yi shiru, can na ji ya kashe wayar. Har na hau gadona ina share hawaye gabaɗaya zama da Innar ya ishe ni kwata-kwata kwana na goma da dawowa amma matsalolinta sun sha min kai, da ma don haka take so in dawo ta uzzura wa rayuwata.
Kiran shi ya kuma shigowa na harari wayar har ta ƙari ɓurarinta ta yanke, ya kuma kira na share hawaye na miƙa hannu na ɗauka ban yi magana ba sai shi ya ce “Mai gadon zinare.”Ban tanka ba ya ce “Kina ji na? Na ɗaga kai kamar yana kallona “Ki yi haƙuri, na san kina yi, ki ƙara kin ji?
Na fara shessheka lallashina ya yi ta yi yana tambayar abin da nake ma kuka na ce “Ni ba ni da lafiya, abincin ma da ƙyar nake yi.” Ya ce “To ki yi haƙuri, me yake damun ki? Na ce “Ba na jin ƙarfin jikina.” Ya ce “Zan sanya miki kudi gobe ki je asibiti.” Na ce “To.”Ko da ya turo kuɗin ban tafi Asibitin ba don ina tunanin na je me zan ce yana damu na ba.
Ina ta dogarawa a haka kwana biyar aka ƙara sai ga Hassan ya dira. Ina ƙofar ɗakina ina girki ya iso kallo ɗaya na mishi na sunkuyar da kaina don Inna ma tana ƙofar na ta ɗakin ta yi shimfiɗa. Can ya wuce har yaran da suka biyo shi da ledoji ya ce su ba ni. Inna ta miƙe suka shiga ɗaki, sosai ya min kyau kwana sha biyar din da muka rabu da shi.
Na karɓi ledojin na kai ɗaki na fitar da kayan ciki na dawo kan girkina. Na gama ina raba wa jikar Inna yar wajen Husainar Hassan mai suna Aliyah ta zo ta ce in bayar da ledojin da kawun su ya zo da su. Na shiga ɗakin na mayar da komai na bata, na kai abincin Hassan ɗaki na ɗauki na Inna na kai mata suna zaune da Hassan na ajiye na juya da na miƙa wa matar Gambo kushin na je na haye don sai da na yi wanka na fara girkin zuciyata ke tashi don ƙamshin girkina da na shaƙa.
Tun ina jiran zuwan Hassan har na sare sai da aka yi kiran sallar magrib ya fito ya nufi masallaci da ya dawo nan ya shigo na gabatar mishi da abinci ya ce ya ci wurin Inna ɗaki muka shiga ya kama ni ya sa a jikinsa wane irin ciwo kika yi, kin rame da yawa Bilkisu? Na ƙara kwantar da kaina a kafaɗarsa na ce “Ba na jin ƙarfin jikina.”Ya ce “Bari a yi ishai sai mu koma asibitin.” Zan yi magana muka ji muryar jikan Inna shi ma a wurin ta yake ya ce Hassan ya zo Inna na kira.
Ya raba ni da jikinsa ya sanya jallabiya ya bar ɗakin, nan ma bai shigo ba sai da ya dawo isha’i yana shigowa ya rufe ƙofar muka wuce ciki, cikin aljihun wandon kayan da ya zo da su ya laluba ya ciro dalleliyar waya samfurin Samsung ya miƙo min “Ga waya mai gadon zinare.”Na yi fara’ar da tunda ya zo ban yi ta ba sai na ɗora da godiya.
“Mu bari zuwa safiya sai mu je asibitin.”Ya ce min na ce mishi “To.” Daga haka kwanciya muka yi muna ji ana buga ƙofa shi ma ya yi kamar bai ji ba ballantana ni. Da safe ina tashi na fara ƙoƙarin yin abin karyawa, Hassan da ma tun yana gado Inna ta aiko kiran shi. Da na gama na kai mata nata ya ce in kawo mishi na shi nan, nan ɗin na kawo mashi na koma ɗaki na ƙudundune ban san iya lokacin da na ɗauka a haka ba sai dai na ji yana bubbuga ni “Tashi Bilkisu.”
Na tashi zaune “Kin karya? Na girgiza kai “Saboda me? Na ce “Idan na ci zuciyata tashi take.” Ya girgiza kai “To me kike ci? Gwoggona tana aiko min da ɗanwake shi nake iya ci, sai da rana in sayi hura, yau ban san me ya sa ba a kawo ba.
“Ya yi murmushi “Anya Bilkisu ba ciki ne da ke ba in sanya rai? Na yi ƙasa da kaina ya ce “To kira Gwoggon a kawo miki ki ci sai mu wuce asibitin.” Ina janyo wayata sai ga sallamar Salim sai da ya gaishe da Hassan ya juyo wuri na “Mama ta ce ki yi haƙuri ba a kawo miki kan lokaci ba.” Na karɓa ina budewa don burina kawai in ga na fara ci Hassan zuba min ido kawai ya yi ganin yadda nake cin ɗanwaken, ya tashi ya haɗa min Tea mai kauri yana daidaita min zafin shi, ganin na ture kwanon ɗanwaken sai ya miƙo min kofin kai na girgiza.
“Ki sha mai gadon zinare. Ya faɗa yana daɗa miƙo min ban son in ta mishi gardama amma tunda na fara laulayi ban iya shan Tea mai madara. Na amsa na kurɓa zuciyata ta tashi kurɓa uku na yi amai ya yunƙuro min da sauri na miƙe na bar ɗakin zuwa banɗaki na yi ta sheƙa amai, da na gama na fito neman ruwa sai Hassan na gani tsaye a ƙofar banɗakin riƙe da bokiti da bota butar ya miƙo min na karba na koma ciki na wanke bakina na dawo don ya bani bokitin in gyara banɗakin ya ce in tafi daki ya shiga.
Ina kwance ina mayar da numfashi ya shigo ya ce Zan iya wanka? Na daga kai sai da na yo wankan ya ce me zan ci to daga na amayar da abin da na ci? Na ce babu komai. Ya ce to in cinye sauran ɗanwaken na ce a’a ya matsa min me zan ci na ce da zan samu koko, ya ce bari ya yi wa Inna magana ko da inda za a samo. Ya fita can ya dawo ya tasa ni Aliyah ta shigo da kokon wanda na yi sa’a da zafi na sha muka tafi Asibitin.
Gwaje-gwajen da aka yi min suka bada sakamakon ciki ne a jikina. Wani irin farin ciki na ga Hassan ciki wanda tunda nake da shi ban taɓa ganin shi cikin shi ba. Haka muka dawo gida ya yi in bar girkin, gudun abin da zai je ya dawo daga Inna na dage zan yi. Ina gamawa kuma na yi ta amai hakan yasa da ya ɗauki na Inna ya miƙa mata ya ce ko su Hajara za su riƙa yin girki daga kusan kullum sai sun zo saboda ban son ƙamshin girkin.”
Ta ce “Sannu mai mata, nan zuwa ka yi gaya min tana da ciki a bar ba ta girki? To ya yi.”Haƙuri ya yi ta ba ta tana faɗa mishi maganganu kaina. Haka ya yi kwanaki ukun da zai yi ina cikin laulayi mai zafi ga Inna da ba ta barin shi ya zauna ɗakina, ya tafi ya bar ni da ita cikin matuƙar gundura da zama da ita. Tun da ya tafi bai kuma samun damar zuwa ba sai da aka kusa wata biyu ya zo da mota wadda Kawu na Kano ya saya mishi duk da ba wata mai tsada can ba ce mun yi murna sosai.
Ya same ni na samu sauƙin laulayi ina cin komai na murmure na yi kyau har na yi masa zancen son zuwa Dukku in gano babana ya ce a’a ba yanzu ba sai na haihu zai kai ni da kanshi. Zagwaɗi mai yawa yake kan cikin nan wannan karon kwana biyu ya yi ya koma sati biyu kuma kacal ya yi sai ga shi ya wuni bai kwana ba ya koma.
Tun daga nan da an tura shi aiki wani wuri sai ya ratso wurina wani irin so yake gwada min da ya kasa ɓoye shi ban ƙara tsinkewa da tashin hankalin da Inna ke ciki ba wadda ke faɗin na karɓe mata ɗa ga duk baƙon da ta yi sai da na je gidan Gwoggo Maryama wuni, sai take bani labarin wata aminiyarta ta saya ma yarinyarta gado mai rumfa da aka ƙawata shi da shimfiɗu na alfarma irin na gidan sarauta amma yarinyar ta ce ba ta so, shi ne take neman mai saye. Na kada baki na ce “Ni kam ina so Gwoggo ki tambaye ta nawa?
Waya ta yi mata ta ce ina so suka yi ciniki ta yi mini ragi sosai na ce su turo acc no suka turo na yi transfer. Washegari sai ga gado an kawo Gwoggo ta yi ma Rahina waya ta ce ta zo ta taya ni kafa gado har ma da matar Gambo suka taya ni sai faɗin kyan da ya yi suke a masu kallo har da Inna har bedroom ɗinmu, a ranar kuma ta ga fridge ɗi na da tsoro ya sa na kai shi bedroom ɗin yaranta ma kowacce sai da ta shigo.
Tun kuma sannan Inna ta ƙara tsaurara mu’amalarmu jin kunnena na ji tana faɗin “Ai wannan ta haihu da shi komai na shi ita zai kwashe ya bai wa. Ni ban ga yana wannan sakarcin wa matarsa ta farko ba da suka yi auren saurayi da budurwa (Bayan ita ta nemo mashi aurenta bai so saboda biyayya ya zauna da ita har ta koma ga Ubangiji) Sai bazawara.
Mai bi ma Gambo Hajara ta ce “Kin ji Inna, to haka za a bar shi, wlh sai kin yi da gaske in ba haka ba ki tura mota ta bule ki da ƙura. Kura da shan bugu gardi da ƙwace kuɗi.” Saurin barin wurin na yi don da ma daga banɗaki na fito na tsinkayi muryoyinsu jin ana ambatar sunana na tsaya. Washegari tunda sassafe ko buɗe ƙofa su Inna ba su yi ba sai ga Hassan ya buga ƙofata. Ba ƙaramin mamaki na ji ba ganin shi ne yayin da na buɗe, muka wuce ciki yana faɗin.
“Abuja za ni mai gadon zinare, ina matuƙar kewar ki dole na ratso in gan ki.” Muna kwanciya aka fara buga ƙofar Hassan kuma bai fasa abin da yake ba har mai bugawar ya haƙura sai zuwa can aka dawo aka ci gaba da bugun har sai da ya gama ya ce in je in buɗe, da na buɗe Aliyah ce ta ce Inna na kiran Kawu. Na koma na shaida mishi ya sanya riga ya fita yana zuwa ta sanya kuka yanzu ita har ta yi lalacewar da zai shigo sai dai da aka fita aka zo aka shaida mata an ga motarsa.
Haƙuri ya yi ta badawa tana fyace hanci ta ce daga wannan ta haramta mishi wannan zuwan ratsen da yake ko zai zo sai wata biyu kamar yadda ya faro da farko. Ya ce mata to. Da ya dawo ɗaki zane na shimfiɗa mashi a bedroom ya yi wankan tsarki don wannan ɗin ma Inna ta yi matuƙar sanya mana ido sai ta riƙa faɗin ya auro jarababbiya za ta tsufar da shi da fitinarta.
Yana gamawa ya goge jiki ya canza kaya ya ce “Zan tafi mai gadon zinare.” Daga nan na yi mishi addu’a ban leƙa ko ƙofa ba gudun leƙowar tawa abin da za ta iya haifarwa. Na koma bedroom na ɗauke zanen da na shimfida wa Hassan na kuma goge wurin na sanya zanen a bokiti na ɗauka zuwa tsakar gida sai da na ƙara dauraye shi na jefa igiya sai ga Hassan ya fito daga dakin Inna yan’uwansa mata na biye da shi wai a safiyar nan har sun iso na san kuma bai wuce a waya aka gaya musu isowar dan’uwan nasu kowacce ta hanzarto ta zo ta samu rabonta, don kowacce tana faɗin abin da take so yana miƙa musu kuɗi.
Ni dai na gama shanyar ban ƙara musu kallo na biyu ba na koma ɗakina. Sati biyu da tafiyarsa muna charting da daddare ya ce “Na gaza barci mai gadon zinare kewarki ta dame ni, anya zan iya kiyaye hukuncin Inna? Dariya na yi mishi na ce “Bin dokar Inna kuwa wajibi.”Ina ta mishi dariya sai na ga ya sauka sai kiran shi ya shigo na ɗaga ya ce “Da safe ki ce wa Inna an muku haihuwa a Kaduna, ba kin ce Gwoggo za ta wurin wani dan’uwan babanku ba a Kaduna?
Na ce E za ta. Ya ce “Ki ce za ku tafi tare zan tsaya daidai GGSS Malumfashi da na shigo zan kira ki ki zo mu wuce. Wani aiki zai kai ni na kwana biyu idan na gama sai in sauke ki.”Na ce “To Allah ya rufa mana asiri kar Inna ta gane.”La