Skip to content
Part 5 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Da asuba anan na yi sallah da na ce mishi zan tafi ya ce “A’a.” Sai zai fita. Haka na zauna har takwas lokacin fitar shi kenan ya ce na sanya ya makara ko gaishe da waɗanda muka zo tare ba zai samu ya shiga ya yi ba. Tare muka fita ya yi waje na koma ciki na samu su Rahina na samu sun bararraje suna kwasar abin karyawa, ta hau yi min tsiya don abokiyar wasa ta ce “Sai muka shafa muka ji shiru mata masu miji an gudu wurin miji.”

Ina tamawa yar’uwar tasu tana dariya ba ta sanya mana baki ba. Na zauna muka karya tare da muka gama muka yi wanka muka shirya muna jiran Haj Asiya ta fito mu yi mata sallama.Da ta shigo muka gaishe ta muka yi mata bankwana ta ce “Ai sai dai su kaɗai za su tafi, ke kam sai kin kwanan mana biyu.”

Ta ba su Rahina kuɗi suka yi mata godiya na rako su har get sai na koma, Hajiyar ta min rakiya part ɗin kawun na gaishe shi sai muka koma wurin ta. Duk yadda take ta ja na da hira na kasa sakewa da ita ita ta hana ni in faɗa wa Hassan ban tafi ba. Sai da ya dawo da daddare ta yi mishi waya ta ce tana son ganin shi ya shigo cikin nutsuwa muna zaune tare da ita ta sanya ni na yi wanka ina ta ƙamshi, cikin kayan da ya ba ni na sanya riga da skirt, da gani ba ƙaramin mamaki ne ya kama shi ba da gani na don da muka yi waya na ce mun sauka. Kallo ɗaya ya yi min ya ɗauke idonsa ya fuskanci Hajiyar yana gaishe ta.

Ta ce “Ka yi mamakin ganin Bilkisu ko? Ni na riƙe maka ita ta ɗan kwana biyu sai ta tafi.” Murmushi kawai ya yi bai tanka zancen ba. Ta ce “Ki kawo mishi abinci.” Na miƙe zuwa kitchen abincin na ajiye an haɗa na ɗauko na kawo gaban shi na ajiye ya ce “Sai dai ai ba ta zo da kaya ba.”Ta miƙe tsam ta shiga wata ƙofa sai ga ta ta fito da kaya “Ga kaya nan sai ka saya mata.” Baki ya kama “Wadannan ai sun fi ƙarfina Haj, wadancan ma ƙuru na yi.”

Ta yi ɗan murmushi “Ni ma zan bayar da gudummawata ta zaɓi biyu, kai kuma sai ka ƙara mata daidai ƙarfin aljihun naka, don ni dai na ga ita ce iyalin da ake wa hidima tunda ba ta gida sai a saya mata kayan kwalliya kawai.”Ya yi murmushi “Akwai Inna a gida.” Ta ce “To haka ne kuma.”Ya ce “Ta ɗauki ɗaya, don wannan kayan na masu da shi ne.”

Ta ce in matso in zaɓa na matsa na zaɓi kala uku ita biyu shi ɗaya na yi mata godiya shi ma ya yi.Ta miƙe da sauran ta ce mana mu kwana lafiya.Na kwashe kwanonin da ya ci abinci na kai kitchen sai muka tafi.Da safe muna kwance don ranar ta kama Lahadi ranar ce kuma kaɗai yake hutawa a gida.Wayarsa ta ɗauki ƙara ya ɗaga ni kuma na yi fakare jin muryar Inna tana complain din rashin dawowa ta.

Ya ce Haj Asiya ta hana ni dawowa wai sai na ɗan kwana biyu.Ta ce to su fa abin da za su ci daga an hana ni dawowa? Ya ce ya kira yaron da ke mishi tsaro zai ci-gaba da zama yana kawo mata abin cefane kafin a yi albashi. Ƙwafa ta zabga ita kuma ba ta da ranar dawowa? Ta kashe wayar Ƙara lafewa na yi kamar barci nake.

Sai goma muka yi wanka anan aka kawo mana abin karyawa muka karya ya ce mu je ya raka ni in gaishe da sauran matan kawu, muka fito a ƙofar sasan ya tsaya ya ce in shiga part ɗin uwargidan, wata mai aikinta ta yi min jagora har falon da take tana hakimce ta cika kujera sai shan ƙamshi take kamar ba ta so ta amsa gaisuwata duk da bayanin da mai aikin ta yi mata daga Malumfashi nake kamar yadda na faɗa mata, na tashi na fito.Ita ma ta biyun duk kanwar ja ce yar ji da kai ce. Muka koma wurin Hassan ya kwaso suturunsa masu datti yana wankewa ina mishi dauraya in shanya muna hira. Kwanakin da suka biyo baya da kaina nake shiga kitchen in yi wa mijina girki irin wanda nake so kamar yadda Hajiyar ta ba ni dama.

Muna hira a falonta da ni da ita da Hassan yake faɗa mata matakin karatunsa da abin da ya karanta.Ta ce ai ba ta sani ba, ita kirkin da na yi musu da suka zauna ɗakina shi ya sa ta yi wa kawu magana ya ɗauko Hassan ya sanya shi cikin ma’aikatan da zai zuba a sabon super market ɗin da ya buɗe, amma yanzun ma za ta yi mishi magana za a samar mishi aikin da ya dace da karatunsa.Sosai Hassan ya yi mata godiya ni ma da ta koma ɗakinta na bi ta na yi mata ta ce kar in damu Allah ne ya haɗa jinina da nata.Tana karbar aikin kuma kawun ya kira Hassan suna tare da ita, ya ce

“Kai ba ka ce wa ga abin da ka karanta muna kiran bare suna cin arziƙi.” Hassan dai ya yi shiru don bai san sau nawa ya turo mishi saƙo na roƙon ya ɗauke shi aiki ba.Ya ƙara da cewa “Gobe za ka fara aiki tare da ni, akwai wasu ginin gidaje da zan yi ina so ka fitar min da tsarin ginin.Ya yi godiya ya tashi ya tafi.Ta waya ya kira ni na same shi ɗakinsa ji na yi mutum ya rungume ni tsam yana juyawa da ni yana dariya “Na ce “Wayyo numfashina.”Ya sake ni yana min wani irin kallo “Na ce “Me ya faru? Ya ce “Albishir?Na ce goro fari.” Ya ce “Alheri ne ya kuma samu na, irin wanda nake ta samu tunda na aure ki.

Murmushi na yi na ce “To faɗa min da sauri. Sai da ya zaunar da ni kusa da shi a gefen katifa ya faɗa min yadda suka yi da kawun, na ƙankame bayansa ina murna na yi mishi addu’a sosai ta fatan alheri da ƙyar muka haƙura da farin cikin ya yi wanka ya shirya ya wuce wurin aiki daga sai gobe za su fara fita da kawu.Washegari suka tare ɗayan washegarin da rana ina tsaye a bedroom ɗin Haj Asiya ina shirya mata kayan da mai guga ya miƙo ta bani ta ce in shirya mata ita kuma tana tsaye gaban dressing mirror tana ƙara duba kwalliyar da ta caɓa fita za ta yi.

Wayarta da ke gefen ta ta ɗauki ƙara sai da ta zauna bakin gado ta amsa da yadda na ji tana wayar na gane da kawu ne sai da ta gama ta fuskance ni tana murmushi “Alh ne, ya yaba ƙwarai da ƙwarewar mijinki wurin fidda tsarin gini. Ni ma murmushin na yi a raina ina faɗin”Alhamdulillahi.”

Da Hassan ya dawo cike da farin ciki ya dawo yana bani labari bayan kawu akwai abokinsa da ya zo daga Abuja shi ma ya yaba ƙwarai da bayanin da ya ji Hassan na yi ya ce idan zai wuce Abuja gobe zai wuce da Hassan akwai kwangilar wasu gine-gine da aka ba shi Hassan ɗin yake so ya fitar mishi da tsarin ginin su.Washegari tare da Hassan ɗin suka wuce duk da kewar shi da ta kama ni bai hana ni in ta yi mishi addu’a ba.

Sai da ya shafe sati guda ya dawo na gyara ɗakinsa fes na sanya turaren ƙamshi,duk da ba komai ba ne a ɗakin daga katifa sai wardrobe ta jikin bango.Ni na shiga kitchen na yi mishi kalolin abincin da na san yana so na je na jere su a dakinsa. Wajen biyar saura ya shigo sai da ya fara zuwa ya gaishe da Haj Asiya wadda aka yi rashin sa’a ta fita.Wani irin kyau na ga Hassan ya ƙara duk da tun zuwa na dama ya soma canzawa. Sai da ya yi wanka ya ci abinci muka zauna kan katifa rabin jikina na jingine jikinsa labarin Abuja yake ba ni da daular da ya gano sai alert da ya nuna min na kuɗin da ya samo a can da kuma na aikin da ya yi wa kawu har albashinsa na super market ɗinsu an sanya mishi don san da ya bar aikin wata ya ƙare.

Nan da wata guda kuma Alhajin ya ce zai kuma neman shi. Ya zaro complimentary card da ya ba shi, ya ƙara da cewa “Gobe kuma za mu fita tare da kawu, shi ma wani aikin ne Bilkisu.”Na ce “Alhamdulillahi Allah ya ƙaro arziƙi.”Ya ce “Amin, lokaci ya zo mai gadon zinare,zan rama miki halarcinki a gare ni, zan jiyar da ke daɗi zan mayar da ke macen kallo cikin mata yan’uwanki.”

Na ƙara kwantar da kaina a kafaɗarsa ya yi sauri ya sa hannu biyu ya rungume ni.Da ƙyar na samu ya bar ni da magrib na koma part ɗin Haj Asiya, don cewa ya yi in bari kawai sai gobe idan ya fita na koma. Da na samu ya bar ni kuma cewa ya yi yana dawowa Isha’i in dawo.

Da ya dawo can ya same ni ya gaishe ta suka taɓa yar hira na kawo mishi abinci anan ya ci sai muka tafi.Ya dawo sallar asuba ina kan sallaya riƙe da Alƙur’ani, kwanciya ya wuce ya yi sai da na idar da karatun na yi addu’o’ina na zame hijab ɗin na hau katifar ina gaishe shi maimakon ya amsa jikinsa ya janyo ni ya fara yamutsa ni wayarsa ta ɗau ƙara ya kai hannu yana tsaki sai dai ganin sunan da ke jikin screen ɗin na ga ya yi saurin gyarawa ya fara gaisuwa cikin girmamawa sai maimaita ki yi haƙuri Inna yake.

Can ya ce “Ba haka ba ne Inna,ki yi haƙuri, ni na isa in zaɓi wata a kanki? Ki yi haƙuri za ta dawo.”Sai ya yi shiru cikin saurare can ya nisa ” Yau kuwa, ki yi haƙuri.”Ya ajiye wayar na kai dubana gare shi na ga yadda duk ya wani birkice yanzu- yanzu.Ya raba ni da jikinsa ya miƙe “Ina zuwa Bilkisu.”Jallabiyar da ya tuɓe ya mayar sai ya bar ɗakin.Na tashi zaune na jingina da bango cikin tunani ko me Innar ke cewa? Na daɗe ganin bai dawo ba na gyara ɗakin na kulle sai na bar wurin.

Ban saurari abin karyawa da mai aiki ta ce min an kammala ba na shige ɗakin da aka sauke mu farkon zuwa na na hau gado, juyi na yi ta yi har na gaji sai na miƙe na shiga bathroom na yi wanka na fito ina kwalliya sai ga Hassan ya shigo, abin ya ba ni mamaki daga bai taɓa yin hakan ba “Bilkisu.” Ya kira sunana na amsa ina mayar da hankali a kan shi “Ki yi haƙuri yau za ki koma gida.

Ga mota can na samo da duk abin da za ki buƙata.” Ya laluba aljihu ya ciro kuɗi yan ɗari biyar masu ɗan dama “Ki riƙe wannan a hannunki sai na zo.”Na saki wata ajiyar zuciya da ta kwace min ina cike da tambayoyi sai dai ban san me zan ce mishi ba na ce “To.”

Yana tsaye na sanya doguwar riga, na gama shirina na shiga kintsa kayana cikin wata madaidaiciyar jaka da ya kawo min ina gamawa ya amsa ya rufe ta sai ya ɗauka ya bar ɗakin.Na fito na samu Haj tsaye fuskarta ba annuri na ce “Zan tafi.” Ta ja tsaki tana girgiza kai.

“Ban da ya ce mahaifiyarsa da ba inda za ki, me za ki koma ki tsinta a can mijinki na nan?Ni dai na yi shiru ta ce in zo mu je in yi wa Alh sallama muka je na yi masa duk da na rasa me ya hana shi fita har wannan lokacin. Da muka koma wurin ta abubuwa da dama ta bani na yi ma masu aikinta sallama, muka fita tare da ita sai ga Hassan, ganin mu sai ya juya muka tafi har bakin gate inda motar da ya ɗauko take, baya na shiga suka yi min fatan sauka lafiya.

Mun ɗauki hanya ina ta tunanin abin da Inna ta gayawa Hassan da ya sa ya tarkato ni ba shiri. Tafiyar awa guda ta kai mu Malumfashi, lokacin rana ta take ƙwanyar, garin ba ko wadatar jama’a saboda tsananin rana. Ina nuna mishi hanya muka isa har ƙofar gidan na fito na tsaya ya fito min da jakata, sai na ga Boot fal da kaya ya soma ciro su buhun shinkafa carton din taliya sugar, maggi, sai wata bagco da na ga nama cike a ciki sai wata ledar mai dauke da kayan Tea, ta karshe ce mai dauke da su tumatur tarugu tattasai da albasa.

Yaran da ke zaune cikin shagon Hassan na yi ma magana suka shigar min da kayan cikin gida, ba kowa tsakar gidan sai uwar rana da ta ƙwalle na san ita ta kori mutan gidan na buɗe ɗaki suka shigar min da kayan sai na fito na rufe shi na wuce wurin Inna, ina ta sallama shiru sai can na ji an amsa na shiga ba kowa a falon na wuce ciki suna zaune ita da yaranta mata sai na ji duk na muzanta da irin kallon da suka ƙure ni da shi na zauna a ƙasa na shiga gaishe da Inna ta amsa da yanayin ta na kodayaushe.

Hajara ta dube ni “Lallai daga zuwa suna sai aka samu wuri.”Ban ce mata komai ba na ce musu ina wuni su dukkan su na miƙe na fito.Ɗakina na gyara da ya yi matuƙar ƙura, matar Gambo ta zo muka gaisa, lokacin da na gama na gaji ƙwarai sai na kwanta na tashi don yin girki wanda ban da tsoron abin da Inna za ta ce da ban yi shi ba.

Na tasa uban nama na rasa yadda zan yi da shi wanda na gane tinkiya ce ko rago aka gyara, ni ba fridge ba.Ina cikin girki wasu matasa suka shigo da sallama suna ɗauke da madaidaicin fridge sabo gadagal a kwali.

Suka ce an ce su kawo ma matar Hassan na ɗauko wayata in kira Hassan sai na samu saƙonsa cewa za a kawo min fridge.Na yi ta murna na kira shi na yi mishi godiya.Naman sosai na zuba wa Inna a abincinta na ɗauka na kai mata sai na samu sun bararraje suna cin gasashshiyar kaza, na ajiye na juya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 4Mutum Da Kaddararsa 6 >>

1 thought on “Mutum Da Kaddararsa 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×