Skip to content
Part 12 of 36 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Khamis ne ke driving ɗinsu a danƙareriyar Jeep ɗinsa, inda Deeni ke zaune gefensa a front seat, yayin da Hajiya Umma da Yaya Asiya ke zaune back seat, sai Lalu na ukunsu da ke zaune a owners corner.

Tafiyar ba ta daɗi bace, shi ya sa kaf hirar da suke ta ta’allaƙa kacokam a kan yanayin rayuwa, musamman da ya kasance azumi ya gabato, duk da su Allah ya rufa musu asiri basa neman komai wurin kowa, toh amma suna tausayin ganin yadda jama’a ke dafifin neman taimako a wurinsu.

Lalu da ya fi su shiga jama’a ne ya ce “Ai abin ya wuce tunanin kowa ma, mutumin da kake gani da ƙarfi, amma chanjin rayuwa ya sa shi Bara”, Yaya Asiya da ke tsakiyarsu na jin haka ta karɓe zancen da faɗin “Wasu fa hada mutuwar zuciya Lalu, idan har lafiyayyen mutum zai kashe zuciyarshi da Bara?, Toh shi kuma mai nakasa ya yi me?”, Hajiya Ummah dake gefenta ta ce “Wallahi kuwa, hada mutuwar zuciya kawai”, Daga can Khamis ya ɗora da faɗin “Lallai kam, tunda ai babu maraya sai raggo, kuma Allah ya ce tashi in taimake ka.”

Tunda suke hirar a nan ne kawai Deeni bai sa baki ba, shi ma don sun taɓo mashi inda yake masa ƙaiƙayi ne, don kuwa tunda ya samu ciwon makanta ya gane babu mai cikakkiyar dama sai wanda Allah ya barma lafiyarsa, saboda ita ce Uwar jiki, wadda babu mai fushi da ita kamar yadda wani mawaƙi ya faɗa. Domin Mailafiya na da ikon da zai yi duk abin da zai kawo mashi cigaban rayuwar shi ta duniya da lahira ba tare da gajiyawa ba.

Toh amma abin mamaki sai ka ga wasu da lafiyarsu sun ɓige da bara, wanda hakan ci baya ne a gare su, shi ya sa ya ɗaukar ma ransa ko ya warke, ko bai warke ba, toh zai kafa wata Foundation da zata taimakawa masu buƙata ta musamman, da masu lafiyar ma ta hanyar daƙile barace-barace da mutuwar zuciya.

Sosai suka yi ta tauna batun, sai da tafiya ta fara nisa ne kowa ya yi shiru, Deeni kuma hankalinsa ya koma a kan surgery ɗin da za’a yi masa, fargabar da ta samu mazauni a ransa ita ce shin zai warke? Ko kuwa dai ƙaddararsa kenan. Haƙiƙa yana son idanunsa sosai, toh amma idan Allah ya karɓe abinsa ba yadda zai yi, tunda kowa da ƙaddarsa.

Kwantar da kansa ɗin da ya yi a bayan kujera tare da lumshe idanu ne ya ɗauki hankalin Khamis, ɗan duban sa ya yi, lokaci ɗaya kuma ya maida hankalinsa a kan driving ka fin ya ce “Dr. Bacci kake?”, a hankali Deeni ya buɗe idanunsa, da zuciya ya kalli Khamis, “A’a”, Khamis ya ji a jikinsa fargaba ce ke damun Deeni, mafarin ya ja maganar ta hanyar faɗin “Kuma ka yi shiru?”, Cikin karyewar zuciya Deeni ya ce “Na dole ne, hankalina ya ƙi kwanciya, gani nake kamar a haka zan dauwama.”

Kusan tare suka buɗe baki da nufin kwantar mashi da hankali, sai dai maganar Hajiya Ummah ta kere tasu, saboda ita da faɗa ta yi ta, inda ta ce “Wace irin magana ce wannan kake faɗa; halan ka san gaibu ne da kake yanke ƙauna ga rahamar Ubangiji?”, Kai ya girgiza “A’a”, ta ce “Toh ka yi addu’a, Allah ya sa a dace kawai”, duk suka ce “Amiiiin.”

Zuciyarsu ba daɗi suka riƙa ba shi maganganu masu tausasa zuciya, har Allah ya sa suka shiga birnin Kano. Kai tsaye hotel suka nufa tunda basu da kowa a garin, kimtsawa tare da cin abinci suka yi, sannan Khamis ya ɗauko su suka nufo Makka specialist eye hospital.

Zamansu kenan a reception wata matashiyar budurwa sanye da Lab-coat ta tunkaro su, sosai ta birge Hajiya Ummah, don duk lokacin da ta ga matashiyar mace sanye da kayan asibiti sai ta ji ina ma ace Afnan ɗinta ce, dan babban burinta kenan ta zama ma’aikaciyar lafiya, da yake Afnan ɗin na da buri, har ta ɗauko hanya, don ta ce babanta Deeni zata gado.

“Kamar Afnan ko?”, Hajiya Umma ta faɗa idanunta na kallon matashiyar lokacin da ta zo dab da su, basu samu zarafin bata amsa ba sakamakon amsa sallamar matashiyar da suka yi.

“Sannunku da zuwa”, ta faɗa cike da girmamawa, idanun Lalu ƙyam a kanta, don wannan ne karon farko da ya fara ganin ta, Khamis kuwa tun zuwansu na farko ya fara ganin ta, kuma tun a lokacin yake jin da ace zai iya ƙara aure, toh da sai ya aure ta a matsayin ta uku, don ta cika duk wata siffa da za a so mace saboda ita, toh rikicin Maryam da Aisha kaɗai ya ishe shi jidalin rayuwa.

Dr. Rahila kenan, ƴa ga Professor Munir Alƙali, masani a kan kimiyyar siyasa. Ita ɗin tana ɗaya daga cikin Optolmologiest ɗin da ake alfahari da su a arewa gabaɗaya ma, don ta ƙware a surgery na idanu, kasantuwar a India ta yi karatunta. Ita ɗin mace ce da aikinta ne kaɗai a gabanta, don duk kyau da ƙasaitar da take da ita, amma bata da tsayayyen saurayi, ba kuma dan babu masu son ta ba, sai dai kawai dan masu zuwa ɗin ne basu dace da zubi da tsarinta ba, sai dai abin mamaki, tana ganin Deeni a karon farko ta ji ya birge ta, duk kuwa da naƙasar da yake da ita, mafarin tun ranar da suka fara zuwa asibitin ta ɗauki nauyin hidimar yi masa aikin.

“Dr. Ya jikin”, ta faɗa tana kallon Deeni da ke bata tausayi, cikin gamsuwa da irin ƙoƙarin da take musu ya ce “Jiki da sauƙi Dr.”, Ta ce “Masha Allah, wani sauƙin ma na tafe after surgery Insha Allah”, kusan a tare suka haɗa baki “Allah ya sa.”

Faɗa musu ta yi sai yamma za’a yi aikin, don haka su je gidansu su shirya sai zuwa anjima sai su fito tare.

Khamis ya ce “A’a Madam, muna da hotel fa”, baki ta ɗan turo “Ai na san da haka, amma na ce ku zo muje gidanmu, tunda an ce baƙonka Annabinka”, Dariya su duka suka yi, Khamis ya ce “Babbar magana”, maida dubanta ta yi ga Deeni “Ko ba haka bane Dr.?”, Deeni na ƴar dariya ya ce “Haka ne.”

Maida dubanta ta yi ga su Hajiya Umma, hannunta a sama ta ce “Dan Allah mu je, already an san da zuwan ku a gidanmu, Abbanmu ma ya sani.”

Hajiya Umma ta ce “Ba damuwa ƴata”, shi kuwa Lalu baki ya mutu, duk yawan tsokanarsa, sai ga Rahila ta masa kwarjinin da ko motsin kirki ya kasa yi.

Gidansu bai da wani nisa da asibitin, don haka ta shiga motarta suna biye da ita har suka isa gidan da ke bakin titin da ya ratso cikin unguwa. Tun a waje zaka gane mazauna gidan daɓensu ya ji makuba, dan gate ɗin gidan kaɗai abin kallo ne.

Da suka shiga gidan kuwa sai da suka ƙara jinjina kai, don ko Khamis da ke taƙama da safarar manyan motoci sai da ya jinjina ma masu gidan.

“Ikon Allah, yau mu ne anan?”, Hajiya Umma ta faɗa tana kallon benen gidan”, Yaya Asiya ta ce “Aikuwa dai.”

Dr. Rahila kuwa tana fitowa ta ce “Mu je ko?”, Khamis ne ya ce “A’a ki fara shiga, idan an yi mana iso sai mu shigo”, langaɓe kai ta yi “Na faɗa muku an san da zuwanku fa.”

Ƙin shiga suka yi, sai dai Yaya Asiya da Hajiya Umma tunda su mata ne, a babban falonsu aka saukar da su, sannan ta haye upstairs, inda ta tarar da Mahaifanta a falo suna hira, cikin ladabi ta gaishe da su, don su boko bai hana su samun tarbiyya ba.

“Har kun iso kenan”, ta ɗaga kai “Yeah Abba, amma mazan suna waje, matan ne suka shigo”, ya ce “Har su nawa ne?”, ta ce “Su biyar ne, kamar duk siblings ɗin patient ɗin ne”, ya ce “Allah Sarki, muje toh”.

Tashi ta yi, inda suma suka miƙe suka sauko downstairs a tare, a falon suka fara zuwa, inda ta gabatar da su Hajiya Umma a wurin mahaifanta, cike da girmamawa suka gaisa da juna, sannan Rahila da abbanta suka fita, nan Ummanta ke tambayar Hajiya Umma “Yaronki ne?”, Saboda ta ga alamar ita ɗin babbar mace ce, “A’a ƙanena ne”, ta ce “Allah Sarki, Allah ya bashi lafiya”, suka ce “Amiiin.”

A can waje kuwa bayan sun gaisa ne Abbansu Rahila ya yi musu iso, da mamaki sai Rahila ta riƙe Stick ɗin Deeni zata yi mashi jagora, Lalu ya ce “Na hutar da ke”, kallonshi ta yi “A’a, patient ɗina ne, ku barni na kula da shi”, Abbansu na dariya ya ce “Rahila uwar rigima”, Khamis kuwa sai dai kallon ikon Allah ya ke, ya san Maryam ɗinsa da rigima, amma ya lura wannan ta sha gabanta.

Cikin Falon suka isa, inda suka zauna a kan kujera, Rahila da Lalu kuwa duk a ƙasa suka zauna.

Wata gaisuwar aka yi, Maman Rahila tana ganin Deeni ta ji wani irin tausayinsa, don kuwa ya tuna mata Babban ɗanta Sagir da yayi accident ya rasu, wanda kaf structure su ɗaya da Deeni.

Idanunta cike da ƙwalla ta ce “Sannu Deeni, ya ce “Yauwa Ummah”, duban Alhajin ta yi “Dan Allah prof ba kamar Sagir ba?”, jikinsa a mace ya ce “Kin riga ni faɗa ne”, Rahila ta ce “Shi ya sa na matsa su zo ai.”

Anan suka basu labarin Babban ɗansu Sagir, wanda ya yi hatsarin mota a hanyarsa ta dawowa Abuja, ya rasu ya bar mata ɗaya da yaranta twins, Sun tausaya musu sosai, wata irin shaƙuwa da ƙaunar juna ce ta shige su a take. Abinci mai rai da lafiya aka shirya musu, bayan sun ɗan ci ne aka sauke su Hajiya Ummah ɗakin baƙi suka yi sallah.

Rahila ta yi gadon kirki a wurin mahaifanta, ba ita kaɗai ba, hatta sauran siblings ɗinta suna da kirki, amma na ta na daban ne, kuma su Deeni sun shaida haka, don da jajircewarta ne Professor ya yi musu albishir ɗin Insha Allah shi ma zai basu gudunmuwa har Allah ya sa ya samu lafiya, don a take ya binciki waye Dr. Deeni a wajen jama’arsa da ke Kaduna, kuma ya ji kyakkyawan labari a tare da shi.

Da ƙarfe huɗu ne aka shirya yi ma Deeni aiki. Inda Dr. Rahila ce ja gaban, sai wasu Dr. Uku maza, wanda dukkansu ƙwararrin likitoci ne.

Kafin su shiga ne Deeni ya kira Hajiyarsu tare da shaida mata yanzu za a shiga da shi, Hajiyarsu ta yi mashi addu’oin da sai da suka sanya shi kuka.

Yana gama wayar ne ya kira Deena, a lokacin kuma Dr. Rahila ta zo dan su shiga ɗakin surgery ɗin, tsaye ta yi lokacin da ta ji ya ce “My Dee-Dee, yanzu za ayi aikin, ki yi mani addu’a.”

Da ƙyar Rahila ta iya control ɗin kanta sakamakon wata irin faɗuwar gaba da ta rike ta. Tabbas ta san Deeni ba zai rasa mata ba, amma bata yi zaton yana son ta kamar yadda idanunta suka gani ba, don yadda suka yi wayar ko hasidin iza hasada ya san ma’auratan na tsananin ƙaunar juna.

Bayan ya gama wayar ne ya ce “Dr. Mu je ko?”, Kai ta ɗaga saboda ruɗu, ta manta da bayan ganin ta.

Sake tambayar ta ya yi “Mu je?”, Kai ta sake ɗagawa sannan ta ce “Eh mu je Dr.”, Da kanta ya yi mashi jagora suka shiga ciki.

Sauran Doctors ɗin da mutuntawa suka karɓi Deeni, basu wani ɓata lokaci ba suka shiga yi masa aiki, Deeni tun yana ji, har ta kai ga bai san me ke wakana ba, ita kuwa sai da ta yi ƙoƙarin gaske wurin danne azababben kishin da ya turnuƙe ta, sannan har ta iya yin abin da ya dace.

Cike da ƙwarewa take yin kowane aiki, shi ya sa kaso mai yawa na marasa lafiyarta suna warkewa da taimakon Allah, amma wannan karon ƙunci ya hana ta motsin kirki, sauran Doctors ɗin suna lura suka zage da aiki.

Suna gamawa a ka turo shi zuwa resting room, inda ita kuma ta samu su Hajiya Ummah da suka yi jugum suna sauraron Allah, “Mama mun gama namu, yanzu dacen Ubangiji kawai muke bukata”, Hajiya Ummah ta ce “Allah ya sa a dace”, yadda jikin Rahila ya mutu ne ya sanya su suma suka sha jinin jikinsu.

A resting room suka ɗunguma, kusan ba wanda bai yi ma Deeni kuka ba saboda tausayi.

Rahila kuwa gidansu ta nufa, Ummansu ta yi mamakin yadda ta dawo gida jiki ba ko ƙwari, tambayar ta ta yi “Ya dai, akwai alamun nasara dai ko?”, Ta ce “Eh Umma”, basu yi wata doguwar magana ba ta wuce ɗakinta.

Jagwab ta zauna kan gado, tambayar kanta ta fara yi “Wai me ke damuna ne?”, a zahiri a ta san answer tambayar ta, amma kuma ta kasa gasgata cewar kishin Deeni take, saboda bata yarda da feelings ɗin da take ji a kansa ba.

Hannuwanta dafe da kai ta lumshe idanu, kwarjinin da fuskar Deeni ta riƙa yi mata lokacin suna yi masa aikin ne ya dawo mata a rai. Toh yana fama da makanta kenan ta shiga wannan halin a kansa, ina ga lokacin yana da lafiya ne ta ganshi, ƙila da sai ta yi ma Deena zalama a kansa.

Wani irin gwauron numfashi ta sauke tare da matse ƙwallan da suka cika mata idanu, wanda idan ka tambaye ta zata ce ƙwallan yanke ƙauna ne a kan abin da take so, wanda kuma ta san ma ba zata same shi ba, tunda a halin da Deeni yake ciki tana da yaƙinin babu sauran wata mace a gabanshi in banda matar shi.

“Allah kada ka ɗaura mani abin da ba zan iya ɗauka ba, ka bani mafita ta Alkhairi daga gareka ya Allah”, Addu’ar da ta yi kenan a ƙasan ranta.

Tana cikin wannan yanayi ne aka murɗa handle ɗin ɗakin, Fadila ce ƙanwarta ta shigo, gefenta ta zauna “Ya dai Yaya, har kin sallami marar lafiyan?”, Kai ta ɗaga “Yeah”, Fadila ta ce “Allah ya sa a dace a surgery ɗin”, Rahila ta ce “Amiiiin”, take kuma wannan addu’a ta Fadila ta tuna mata sanyin jikinta lokacin da suke ma Deeni aiki, kawai sai ta ji sam bata taɓuka abin kirki ba, tunda hankalinta ma ba a wurin aikin yake ba, gabanta na faɗuwa ta ce “Allah ka ba Deeni Lafiya”, Fadila ta ce “Sunan shi kenan?”, Rahila ta ɗaga kai “Umm!”, Kai kawai Fadila ta rausaya alamun “Toh.”

A can asibitin kuwa su Hajiya Ummah sun yi jugum, jira suke kawai Deeni ya falka su ga sakamakon aiki, aikuwa can bayan Isha’i ne ya falka da faɗuwar gaba, zagaye shi suka yi suna yi mashi sannu, hannunsa cikin na Khamis ya riƙa amsawa, lokaci ɗaya kuma yana jin fargabar da ke ransa tana ƙaruwa.

Dr. Jameel aka kira, wanda yana cikin waɗanda suka yi mashi aiki, Khamis ne ya tambaye shi “Dr. Ita wannan plaster yanzu za’a cire ta?”, Dan burinsu shi ne suga idanun Deeni a buɗe, Kai ya girgiza “Tukunna dai, Insha Allahu da lokaci ya yi za’a cire, ku dai mu yi ta masa addu’a kawai”, ƴan maganganu masu nutsar da zuciya ya faɗa masu, sannan ya fita.

A nan asibitin Khamis da Lalu suka kwana, Hajiya Ummah da Yaya Asiya kuma a gidansu Rahila suka kwana, sakamakon tursasa musu da ta yi. Washegari wurin ƙarfe tara ne suka dawo a asibitin, kuma a lokacin ne ake sa ran yaye shamakin dake tsakanin idanun Deeni domin gane idan ya samu lafiya.

<< Mutuwar Tsaye 11Mutuwar Tsaye 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×