Skip to content
Part 17 of 26 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Idan har akwai abin da Deena za ta iya faɗa dangane da wannan al’amarin, toh shi ne a bar mata mijinta, domin shi ne cikamakon farincinta kamar yadda mahaifiyarta ta fi kowa sani, toh amma bakinta ba zai iya furtawa ba, saboda gudun sake samun saɓani tsakanin ta da mahaifiyarta.

Kasa ɗago kanta ta yi, bare har ta iya magana, sai ma wani sabon kuka da ya ƙwace mata ba tare da ta shirya ba.

“Inyee! Zan raba ki da rayuwarki ko?”, Cike da izza irin ta uwa Maman Deena ta faɗi haka, ƙasan ranta kuma tana jin kamar ta yi kukan itama, saboda yadda Deena ke wannan kukan da wahala idan ba matsala zata bata ba, kamar yadda ta yi a can baya, lokacin da ta so hana ta auren Deeni.

Kai Deena ta girgiza tare da ɗago kanta ta dube ta “A’a Mommah”, wani irin kallo ta yi mata sannan ta ce “Ba wani a’a, ke dai kina son mijinki, kuma ba iya iya rabuwa da shi”, tarbar numfashinta Deena ta yi da faɗin “Ba haka bane ba Mommah”, lokaci ɗaya kuma ta ruƙo mata hannaye, saboda ta ga alamun wasan na shirin chanja salo, janye hannyenta ta yi ta ce “Toh ya abin yake Deena, faɗa mani ina jin ki.”

Deena bata san me zata faɗa ba wanda zai ɓoye tsananin son da take yi ma mijinta, wanda kuma wannan kukan da take kaɗai shaida ce da ke nuna bata iya rayuwa idan ba da shi ba. Faɗa mai tattare da illar ci gaba da rayuwa da Deeni ta shiga yi mata, ita kuwa ba abin da take fahimta a cikin faɗan bare har ta ɗauki abin da zai amfane ta a ciki, har kuma Maman ta ƙaraci faɗanta tare da ficewa daga ɗakin Deena bata yi magana ba.

Kitchen ta nufa tana faɗin “Na rantse ba zan lamunci ƴata ta koma baiwa ba, ko ta ƙi ko ta so sai ta rabu da shi”, ɗaya daga cikin mai aikinta da ta tarar a kitchen ɗin ta ce “Hajiya ke da wa?”, Cike da ƙunar rai ta ce “Deena mana, a ce yarinya ba zata yi ma kanta karatun ta nutsu ba ta san abin da zai fidda ta ba, yanzu wancan mijin na ta so take ta ƙare ƙuruciyarta a yi masa jagora?”, Duk da Turai bata san takamaiman maganar ba, amma ta fahimci inda Maman Deena ta dosa, mafarin ta tambaye ta “Yanzu sun ce ta koma ne?”, Umman Deena ta ce “Sun ce mana, ni kuma ban yarda ba sam, ko dai su bari ya samu lafiya, ko kuma a raba auren, don ba baiwa na haifa musu ba”, cike da neman wurin zama Turai ta ce “Gaskiya ne Hajiya, duka Deenar guda nawa ce da za a ƙalla da mata wannan wahala”, Maman Deena ta ce “Kin gani dai Turai”, Turai ta ce “Nima in dai ƴata ce ba zan yarda ba sam”, nan Turai ta yi ta ma Umman Deena famfo, aikuwa ta harzuƙa sosai. Shi ya sa Turai na ɗaya daga cikin masu aikin da basu da farinjini a gidan, saboda ƙulla munafurci.

Deena kuwa da ace ta rabu da Deeni, gwara mutuwa ta ɗauke ta, don in dai da ranta, bata san ya zata yi rayuwa a duniya ba tare da shi ba. Tunda mahaifiyarta ta fita ta dasa sabon kuka, a cikin ranta take addu’a tana faɗin “Ya Allah kada ka bari a raba ni da mijina, saboda ba zan iya rayuwa idan ba da shi ba.”

Kamar Deeni ya san halin da take ciki ya danno mata kira ta a waya, sai dai har ta tsinke bata ɗaga ba.

Sai da ya kira har a karo na biyar ne ta iya ɗago kanta daga kwantar da shi ɗin da ta yi da kan fillow ta dubi wayar, tsagaita kukan ta yi, sannan murya a disashe ta ɗaga kiran.

Yana jin muryarta ya ce “Subhanallah, me ya faru”, kasa magana ta yi sai dai shaesshekar kuka, daga can ya ce “Mommah ce ko?”, don ya san tatsuniyar gizo bata wuce ƙoƙi, tamkar a gaban shi take ta ɗaga kai, ya ce “Oh Sorry, ki yi haƙuri, kuma ki kasance mai biyayya a wurin Mahaifiyarki”, ƴan maganagnu ya faɗa mata saboda duk jikinsa ya mutu shi ma, daga bisani suka yi sallama.

A ƙasan ran Deena ta ce “Don baka san halin da nake ciki ba ne zaka ce in yi biyayya”, toh amma kuma maganarsa ai gaskiya ce, abin da kenan ya kuma zo mata a rai a take.

“Ya zan yi?”, Ta tambayi kanta tare da rushewa da kuka, lokaci ɗaya kuma ta haɗe kai da gyuiwa tana rusar kuka, wanda ta kasa gane ba shi ne kaɗai mafita a wurinta ba.

A ɓangaren Deeni kuwa duk ya kasa sukuni, yana son ya sake kiran ta, amma baya son jin ta a damuwa, domin damuwar shi ma yake shiga, jugum ya yi akan sallayar da ya gabatar da nafilar da ya saba yi kafin ya yi barci, “Me ya haɗa Deena da Mamanta ne?”, Ya tambayi kansa, ba shi da amsa, don haka sai dai ya ce “Allah ya kyauta.”

Wayarsa ce ta fara ruri, an yi sa’a kuwa Lalu ya shigo, tambayar sa ya yi “Waye?”, don kwata-kwata baya jin amsa kiran kowa, amsa ya ba shi “Rahila ce”, kai kawai ya jinjina tare da karɓar wayar ya aje ta a gefensa, har ta ƙaraci rurinta bai ɗaga ba.

Wani kiran ne ya sake biyo wancan, still shi ma bai ɗaga ba, a na ukun ne Lalu da tuni ya zauna a gefen gado ya ce “Kana ji tana ta kira fa”, muryar Deeni ba wani karsashi ya ce “Bana jin wayar yanzu, idan na tashi zan kira ta”, sosai Lalu ya fahimci yana cikin ƴar damuwa, tambayar sa ya yi “Lafiya dai ko?”, amsa ya ba shi “Lafiya ƙalau”, ba dan Lalu ya gamsu ba ya ce “Shikenan.”

Saƙon Rahila ta manhajar WhatsApp ne ya shigo wayar Lalu, inda ta rubuta “Allah ya sa dai lafiya, na kira wayar Dr. Three times bai yi picking ba”, sai da Lalu ya kalli Deeni sannan ya yi mata reply da “Bana gida, sai zuwa anjima zan koma”, gajeren reply ta yi mashi “Okay, thank you”, bai wani damu ba, duk da yana son hira da ita, yanzu kawai abin da ke gabanshi shi ne harkar Crypto, me zai samu, sannan kuma me ya rasa, tunda harka ce mai hawa da saukar farashi.

Baro WhatsApp ɗin ya ya yi gami da dawowa Telegram, bai wani ɓata lokaci ba ya shiga fara mining duka projects ɗin da ya yi register, don a ganinsa wannan harkas ta fi, shi ya sa gashi nan crypto na shirin maida shi wani Alhaji, wanda hatta mahaifiyarsu da danginsa suna alfahari da hakan, saboda duk sadda ta fashe mashi, sai kowa ya shaida.

A ɓangaren Rahila kuwa yau kaɗai da ta taɓa kiran Deeni bai ɗaga ba hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, musamman da ta sake kira ta ji line busy, kuma bai biyo kiran ba kamar yadda ya saba, “Ko ya fara gajiya da ni ne”, ta faɗa a ranta, lokaci ɗaya kuma ta gyara kwanciyarta a kan kafaɗa tare da lumshe idanu.

Wata irin ƙuna take ji a ranta, wadda maganinta ɗaya ne ta samu zuciyar Deeni, kuma abu ne mai matuƙar wahalar gaske, kamar yadda ta saba ta shiga ba zuciyarta magana, a kan ta yi ma kanta ƙiyamullaili ta cire Deeni a rai, “Ta ya?”, Ta tambayi kanta, bata sani ba, don cire so a zuciya abu ne wanda sai da taimakon Allah kawai, amma mutum shi kaɗai ba zai iya ba, mafarin a ƙasan ranta ta ce “Allah ka dubi raunina, ka yaye mani wannan jarabi da ke hanani sukuni a rayuwa, don kuwa duk wanda ya san Rahila da exposure, zai yi mamakin yadda yanzu ta yi sanyi, dan zata iya kwashe lokaci mai tsawo a wuri, ba tare da an san tana wurin ba.

A wannan dare rutsum Rahila bata rumtsa ba, kamar yadda ta saba ukun dare na bugawa ta miƙe ta yo alwala ta kabbara sallah. A irin wannan lokacin ne Deena itama ta kai maƙura wurin kai kukanta a wurin Allah, dukkaninsu Deeni suke yi mawa, ita wannan fatanta Allah ya bata shi, ita kuma Deena tana tsoron rasa shi.

Shi kuwa duk ba ta su yake ba, don ya san Deena matarshi ce, shi kuma lafiya yake nema a wurin Allah, don ita ce babbar matsalar shi, mafarin shi ma a wannan lokacin kan shi na ƙasa yana addu’a.

Ya sallame sallah kenan ya ji kiran Deena ya shigo wayarshi, sai da ya kai salatin da ke bakinsa sannan ya ɗaga kiran tare da sallama, bayan ta amsa ne ya ce “Baki yi barci ba?”, Daga can ta ce “Uhmm”, cike da kulawa ya ce “Why?”, ta ce “Bana iyawa”, ya kuma tambayar ta “Wai meye matsalar ne?”, Shiru ta yi, don ba zata iya faɗa mashi ba, a wannan karon ma bai matsa mata ba, ya san da bakinta zata faɗa mashi.

Sai dai ya lallashi matarshi da maganganu masu daɗi, hakan ya bata damar faɗin “Allah ya bar mani kai mijina”, cike da jin daɗi ya ce “Amiiin”, Sallama suka yi, sannan ya cigaba da azkar har aka kira sallar asuba.

A ɓangaren Mahifiyar Deena kuwa ita ma bata yi barcin ba, sai dai ta juya nan ta juya can, Alhaji Lawan ya lura da yanayinta sosai, daga kan sofar da yake yana aiki a system ɗinsa ya ce “Madam, wai lafiya”, pretending ta yi ta hanyar tamabayar shi “Me ka gani?”, Ya ce “Na ga kin kasa barci”, ta ce “Ai bana ji ne”, ya ce “Ko?”, Dan bai yarda ba, saboda abin da ke hana ta barci ba ƙarami bane, kasantuwar hidimar da take yi da rana.

Cigaba da aikinsa ya yi, ita ma ta juya mashi baya yadda zata samu damar yin tunaninta son rai. Idanunta a lumshe ta ce “Ya zan ɓullo ma wannan al’amari?”, Dan kuwa ta fi son Deena ta furta da bakinta a kan zata rabu da Deeni, ba wai a tursasa mata ba, toh kuma wannan abu ne mai wahalar gaske, wanda dole sai ta tashi tsaye sosai.

Washegari da safe sun zo breakfast Deena bata fito ba, kuma a ƙa’ida duk weekend tare suke breakfast saboda kowa na gida, tambayar ta Alhaji Lawan ya yi “Ina Deena?”, amsa ta ba shi “Tana ɗakinta”, kai ya ɗan rausaya, tare da ɗaukar waya ya shiga kiran Deena, tana ɗagawa ya ce “Breakfast is arrived”, daga can ta ce “Toh Daddy.”

Ba’a fi minti biyar da wayar ba sai ga Deena ta sauko, yanayin fuskara kaɗai ya tabbatar da tana cikin damuwa, dan kuwa ko light make-up babu, bare kuma heavy one.

Babbar mantuwar da ta yi ne Alhaji Lawan ya tuna mata ta hanyar faɗin “Ina Raihan ɗin?”, Take kuwa ta tuna, basarwa ta yi ta hanyar faɗin “Barci yake.”

“Da mutum a ɗakin ne?”, Mamar ta tambaye ta, “A’a”, ta faɗa, dan mai aikin da suke kwana tare tana kitchen.

“An faɗa maki ki daina baro yaro upstairs shi kaɗai”, Alhaji Lawan ya faɗa okaci ɗaya kuma yana karantar yanayinta, cikin faɗa Ummanta ta ce “Ai ba ji take ba, shashahar banza.”

Kai Alhaji Lawan ya girgiza, lokaci ɗaya kuma ya ce “A’a”, tamkar ba da ita yake ba ta shiga serving ɗinsa, ba’a jima ba sai ga Deena ta sauko ɗauke da Raihan a kafaɗarta.

Bayan ta zauna ne cike da girmamawa ta gaida Alhaji Lawan “Daddy barka da safiya”, cike da tausayinta ya amsa “Lafiya ƙalau Deena, ya Raihan”, amsawa ta yi da “Lafiya ƙalau yake”, ya ce “Masha Allah.”

Juyawa ta yi wurin Mahaifiyarta da ke shirin kai mug a baki, “Momma barka da Safiya”, sai da ta yi kurɓi tea ɗinta sannan ta amsa mata, “Lafiya.”

Shi dai Alhaji Lawan bai ce musu komai ba, amma yana observing abin da yake faruwa, musamman da ya ga Deena ba wani breakfast ɗin kirki ta yi ba, hakan ne ya tabbatar mashi da akwai babban al’amari, wanda jikinsa ya faɗa mashi batun Deeni ne, dan lamarinsa ne kaɗai ke dauwamar da walwala ko rashinta a wurin Deena.

Sai da Deena ta gama tsakurar omelate ɗin da ke gabanta ta tashi ne ya ke tambayar Hajiya Hadiza “Me ke faruwa ne.?”

Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce “Jiya bayan mun je gidansu Deeni, shi ne Mamansa ke batun dawowar Deena”, tana kai wa nan ta yi shiru.

Cewa ya yi “Ina sauraron ki”, lokaci ɗaya kuma ya ɗan rausaya kai, ɗorawa ta yi da “Shi ne nake ganin bai kamata a ce yanzu Deena ta koma ba” ya ce “Saboda me?”, Ta ce “Saboda wahalar zata yi mata yawa, ga goyo, ga kuma ɗawainiya da miji”, wata tambayar ya sake jefo mata “Toh sai yaushe zata koma?”, Shiru ta yi, dan babu rana, ya kuma maimaita faɗin “Na ce sai yaushe zata koma.?”

“Alhaji, gaskiya idan ra’ayina ne Deena ba zata koma ba, saboda ban haife ta dan ta yi ma Deeni wahala ba.”

Abin da dama ya ke son ji kenan, zama ya gyara tare da faɗin “Hajiya Hadiza, in baki shawara?”, Ta ce “Eh”, ya ce “Ki bar Deena ta zauna lafiya, tunda na tabbatar da tana son mijinta a haka, idan ba haka ba duk matsalar da ta biyo baya laifinki ne?”, Tarbar shi ta yi da faɗin “Ba wata matsala da zata faru Insha Allah”, ya ce “Toh shikenan, wanda bai ji bari ba dai zai ji wohoho!”

Nuna mashi ta yi ita fa ba don ta cutar da Deena ko Deeni ba ta ke son aurensu ya rabu ba, sai dai kawai don ta raba Deena da wahala, saboda a ƙuruciyar da take da ita ba zata iya ɗaukar nauyin Deeni ba, ga yaro ƙarami, hakan ba ƙaramar wahala zai bata ba.

Sosai ya ɗan fahimce ta, shawara ya bata a kan duk da haka kada ta yi gaugawa wurin yanke hukunci, nuna mashi ta yi ita yanzu shawarar Deena kawai take jira, muddin ta amince, toh zata raba auren, idan kuma bata amince ba, toh ta fidda hannunta a lamarin Deena.

Cewa ya yi “Ba wannan maganar ta kin fidda hannunki a lamarinta don ta zaɓi zama da mijinta”, cikin fusata ta ce “Toh me zan yi da ita, tunda ta zaɓi mijinta a kaina! Alhaji duk da Deena kaɗai na haifa, bana jin baƙinciki don na rasa ta, tunda ita ba ƴar arziki ba ce.”,

A fusace shi ma ya taka mata birki “Akan wani ra’ayinki zaki ɓata ƴarki? Toh ki iya bakinki Hadiza, kada ki manta uwa ce ke, bakinki kaifi ne da shi fiye da reza”, ba don ranta ya so ba ta yi shiru, saboda ya fi ta gaskiya.

Faɗa sosai ya yi mata a kan ragon azancin nan da ta nace a dole sai ta yi, ko kusa bata fahimci inda ya dosa ba, sai ma ta tashi ta bar masa dining ɗin, da idanu ya bi ta tare da faɗin “Allah ya ganar da ke gaskiya Hadiza.”

<< Mutuwar Tsaye 16Mutuwar Tsaye 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×