Skip to content
Part 16 of 36 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Har sun kai bakin ƙofa wayar Deeni ta tunatar da su cewar sun manta da ita a kan gado, da hanzari Deena ta zare hannunta a cikin na Deeni ta nufi wurin wayar, “Dr. Rahila” da ta gani yana yawo a screen ɗin wayar ne ya haifar mata da faɗuwar gaba duk da cewar ta san ko wacece, don ba a wurin Deeni kaɗai ba, hatta su Asma’u da ba su taɓa ganin Rahila one on one ba, sai da Deena ta ji labarin ta a wurinsu.

“Waye ke kira?”, Deeni ya tambaye ta, saboda number Rahila na cikin odinary numbers da ring tone ɗaya ke jagoranta.

“Rahila ce”, ta ba shi answer lokacin da ta ƙaraso inda yake da ɗan hanzari, kai ya ɗan rausaya alamar “Okay”, tare da saka wayar a kunne haɗe da sallama.

Duk da ba a handsfree wayar take ba, amma Deena na jiyo yadda Rahila ta amsa ma Deeni sallama cike da sauti mai ɗaukar hankali. Take kumallon mata ya ida tuƙaƙato ta har ta sauke numfashi “Hum’um!” ba tare da ta sani ba. Deeni ya san wacece Deena a kishi, mafarin ya jawo matarsa a jiki, wanda ke nuna ta sa ranta a inuwa, shi yanzu idan ba ita ba, babu wata mace da take birge shi, bare har ya iya saurarenta da sunan soyayya ko aure.

Daga can Rahila ke tambayar shi “Ya Madam da baby Raihan?”, Aikuwa ya ce “Alhamdulillah, baby Raihan na can wurin mutanen gida, madam kuma ga ta a kusa da ni, sai ma ku gaisa.”

Rahila da ke can nesa, da kuma Deena da ke kusa da shi, ba wadda bai ji alamun firgitarta ba, dan kuwa ita dake can da stammering ta ce “O’okkkay! A bata wayar.?”

Deena ma kusan haka ne, lokacin da Rahila ta ce “Madam an wuni lafiya?”, Gabanta na muguwar faɗuwa gami da tsanar Rahila ta ce “Ƙƙalau, ya ƙoƙari?”, Rahila ta ce “Alhamdulillah”, raɗar da Deeni ya yi mata kan ta yi ma Rahila godiya ne ya sa ta faɗin “Masha Allah, ana ta ƙokari wurin ganin Oga ya samu lafiya, Allah ya saka da Alkhairi”, daga can Rahila ta ce “Ai ba komai Madam, Amiin ya Allah.”

Miƙa ma Deeni wayar ta yi “Karɓi”, yana karɓa suka ƙara ƴar magana kan ya kula da maganinsa sosai, duk da ta san baya sakaci, godiya ya yi mata, sannan suka yi sallama.

Miƙa ma Deena wayar ya yi “Riƙe Mani”, murya a dakushe ta ce “Ka rike kayanka, ko so kake a sake kira phone ɗin na hannuna”, ya fahimci dalili, murmushi mai sauti ya yi “Haka ne, bari in aje ta a wurina”, yana rufe baki ya zura ta a aljihun gaba.

Hannunta ya laluba ya riƙe, “Mu je toh”, maƙe kafaɗa ta yi “Uhmm-uhmm”, duk da ya san dalilin amma sai da ya tambaye ta “Why?”, bata yi zurfin ciki ba ta ce “Ita Rahila meye na kiran ka tana wani kashe murya?”, sam baya ɗaukar fushin matarsa da wasa, mafarin ya ce “Ban sani ba Deena, kuma ai haka take da sanyin hali, sam bata da hayaniya ko kaɗan”, da gatse Deena ta ce “Ko?”, Dariya ya yi tare da sakin maganar “Mu je in gaida su Ummah, idan mun dawo sai mu yi batun Rahilar, tunda ta tsaya maki a rai”, yana rufe baki ya shafi fuskarta da ta kicincine “Ki saki fuskar nan kada Asma’u ta yi maki dariya.” Da ƙyar ta iya haɗe damuwar da ke ranta suka fita.

Ta ɓangaren Rahila kuwa tamkar ta mutu sakamakon muryar Deena da ta ji, musamman kuma da ya kasance a kusa da Deeni take, garden suke suna shan iska, amma bata san lokacin da ta dawo cikin gida ta shige ɗakinsu ba.

Daga kifen da take tana kukan zuci ta ce “Ya Allah, ka san irin tsananin son da nake ma bawan nan naka Deeni, dan girman zatinka ka sassauta mani ta yadda zan samu sauƙi a zuciyata”, wasu hawaye masu kaurin gaske ne suka ɓuɓɓugo mata a idanu suka dira a kan filon da ta kifa kanta a kai.

Haƙiƙa Rahila tana son Deeni duk da naƙasar da ke tare da shi, kuma da a ce zata same shi, toh zata taimaka mashi da dukkan abin da zata iya, toh da alamun shi ta matarsa yake ba ta ita ba, bare ta sa ran zai iya kula ta.

Wani sashe na zuciyarta ne ya fara faɗa mata ta yi ta kanta, Deeni ko bai da mata da wahala tashin hankalin da ke ransa ya bar shi ya iya kula wata mace, don haka ta sa ma zuciyarta salama, sannan ta cigaba da addu’ar neman mafita a wurin Allah. Sosai kuwa ta ɗauki huɗubar wannan sashe na zuciya, mafarin ta tashi kamar wadda aka zungura, saukowa ta yi daga kan gadon tare da nufar ban ɗaki, wanke fuskarta ta yi, tana fitowa ta gyara ta da light make’up ɗin da dama akwai ta a fuskarta, ta yadda ba za’a gane ta yi kuka ba idan ta koma can cikin garden wurin ƴan’uwanta.

Dr. Safiyya kuwa ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba lokacin da ta gane Deeni ne mijin Deena, saboda sun taɓa haɗuwa a wata seminar da aka yi ma manyan Doctors na Nigeria a Lagos. Ƙaƙorin Deeni a wurin Seminar ne ya ƙara ɗaga darajar ƴan arewa a kudancin Nigeria, wanda ba ƴan arewa ba, hatta ƴan kudun sun yi alfahari da kasancewar shi ɗan Nigeria, don ya ƙara ɗaga musu darajar ƙasa a wurin fararen fatar da suka halarci seminar.

Sannan abin da ya sa bata san akwai alaƙar surukuta tsakaninta da Deeni ba shi ne, lokacin da aka yi hidimar bikinsu da Deena bata ƙasar, haka lokacin da Deenar ma ta haihu sun yi tafiya Abuja. Sannan dai Uwar gayyar ba wani son shi take ba, bare ta nuna ma duniya shi cewar shi ne surukinta.

Idanunta a kansa ta ce “Sannu Dr. Allah ya baka lafiya”, cike da girmamawa ya ce “Amiin ya Allah, thank you Ma”, kai kawai ta jinjina, don ranta na faɗa mata bakin jama’a kaɗai zai iya cinye Deeni ya hana shi aiki, bare kuma mahassada na fili da na ɓoye.

Ita kuwa uwar gayya tuni ta ƙarasa yanke hukuncin raba auren, musamman ganin Deena ce ta yi mashi jagora har ɗakin, kowa ya ji daɗin yadda ta ruƙo hannun mijinta har ya samu wuri kan kujera one seater ya zauna in banda ita, kawai abin da ranta ke faɗa mata Deena zata shiga gararin rayuwa, don jagora kaɗai ta ishe ta jidali a gidan aure, don duk abin da ya kamata ya yi da kansa, toh ya dawo kan Deena, ga ƙaramin yaro, shikenan sai yadda Allah ya yi da ita.

Wannan duk tunaninta ne wanda zuciya ta saƙa mata, kuma ta zauna daram a kansa, kawai lokaci ne take jira, wanda shi ma saura ƙiris.

Kamar Hajiyarsu Deeni ta san me take ta saƙawa da kwancewa a zuciyarta, cewa ta yi “Toh Hajiya Hadiza, yaushe su Raihan zasu dawo mana, mu fara shirin tarbar su.?”

Wani irin ras Umman Deena ta ji, kamar wadda aka nemi ta bada rayuwarta, sam ita bata shakkar faɗin abin da ke ranta ko da a kaikaice ne, cikin dubara irin tata ta ce “Tun yanzu Hajiya, a ganina tunda Deeni ba lafiya ne da shi ba, a bari ya ƙara samun sauƙi ko?”, Ko da dai Hajiyarsu Deeni bata shekara ɗari ba, toh amma ai ta kwana fiye da dubu ma a duniya, don haka ba wani jurwaye mai kama da wankan da Umman Deena zata yi mata, cewa ta yi “Ko Hajiya Hadiza?”, ta kuwa ce “Eh Hajiya”, tare da ɗorawa da “Ga Ɗanyen Jego, kin ga abin zai yi ma Deena yawa”, Dr. Safiyya na jin komai, karɓar zancen ta yi ta hanyar jefo tambaya “Babu masu aiki ne?”, Hajiyarsu Deeni ta ce “Akwai kuwa, kuma ma ai yanzu zaman bai yi dole sai an samar musu mataimaka, don Deena ba zata iya ɗaukar wannan nauyin ita kaɗai ba”, Dr. Safiyya ta ce “Gaskiya ne”, yayin da Umman Deena ta ce “Toh shikenan Hajiya, sai an fidda lokaci sai a faɗa maku”, Hajiyarsu Deeni ta ce”Toh shikenan Hajiya Hadiza.”

Deena da Deeni haɗe da Asma’u kuwa na can tsakar gida basu san wainar da ake toyawa ba, hirar su kawai su ke mai cike da nishaɗi. Deena kuma burinta bai wuce ta sake keɓencewa da mijinta ba, Asma’u na shigewa kitchen ta raɗa mashi “Yaya don Allah mu je ɗakinka”, shi ma abin da yake so kenan, cikin dubara ya miƙe ya yi gaba, da wayau Deena ta ɗaga murya “Yaya bari ina maka jagora”, tana rufe baki ta riƙe mashi hannu, Asma’u kuwa bata taɓa zaton haɗin baki ne suka yi ba wurin tashi.

Suna shigewa ɗakin tun a tsakiyar falon ta shige jikinsa ta yi shiru tare da kwantar da kai a ƙirjinsa, zagayo da hannayensa ya yi a bayanta gami da faɗin “”Wife!”, ba tare da ta ɗago kanta ba ta amsa mashi, cewa ya yi “Me nene?”, Saboda in dai ta yi irin wannan sanyin jikin toh akwai magana”, ɗago da kanta ta yi, cikin sanyin murya ta ce “Wacece Rahila a wurinka, and why she always calling you? And you know ne bana son a raɓe ka, saboda tsaf za a iya raba ni da kai”, dogon numfashi shi ya sauke tare da amsa mata tambayarta, “Rahila ba kowa bace sai doctor da ta yi tsaye wurin ganin na samu lafiya, and babu wata alaƙar da ta wuce mutunta juna ni da ita, ina ganin ƙimarta sosai, itama tana ganin tawa”, katse shi ta yi “Kana son ta kenan?”, Ya ce “Nope, ai so daban, ganin ƙima daban ko?”, ba don ta gamsu ba ta ce “Haka ne”, ya ce “Yauwa, kawai ki kwantar da hankalinki, duk duniya ke kaɗai ce matata, ke nake so ke da yaron da kika haifa mani, ko lafiya ta ƙalau ba zan iya son wata ba, bare yanzu da nake makaho.”

Makahon da ya kira kansa ne ya chanja akalar hirar a take, kamar zata yi kuka ta ce “Ka daina kiran kanka da makaho”, cewa ya yi “Ai makahon ne Deena”, ta ce “Ba wani nan”, ya ce “Toh miye?”, Shiru ta yi saboda ya fi ta gaskiya.

Idanunta cike da ƙwallan tausayi ta ce “Allah ya baka lafiya mijina”, tamkar zasu maida juna a ciki suka kasance.

Can Deena ta jiyo muryar Asma’u na kiran ta, da hanzari suka rabu, Deeni da ya kusa rasa kansa ya ce “Ki matsa ma Mommah cewar zaki dawo please”, kai kawai ta jinjina sannan ta fice.

“Daudawa uwar Aure”, Asma’u ta faɗa cike da tsokana, dariya kawai Deena ta yi “Ya aka yi ne?”, Ta ce “Kiran ki ake a ɗaki”, toh Deena ta faɗa, sannan ta nufi ɗakin.

Cike da ladabi ta ce “Ga ni”, dan bata san wa ke kiran ta ba, Dr. Safiyya ce “Gida zamu tafi”, ba dan Deena ta so tafiyar ba ta ce “Toh Mammy.”

Shirin tafiya suka yi, bayan sun fito tsakar gida ne Dr. Safiyya ta dubi Deeni da ke tsaye a ƙofar ɗakunsu, Dr. Zan karbi number ka a wurin Deena, zamu yi magana, “Toh” ya ce tare da yi masu godiya, har waje shi da Asma’u suka raka su, bayan sun tafi ne Asma’u ta riƙe mashi hannu “Yaya mu je ciki”, zare hannunshi ya yi tare da faɗin “Bari in mayar da kaina Asma’u.”

Idanun Asma’u a kansa ta ce “Toh Yaya”, lokaci ɗaya kuma tana tunanin yadda zai iya shigar da kansa gida.

“Allah Sarki, sannu dafta”, kamar daga sama suka ji muryar Inna Lami tana faɗin haka, a bangaren da Deeni ya ji sautinta ya juya, lokaci ɗaya kuma hannunsa na dafe da bango, “Ah! Inna barka da yammaci”, ya faɗa cikin girmamawa, kasantuwar ta na dattijuwar da kowa ya sani a unguwa.

Amsawa ta yi “Yauwa barka dai, ya jikin?”, Ya ce “Alhamdulillah”, bayan ta amsa gaisuwar da Asma’u ta yi mata ne ta ce mashi “Ciki zaka shiga?”, ya ce “Eh”, maganganu gare ta da yawa a baki, mafarin ta ce mashi “Mu je in maka Jagora”, karɓar sandar ta yi, yayin da Asma’u ta rufa musu baya suka shiga ciki.

Fitowar Hajiyarsu Deeni kenan daga ɗakin suka shiga, a nan cikin varender suka zauna kowanen su kan plastic chair, yayin da Deeni kuma ya wuce ɗakinsu.

Bayan sun gaisa ne Inna Lami ta ƙara jajajnta ma Hajiyarsu Deeni, sannan ta ɗora da faɗin “Hajiya, wannan ciwon na Dafta babu sa hannu kuwa?”, Hajiyarsu Deeni ta ce “Sa hannu kuma Lami?”, Ta ce “Eh, kin san yanzu mutane basu da gadonka, amma suna da gadon batunka, musamman yadda ɗaukaka ta zo mashi a lokaci ɗaya.”

Sai da hajiyarsu Deeni ta nisa kafin tace “Allah ne masani Lami, idan ma wani ya yi ai don kansa, bare na fi jingina lamarin a wurin Allah”, Lami ta ce “Haka ne, amma ni kuwa akwai wani mai bada taimako a nan bayan gari, idan kin amince sai mu je ko da Hajiya Umma ne a gani ko za’a da ce”, Hajiyarsu Deeni ta ce”Ai ba dole sai da Hajiya Umma ba Lami, ke kaɗai ma zaki iya zuwa, tunda duk an zama ɗaya.”

Asma’u dake ɗaki duk ta ji hirar su, sai bayan tafiyar Lami ne ta ce “Hajja na ji kuna ta magana da Lami, don Allah kada ki biye mata har a saɓa hanya wurin neman magani” cewa ta yi “Haba Asma’u, so nake mu rabu cikin ruwan sanyi ne, amma ba da ni ba”, Asma’u ta ce “Yauwa.”

Hajiya Hadiza kuwa tun a mota ta nemi tada ballin cewa Deena ba zata koma ba, sai da Dr. Safiyya ta tattashe ta da magana, a kan ta bi komai a hankali sannan ta yi shiru.

Deena kuwa tuni ta ɗimauce, don abin da zai raba ta da Deeni mutuwa ce kawai, suna komawa gida ta yi ɗakinta ta fara kuka.

A falo kuwa Dr. Safiyya ta shiga nuna ma Ummanta illar kuskuren da take shirin tafka wa, bakam ta yi kamar ta ji nasihar, sai bayan ta tafi ta iske Deena a ɗaki, sai da ta ƙare ma ta kallo tare da fahimtar kuka ta yi kafin ta ce, “Har kin fara kukan rabuwa da mijinki ko?”, Kai Deena ta girgiza “A’a Mommah.”, lokaci ɗaya kuma ta goge hawayen da suka malalo mata a kumci da bayan hannu.

Uwa da ɗiya sai Allah, take wani irin tausayin Deena ya kama ta, sai dai duk da haka bai sa ta karaya a kan ƙudurinta ba, sai dai ya sassauta mata fusatar da ta yi.

Zama ta yi gefen gado tare da sassauta Murya “Deena”, cikin dakusasshiyar murya Deena ta amsa “Na’am”, lokaci ɗaya kuma ta kalli mahaifiyarta.

“Iyayen mijinki so suke ki koma ki ci gaba da yi ma ɗansu bauta, ni kuma a ganina ki haƙura da Deeni tun kafin da ƙuruciyarki ki faɗa garari, ko ya kika ce..?”

<< Mutuwar Tsaye 15Mutuwar Tsaye 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×