Washegari kuma kwana huɗu Mamana ta iso kwananta biyu ta ce za ta koma duk da son da na yi ta yi bakwai ta ce ta baro yaranta. Kayan ɗakina na yi mata kyautar su na ce ta tafi da su ta sanya ma ɗakinta, Gwoggo Maryama da ita kaɗai ta rage tana ta kallona na san tana son yin magana da ganin na kyautar da kayan ɗakina amma ganin uwata na ba yasa ba ta iya yi min magana ba ni kuwa ni kaɗai na san me ke zuciyata babana shi ne komai ɗi na a rayuwa shi na sani yau na wayi gari na rasa shi.
Zuciyata ta yi nauyi rayuwar duniyar da komai da ke cikin ta ya sire min.Na biya mata kuɗin motar da za ta kai ta Adamawa daga ita sai ƙaramin ɗanta da yar da ta fara haihuwa bayan ni da ta fara zama yar budurwa ta zo. Da ta tafi daga ni sai Gwoggo Maryama a ɗakina sai ɗaiɗaikun mutanen da ke shigowa gaisuwa. Gwoggo Maryama ta fita ta nemo aminan babana da maƙwabcin shi ta nemi a raba gado kafin ta wuce da ni idan ya yi sati biyu, Inna keso ba ta so wannan al’amari ba ta dinga sakin magana idan ta fakaici idon Gwoggo Maryama.
Babana yana da rumfa a kasuwa, kasantuwa ta ɗiya ɗaya tilo da ya haifa rabi na abin da ya bari nawa ne gida na ci da wani yanki na rumfar, Inna keso da ta ci runfar za ta yi min ciko, sam ba ta so wannan kaso ba gidan ta so kasantuwar sun sayar ma ƙanen Iya da ɗakinsu da suka ci gado ita da ƙanwarta, sai wani nan nan take da ni don kar a tada ita. Komai ban ce mata ba don ni tunda na rasa babana ban kuma ga abin da zai ɗaga min hankali ba.
Gwoggo Maryama ce ta dage sai da ta bayar da kuɗin da za ta yi min ciko da ta bayar kuma ta bada su aka sanya min a acc ɗi na gidan ma ta ce ko ta tashi a zuba yan haya ko kuma ta karɓi hayar na ce ta rabu da ita. Kwanan babana sha biyu da rasuwa sai ga Alh Kabiru ɗan’uwan babana ya kuma dawowa da sassafe wanda ya samu tunanin garin ya kwana.
Ba Gwoggo Maryama ba ko ni na yi mamakin abin da ya dawo da shi. Aka yi mishi iso bayan an yi mishi shimfiɗa a cikin gida ya shigo aka zazzauna ana gaisawa, ni dai ina gaishe shi daki na koma na hau gado, da yake saitin windona nan suke zaune ina jin komai da suke tattaunawa “Sai kika ga na dawo Haj Maryama.” Ta ce “Wallahi kuwa.”Ya ce “Ko da na koma na kasa nutsuwa, hankalina ya ƙi kwanciya da yarinyar nan da na bari, abin da kawai ya rage da za mu yi wa Abubakar shi ne mu kula da rayuwar wannan diya guda ɗaya da ya bari. Shi ne na yanke dawowa in tafi da ita can gabana in haɗa ta da yarana da ba su wuce sa’anninta ba, su ko auren ma ba su kai ga yi ba.
Gwoggo Maryama ta shiga godiya da ba shi labarin da ma jibi za ta tafi tare da ni daga an yi haka sai kawai mu tafi tare daga can gidan nashi sai ta wuce gida. Ya ce “Yau za mu koma tare don haka ki shiga ki gaya mata ta kintsa mu wuce.” Gwoggo ta shigo shi kuma ya fita waje wajen ƙafafuwana ta zauna ta ƙara yi min bayanin da na riga na ji su. Sam ban ji daɗin inda ƙaddara za ta kuma wulla ni ba, rashin babana yasa yau kuma zan cilla wani gidan in tsunduma sabuwar rayuwa.
Kuka na fara tana lallashina dole saboda ita na yi shiru sai hawayen da loll nake gogewa da suka gagara tsayuwa. Ina haɗa suturuna tana taya ni Inna keso jin zan tafi sai da abin da ke zuciyarta ya suɓuce ya fito fili murna ta nuna don zan tafi ga kuma gida ba wanda ya yi mata maganar shi. Ƙarfe sha ɗaya muka bar garin Alh Kabiru na gaba kusa da direbansa ni da Gwoggo muna baya. Kamar yadda nake ta share hawaye ita ɗin ma hawayen take kuma a hankali tana bani baki in yi hakuri kar ya gane kuka nake.
Bayan doguwar tafiya da muka sha ƙarfe bakwai muka shiga Kaduna ina ta ƙara kallon garin ta hanyar hasken da ke bisa hanya don tuni duhu ya shigo da tuna zama na garin sai kuma Amir da tunanin ko wane hali yake? Sai dai na ji daɗi ko ba komai zama na garin zai kusanta ni da shi. Wata unguwa mai kyawawan gine-gine da fitilu ko’ina ya haske ga tituna a kowane layi. Gwoggo Maryama ta ce min sunan unguwar tasu yan majalisu. Wasu tagwayen gidaje guda biyu da komai na su iri ɗaya ne ta waje ya tsaya gaban daya ya danna horn, wani tsoho ya buɗe motar ta sulala ciki, harabar gidan mai tsananin girma ce cikin wata rumfa da motoci biyu ke ajiye ya parker motar, sai da suka buɗe suka fita shi da direban mu ma muka buɗe muka fito cike da gajiya.
Ya ce “Bismillah Haj Maryam.” Muka bi bayan shi ni da Gwoggo, wani lungu muka shiga sai muka haɗu da wata ƙofa da muka shiga muka iske dan madaidaicin fili muka wuce zuwa wani corridor sannan muka samu wata kofar ya daga labulai mazauna ciki suka shiga fadin barka da dawowa baba. Wata mata da shekarunta ba su gaza arba’in ba ta mike tana mana maraba ta ce mu zauna tana zuwa sai ta bi bayan mai gidan. Sai sannan na ƙare ma mazauna falon kallo yammata ne waɗanda da gani yaran matar da ta fita ne don yadda suke farare kamar ita. Daya daga ciki ta miƙe ta kawo mana ruwa daya kuma ta kawo mana abinci.
Gwoggo ta ce za mu fara yin sallah, wani daki da ke haɗe da toilet aka kai mu mun yi Azahar da La’asar a hanya don haka magrib da Isha’i muka gabatar mun idar matar ta shigo cikin fara’a take ta mana maraba aka gaisa ta yi mana gaisuwa.Ta ƙwalla kiran sunan Rabi’ah cikin yammatan wata ta shigo da ba za ta wuce shekaru ashirin ba ta ce ta ɗauko abinci ta kawo mana, nan ɗin ta kawo ban ci wani da yawa ba sakamakon tun mutuwar babana na rasa test ɗin bakina.
Ɗakin muka kwana muna tashi kuma Gwoggo ta kama shirin tafiya sai na fara kuka rarrashina ta hau yi da gaya min kalmomin tawakkali kafin muka tafi wurin kiran da aka zo aka yi mana zuwa part ɗin mai gidan. Ƙayataccen wuri ne da ya ji komai na more rayuwa, a ƙasan carpet na zauna shi da matarsa da Gwoggo Maryama suna bisa kujera matar ya yi ma umarni ta kira yaran, da wayarta ta yi amfani wurin kiran su. Suka iso su biyar cikin shirin makaranta, uku wadanda sune ƙananu cikin unifoam suke na makarantar boko gabatar musu ya yi da ni da dangantaka ta da shi ni ma ɗiyarsa ce idan sun dawo makaranta su kai min kayana ɗakinsu ya faɗi yana kallon manyan su biyu waɗanda cikin su za ka rasa wace ce babba don tsawon su daya matsakaicin tsawo suke da shi ga su jawur yan jika jika sai daya da take kyakkyawa a fuska dayar kuma farin da gogewa kawai suka fiddo ta.Allah ya jiƙan babana suka kuma cewa suka tashi suka tafi bayan ya sallame su.
Alheri na kuɗi ya yi ma Gwoggo Maryama ya sa direba ya kai ta tasha ya ce mu je tare in yi mata rakiya. Muna tafiya tana ƙara gaya min in yi hakuri komai ya samu bawa a rayuwa da sanin Ubangijinsa. Da ba direban ba zan tafi ba sai na ga tashin motarsu, amma hakanan muka yi bankwana na nufi inda ya tsaida motar ina share hawaye. Muna komawa na samu ɗaya daga cikin manyan yammatan ta dawo wadda ta fi kyan fuskar, ta tare ni da fara’a ita da mahaifiyarsu ta shiga dakin da muka kwana ta fito da jakata ɗaya ganin ta da ita sai ni ma na shiga na dauko daya da ma uku ne ta yafuto ni na bi ta a baya Muka taka step zuwa sama wani babban daki muka shiga mai gadaje biyu sai wardrobe har da mirror.
Ta buɗe wardrobe “Ki shirya kayanki a ciki, ɗakinmu ne ni da yayata Khadija duk gadon wadda kike so a cikin mu sai mu yi squatting, ni kuma sunana Zainab, duk abin da kike so sai ki min magana.” Na ce na gode Zainab, ni kuma sunana Bilkisu. Ta jinjina kai “Bilkisu mai gadon zinare kenan.” Saurin duban ta na yi don kiran mai gadon zinare ya tuna min da Hassan da babana.
Ta yi murmushi “Ko ba inkiyar kenan ba? Ni ma na taya ta murmushin “Haka ne.” Sai na isa gaban wardrobe ɗin na fara shirya kayana ita kuma ta zauna gefen gadon da ta fi kusa da shi ta ɗauki wani littafi da ke ajiye gefe na kusa gamawa ta taso “Har yanzu ba ki gama ba, ko in taya ki? Na ce “Ai na kusa ma sai masu datti da ba su da yawa na ce “Ina zan wanke su? Ta ce “Mu je toilet, akwai laundry sai ki wanke.”
Ta taimaka min na wanke muka fito zuwa dan wani wuri muka shanya, muka dawo ɗakin muka zauna tana ja na da hira a hankali labarin yan’uwanta take ba ni Khadijah ta kammala digirinta yanzu kuma tana NYSC da a halin yanzu ma ta kusa gamawa. Ita kuma ta yi karatun unguwar zoma da take gab da kammalawa. Mai bi mata Rabi’ah bana ta shiga jami’ar KASU. Sai ta huɗu Ihsan tana shekarar ƙarshe a Secondary. Autar su Asma’u aji uku take ita ma a Secondary.
Na jinjina kai ina tunanin su manyan su ne za mu kama sa’anni su ko auren farko ba su kai ga yi ba ni kam har na yi aure huɗu.Ta ja ni zuwa gidan da ke jikin nasu da suke iri ɗaya,ashe ƙannen babansu ne su uku part part ne sai da muka shiga ko’ina suka amshe ni faran-faran, ba mu jima ba muka taho.Za mu hau sama zuwa ɗakinsu wata mata da ta fara shiga shekarun girma ta ce ma Zainab an kammala abinci.
Ta ce “Za mu yi sallah baba Talatu sanya ma’unki ta kawo mana sama.”Ta ce “To.”Sai da muka yi sallah Zainab ta zauna gaban ƙaton tray da aka kawo ta soma buɗe kwanonin akwai ɗan wake da aka ƙayata da salad da kwai sai jallop ta shinkafa da ta ji kayan lambu da kayan ciki. Ta ce in zo mu ci ɗan waken na ci don mutumina ne. Ina shan drinks Khadijah ta shigo na yi mata sannu da dawowa ita kuma Zainab ta ce “Har kin dawo? Ta ce “Na gama abin da ya kai ni.” Ta zo ta zauna tana faɗin irin yunwar da take ji su biyu suke hirar su ina sauraren su da muka gama falon mamansu muka koma can muka zauna har dare sai da za mu kwanta muka hau sama, kamar yadda Zainab ta ce a gadonta muka kwana muka yi kai da ƙafa Khadijah tana nata gadon.
Na daɗe ina kallon Pop din dakin ba tare da barci ya yi nasarar sace ni ba babana nake tunawa da kuma rayuwa inda ta cillo ni. Da muka idar da sallah yau komawa muka yi muka kwanta don su duka biyun sun ce ba wadda za ta fita su dai suke barcin ni tunanin babana na dasa, san da suka tashi ni kuma barcin bai daɗe da ɗauka ta ba hakan yasa sai da Zainab ta tashe ni, ta yi wanka ta ce in je ni ma in yi san da na fito mai ta miƙo min da farar hoda da wet lips da turare duk da akwai kayan kwalliya masu yawa saman mirror. Na karɓa na koma bakin gado na soma shafa man, Khadijah na bakin nata gadon tana duba wani littafi ita ko wankan ma ba ta kai ga yi ba sai da na sanya kaya muka karya da kayan karin da aka daɗe da kawowa muka sauka ƙasa muka bar Khadijah da ta ce za ta yi wanka.
Mamansu na zaune a falo cikin shiri take har Zainab ta tambaye ta fita za ta yi ta ce E kasuwa za ta leƙa. Da na gaishe ta cikin murmushi ta ce “Ya baƙunta? Zainab ta yi zaraf ta ce “Ai ta zama yar gida.”Ta dube ni muka yi murmushi kusa da kusa muka zauna a kujera ɗaya tana duba hotunan cikin wayata, da ta zo kan hoton babana da na bata tabbacin shi ne babana sai ƙwalla ta shiga ɗigo min ina sharewa da bayan hannu tana bani baki a hankali ba tare da mahaifiyarsu da ke zaune ta mayar da hankali kan TV ta fahimci abin da muke ciki ba.
Takun ƙwas ƙwas da muka ji yasa mu kai ido step ɗin benen Khadijah ce cikin kwalliya take da wani matsiyacin ƙamshi da har sai da na lumshe idona don daɗin shi. Wasu yara su biyu maza da ke zaune tun shigowar mu suka taro ta suna kama mayafinta tare da ƙara buɗe ƙofofin hancin su suna faɗin daɗin ƙamshin da take ta kama hannayensu suka zauna tare kusa da Maman, maman ta ciro kuɗaɗe cikin jakar da ke gefen ta “Babanku ne ya ce mu shiga kasuwa ki zaɓi abubuwan buƙatunki.
“Khadijah ta yi yar dariya “Na gode da ma komai nawa ya kusa ƙarewa. Maman ta ce “Ki shiga bedroom ɗi na ki ɗauko keyn motata a cikin drawer mu je.” Khadijan ta miƙe zuwa dakin ta dawo riƙe da keyn suka fita tare muka yi musu fatan dawowa lafiya.
Suna fita sauran kannensu da suka fita zuwa islamiya suka shigo ƙaramar Asma’u ta ce “Aunty Zainab Najib na waje yana jiran ki.” Ta miƙe ta haura sama tana cewa “Na manta da wayata a ɗaki ina ga ya yi ta kira.” Da mayafai biyu ta dawo ta miƙo min daya “Mu je ki yi min rakiya.” Na ɗan dafe ƙirji “Mu je kuma?
Ta ɗan ɓata fuska “E rakiya za ki min.” Na miƙe muka jera ba dan na so ba. Wata dalleliyar baƙar mota da ke ta sheƙin ɗauke ido muka gani da fitar mu get wani haɗaɗɗen matashi na tsaye jikin ta ya ƙaraso gaban mu yana jifan Zainab da murmushi ta ce “Mu shiga ciki mana.” Ya girgiza kai “Tsaraba na kawo miki, zan dawo musamman.”
Ya koma motar bayan ya amsa gaisuwata ta kuma gabatar da ni a gare shi manyan ledoji biyu ya miƙo mata ta karɓa ya faɗa motar muka koma ciki ɗakinsu ta ja ni, muka zazzage abin da ke cikin ledojin kayan kwalliya ne da takalma da mayafai masu matuƙar kyau. Ta isa gaban mirror sai da ta ciro kayan kwalliyar da ta bani dazu na yi amfani da su sai ta jera sababbin gefen na Khadijah tare da furta wadannan kuma baba Talatu ta samu ta kai wa jikarta. Muna nan zaune har Khadijah ta dawo ganin sababbin kayan kwalliya saman mirror ta ce,
“Waɗannan fa? Ta ce “Najib ya kawo min.” Ta shiga ɗaga su tana yaba kyan su ita ma ta ciro nata sayayyar ta nuna mana Zainab ta shiga dubawa ta furta “Fi ni gidan uba in fi ki gidan miji.” Da uban mamaki Khadijah ta ce “Me kike nufi Zainab?
Ta noƙe kafaɗa tana girgiza hannuwa “Ban nufin komai na ga baba ya saya miki ni kuma Najib ya saya min. Nan da nan idanun Khadijah suka kaɗa ba ta ƙara magana ba amma kallo ɗaya za ka yi mata ka gane ranta ya gama ɓaci.
Zainab ta dauki tsofaffin kayan kwalliyarta ta ce in zo mu je ta bai wa baba Talatu mai musu aiki, da ta ba Babar sai godiya take muka wuce falon Mama ta faɗa mata Najib ya zo ya kawo mata tsarabar tafiyar da ya yi ta ce an gode.