Skip to content
Part 10 of 31 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Fuskar Deena jiri-jirin ta ce “Aunty Hafsat ina zan je in bar Yaya, da a ce dai lafiya lau yake sai in tafi, amma a irin wannan yanayin gaskiya ba zan iya barin shi ba.”

Deena ta yi wannan ƙarfin halin ne saboda ta fahimci shigar shugular da Aunty Hafsat ke yawan yi mata, wadda ko shakka babu ita ce ke haɗa ta faɗa da mamanta, sosai Aunty Hafsat ta ji zafin maganar Deena, wasu ƴan’uwan Deeni da ke ɗakin ne ya hana ta zagin ta, amma duk da haka sai da ta maida mata magana cikin gatsali, inda ta ce “A’a gaskiya bai kamata ki bar mijinki ba, gwara ki zauna ku yi jiyyar juna a tare.”

Labarin zuciya a tambayi fuska, matan da ke ɗakin sun fahimci ba abin da ke ran Aunty Hatsat ne ta faɗa ba, cewa ɗaya daga cikinsu ta yi “A’a Deena, ta ya zaki iya kula da miji, ga jego kina yi, kuma haihuwar farko, gwara dai ki koma gida kema a kula da ke..”, bata ƙarasa maganar ba Aunty Hafsat ta tarbi numfashinta “Faɗa mata dai baiwar Allah, kin san ita bata ganewa.”

Baki Deena ta Turo “Allah kuwa tsaf zan iya kula da shi”, harara Aunty Hafsat ta watsa mata “Ai sai ki kula shi mu gani ɗin, ja’irar banza, ana magana ke kuma kina gardama, wato ke mai miji ko?”

Deena na ganin Aunty Hafsat ta fara fusata sai ta yi guumm da bakinta, don tsaf zata haɗa mata Bomb da zai tarwatse da ita a wurin Ummanta.

Wannan batu na Deena zata koma gida ya tsaya mata a rai, har ta nemi duk wata walwala dake gareta ta rasa, Aunty Salma na shigowa ta ganta rungume da yaro ta yi jugum, gefen gadon ta zauna “Ya dai Maijego, jikin ko garin?” Kamar Deena zata yi kuka ta ce “Garin dai Aunty Salma”, duban tsanaki Aunty Salma ta yi mata ta ga duk ta susuce “Ayya, bari a kawo maki abinci toh, yanzu aka gama”, a tsammaninta yunwa Deena take ji, ɗan yamutsa fuska Deena ta yi “Ba yunwa nake ji ba, kawai waccan Aunty Hafsat ɗin ce zata wani hargitsa ma mutane lissafi.”

Duk lokacin da Deena ta kawo musu koken da ya shafi ɓangaren mahaifiyarta, toh basu cika sanya baki ba, don duk kusancinsu da ita, bai kai na wanda take da shi da mahaifiyarta ba, ƴar dariyar yaƙe Aunty Salma ta yi “Ki basar kawai, kada ki bari wani ya sanya maki damuwa a rai”, shiru Deena ta yi tana tunanin ta ya ba zata yi damuwa ba a kan shigar mata rayuwa da kullum ake yi?

Aunty Salma kuwa tuni ta maida hankalinta kan babyn da ke hannun Deena, yadda ya buɗe idanu tare da sa fingers a baki yana tsotsa ne ya ɗauke hankalinta, cike da son yaron ta yi ƴar dariya tare da lakatar kumcinsa “Kai acici, daga buɗe idanu ka fara shan yatsa”, maido duba Deena ta yi itama a kanshi tana kallon shi, sai dai bata yi magana ba.

“Ki ba shi mamansa ya sha”, Aunty Salma ta faɗa tana dubanta, gyarawa Deena ta yi ta cigaba da ba shi abincinsa.

Daddare bayan kowa ya watse, ya rage daga ita sai Deeni ne ta ce “Yaya, wai ta zan je wanka a gida?”, Ras gaban Deeni ya faɗi, don shi ma abin da ke ta ci masa tuwo a ƙwarya kenan, saboda mahaifiyarsu ta ce Deena ta koma wanka, idan ya so shi ma ya tafi gidansu bayan an mashi aikin, daƙyar ya iya ɓoye damuwarsa kafin ya ce “Eh mana gwara ki koma, kin ga bakya nan ma za a yi mani aiki” cikin muryar kuka ta ce “Ni ba inda zan je”, ya ce “Saboda me?”, Ta ce “Toh ta ya zan bar ka a gida kai kaɗai”, cikin muryar lallashi ya ce “Kada wannan ya dame ki, nima gidanmu zan koma a kula da ni a can.” 

Sosai ta fahimci kamar shi ma so yake ta tafi, ƙara shagwaɓe fuska ta yi gami da zumɓuro baki, duk da ta san ba ganin ta yake ba ta ce “Taɓ, ina duniyar me zai kai ka gida? Don Allah ni dai bana so”, ya fahimci da gaske take, lallaɓa ta ya yi da faɗin “Ki kwantar da hankalinki, ai kullum zan riƙa zuwa ganinki ko.”

Gardama sosai ta yi hada kuka a kan ita ba zata koma wanka ba, da ƙyar ya shawo kanta har ta haƙura.

Aunty Hafsat kuwa suna haɗuwa da Umman Deena a wurin aiki ta kai mata gulmar wai Deena ta ce ba zata dawo wanka ba, har sai da suka shawo kanta. Zuciyar Umman Deena iya wuya ta ce “Maganar banza ce wannan, kuma ai dai ƙarshen tuka-tuka tuk, idan dai ta baro gidan sai inga yadda zata yi”, Aunty Hafsat ta ce “Ke dai bari, kamar sun asirce mana ita”, Umman Deena ta ce “Ko asirin ne ai lokacin karyewarsa ya zo, na rantse da Allah idan ta bar gidan ba zata koma ba.”

Aunty Hafsat ta san dangin Deeni na matukar son Deena, kuma raba ta da su zai sanya su a damuwa sosai, domin ta ƙara zuga Umman Deena sai cewa ta yi “Sauƙin ma dangin mijin suna son ta kamar yadda itama take son su, ko yanzu baki ga yadda suke ririta ta ba.”

Ko Aunty Hafsat bata faɗa ba Umman Deena ta san haka, don idan dangin Deeni basu son ta ba zasu ƙara cunkusa mata son ɗan’uwansu ba, don duk yadda mace ke son mijinta, madamar bata zaman lafiya da ƴan’uwansa da wahala ta jure zama da shi, idan kuma har ta jure, toh zaman ba zai taɓa yi mata daɗi ba, “Can masu dai, ni dai ƴata zasu bani”, Umman Deena ta faɗa a takaice.

Ta ɓangaren Deena kuwa duk da ta tabbatar da zuwa wanka ba fashi amma ta kasa sakin jikinta, asali ma wata fargaba ta musamman ce ta mamaye ta, wadda duk wanda ya san yadda Deena da sakin jiki sai ya fahimci tana cikin damuwa.

“Wai Deena ko bakya lafiya ne?”, Tambayar ta Maryam matar Khamis ta yi, wadda kuma babbar aminiyarta ce, saboda suna da alaƙa a can Katsina, ta ɓangaren iyayensu maza, kuma sai aka yi sa’a mazansu abokai ko kuma ma ƴan’uwan juna ne, shi ya sa amincinsu ya zama na musamman.

Ganin ɗakin ba kowa sai su biyu yaba Deena damar buɗe ma Maryam cikinta, inda ta ce “Sister wai wankan Jego zan koma, ga shi kuma za a yi wa Yaya aiki, yanzu dan Allah idan na tafi wa zai kula da shi?”

Sosai Maryam ta fi Deena sanin me ake ce ma rayuwa, tunda shekarun ba ɗaya ba, cikin lallashi ta ce “Deena zuwa wanka fa alkhairi ne, saboda kema za ki samu gyaran da za ki ba mijinki kulawa ta musamman idan kin dawo, kawai ki kwantar da hankalinki, tunda an ce ai gida zai koma shi ma ko?”

Ba tare da gamsuwa da batun Maryam ba ta ce “Toh mutum da matarsa dan Allah ta ya zai koma gidansu, a barshi mana ni da ya zame ma wajibi in kula da mijina”, tabbas Deena na da gaskiya, amma ba yadda za a yi Maryam ta zuga ta, musamman yadda ta san Mahaifiyar Deena da ɗaukar zafi.

Cewa ta yi, “Kawai ki yi haƙuri ki bi abin da manya suka ce, tunda shi ma mijinki ai ya yarda ki je wankan, duka sati huɗu ne zuwa biyar kin dawo, kuma shi ma ai zai riƙa zuwa wurinku yana duba ku, kawai kada ki sanya wannan ya zama damuwa a gare ki”, sosai Maryam ta lallashi Deena har ta samu nutsuwar da bata sake ƙorafin tafiya wanka ba.

Dangin Deeni kuwa tsaye suke kai da fata wurin ganin Deena ta fita daban a matsayinta na mai jego. Hidima suke dai-dai ƙarfinsu, don kuwa sun haɗa mata kaya ita da baby tamkar lefe.

Mamanta da Alhaji Lawan sun yi mata kayan gani a faɗa ita da ɗanta. A ranar suna kuwa ƙayataccen event center aka kama, inda aka shirya taron a can, wanda wannan kuma aikin Yaya Asiya ne, ta yi haka ne kuma don ta nuna ma Umman Deena su ma cikakkin ƴan gari ne.

Dangi na kusa da na nesa duk sun zo, Itama Umman Deena ta zo ita da jama’arta, Deeni ma ya zo, inda suka jera shi da Deena da babynsu gwanin birgewa. An ci an sha, wasu har na guzuri sun kwasa. An yi hotuna ba kaɗan ba. Deena kam ta ga gata ta ko ina, kuma ta gode ma Allah, da duk wani mai hannu wurin ganin ta samu farinciki.

Daddare kuwa Deena da wuri ta kwanta saboda gajiya, inda Deeni ya riƙe jaririn, wanda suka sanya ma suna Abdullahi, amma Asma’u ta yi masa laƙani da Raihan. Deeni bai cika yin baƙincikin rashin ganinsa ba, amma a wannan karon sai da ya yi kukan rashin ganin fuskar ɗansa da yake yi ma so na musamman.

“Allah ka sa ina da rabon ganin fuskar Ɗana Amiin”, ya faɗa a fili, lokaci ɗaya kuma ya shafi kan Raihan har zuwa fuskarsa, a hankali ya ɗago shi ya rungume shi tsam a ƙirjinsa, lokaci ɗaya kuma ya sumbace shi, haƙiƙa yana son Raihan sosai, mafarin ya shiga yi masa addu’ar neman albarka da kuma kariyar Ubangiji, bayan ya gama ne ya kwantar da kansa a bayan gado ya yi shiru.

Deena kuwa in banda jibga masa ƙafa ba abin da take yi, yana ji, amma ya kasa janye mata ƙafar, saboda ya san wannan na mata daɗi.

Sai can ta falka ta gan shi zaune, “Yaya har yanzu baka yi bacci ba?”, Ta tambaye shi daga kwancen da take.

“Ina nan kewar ku ta hana ni bacci, na san gobe kamar yanzu kina can ke da Ummah” inda ke yi mata ƙaiƙayi ne ya sosa mata, cewa ta yi “Toh ai laifinka ne, idan da ka hana ai ba zan tafi ba”, cikin maida maganar ta yi daɗi ne ya ce “Toh ni kuwa ta ya ba zan bari ki tafi ba, na san ai za’a gyara mani ke sosai, yadda idan kika dawo zan ji ki ta musamman”, da ƴan manganu na zuga ya basar da maganar, har Allah ya sa ta sauko, ƴar hira suka taɓa, sannan suka yi bacci.

Washegari sai da aka gama soya manyan ragunan da aka yanka ma Deena, sannan aka kimtsa ta ita da Raihan dan shirin tafiya. Kowa ya lura da yadda ta sha jinin jikinta, amma suka basar saboda sun lura ba son tafiyar take ba, ɗaki ta iske Deeni domin su yi bankwana.

Zaune ta yi akan cinyarsa suka maƙale juna, bankwana mai cike da soyayya suka yi, don ba wanda bai yi kuka ba, “Dan Allah kullum ka riƙa zuwa Yaya”, ta faɗa cike da roƙonsa, dan ta san abu ne mai wahala, saboda kunyarsa da kawaici, uwa uba kuma Mahaifiyata ba son shi take ba, cewa ya yi “Insha Allahu zan riƙa zuwa Deena, ki kula mani da kanki”, ta ce “Insha Allahu.”

Rayukansu ba daɗi suka rabu, inda aka yi mota biyu ta rakiyar Deena, Lalu ya kwashi kaya da wasu mutanen, Yaya Asiya kuma ta ɗauki Deena da su Hajiya Ummah suka raka Deena har gida.

Sun ga sha tara ta arziki a wurin Alhaji Lawan, don kuwa dubu ɗari ya basu su sha mai, Umman Deena kuma ta haɗa musu manyan turaremen atamfofi da lesuna da Shaddoji, wanda wannan kayan iyayen miji ne da kuma shi kanshi mijin, banda kayan maƙulashe a manyan kuloli biyu, kai ka ce babu wata ƙullalliya a ƙasa.

Bayan sun tafi ne Deena ta shiga ɗakinta, komai an chanja kamar yadda dama aka faɗa mata, Ummanta na shigowa ta ce “Ɗakin ya yi kyau Ummah”, Ummanta ta ce “Daddy ɗinki ne da wannan”, Deena ta ji daɗi sosai, don Alhaji Lawan na mantar da ita kewar mahaifinta, don bata taɓa neman wani abu ta rasa ba, shi ya sa kullum take mashi addu’a shi da mahaifinta da ke ƙasa.

Tare da Raihan Umman Deena ta sauka can downstairs, zamanta kenan kusa da Alhaji Lawan a kan kujerar two seater ya ce “Deena ta yi sa’ar dangin miji”, don yadda suka yi bankwana idan har ba su zaman lafiya da juna ba zasu yi ba.

Dariya kawai Umman Deena ta yi, don babu wani yabo da za a yi ma dangin Deeni ya sa su birge ta, karɓar Raihan ya yi yana masa wasa, shi kuwa ƙyam da idanu yana kallon sa, cikin ƙaunar da Umman Deena ke ma Raihan ta ce “Kallar sa, Ɗan kusun uwa, sai ƙare ma mutane kallo yake.” Dariya Alhaji Lawan ya yi “Yaran zamani kenan, da wayonsu ake haihuwarsu”, Umman Deena ta ce “Aikam, lokaci ɗaya kuma ta yi masa ƙuri, wani irin so take ma Raihan, wanda bai rasa nasaba da dan yana Ɗan Deena, kuma hausawa sun ce “Ɗan cikin ƙwai, wanda ya fi ƙwan daɗi.”

Daddare Deena kuwa kasa bacci ta yi, don ma an haɗa ta da mai kula da ita dake kwance a kan katifarta da ke ƙasa.

Juyi ta riƙa yi mai cike da alaƙa da kewar mijinta, da a ce Deeni na iya chat, toh da yau sun kwana online.

Sai da ta rungume ɗanta tsam a jiki sannan ta kira wayar Deeni, aikuwa ringin biyu ya ɗaga da hanzari, “I miss You Dee-dee”, abin da ya fara faɗa kenan”, cikin shagwaɓa ta ce “Miss you too Yaya”, daga can ya ce “Toh me ya faru?”, Amsa ta ba shi da “Na kasa bacci”, cikin zolaya ya ce “Da gaske?”, Kamar zata yi kuka ta ce “Kai Yaya, baka yarda ba?”, Yanayin da yake son jin ta kenan, don shagwaɓarta ba ƙaramin tsuma shi take ba, cewa ya yi “Na yarda my Golden Dee.”

Raba dare suka yi suna shan soyayya, sai da suka yi mai isarsu sannan suka yi sallama, dama Deena ba jin kunyar mai tsaron ta take ba tunda sun saba da juna sosai, sai can cikin dare suka yi sallama ita da mijinta. Zaune ta tashi ta ba Raihan Mama, sannan ta sake rungume ɗanta suka kwanta, bacci mai daɗi ne ya yi awon gaba da ita.

Sosai Deena take ganin kulawa a wurin mahaifiyarta, bata taɓa kuma kawo ma ranta da sauran ƙiyayyar Deeni a ran Ummanta ba, saboda ƙaunar da take nuna ma Raihan, don kuwa indai tana gidan, Toh yana tare da ita tana ririta shi saboda akwai kwaɗayin sake haihuwa a ranta, zuwan Raihan ɗin ne ya rage mata wannan kwaɗayi.

Deeni kuwa kullum suna maƙale a waya da Deena, bai samu damar zuwa ba kuma sai ana jibi za a yi mashi aiki. Tarba ta musamman ta yi musu shi da Lalu ɗan rakiya, duk da Lalu ɗin bai daɗe ba ya tafi da niyyar zai dawo ɗaukar Deeni. 

Bayan falon ya kasance su biyu ne sai Raihan na ukunsu Deeni ya ce “Deena ki cigaba da yi mani addu’a, duk da na san kina yi”, cikin nutsuwar murya ta ce “Insha Allahu Yaya, Allah ya sa ayi maka aikin a Sa’a”, ya ce “Amiin Dee-dee..” 

<< Mutuwar Tsaye 9Mutuwar Tsaye 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×