Skip to content
Part 11 of 31 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Shiru ɗin da ya ratsa falon ne ya ba Deena damar matsowa sosai a kusa da Deeni ba tare da ya yi tsammanin haka ba. Saƙalo hannunta ta yi cikin nasa tare da kwantar da kanta a kafaɗarsa, cikin raunin murya ta ambaci “yaya”, idanunsa a lumshe ya amsa “na’am”, saboda yanayin ya masa daɗi, sakamakon muguwar kewar ta da shi ma take addabar sa, cewa ta yi, “sai nake jin dama a gidanmu ne”, sosai ya fahimci inda ta dosa, amma sai ya basar ta hanyar faɗin “To nan ina ne idan ba gidanku ba?”, da ƴar shagwaɓa ta ɗan goga kanta a kafaɗarsa kafin ta ce “gidan aurena fa nake nufi”, murmushi mai haɗe da ƴar dariya ya yi “ayya, to duka kwana nawa ne za ki koma ɗakin ki?”

Cikin ganin nisan kwanakin da suka rage ta ce “da saura fa”, kai ya jinjina “lallai kam, amma kamar gobe ne ai In sha Allahu.”

Wani shirun ne ya sake ratsa su, lokaci ɗaya kuma a ƙasan ran Deeni yana jin kamar ya ɗauke ta su gudu, don ba za a haɗa kewar da yake mata a kan wadda ta ke yi mashi ba, sai dai ko kusa bai bari ta fahimci susucewar da jikinsa ya yi ba, don gudun faɗawa yanayin da zai sha wahala kafin ya fita, ita dai gidansu ne, kuma wanka ta zo, bare ya samu sassaucin buƙatuwarsa a wurinta.

Ita kuwa sai ƙara shige mashi take, hannunta ta ɗora a kan cinyarsa, aikuwa da hanzari ya janye, sosai ta ji ba daɗi, ɗago da kanta ta yi “Yaya”, ya ce “Na’am ƴar gidan Yaya.”

“Ko dai Golden Dee ta fara yi maka fading ne?”, da mamaki ya ce “Me kika gani?”, Ta ce “Kamar baka son na taɓa ka”, shiru ya yi, saboda in har ya yi doguwar magana sai ta gane yanayin da yake ciki.

Cikin rawar murya ta ce “ka yi shiru”, ɗan gyara zama ya yi suna fuskantar juna, da zuciya ya riƙa kallon yadda ta ke ta narke mashi, hannunta ya riƙo ya ce “Dee-dee”, ta ce “Ina jin ka”, ya ce “nan ina ne?”, Ta ce “gidanmu”, ya ce “To ya dace in bari mu shiga yanayin da zamu ji kunya idan wani ya tarar da mu?”, Tabbas ta san bai dace ba, amma sai cewa ta yi “To ai ba kowa, kuma Mommah sai nan da two hours za ta dawo”, ya ce “Maids fa?”, Ta ce “Duk sun fita su ma, kuma a ƙa’ida basa shigowa idan an yi baƙi”, ya ce “Kin tabbatar”, ta ce “Uhm”, ya ce

“Okay.”

Ba ta yi tsammani ba sai jinta ta yi a kan cinyarsa, rungume juna suka yi sosai, ba zato sai jin mouth ɗinsu ta yi a haɗe, a gaggauce suka rage ma juna damuwa, saboda Deeni ya kasa nutsuwa, tsoronsa ɗaya ne a yanzu, kada Lalu ya dawo suna a cikin wannan yanayi su ji kunya.

Bayan sun samu nutsuwa ne suka yi shiru, can Deeni ya samu damar faɗin “Ina sonki Dee-dee”, ta ce “Nima ina son ka Abban Raihan”, ya ce “Abban Raihan kuma?”, fuskokinsu a haɗe ta ce “To Abban waye?”, Ya ce “Na Raihan”, ta ce “To yanzu daga Yaya ka koma Abban Raihan”, cike da jin daɗi ya ɗan sumbaci Lips ɗinta “Wow! Thank you.”

Suna cikin wannan yanayi ne suka ji ƙarar buɗe gate, da hanzari Deena ta tashi daga jikinsa, “me ya faru?”, ta ce “Kamar Mommah”, ya ce “Da gaske?”, Ta ɗaga kai, ya ce “Je ki gani to”, tashi ta yi ta kimtsa jikinta sannan ta fita, a parking space suka haɗu da Umman ta har ta fito daga mota, karɓar jakarta ta yi lokaci ɗaya kuma bakinta na faɗin “Mommah sannu da zuwa”, da mamakin fitowar Deena ta ce “Yauwa Uwar Raihan”, haka take tsokanar ta idan ƴan wasan suna a kai.

Dariya Deena ta yi, sannan suka tafi, a hanya ne ta ce “Yaya Deeni ne ya zo”, Kawai Umman Deena sai ta ji gaban ta ya faɗi, basarwa ta yi ta ce “Da kyau, shi da wa?”, ta ce “Tare Da Lalu, amma Lalu ɗin ya je ya dawo”, ba yabo ba fallasa ta ce “Okay.”

Deeni kuwa yana rungume da Raihan ya ji shigowar su, sannu da zuwa Umman Deena ta yi mashi, shi ma guiwa har ƙasa ya gaishe ta. Bayan sun ta amsa ne ya koma ya zauna, a ransa kuma yana jin wata ƴar fargaba shi ma, Deena kuwa a gefen Ummanta ta zauna a kan Kujerar da ke fuskantar wadda Deeni yake zaune, ƙuri Umman Deena ta yi ma Deeni, ba ƙaramar kiɗima ta yi ba da ta ga yadda idanun Deeni suka canja, dan kuwa kana ganinsa ka san cikakken makaho ne.

“Rayuwa kenan”, ta faɗa a ranta, don duk yadda ta tsani Deeni, toh kuma ta wani ɓangaren tana tausayinsa, domin rasa idanu ba ƙaramar masifa bace. Deeni ya ji a jikinsa kallonsa ta ke, mafarin ya ɗan lumshe idanu, a ransa kuma yana jin tamkar a kan ƙaya yake, dan kuwa ko lokacin da yake da lafiya baya iya dogon zama da Umman Deena, saboda kwarjini da take mashi, sannan ga tsanar da take mashi, bare kuma yanzu da suffofin nakasa suka bayyana a jikinsa.

Ta lura da shan jinin jikinsa da ya yi, mafarin ta maido da dubanta ga Deena da itama ta yi tsuru da idanu, “Haba Deena, wai ba ko ruwa ki kawo mashi?”, Deeni da kansa ya ce “Ai mun ci abinci Ummah”, ta ce “Ayya, na san halin Deena da salulanci i”, da ƴar shagwaɓa Deena ta ce “Kai Mommah”, Umman ta ce “Toh ba salular ba ce, Deeni dai mijinki ne, ya san halinki sarai”, kamar Deena zata yi kuka ta ce “Wai Yaya Ni Salula ce?”, ya san tsokana ce Ummanta ke mata, mafarin shi ma ya ɗaura da na shi “Ai gaskiya Mommah ta faɗa”, aikuwa ta ida shagwaɓewa hade da turo baki tana faɗin “Allah kuwa ina aiki, kuma shi Yaya ai ya sani”, miƙewa Ummanta ta yi “Ke ni bani wuri”, lokaci ɗaya kuma tana dariya, duban Deeni da shi ma yake dariyar ta yi “Bari in shiga ciki”, Deeni ya ce “Toh Ummah.”

Bayanta Deena ta bi da jaka a hannu, suna shiga ciki Umman ta ce “Wai haka ciwon nan ya chanja Deeni?”, Jikin Deena a sanyaye ta ce “Wallahi kuwa Mommah”, sai da Umman Deena ta nisa kafin ta ce “Allah ya kyauta”, Deena ta ce “Amiiiin”, ɗan shiru Deena ta yi saboda ta lura da akwai tarin maganganu a bakin Ummanta, tunda an ce labarin zuciya a tambayi fuska.

Katse mata shirun Ummanta ta yi ta hanyar faɗin “Ki je wurin mijinki”, Kamar dama Deena jira take ta tafi, da kallo Ummanta ta raka ta tare da yin murmushin takaici, “Bana jin wannan tafiyar zata ɗore, mutum kamar dama a makance aka haife shi?”, a ranta ta faɗa, dan kuwa a bin kunya ne a wurinta a ga Deeni a matsayin sirikinta, gefen gado ta zauna tare da cigaba da saƙawa da kwancewa.

Deena na saukowa suka cigaba da hira, bayan wasu ƴan mintina ne ya ɗauko wayarsa keypad ya danna kira, tambayar shi ta yi “Wa kake kira?”, ya ce “Lalu”, kafin ta sake magana daga can ɗin Lalu ya ɗaga, Deeni ya ce “Lalu kana ina yanzu?”, Lalu ya ce “Ina hanyar ƙarasowa”, Deeni ya ce “Okay, a ƙaraso lafiya.” bayan ya gama wayar ne Deena ta ce “Har ka gaji da ganin mu?” Kai ya girgiza “A’a, kin ga Ummah ta dawo”, ta ce “Toh ai ita ba ruwan ta”, ya ce “Duk da haka dai gwara in tafi”, ta fara gardamar ba zasu tafi yanzu ba sai ga Lalu ya dawo.

Ko zama Lalu bai yi ba Deeni ya ce “Ki faɗa ma Ummah zamu ta fi”, kamar zata yi kuka ta ce “To ka bar shi ya huta mana”, da ace ta san tsananin takurar da yake ji da bata nace a kan su ƙara zama ba.

Lalu ma ya san gidan ba wurin zamnasu bane, dan haka ya ce “Ba sai na zauna ba, tafiya zamu yi, akwai inda zan je”, jikinta a sanyaye ta tashi, ba a jima ba sai ga ta tare da Ummanta, Umman Deena ta ce “Wai har zaku tafi?”, Lalu ya ce “Eh Ummah”, kai ta ɗan jinjina tare da yi ma Deeni maganar aikin idon, ce mata ya yi “Sai Jibi, zamu je Kano”, cike da jimami ta ce “Allah ya sa ayi aikin a sa’a”, ya ce “Amin ya Allah”, sallama suka yi sannan ta koma sama.

Itama Deena ɗakinta ta koma ta ɗauko tsaraba a leda ta kawo ma Lalu “Ka kai ma ƙawata”, karɓa ya yi tare da ɗan taɓe baki “Uhmm! Komai ƙawa”, lokaci ɗaya kuma ya fara ƙoƙarin buɗe ledar “Miye a ciki?”, Da hanzari ta dakatar da shi “Kai-Kai! Amana ce fa”, fasa budewa ya yi “Toh fah! Na fasa, kada amanar ƙawaye ta cinye ni”, Deeni dai na riƙe da sandarshi yana dariya, cikin ransa kuma yana jin daɗin amincin da ke tsakanin ƙanwarsa da matarsa, don duk rashin kirkin Asma’u, ba a taɓa jin su da Deena ba, kuma baya fatan haka.

Riƙe mashi sandar Deena ta yi, hannunta ɗaya kuma riƙe da Raihan suka fice falon, inda ta raka su har wurin motarsu, ba tare da jin kunya ba Deeni ya rungume ɗansa da matarsa ya sumbace su, lokaci ɗaya ya ce “Zan yi kewarku”, da ƴan ƙwallanta a idanu ta ce “Muna haka Yaya.”

Lalu kuwa take suka sanya mashi kwaɗayin aure, don yadda Suke ta nan-nan da juna ya ƙara tabbatar mashi da ba ƙaramin farinciki ne a cikin aure ba, musamman idan mutum ya dace da matar aure.

Bayan Deena ta yi ma Deeni addu’ar samun nasarar aikin ne ta juya wurin Lalu “Uncle Lalu, Allah ya tsare”, cike da tsokana ya ce “Ki ce Allah ya aurar da mu mu huta kuma”, dariya su duka suka yi, Deeni ya ce “Ai ba wanda ya hana ka aure”, suka ƙara wata dariyar.

Hannu Deena ta ɗaga musu lokacin da suka shige motar, cike da jaddadawa ta ce musu Dan Allah ku gaishe mani da Hajiyarmu”, Deeni ya ce “Baki da matsala tawan!” Ƙuri ta yi ma mijinta har ya rufe motar, Lalu bai wani ɓata lokaci ya sa mata key tare da yin reverse, cike da kewar su ta ɗaga musu hannu, tare da raka su da idanu har suka bar gidan.

Ciki ta koma, inda ta tarar da mahaifiyarta a falo, don kuwa a can ɗakinta ta ga yadda suka yi bankwana ta jikin window, kuma hakan ya ƙara tabbatar mata da mugun son da Deena ke yi ma Deeni, wanda ke nuna raba su ba ƙaramin jidali bane, don haka ta ɗaukar ma ranta a hankali zata fara cire ma Deena wannan ƙwallafa, cikin salo ta fara convincing ɗinta da faɗin “Deena, yanzu haka ake fama da shi, duk inda zai je sai da ɗan jagora?”, Cike da ƙwarin guiwa Deena ta ce “Haka yake, amma yana ɗan kwatanta yin wasu ayyukan da kansa”, ta ce “Amma ba sosai ba ko?”, Deena ta ce “Eh ba sosai ba”, bakin Ummanta a taɓe ta ce “Allah ya kyauta, amma ke zaki iya rayuwa da shi a haka kuwa?”, Deena ta yi mamakin wannan tambayar, amma sai ta adana mamakin a ranta ta ce “Eh Mommah zan iya?”, kallon sakarya marar wayau Ummanta ta yi mata, don ƙaramin abu ke harzuƙa ta “Da ƙuruciyarki zaki ƙare a ƴar jagora?”, Shiru Deena ta yi, saboda lura da fusatar ta, hakan ya ba Ummanta zarafin cigaba da faɗin “Ki dai sake nazari Deena, madamar aka yi ma Deeni aiki, kuma bai warke ba, toh rayuwarki zata ƙare a makance kema muddin kuna tare, don haka ki yi ma kanki karatun ta nutsu.”

Cike da ladabi Deena ta ce “To Ummah, in sha Allah Allahu zan yi nazari”, ta yi haka ne saboda ta san mahaifiyarta ba ta son musu, amma ba don ita ta haife ta ba ai sai ta hukunta duk wanda ya kawo mata batun rabuwa da Deeni.

Sosai ta danne tashin hankalin da ke ranta suka cigaba da maganar, inda mahaifiyarta ta cigaba da bata shawarar da take ganin ita ce mafita ga Deena. Sai da Deena ta koma ɗakinta ne ta fashe da kuka, lokaci ɗaya kuma ta ɗaga hannunta sama tana faɗin “Ya Allah kada ka jarabce ni da rabuwa mijina, don wallahi ba zan iya ɗaukar wannan ƙaddara ba”, kuka sosai ta riƙa yi, sai da Raihan da ke kwance a gefenta ya falka ne ta tsagaita kukan, ɗaukar shi ta yi ta ba shi Mama, lokaci ɗaya kuma hannunta riƙe da waya tana kallon pics ɗin Deeni a lokacin da yake da lafiya, tana zuwa kan wani hoto da suka yi tare ta sumbaci wayar, “Allah ka bar mani kai mijina, Allah kuma ka ba shi lafiya Amiin.”

Kamar yadda addu’ar samun nasarar aikin da za a yi ma Deeni ta zama wajibi a wurin Deena, toh hakan yake a wurin duk wani wanda yake da alaƙa ta kusa da ta nesa da shi, musamman mahaifiyarshi wadda Allah da Manzonsa ne kaɗai suka fi ta son Deeni. A daren da zasu ta fi Kano ne suna zaune a falonta suna tauna maganar ne ta ce “Gobe e’ yanzu an maka aikin ko?” Ya ce “Eh Insha Allahu”, ta ce “Allah ya sa a dace”, ya ce “Amiiin Ya Allah”, wayarshi ce ta katse musu hirar, ɗagawa ya yi tare da faɗin Dee-dee, ya kuma gane ita ce ta kira saboda ya ware ma duk wasu na kusa da shi ring tone ɗinsu.

Daga can ta gaishe shi, bayan ya amsa ne ya ce “Ina Ummah da yarona?” Amsa ta ba shi “Ummah na can ɗakinta, ga yaronka nan kuma yana barci”, cike da son yaron ya ce “To ki shafa mani kansa”, ta ce “In sha Allahu.”

Faɗa mata ya yi kusa da Hajiyarsu ya ke, aikuwa ta buƙaci ya haɗa su, miƙa ma Hajiyar waya ya yi “Ku gaisa”, karɓa ta yi da sallama, daga can Deena ta amsa da girmamawa tare da gaishe ta, bayan ta amsa ne ta ce “ina wannan angon da ba cefane, ko Hajiya Hadiza ta hana shi kula sauran matan ne?”.

Deena na dariya ta ce “A’a Umma, yana nan zuwa gaishe ki ai”, Hajiyarsu Deeni ta ce “Toh shikenan”, cike da ƙaunar juna suka yi wayar, sannan ta miƙa ma Deeni wayarshi.

Yana karɓa Deena ta langaɓe “Anjima zan kira ka mu sha Love”, bakinsa ɗauke da dariya ya ce “Baki da case tawan!”

Bayan ya aje wayar ne Hajiyarsu ta ce “Deena na da haƙuri, kawai Hajiya Hadiza ce damuwarta”, ɗan nisawa ya yi “Wallahi kuwa, Allah dai ya bamu mafita ta alkhairi”, ta ce “Amiin ya Allah”, sun daɗe suna hira, sai da Lalu ya dawo ne ya yi mashi jagora a ɗakinshi. Kwana suka yi kamar wani saurayi da budurwa suna waya mai cike da ƙauna shi da Deena.

Washe gari tunda safe suka shirya shi da Lalu, da Hajiya Umma da kuma Yaya Asiya, sai kuma Khamis suka nufi Kano.

<< Mutuwar Tsaye 10Mutuwar Tsaye 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×