Skip to content
Part 4 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Washegari kwana huɗu kenan da mutuwar Inna ta aiko in je na tashi na tafi. Tana zaune a ƙuryar ɗakinta da ta dafa daga shi mijin naki ba zai iya gaya miki ba, idan ta ƙare ta garar ba shi zai riƙa saye ba? Meye a ciki don kin bada abincin gararki? Na amsa mata na tashi na tafi sauran shinkafar garata na janyo na fito da ita na kai ɗakin Inna. Sati da ya cika aka tashi zaman makokin.

Tun kuma da aka tashi na lura akwai damuwar da ke damun Hassan wadda idan na tambaye shi sai ya ce babu komai, har sai da ya ga ni ma na fara shiga damuwar.

Ranar ya tashi shago da daddare ina kwance kan prayer mat inda na idar da shafa’i da wuturi na ji an ɗan buɗe window na kai idona wurin sai hannun Hassan na gani bakar leda ya jeho ta faɗo tim sai ya wuce na miƙe na leƙa ta window ɗakin mahaifiyarsa ya wuce cikin sauri da wata ledar a hannunsa murmushi na yi a raina na dawo na ɗauke ledar na ɗaura saman wani ɗan stool ina tuna maganar Inna da na saurara kwanaki tana faɗi ma wasu baƙinta.

“Ai Hassan ɗan albarka ne sai ya sai min nama bai saya ya kai ɗakinsa ba.”Ya ɗan jima sannan ya shigo na yi mishi sannu bai jira na juye mishi ruwan wanka ba ya juye ya fita ya yo wankansa sai da ya kintsa ya zauna “Ba ki ci naman ba Bilkisu? Murmushi na yi ban yi magana ba ya bude naman “To Bismillah zo ki ci mai gadon zinare.”

Murmushin na ƙara na matsa na ɗauka na fara ci ya ce “Ki yi haƙuri yaushe rabon da in sai miki nama.”Wani kallo na yi mishi mai kama da harara sai na ci-gaba da cin naman. Sau uku kawai ya ɗauka sai ya bar min ko da na yi mishi magana ya ce ni ya sai ma wa.

Da safe ko da muka tashi duk da tun dare bai shigo da damuwar da ya saba shigowa da ita ba komawa ya yi ya kwanta ƙafafuwansa na ƙasa idanuwansa na kallon rufin ɗakin.

Ina shigowa sai na yi turus na zo na leƙa fuskarsa sai na ga idonsa biyu na zauna kusa da shi na kai hannuna a hankali cikin na shi “Me ya same ka? Me ya sa ba za ka faɗi min damuwar ka ba?”

Firgigit! Ya tashi zaune yana ƙaƙaro fara’a “Ni ba ni da wata damuwa.”Na haɗiye miyau “Shi kenan daga ba za ka faɗi min ba.”Na miƙe don barin ɗakin, ya janyo hannuna na faɗa kanshi kafin ya kai ga magana wayarsa ta ɗauki ƙara a tare muka kai ido inda take na miƙa hannu na ɗauko ta na miƙa mishi baki buɗe na ji ya ambaci kawu ganin sunan da ke yawo kan screen ɗin wayar.

Ya latsa sai ya kai ta kunnensa ya soma gaishe shi cikin girmamawa da ya ƙare gaisuwar sai ya yi shiru cikin saurare karshe na ji yana godiya, gefen shi ya ajiye ta “Kawu na Kano ne ya kira ya nemi in tafi Kano yau zan kulan mishi da wani sabon super market da ya buɗe.” Na ce “Ma sha Allah. Ina taya ka murna.”

Ya cigaba “Kin san tunda na kammala karatu da na buga ban samu aiki ba na nemi ya samar min aiki a wurin sa to na dai yi ta bi ban samu ba har na haƙura,don babban ɗan kasuwa ne bayan manyan runfunan da yake da su yana kuma harkar gine-gine ya gina ya sayar.”

Na gyada kai Alhamdulillahi. Allah ya sa alheri.” Ya mike don zuwa ya sanar da Inna sai da ya dawo ya ce “Kin san dalilin shiga ta damuwa a yan kwanakin nan? Na girgiza kai “Zaman makokin nan da aka yi ranar da aka yi rasuwar ranar za ni kasuwa don kayana sun yi ƙasa, kwatsam aka yi mutuwar nan kuɗaɗen su na yi ta kashewa ƙarshe har sai da na ciyo bashi, shi ne abin ya dame ni. Ina komawa shago dan cinikin da nake yi su nake harhaɗawa don biyan bashi don alƙawarin sati guda na yi.

To kin ga Allah Almusawwiru ya kawo min wata hanyar.” Na ce “Allah abin godiya.”Sai kuma na narke fuska ya ce “Meye? Na ce “Za ka tafi ka bar ni.”

Ya ce “Ba ke kaɗai ba,ni ma zan ji a jikina tafiya in bar ki. Amma ya za mu yi? Bari in je in dawo.”Na ɗaga ido ina duban shi “Ina za ka? Ya ce “Wani abokina zan gani, zan ɗan samu abin da zan bari a gida.”Na ce “In don wannan ba sai ka ciyo bashi ba.” Na isa jikin drawer ta ta gado na buɗe na ciro kuɗi na dawo gaban shi na miƙa mishi.””Ga su ka yi amfani da su, ranar bakwai da Gwoggo Maryama za ta dawo gaisuwa ta zo min da su juya min ake to mai juyawar ya dawo da su.”Ya yi ɗan jim “Ki riƙe kuɗinki Bilkisu.”

Na yi saurin duban shi “Wai me ka ɗauke ni? Daga haka na juya na mayar da kuɗin na kama hanya zan yi tafiyata.”Ɗauko su Bilkisu.”Ba musu na koma na ɗauko na dawo inda yake zaune ya kirga kudin sai ya cire dubu biyar ya ba ni sauran “Ki riƙe su a hannunki kina hidimar gida da su, wadannan dubu biyar ɗin kuma zan kaiwa Inna. Ki dinga abinci kina ba ta. Zan ba ki kuɗinki da na samu, haɗa min kayana.”Cikin sanyin jiki na miƙe wata jaka tawa na dauko na shirya mishi kayan a ciki sai da na haɗa mishi duk abubuwan da ya bukata sai ya yi wanka ya shirya, zuwa lokacin gaba ɗaya jikina ya saki don tunanin yadda zai tafi ya bar ni daga ni sai su Inna.

Da na ce idan ya tafi sai yaushe? Cewa ya yi shi ma bai sani ba sai ya je ya gani. Bayan wucewar shi kuka na yi ta yi kafin na ba kaina Haƙuri na fito na kama harkar gaba na.Da na san ba ni da kayan tea Inna ma ba ta da su gero na bayar aka sawo mini da wake, da gari ya waye zan dama in wanke wake a markaɗo min in soya ƙosai in kai wa Inna da jikokinta, da ke gabanta in gama ayyukana in tafi Islamiyya, idan na dawo sai in ɗora girkin rana.

Waya sosai muke yi da Hassan kodayaushe cikin tambayata yake ba matsala in ce babu. Shi kuma ya yi ta fadi min yadda al’amura suka kasance a nashi ɓangaren, idan na ce yaushe zai zo sai ya ce kin san yanzu ina ƙarƙashin wani ne ba zan yanke ranar da zan zo ba.

Har ya kwashe wata guda bai zo ba sai dai an yi mishi albashi ya turo mana kudi ni da Inna ni ya ce in riƙe saboda hidimar gida, sai kuma rabin kuɗina rabin ya ce sai an kuma wani albashin zai cika min. Kwanan shi arba’in muka yi waya da Gwoggo Maryama yarinyarta da ke aure ta haihu washegari na je na yi mata barka da muka yi waya da Hassan kuma na ce za ni suna murmushi mai sauti ya yi ya ce.

“Ai ko don in gan ki ba zan hana ki ba. Ana gobe suna muka tafi gidan mai jegon a Tudun Yola yake da muka yi waya da Hassan ya ce yana nan zuwa da daddare idan ya tashi wurin aiki, sai dai bai samu zuwa ba sai washegari ranar suna kenan da daddare sai ga shi da wani abokin aikin shi a mashin ɗin wancan ɗin, ba su daɗe ba suka tafi, ya jaddada min gobe in tafi gidan kawunsa idan na kwana sai in koma gida. Sai dai da na shirya zan tafi Rahina yarinyar Gwoggo Maryama ta biyu mai bi ma mai jegon ta ce za ta bi ni, da ma kwana uku za ta yi sai wata ƙanwar babansu bazawara ta ce ita ma za ta don haka mu uku muka rankaya zuwa Hotoro.

Keke nafef muka ɗauka Hassan ya yi wa mai keken kwatance har muka isa, na kaɗu da ganin gidan da muka tsaya wai kuma shi ne na kawun Hassan, ban gasgata ba sai da na kuma kiran Hassan ya ce E gidan ne, bari ya turo min lambar amaryar kawun in kira ta za ta turo a tafi da mu.Hakan aka yi daga kiranta ba ɓata lokaci ta turo wata dattijuwa da alamu ke gwada mai aiki ce.

Duk yadda muka so kannewa sai da muka bi harabar gidan da kallo don tsananin girman shi da motoci na alfarma da aka ajiye uwa uba yadda aka tsara ko’ina, yamma da gidan ta nufa da mu wani ƙayataccen gini ne hawa ɗaya ta shigar da mu, “Aljannar duniya.” Shi Rahina ta furta yayin da muke kai mazaunanmu don zama haɗaɗɗen falon da tsayawa faɗin ƙayatuwar da ya yi zai zam kamar ɓata baki ne.

Wata daban mai matsakaitan shekaru ta shigo ta ajiye mana wani ƙaton tray ta juya sai ga amaryar kawu ta shigo cikin matuƙar fara’a muka gaishe ta ta yi ta jan mu da hira kafin ta fita ta ba mu damar taɓa kayan maƙulashen da aka ajiye mana muka yi sallah. Muna idar da sallar Isha’i ita da kanta ta kaimu wani daki su Rahina suka yi ɗaiɗai bisa luntsumemen gadon, ni kam ba zan iya barci ban ga Hassan ba na dai kwanta ne kawai, ba mu jima ba barci ya yi awon gaba da su.

Na lumshe idona cikin tunani, motsi na ji ya sa na buɗe idon “Bilkisu.” Na ji ta kira sunana na amsa a hankali sai ta yafuto ni ganin ta juya na tashi na bi bayan ta step ɗin bene ta fara takawa ina biye da ita har muka isa wani falon da ya fi na ƙasa haɗuwa sai ta tsaya.

“Mijinki ya dawo, bai kuma kamata duk daɗewar nan da ya yi ba ku tare ki zo kuma ki tafi.”Z ta ba ni “Ki yi wanka ki shirya ki je ki same shi.”

Ba tare da na ɗago ba na kaɗa kai, bedroom ta shigar da ni ta nuna min bathroom ta ce in shiga in yi wanka hatta ruwan da zan yi amfani da shi an haɗa min na yi wanka ruwan na ta fitar da daddaɗan ƙamshi. Na tsane jikina mirror ta nuna min ta fita na murza maimasu dadin ƙamshi da turaruka na murza hoda na sa wet lips wasu kyawawan rigunan barci ta ajiye min na zaɓi ɗaya pink color don guda shida ne. Na yi ta duban kaina don kyan da na ga na yi. Sai ga ta ta shigo.

“Kin yi kyau.” Ta faɗi tana murmushi ni ma murmushin na yi “To zo mu je Larai ta raka ki.” Abin da ta ce min kenan ta fita ɗakin. Na fito na samu suna waya da wadda ta kira Larai, ba a jima ba dattijuwar da ta yo mana jagora zuwan mu ta hauro saman, cikin girmamawa ta gurfana ta ce ta yi min rakiya dakin Hassan tana gaba ina biye da ita da muka sauka na ce mata bari in ɗan shiga ɗaki, ta jira ni na dauko hijab sai na fito tafiya muka yi sosai don ma gidan ko’ina haske ne tarwai kamar rana. Boys questers anan Hassan yake ta juya na ranƙwashi ƙofar da ta nuna min daga ciki na ji an ambaci “Waye?

Na ƙi magana sai ma gyara tsayuwa da na yi na ƙara taɓa ƙofar ya ƙara tambayar waye sai sannan na ce “Ni ce.” Gane ba zai yarda ya buɗe ƙofar ba matuƙar bai san waye ba.

Takun tafiya na ji sai ya buɗe hannunsakawai ya miƙo sai ya sanya ni ƙirjinsa ya ƙankame ni ya rufe ƙofar muka dire kan ƙatuwar katifar da ke yashe tsakar ɗakin “Allah ya yi wa Haj Asiya albarka, don na san aikin ta ne.”

Ya faɗi yana kara maƙale ni murmushi na yi sai kuma ya sake ni ya miƙe na raka shi da ido wardrobe ɗin jikin bango ya buɗe ya shiga fiddo wasu kaya “Taso ki gwada Gimbiya Bilkisu.”

Murmushi na saki jin sunan da ya kira ni riga da wando ne wasu masu kyau sai riga da skirt sai doguwar riga duk sai da na gwada yana yaba kyan da suka yi min “Haj Asiya ta sanya ni na saya miki.” Har muka kwanta yana faɗin kirkin amaryar kawun nasa na ce “Ni ma na ga kirkinta ta amshe mu hannu bi biyu, ina sauran matan ko ba anan suke ba?

Ya ce “Kowacce na wurin ta, ita ɗin ce dai mai taron mutanen kawu ko da suke cewa don ta ƙara samun shiga wurin shi ne take yi, to ko don hakan ne ni kam ta kyauta min ƙwarai tunda na zo sai dai in na dawo in samu abinci ta sa an kawo min, ga wannan babban karamcin turo min ke da ta yi.”

A raina na ce “In dai dangin miji ne ai ba a yi musu abin kirki.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 3Mutum Da Kaddararsa 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×