Skip to content
Part 3 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Sai da ya gama zantukansa na ce “Ka shirya aurena Hassan? Ya dube ni da idanuwansa da suka canza don damuwa ya ce “E” Na ce “To ka je ka zo da abin da Allah ya hore maka ka aiko gidanmu, ba komai nake gudu ba a aure ni a sake ni.” Sai na fara mishi kuka. Rarrashina ya shiga yi da alƙawura na irin ruƙon da zai min matuƙar ya dace da samu na.

Muka yi sallama na koma ciki sai dai na kasa faɗi ma Gwoggo shawarar da na yanke ta har sai da Hassan ya yo aike na sadaki Naira dubu hamsin ta fara faɗa ya za a yi ya kawo ba a sanya shi ba? Sai aka kira ni falon babansu Bilkisu na ce ni na ce ya kawo. Wani kallo ta rinƙa yi min baki buɗe shi kuma ya ce in tashi in tafi. Na koma ɗaki na kwanta Gwoggo ta shigo hankalinta a tashe “Me zai sa ki yanke wa kanki wannan ɗanyen hukuncin Bilkisu? Ga irin mijin da kowace mace ke so kin samu, mijin da za ki fanshe wahalar da kika sha a baya har na kusa da ke ma ya huta, za ki yi ma kanki wannan santattar.”

Sai da na ji ta numfasa na ce “Gwoggo ki yi haƙuri na gaji da zawarci a yan ƙananan shekaruna ina jin tsoron faɗawa inda za a kuma sako ni. Ina ta addu’a na yi istikhara amma ni dai mutumin nan ya ƙi kwanciyar mun sai Hassan ki yi min addu’a Gwoggo.”

Ta gyaɗa kai “Shi kenan daga hakan kika zaɓa.” Ta juya ta bar ni cikin tunani. Gwoggo ta hana a sallami Yallaɓai tana ta lallaɓa ni ko za ta ciyo kaina amma na tsaya akan a sallame shi kawai. Da baban su Bilkisu ya aika mishi da saƙo ya kuma nemi za a maido mishi da abin da ya bani ya ce ya bar min.

Ranar Gwoggo Maryama ta yi baƙin ciki ko babana kasa kira ta yi ta faɗa mishi zancen auren nawa, sai babansu Bilkisu ne ya kira shi. Shi kuma ya ce ya damƙa komai na auren nawa a hannunsa ba sai an je Dukku ba amma babansu Bilkisu ya ce sai Hassan ya je Dukku ya gaishe da mahaifina.

Hakan aka yi shi da abokansa biyu suka yi tafiyar kuma da ya dawo ya nemi a sanya rana baban Bilkisu ya tambayi Gwoggona yaushe ta ga za a sanya ta ce sai ta shirya. Shirin ta fara yi a hankali wanda Hassan har ya damu kullum sai ya ce min “Ki roƙi Gwoggonmu ta sanya ranar nan a matse nake in ga kin zama mallakina mai gadon zinare. Ban iya hana kaina murmushi idan ya kira ni da mai gadon zinare.

Gwoggo dai ƙin sanya ranar ta yi har sai da wata rana da La’asar muna shan iska a barandar gidan ni da Gwoggo da Salim, ranar ta kama Alhamis littafin akhdari nake dubawa Gwoggo na latsa wayarta.Wata dattijuwa mai matsakaicin jiki ta shigo da sallama gabaɗayan mu muka amsa Gwoggo ta nuna mata gefen shimfiɗa ta zauna suna gaisawa da suka ƙare gaisuwar ni ma na miƙa mata tawa.

Ta fuskanci Gwoggo sosai “Na san ba ki gane ni ba Haj Maryam, mahaifiyar Hassan ce mai son yar gidan nan. Jin zancen ta na yi saurin miƙewa na wuce ciki ina ji tana cewa “Ita ce Bilkisun? Na daɗe a ɗaki kafin Salim ya zo ya ce Gwoggo na kira na na ce “Bakuwar ta tafi ne? Ya ɗaga min kai na miƙe ina mayar da ɗankwalina da ya zame daga kaina na bi shi a baya.

Tana zaune a inda na bar ta na zauna ta dube ni fuskarta ba yabo ba fallasa “Mahaifiyar Hassan ce ta zo roƙo a tsaida ranar da za a ɗaura aure.”Shiru na yi ina jiran jin ranar da za ta ce ta sanya sai ta ce “Na ce ta je za a sanya da zarar mun ƙare shiri.”Wasa gaske sai da mahaifiyar Hassan ta kuma zuwa biyu tana roƙo sai kuma da babansu Bilkisu ya nuna ma Gwoggo ɓacin ransa sannan ta sanya sati biyu, kafin zuwan sati biyun kuma Gwoggo Maryama ta sawo min saitin kaya na gani a faɗa kuɗaɗen waɗancan kayan nawa da ta bayar a juya min sai ta rage dubu talatin ta ce a ci-gaba da juyawa Da kuɗin da Yallaɓai ya yi ta ba ni da dubu hamsin ɗi ta ta sadaki ta haɗa. Ya rage saura sati ɗaya Hassan ya kawo min wata dubu hamsin ɗin ya ce in yi haƙuri bai samu haɗa min akwati ba in sayi kaya.Da na kai wa Gwoggo ƙwafa ta yi ta ce “Dubi abin da kika ja wa kanki Bilkisu.”

Labulai da zanen gado ta saya min da kuɗin, don suturun da Yallaɓai ya ba ni su ta bayar min ɗinki ɗinki kuma na musamman. Saura kwana huɗu ɗaurin aure ta ce in shaida mishi za a je a yi jere cewa ya yi in ba ta haƙuri ba a gama gyaran ɗakunan ba. Don haka sai ranar ɗaurin aure aka je aka gyara min ɗaki.

*******

An ɗaura aure mutum biyu suka zo daga Dukku. Mamana sai ta waya na faɗi mata. Da daddare aka miƙa ni ɗakin Hassan, gidan ginin ƙasa ne da ka shiga zaure za ka tarar sai ya sa da ka da filin tsakar gidan ɗakina yana kallon zauren an yi runfa a kofar ɗakin ciki ne da falo masu girma an kuma matuƙar gyara su, bayan shafe su da aka yi da siminti an yi musu fenti na zamani, kana yin Gabas kuma nan dakin mahaifiyarsa yake sai gaban nata dakin dakin ƙanensa Gambo da shi ma ke zaune da matarsa, abokiyar haihuwar Hassan mace ce tana aure a cikin gari.

Yana da yaya ɗaya da ƙanne mata uku duk sun yi aure. Minti talatin da fitar masu kawo ni Hassan ya shigo ya yi kyau ƙwarai cikin farar shadda, ina zaune a kujera ta zaman mutum ɗaya na sha kwalliya ba magana ga ƙamshi na musamman ina yi .Tsayawa ya yi daga inda yake riƙe da baƙaƙen ledoji guda biyu yana aiko min da wani irin kallo kallo ɗaya na yi mishi ganin irin kallon da yake min sai na sunkuyar da kai, daga indj a yake ya ajiye ledojin ya tako gabana malum malum ɗin jikinsa da ban san san da ya tuɓe ta ba ya ɗora saman jikina ƙamshin da take yi ya shige cikin kofofin hancina, hannuwansa duka ya sa ya tallafo ni ya miƙar da ni tsaye sai ya sanya ni jikinsa ina jin ajiyar zuciyar da yake fiddawa, kafin ya shiga jera min kalaman ƙauna da alƙawura masu yawa a cikin kunnena.

Mun dade a haka kafin tsayuwar ta fara neman gagarar mu ya zauna tare da ni kan two sitter ya tuɓe yar ciki da wandonsa ya rage daga shi sai boxer da Singlet kai na kauda ya sauka ƙasa ya buɗe lodojin kan plate ɗin da ya je ya dauko hannu ya sa ya ruƙo ni wani abu na riƙa ji kamar shi ne rana ta farko da wani namiji ya taɓa ni.Duk yadda ya so kaɗan na gutsiri kazar da ya shigo da ita da ke ta fitar da tururi da ƙamshi mai daɗi.

Nan na bar shi zaune na shiga ɗaki na tuɓe kayan jikina na mayar da wata riga mara nauyi sai na haye gado ban koma falon ba.Ko gajiya ya yi da jirana sai ga shi ya leƙo.

Ya ce “Au kwanciya kika yi kika bar ni?Ya shigo gabaɗaya ya tsaya kaina yana dubana na rufe idanuwa da ƙarfi ya juya sai na ji yana rufe ƙofa ya kashe fitilar ya kunna wata charger da ya shigo da ita ya hawo gadon sai ya sanya ni jikinsa. Abin da ya faru a tsakanin mu a wannan dare masu tsayawa a rai ne sam ya hana mu mu runtsa sai da dare ya raba abin da ya ja muka makara, ni dai cikin barcin na ji ana buga ƙofa kamar za a karya ta na zare jikina daga na Hassan na sauka na fito na zo falo na ji yo muryar dattijuwar tana kiran sunan Hassan tana faɗin Me yake yi har gari ya waye bai fito ba?

Da sauri na koma ciki na same shi zaune daga shi sai boxer, na miƙa mishi jallabiyar da ya ajiye a daren jiya ya zura sai ya miƙe.Daga ƙofar bedroom ɗin na tsaya ina ji ya buɗe ƙofa ta ce mishi. “Kanka lafiya yau ba ka fito sallah ba? Daga zuwan mace za ka biye mata.”

Gabana na ji ya buga na koma bakin gado na zauna ya dawo ya dauki sabuwar Kettle ɗi ta ya jona, yana fara zafi ya juye a buta sai ya jona wani sai ya bar ɗakin, da ya dawo pray mat ya shimfiɗa ya gabatar da sallah sannan ya juye ruwan a bokiti ya surka sai ya fita da shi, da ya dawo ya kwatanta min inda makewayin yake.Dogon hijab na sanya na fita ɗakin a ɗarare.Sai da na yi wankan tsarki na yi wankan sabulu na dawo daki na yi sallah lokacin har bakwai ta kusa ina idarwa shi ma yana gama shirin shi ya ce min zai fita shago na ce bai karya ba ya ce zai fita saboda cinikin safe na yi mishi addu’ar Allah ya bada sa’a ya ce in haɗa abin karyawa in karya na ce to. A kayan da ya shigo jiya har da kayan shayi da kwai, da na soya ƙwan na kira shi a waya ya shigo muka karya. Lokacin na yi kwalliya cikin atamfa da ya fita sai na fita don gaishe da mahaifiyarsa. Sallamata uku a ƙofar ɗakin sannan aka amsa, tana zaune sai wasu yara su uku na gaishe ta ta amsa ba yabo ba fallasa sai na ji ta ba ni mamaki yadda take zuwa gidanmu tana magiyar a sanya ranar aurena da ɗan ta.

Ban jima ba na miƙe na koma ɗakina duk da ɗakin ba abin da ya yi ƙara kakkaɓe shi na yi na gyara sai na kwanta saman doguwar cushion sai barci ya ɗauke ni. Wayar Hassan ta tashe ni ya ce me zan dafa a kawo min kayan cefane? Na ce ya turo ɗan aiken, yaron shagonsa ya zo na lissafa mishi abin da zan buƙata. Koda ya kawo min ƙofar ɗakina na fiddo ƙaramin gas ɗi na da na yi sa’a har refiling Gwoggo Maryama ta sanya an yi min, jallop na daura ta shinkafa da taliya akwai kifi Geisha a cikin kayan cefanen sai na yi amfani da su da alayyahu da albasa mai lawashi nan da nan gidan ya karaɗe da ƙamshi na kammala na zuba mana namu na zuba ma mahaifiyarsa sai na zuba wa matar ƙanensa da na kai wa Inna kamar yadda na ji yana kiran ta sai na kai wa matar Gambo.

Na dawo ɗakina na tura mishi sakon text message sai na yi sallah ina idarwa yana shigowa “Sannu da aiki mai gadon zinare.”Ya ce yana murmushi ni ma murmushin ne ya ƙwace min na miƙe zuwa inda na jere abincin na zuba mishi zan zuba nawa ya ce a’a tare za mu ci, taren muka ci da muka kammala ya kamo ni ya ce “Bari in bayar da tukwicin wannan girki da aka yi min mai daɗi.”Gado ya kai ni ya fara yamutsa ni aka fara sallama a ƙofar daki shi ya leƙa a ka ce mahaifiyarsa na kiran shi.

Ni dai jin shirun ya yi yawa bai dawo ba sai na ɗauko wayata in kira shi sakon shi na gani “Na koma shago mai gadon zinare, ki kwanta ki yi barci ki huta.”Ƙarfe tara ya rufo shagon ya shigo gida wanda ya ce min goma da rabi yake tashi da na yi mishi magana cewa ya yi “Ban yi ƙoƙari ina da sabuwar amarya har na kai tara a waje? Kamar jiya yau ma mahaifiyarsa sai da ta zo ta buga mana duk da Hassan ya fita sallar asuba, faɗa na ji tana yi mishi zai maƙale gindin mace ba zai fita ya samu cinikin safiya ba. Gabana ya ƙara faɗuwa da kalamanta har na rasa wane irin tunani zan yi. Ranar da na cika sati guda sai ga Gwoggo Maryama ita da ɗiyarta ta biyu ta zo ganin ɗakina,don ta farkon Kano take aure na yi murna ina ta ina a saka ina za a aje da su, haka Hassan aike yake ta yi musu na abin ci da na sha sai bayan sun tafi uwar ta sa aka kira shi faɗa ta yi mishi sosai da babbar murya zai ƙarar da ɗan abin da yake da shi gindin mace. Ko da na kai mata abinci wani irin kallo ta riƙa bi na da shi da ya sa jikina ƙara yin sanyi tunda na ji kalamanta.

Na shaida ma Hassan zan koma islamiya ya ce ba laifi. Don haka na koma makaranta ta. Shigowar da Hassan yake ya ci abinci da rana Innar ta hana sai dai in aika mishi shago, tsakanina da Hassan zama ne mai daɗi cike da soyayya hakan ya shagaltar da ni na lallaɓa na tafi Asibiti aka cire min abin da na maƙala a mahaifa na hana haihuwa, matsala ta uwar shi ce wadda nake ganin tunda mijina na so na ba ni da damuwa da ita.

Ana haka ƙanwar Hassan autar su da aka aurar bara ta dawo gida haihuwa satin ta biyu haihuwa ta tashi sai dai jini ne ya ɓalle mata aka kwashe ta aka yi Asibiti cikin dare, gari na wayewa ta amsa kiran mahaliccinta ba tare da ta haife abin da ke cikin nata ba.

Nan aka kawo gawar ta aka yi mata sallah aka shiga zaman makoki, komai Hassan ke yi ga jama’a ko ta ina don dangi ne da su masu tarin yawa.

Ranar uku tun hantsi sai ga ƙanen mahaifiyar Hassan da suke uba daya daga Kano ya zo tare da matarsa har ciki ya shigo babban mutum ne mai ƙumbar susa, bayan ya fita waje inda ake zaman makoki Inna da kanta ta kawo matar ta shi ɗakina ita da ƙawarta ta ce su zauna daga ba mutane.

Wuri ɗaya na koma na zauna a takure ina sauraren hirarrakin su don manyan mata ne gogaggu, tunani ya shige ni zai yi wahala waɗannan matan su iya cin abincin da ake dafa wa a gidan makokin, Hassan na yi wa text ya ɗan aiko da kifi in yi wa baki girki, duk da yawan ƙorafin da Inna ke mishi na sawo nama ko kifi zai ƙarar da ɗan shagonsa, yau dai ai tana cikin jama’a ba sani za ta yi ba. Ba ɓata lokaci ya aiko da shi na zauna na dafa musu taliya mai daɗi har da drinks da ruwan gora ya haɗo na jera musu suna ta min sannu, suna cikin ci aka aiko musu da abincin da aka yi a gidan ko buɗe shi ba su yi ba cin taliyar suka yi suka ƙoshi suka yi sallah sannan aka yi ma matar kawun waya ta fito su tafi sai da suka miƙe ta ce “Ke ce amaryar da aka yi wata biyu da suka wuce?

Na ɗaga mata kai cikin jin kunya na yi musu Allah ya kiyaye hanya suka tafi sai na dauki abincin da aka aiko musu na fita da shi Husainar Hassan da dayar ƙanwarsa da matar Gambo suna zaune gindin bishiyar da ke tsakar gidan Husainar Hassan ta kira ni na karasa inda suke abincin ta ce in ba ta na miƙa mata ta karɓa tana buɗewa “Ba su ci ba ko? Ta tambaya tana taɓe baki nan na ji suna faɗin amaryar da kawun nasu ya yi ce shekaru biyu da suka wuce sai abin da ta ce ake yi a gidan. Ni dai na juya na koma ɗakina.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 2Mutum Da Kaddararsa 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×