Skip to content
Part 10 of 64 in the Series Mutum Da Kaddararsa by Maryam Ibrahim Litee

Tun daga ranar Zainab ta komamakaranta da ta ce min ba za ta wuce sati uku ba za ta gama. Idan duk suka tafi na kan kasance ni kaɗai. Ranar da na cika sati guda muna karyawa Maman su ta kira Zainab a waya ta ce mu sauko mu yi sallama da baba zai yi tafiya zuwa Cotonou saro motoci ta fadi mana ni da Khadijah.

Da ta ƙare wayar kuma ta faɗa mana. A gurguje muka ƙarasa muka sauko zuwa part ɗinsa, yana zaune da cup ɗin tea a hannunsa wata siririyar doguwar mata na gefensa tana zuba mishi dankali. Na cika da tsananin mamaki don ni ban san akwai wata mata bayan Maman su Zainab ba, duk da ina ganin wani part ɗin sai dai ban taɓa katarin ganin fitowar wani ba daga ma ba fitowar nake ba.

Sai da muka gaishe shi sai muka gaishe ta bayan ya tambaye ni ba wata matsala ko na ce babu ya ce muna waya da Gwoggo Maryama na ce E. Mun fito Compound Khadijah ta nufi wurin motarta, Zainab ta ce “Bari in bi ki ki sauke ni, idan na bi direban yaran nan makara zan yi.” Ta ce “Ok mu je.”

Sai da na ga fitar motar daga gidan sai na kama hanya don komawa ciki “Yammata tunda kika zo ba ki shigo mun gaisa ba.” Wata siririyar murya na ji a bayana, na waiwaya siririyar matar nan ce ta ɗakin Abba. Murmushi na yi gane da ni take “Mu je part ɗin nawa.” Ta ƙara faɗi sum sum na bi bayanta.

Da buɗe ƙofarta muka shiga wani irin ƙamshi ne ya daki hancina, wurin nata ya haɗu ƙarshe ta ce in zauna tana murmushi ta shiga ciki dambun nama ta dawo da shi da wani irin cincin mai dagargajewa a baki ta dawo da shi ta kuma sanya ni sai na ci.Da na cin kuma ji na yi kunnena kamar zai tsinke don daɗin da suka yi. Idona ya tsaya kan hoton wasu yara maza su biyu tunda na zo gidan nake ganin su falon Maman su Zainab sunan su Ahmad da Al’amin, tunanina yaran ƙannen babansu ne da ke yawan shigowa, tsananin kamar ta da su ya bani tabbacin yaranta ne.

Tana ta ja na da hira ni kuma hankalina ya rabu na ƙosa in ga na fita don ban ga alamar akwai wata mu’amala tsakanin ta da su Zainab ba, kuma a ga na shige wurin ta na yi mulumbuƙui.Na zauna na kusa awa baban ya kira ta a waya sai na samu na ce mata zan je in yi wanka da ta ce min tana zuwa, ta ce amma zan dinga zuwa mata hira ko?Ba dan zan dinga zuwan ba da gaske na ɗaga mata kai.Ɗakinmu na tafi na yi wanka na shirya sai na sauko ƙasa wurin mama.Da daddare muna ɗaki don ba mu yi doguwar hira falon Mama ba Zainab ke ta waya da Najib ɗinta ina gefenta ina sauraren ta, Khadijah kuma karatu take. Aka yi knocking Khadijah ta bada iznin shigowa yaran amaryar gidan ne su Ahmad, Ahmad ɗin da yake babba ɗauke da flask wanda da ƙyar yake riƙon shi ƙanen shi Al’amin kuma da wata madaidaicin jug.Wurina ya nufo kai tsaye “Ga shi in ji mamanmu.”

Na amsa da mamaki na ce ka ce mata na gode, suka juya, a tare Khadijah da Zainab suka dube ni sai na ji duk na muzanta na fuskanci Khadijah na labarta mata yadda na haɗu da Maman su Ahmad ɗin har ta ja ni zuwa part ɗinta.Ta taɓe baki “Ta iya wannan salon, duk wani ɗan’uwan baba burin ta ta janye shi wurin ta.

Zainab ta ajiye waya ta miƙa hannu ta janyo flask ɗin ta buɗe, ƙamshi ya cika hancinmu plate ɗinta da cokali da aka kawo mana abinci ba mu ci ba saboda tana waya ta dauko ta zuba hadaddiyar jallop ce da ta ji kayan ciki da kayan lambu.

“Da abinci ke kuma take so ta saye ki Bilkisu, wani irin bala’in iya girki gare ta mayyar matar nan ga shi duk ƙwaƙwata na kasa gane yadda take sarrafa girkinta, don bala’i ma daidai da kalolin magin da take amfani da su bare su take ta ɓoye takardun.

Har suka yi faɗa da Khadijah muka daina shiga harkar juna mu da ita ban samu na fahimci komai ba.”Na gyara zama “Ku ma da za ku gidan miji ku ya kamata kuna girkin gidan nan.”Ta ce “Muna yi, mun ɗan sarara ne amma ai mune masu yi.” Na gyaɗa kai, ta ce mu ci bayan ta yi wa Khadijah tayi wata yar banzar harara ta galla ma Zainab ɗin ita kuma ta saki dariya.

“A da fa mutumniyarta ce Bilkisu, saboda rainin wayon da take wa mamanmu ita kuma saboda tsananin hakurinta ba ta kula ta yasa Khadijah shiga faɗan, da ita suke yi.

“Na gyaɗa kai tana ta bani labari har muka ƙare cin abincin. Haka aka kuma washegari ma ta ƙara aiko min da abinci, ni dai a tsorace nake waɗanda nake wurin su ba su mu’amala da ita ni ta ina zan jefa kaina cikin sha’anin ta, ko abincin ma ƙin ci na yi na bar Zainab da shi na ce mata zan je in yi wanka wani irin duba ta min.

“Wanka kuma da yamman nan sai ka ce wadda za ta yi baƙo? Na wuce ta kawai na hau sama wankan na wuce na yi daga na furta na fito na zauna gaban mirror na yi kwalliya da ba ta wuce hoda da wet lips ba sai turare da na sanya. Na nufi wurin kayana wasu ubansun riga da wando masu laushi na samu kaina da daukowa, daf da rabuwar mu da Hassan tafiyar mu ta karshe ya saya min su guda shida, kaloli daban daban ban kuma taɓa sanya wannan da na sanya yau ba.

Shiru na yi ina tuna zama na da Hassan, kafin na dawo nutsuwa ta na sanya kayan sun kwanta a fatar jikina na ɗauko siririn gyale na rufe kaina na dubi kaina a mudubi na yi kyau sai dai nake ji kamar ba zan iya fita a haka ba duk da dai duk mata ne.

Na dai zura takalmi na fito, tun kafin in karasa saukowa nake jin hayaniyar mazauna falon ban ga abun da suka kewaye ba sai da na iso kasa wani matashin saurayi ne da na ji suna kira ya Najib kayan jikinsa na yan bautar ƙasa yasa na tuna ko shi waye Zainab ta bani labarin shi, ubansu ɗaya da shi wata uku Khadijah ta ba shi mahaifiyarsa ta fita tun yana goye sai da za a sanya shi makaranta baban ya karɓo shi.

Da ma ta ce min yana bautar ƙasa a Ibadan shi ma ya kusa kammalawa. Na zauna kusa da Zainab na ce mishi “Ina wuni? Sai sannan ya ankare da ni ya kuwa zuba min ido sai kuma ta sake maida duban kan Zainab “Ina muka samu baƙuwa ta ce “Ɗiyar dan’uwan baba ne na Dukku.”Ya ce “Yes na gane shi na taɓa wa baba rakiya can Dukkun.” Sai ta faɗa mishi rasuwar babana ya nuna jimami da faɗin Allah ya ji kanshi.

Ya taɓa kafaɗar Khadijah da ke zaune cikin kujera ta sanya earpies idonta na kan wayar “Wai sisina abin ya motsa kenan, kowa na tsallen ganina amma ke kin mayar da hankali kan waya.” Ta ɗago “Sorry bros ya za a yi in yi banza da ɗan ƙanena? Ya ɓata fuska sai kuma ya yi saurin dubana “Meye haka kike yi ke fa matsalarki kenan, waye ƙanen naki?

Sauran yaran suka sa dariya sai ya sha mur take suka shiga nutsuwar su, ko ni ban da Zainab ta ce min Khadijah tsarar shi ce har ma tana gaba da shi zan ce shi ne babba ya zama ƙaton saurayi don ba za ka taɓa jingina mishi shekarun shi ba. Suna hirar su na miƙe Zainab ta ce “Ina za ki? Na ce “Kwanciya zan yi.” Ta ce “Haba tun yanzu ko fa abinci ba ki ci ba.” Na ce “Barci nake ji na ƙoshi.”

Ban tsaya ƙara jin me za ta ce ba na wuce da sauri na hau sama duk da jikina na bani kallona ake ban waiwaya ba har na shiga ɗakin sai na saki wata gwauruwar ajiyar zuciya. Wani mayataccen kallo da Najib ɗin ya dame ni da shi da ya sa zaman falon duk ya ishe ni. Alwala na yo na zo na yi shafa’i da wutri na idar ina addu’a wayata ta dauki ƙara daga inda nake na miƙa hannu na ɗauko ta Gwoggona ce, na yi picking ina murmushi, sai da muka gama gaisawa da tambayar al’amura, ta ce “Ni fa tsohon mijin nan naki ya ishe ni da sintiri.”

Sai da na saki wani malalacin murmushi na ce “Jiya ma Inna keso ta kira ni wai ya je Dukku satin da ya wuce, ta ce mishi ina Kaduna. Ni fa saboda shi na hakura da tsohon layina, Gwoggo ba zan iya da mahaifiyarsa ba da yake damuna uwar tashi dai ai tana nan. Mai hali kuma ba fasa halin shi yake ba “Gwoggo ta ce “Nan ma ya nemi lambarki don tsiya sai ya ba shi ba daidai ba.

Matar kawun shi kuma Haj Asiya sai ga ta har nan wurina, ta ce ba su sani ba sai daga baya da take tambayar Hassan idan ta kira ki ba ta shiga ya ce kun rabu, ta yi ƙoƙarin roƙon Inna jin kalaman Innar yasa ta fahimci gara a haƙura ko kin dawo ba canza zane za ta yi ba. Ta bayar da lambarta ta ce a ba ki, za a turo miki sai ki kira ta don tana son ki matar.

“Na ce “To.” Mun ci-gaba da magana har kuɗaɗen wayarta suka ƙare sai na miƙe na hau gado na kwanta. Khadijah ta fara shigowa ta zauna gefen gadonta tana karatu a wayarta. Zainab da ta shigo karshe sai da ta gama shirin kwanciyar ta ta hawo gadon muka yi kai da ƙafa.Waya take da saurayinta Najib ni kuma tunanin rayuwata ya dabaibaye ni muhimmi a ciki ɗa na Amir da tun da aka karɓe shi ban ƙara sanya shi a ido ba, ga ni gari daya da shi amma ban san yadda zan haɗu da shi ba.

Har Zainab ta gama wayar kusan awa daya ban samu barci ba sai da na ji numfashinta na sauka a hankali, shedar ta samu barci na rufe idona da ƙarfi na ƙara addu’a sai na cire tunanin komai cikin sa’a barcin ya yi awon gaba da ni. Da safe ko da muka tashi ba mu sauka ƙasa ba yar autar su Asma’u ta kawo mana tsarabar baba da ya dawo jiya, ni da Zainab atamfa biyu da less ɗaya ko waccan mu, ta turo min ta ce in zaɓa ta shafa cikinta ni fa yunwa nake ji ki zo mu sauka ƙasa yau baba Talatu ta gaji da mu ba ta aiko mana da abinci ba.

“Na ce “Zan fara wanka tukuna zan sauko in same ki.” Ta kama baki “Jiya fa ba ki ci abinci ba kika kwanta, Allah na lura ba ki son cin abinci.”Na yi murmushin iya laɓba “Idan abin nan ya zo min takura ni yake, gara in fara wankan.” Ta yi murmushi “Wai abin nan sai ka ce wani surukinki. Akwai pad cikin kayan provision ɗin da ta ba mu jiya.

“Na ɗaga mata kai na faɗa bathroom ɗin na yi wanka har na fito Khadijah na zaune kan gadonta nata kayan tsarabar na zube tunda aka miƙo bata duba ba lace biyu atamfa uku. Na yi kwalliya na sanya wasu riga da wando masu matuƙar kyau har da ɗan hijab ɗinsu, rigar tana da tsawo iya gwiwa na sanya takalmi flat. Wayata na zare a charge sai ga kiran Zainab ya shigo na ɗaga ta shaida min tela ne ya zo in sauko da atamfofin nan.

Na kwashe su na sauka ban samu Zainab a falon ba sai Mama da sauran yaran don yau ana Children day ba su je Sch ba. Sai hayaniya suke kowa na ba telan na shi ɗinkin, na zauna kusa da Mama na gaishe ta ta ce in miƙa ma telan namu ita ma na ga na ta kala huɗu lace ɗaya atamfa uku.Ta ƙara da cewa Zainab ta ce idan na sauko in same ta kitchen.

Na fita na nufi kitchen ɗin tana tsaye tana soya Irish na ce “Ya haka? Ta taɓe baki “Wai baba Talatu ba ta zo ba ta je ƙauye duba yar ta tana ciwon hannu. Mu za mu kasance a kitchen har ta dawo.” Ta nuna min flask “Ki haɗa Tea ga Irish, in kuma indomie za ki ci bismillah matso ki dafa.” Na girgiza kai “Tea ɗin ma ya yi.”

Anan muka karya har muka wanke abin da muka ɓata, sai muka fita zuwa part ɗin Baba don yi mishi godiya.Yau ma amaryar shi na tare da shi ban ƙara sanya ta a ido ba tun ranar da ta sanya ni zuwa ɗakinta, sai Najib da wanzuwar mahaifinsa a wurin bai hana shi bi na da kallo na yan duniya ba, irin wanda ya yi ta min a jiya. Muka gaishe su muka fito Baba ya ƙara tambaya ta babu matsala na ce bani da ita.

Nesa da part ɗin muka tsaya, Zainab na min hirar abin ƙaunarta Najib, da tun tana Secondary yake son ta, amma har yau baba bai ba shi dama ba saboda Khadijah ba ta samu tsayayye ba. Amaryar Baba ta fito wurin mu ta yo kai tsaye “Bilkisu.” Ta kira sunana na amsa ta ce “Zo mu je mana.” Ta ce min sai ta ƙara gaba, na ɗan tsaya jim ina duban Zainab sai ta matso daidai kunnena “Ki je kya koyo mana yadda take haɗa munafukan girkinta.”

Na yi ɗan murmushin jin zancen ta sai na bi bayan Maman su Ahmad ɗin. Kamar ta ji zancen Zainab kitchen ta ja ni ta ce abinci take haɗawa Baba. “Ki koyi girki Bilkisu, shi ne mace ba ka tasa manyan yammata riɗi-riɗi ba ka koya musu abinci ba. Sai dai a yi a kai musu har ɗaki.

“Kai na jinjina ban ce komai ba don na fahimci kamar da su Zainab take. Kunun gyaɗa ta dama sai wata alale mai shegen daɗi don ta ji ƙwai da kayan ciki ga miyar niƙaƙƙen nama an mata, ta shirya komai ta wuce kai ma Baba ta bar ni ina gyara wurin.

Ta fita Najib ya shigo har ya biyo ni kitchen ɗin me kuma ya tuna sai ya koma falon, da ta dawo ina ji suna magana ta same ni ta ce in haɗa kunun in kai mishi na haɗa na kai mishi yana min wannan kallon, ina son tafiya ban san yadda zan yi ba kiran da take min daga bedroom ɗinta ya cece ni tana tsaye ta ce za ta yi wanka in gyara mata dakin, ta shige na dubi ko’ina tsaf sai tashin ƙamshi yake ni kam ban san me zan gyara ba. Baki na taɓe na ɗauki wani ɗan kyalle na shiga goge mirror da abin da ke kai.Har ta fito ta zauna tana kwalliyarta.

“Ki ɗauki duk abin da ya baki sha’awa anan Bilkisu.” Na ce “Na gode.” Ba tare da na ɗauki komai ba har ta gama sheka kwalliyarta wadda za ka san ta laƙanci kwalliyar duk matsalarki ki zo ki faɗa min Bilkisu.”

Abin da ta ce min kenan, lokacin da ta kammala muka fito Najib na nan zaune sai dai ya kammala idonsa na kan TV ya riƙe remote na yi mata sallama ta ce “Har za ki tafi ba za ki tsaya mu yi hira ba? Na ce “Wanki zan yi.” Ta ce “To ki shiga kitchen ki debi kunun da alale, amma ina mai yi muku wankin? Na yi shiru don ban san me zan ce mata ba.

“Shi kenan ki zo ki taya ni girki da yamma, koda yake bani lambarki da yamman sai in taɓo ki.”Sai da na ba ta ta sanya a faskekiyar wayarta, na wuce kitchen ɗin na haɗo kunu da alalen na fice da sauri har ina fidda wata munafukar ajiyar zuciya.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Mutum Da Kaddararsa 9Mutum Da Kaddararsa 11 >>

1 thought on “Mutum Da Kaddararsa 10”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×