Idan har akwai abin da Deena za ta iya faɗa dangane da wannan al'amarin, toh shi ne a bar mata mijinta, domin shi ne cikamakon farincinta kamar yadda mahaifiyarta ta fi kowa sani, toh amma bakinta ba zai iya furtawa ba, saboda gudun sake samun saɓani tsakanin ta da mahaifiyarta.
Kasa ɗago kanta ta yi, bare har ta iya magana, sai ma wani sabon kuka da ya ƙwace mata ba tare da ta shirya ba.
"Inyee! Zan raba ki da rayuwarki ko?", Cike da izza irin ta uwa Maman Deena ta faɗi haka, ƙasan ranta kuma. . .