Skip to content
Part 19 of 23 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Hausawa suka ce “So hana ganin laifi”, take Rahila ta tabbatar mashi da ta karɓi uzurinsa, ya kuma ji daɗi sosai saboda uzuri na ɗaya daga cikin abin da ke masa daɗi.

Hira suka sha sosai, har yake tsokanar ta yaushe ne aurenta don su fara shiri? Wayancewa ta yi tare da faɗin “Idan time ya yi zan faɗa maku ai”, cike da yi mata kyakkyawan fata ya ce “Allah ya nuna mana lokacin lafiya”, daga can ta ce “Amiiiin”, duk da a zahiri da baɗini shi ne take fatan ya zama angonta.

Suna cikin magana a kan lafiyar idanunsa ne kira ya shigo wayarsa, ce ma Rahila ya yi “Ina zuwa please!”, murya can ciki ta ce “Okay”, lokaci ɗaya kuma ƙit! Ta katse kiran.

Deeni kuwa ba tare da ya san mai kira ba ya amsa kiran da ya shigo masa, muryar babbar mace ya ji ta yi mashi sallama, amsawa ya yi tare da gaishe ta, bayan ta amsa ne ta faɗa nashi Dr. Safiyya ce, take Deeni ya gane ta, tunda ya san da maganar kiran. Cike da girmamawa ya ce “Na gane Maa! Ya aiki?”, Ta ce “Alhamdulillah, ya jikin naka?”, Cikin raunin murya ya ce “Da sauƙi”, duk da ba wani sauƙi sai a wurin Allah kawai.

“Masha Allah, Allah ya ƙara lafiya”, ya ce “Amiiiin Maa, Nagode sosai.”

Ɗan shirun da ya ratsa tsakaninsu ne ya bata damar zayyana mashi manufar kiransa, inda ta fara da tambayar shi ya matsayin aikinsa ne.?

Wannan tambaya ta tunatar da Deeni abin da ya manta dangane da matsyar aikinsa, saboda ko a asibintsu kwana biyu bai ji motsin kowa ba, hatta MD da ke ta ƙoƙarin wurin ganin ya dawo a bakin aikinsa shi ma ba wani labari. Don ma salary ɗinsa da ke shigowa bai datse ba, shi ya sa bai damu ba, hankalinsa ya fi karkata ne kawai a wurin ganin ya samu lafiya.

Amsa ya bata da “Yanzu dai a wurina tamkar babu wannan aikin har sai na samu lafiya”, ta ce “Kamar ya kenan?”, Ya ce ‘Saboda management ɗinmu su ma ba wata magana a wurinsu, mai yiyuwa sun ga ba zan iya ba, duk da every month Ina karɓar salary na.” Cewa ta yi “Okay”, ɗan shiru ta yi, sannan ta sake tambayar shi, “A wurinka me ka shirya?”, Ya ce “Nothing”, ta ce “Why?”, Ya ce “Because I am not capable to work as am blinder”, cike ƙarfafa mashi guiwa ta ce “You can.”

Tabbas a ransa ya san zai iya, toh amma ya san da wahala mutane su gamsu da haka, mafarin ya ce “No Maa”, ta ce “Ka sa ma ranka zaka iya”, ya ce “Insha Allahu.”

Faɗa mashi ta yi rasa nagartaccen Dr. Kamarshi ba ƙaramin ƙalubale ne ga al’umma ba, don ta yi bincike a kansa, don haka dole a organization ɗinsu na likitoci su yi wani abu domin ceto rayuwarsa da ta al’umma baki ɗaya wurin ganin ya samu lafiya, kasantuwar tana ɗaya daga cikin officials ɗin ƙungiyar, abin da ya rage mata shi ne tattara data a asibitin su, idan ta gama duk abin da kenan zata zo har gida su yi magana.

Ya ji daɗi sosai, godiya ya yi mata, sannan suka yi bankwana.

A ɓangaren Rahila kuwa ta gama cika da tumbatsa, saboda ta yi zaton Deena ce ta kira shi har ya katse mata waya don ya amsa kiran matarshi, wannan abu ne ya cire mata son komai saboda tsabar baƙinciki, breakfast zata yi amma ɗaya ta ji ya fice a ranta, duk da abinda ta tashi da sha’awarsa ne wato soyayyar awara, sai kuma black tea, ƴar wadda ta ɗan ci ma ji ta yi ta tokare mata wuya, mafarin ta matsar da ita gefe, cup ɗin tea ta kai baki don ta samu salama, kawai sai amai ya taso mata, da sauri ta nufi ban ɗaki ta shiga sheƙa shi, ɗaya daga cikin maids na gidan mai suna Karime ce ta shigo don fidda kayan da suke buƙatar wanki ta tarar da Rahila a ban ɗaki, da sauri shiga ban ɗakin bakinta na faɗin “Subhanallah, lafiya?” Kasa magana Rahila ta yi, sai dai ta ɗaga mata hannu. Sannu ta riƙa yi ma Rahila har ta gama aman tare da buɗe mashi ruwa ya wuce.

Jiri na ɗibar Rahila ta fito ban ɗakin tare da kwantawa kan gado, cikin muryarta da ke fita da ƙyar ta ce Karime “Rufe ni da blanket”, rufa mata blanket ɗin Karime ta yi, sannan ta fice daga ɗakin da nufin sanar da mahaifiyar Rahila, bata jima ba sai ga ta a ɗakin, cike da mamaki ta zauna gefen gado, don Rahila bata daɗe da fitowa ɗakinta ba.

“Meke faruwa ne?”, Ta tambaye ta, lokaci ɗaya kuma ta ɗan yaye blanket ɗin. Take gululun da ya tokare ma Rahila wuya ya fashe, cikin muryar kuka ta ce “Zazzaɓi nake Ammi”, cike da damuwa ta ce “Amma yanzu zazzaɓin ko?, Kai Rahila ta ɗaga daga kwancen”, cikin kulawa “Allah ya baki lafiya.”

Rahila ta ce “Amiiin”, duk da a ƙasan ranta ta san Deeni shi ne warakar ciwonta. Amminsu bata bar ɗakin ba sai da ta kira Dr. A kan ya zo ya duba Rahila ya ga kalar zazzaɓin da ke damunta, wanda a ƙa’idar gidansu ba sa shan magani ba tare da umarnin likita ba, duk don su kare kansu daga faɗawa wasu cutukan.

Tamkar ba rai a jikin Rahila ta kasance, don kuwa ko motsi bata yi, sai dai zuciyarta ce kaɗai ke aiki, yayin da ta rasa ya zata yi, don kuwa duk yadda ta so kauda al’amarin Deeni a ranta sai ta kasa, musamman idan ya haɗa da lamarin matarsa, don yanzu kishi ne ke ta ɗawainiya da ita, idanunta na fitar da hawaye ta shiga miƙa lamarinta ga Allah, wanda shi kaɗai ne zai yi mata abin da ya dace, ko dai ya bata Deeni, ko kuma bata wanda ya fi shi.

A irin wannan lokaci ne Deena ta kasance cikin ƙuncin da ko rabin na Rahila bai kai ba, don kuwa ita ta san waye Deeni a ciki da wajensa, yanzu kuma da ta san daɗin zama da shi ne za’a raba su, wanda ba zata iya ɗaukar wannan ƙuncin ba.

Tun bayan da suka gama magana da mahaifiyarta ta dawo ɗaki take zaune a kan gado tare da haɗe kai da guiwa tana kuka, tun hawayen idanunta na fita, har suka ƙafe, sanadin haka ne ta gwammace ta mutu a kan ganin ranar rabuwar ta da Deeni.

A cikin zuciyarta da ke ta aman wuta ta ce “Ya Allah, ka san yadda nake ƙaunar mijina, bana iya rayuwa idan babu shi”, wani sabon kuka ne ya ƙwace mata.

Can ta jiyo sautin mahaifiyata tana magana, wanda da alama ɗakinta ta nufo, da sauri ta diro kan gado tare da shigewa ban ɗaki ta sa key daga ciki, tana jin shigowarsu ta saki shower.

Take Ummanta da Aunty Hafsat da ke a tsakiyar ɗakin suka gane tana cikin ban ɗakin, Ummanta ce ta ce “Idan kin fito ki same mu a falo”, juyawa suka yi su zasu fita, Aunty Hafsah da ta buɗe hanci ta ce “Ɗakin ba dai ƙamshi ba”

Umman Deena na jin daɗi a ranta ta ce “Ai ita bata wasa da wannan”, Aunty Hafsah ta ce “Gado ta yi ai”, suka fice suna dariya.

Ita kuwa Deena zuwan Aunty Hafsah ba ƙaramin ƙuntata mata yayi ba, don zai ƙara wargaza dukkan komai.

Silalewa ta yi jikin ƙofa tare da sake haɗe kai da guiwa ta yi shiru, ta ɗauki mintoci a haka sannan ta wanke fuskarta ta fita.

Gaban dressing mirror ta tsaya ta kalli fuskarta da ta kumbura, idon a son ranta ne bata so haka ba, saboda bata son Ummanta ta gane abin na ci mata rai.

Foam ɗin powder ta ɗauka ta ɗan goge fuskarta, a ranta ta ce “A daki mutum kuma a hana shi kuka.” Lokaci ɗaya kuma wasu hawaye suka ɓuɓɓugo mata a zuciya tare da bayyana a idanunta.

Ba tare da ta sake kallon yanayin fuskarta ba ta aje foam ɗin, plat shoes ɗinta da ke gefe ta zura tare da ficewa.

Kafin ta ƙarasa a downstairs ne ta cunkusa ma ranta dakiya, don kuwa muddin ta sauka da raunin zuciya da wahala zaman ya tashi lafiya, saboda Ummanta bata son fushi bayan an gama yarjejeniya, sannan uwa uba ga Aunty Hafsah, wadda ko zaman lafiya ake yi da wahala idan ta zo ba a samu saɓani ba saboda ta ƙware wurin haɗin annas.

Su kuwa dukkansu idanunsu na kanta har ta ƙaraso tsakiyar falon, kuma duk sun yi observing damuwar da ke kwance cikin zuciyarta, sai dai ƙarfin halin da ta nuna ya sa basu damu ba.

Cike da girmamawa ta gaishe da Aunty Hafsah, sannan ta zauna kan kujera one seater.

Shi kuwa Raihan da ke rike wurin Aunty Hafsah kamar ya san mamansa, motsi ya shiga yi da kuka, Aunty Hafsah ta ce “Ki ji mun yaro dan Allah, ya ji muryar mamansa”, Umman Deena na dariya ta ce “Rabu da wannan ɗan ƙwaƙur ɗin, wayau gare shi hada na siyarwa.

Dariya sosai Aunty Hafsah ta yi, lokaci ɗaya kuma ta miƙa ma Deena shi, karɓar shi ta yi tare komawa kan kujera.

“Ki ba shi Mama”, Aunty Hafsah ta faɗa, don ya cigaba da kukan, Ummanta ta ce “Aikuwa ba, don ya dade baya tare da ita.”

Kamar yadda aka umurce ta haka ta yi, aikuwa da yake yunwa yake ji sai ya yi shiru, cikin abin da bai fi minti ɗaya ba sai gashi ya yi bacci.

Maganun da ke cike da cikin Aunty Hafsah ne ta fara amayar da su ta hanyar ambaton sunan Deena, bayan Deena ta amsa tare da dubanta ne ta ce “Mun yi magana da Ummanki, akan hukuncin da ta yanke a zamanki tare da mijinki, don haka ki yi haƙuri da hukuncin kin ji ko?”, Kai Deena ta ɗaga alamar ta ji, amma ba wai don girmama Aunty Hafsah ba, sai don kawai ta girmama Mahaifiyarta, don muddin aka kuskure, sai Aunty Hafsah ta ƙara gaba da zancen tana yaɗa ma duniya.

Ɗorawa ta yi da “Wannan hukunci ba a yi don a cutar da ke ba, sai don kawai ki samu mafita mai cike da jin daɗi a rayuwarki ta gaba.”

Cike da tsanar ta Deena ta yi magana a ranta ta hanyar faɗin “Sai kuma aka ce bana jin daɗi a yanzu ko?”, Tamkar Aunty Hafsah ta ji maganar da Deena take yi a ranta, cewa ta yi “Duk da a yanzun ma ba a ce bakya jin daɗi ba, kawai dai zama da makaho ga ƙaramar yarinya irinki abu ne mai wahala, don haka ki yi haƙuri, mahaifiyarki tana matuƙar son ki, sannan tana alfahari da ke a matsayin ƴarta tilo da Allah ya bata.”

Ita kuwa Umman Deena yadda Deena ta dake ne ya birge ta, wanda hakan ya ɗarsu a ranta cewar Deena ta haƙura.

Nasiha su duka suka yi mata, tare da yi mata albishir ɗin komawa school a duk inda take so a faɗin duniya duk da kasancewar tana da goyo, a ganinsu wannan ba wata illa ba ce.

Kafin Deena ta haɗu da Deeni ne take son karatu, yanzu da ta haɗu da shi kuma ta san daɗin zama da shi ne ta ji bata sha’awar karatun da ya wuce zama gidan aure.

Suna cikin wannan tattaunawa ne wayar Aunty Hafsah ta fara ruri, ƴarta da aka yi ma aure a wata ɗaya da Deena ce ta kira ta, da sauri ta ɗaga tana faɗin “Ko an sauka”, da yake itama haihuwa ko yau ko gobe.

Daga can ta ce “A’a, kira na yi dai mu gaisa”, Aunty Hafsah na dariya ta ce “Aikuwa kin kyauta, ya mai gidan?”, Daga can ta ce “Ga shi a kusa”, Aunty Hafsah ta ce “Ayya, da yake weekend ne!”,

Gaisawa suka yi da surikin nata tare da sa mashi albarka, bayan ƴar ta karɓi waya ne ita kuma ta gaisa da Umman Deena. Suna gama wayar ne Aunty Hafsah ta shiga kuranta surukinta tana faɗa ma Umman Deena irin daɗi da ƙaunar da yake ma ƴarta, wanda wani zai iya cewa ma kamar yankar Umman Deena take yi da ita take son raba Deena da mijinta, wanda ko kusa ƴar Aunty Hafsah ɗin bata kai Deena jin daɗi ba, matsayin ma ba ɗaya bane.

Deena kuwa ko kallon Aunty Hafsah bata sake yi ba, saboda ji take kamar ta kore ta a gidan. Sun daɗe wurin a zaune, sai da aka fara kiran azuhur ne suka tashi.

Dr. Safiyya kuwa MD ɗin su Deeni ta nema a waya, inda suka yi appointment zasu haɗu On Monday, haka kuwa aka yi, ranar Monday da misalin ƙarfe goma na safiya ta shigo hospital ɗin.

Kusan duk staff ɗin asibitin sun san ta, saboda ƙoƙarin da take a fannin lafiya. Sosai suka girmama ta. Bayan ta shiga office ɗin MD ne sai ga Dr. Bello ya shigo domin kawo gaisuwa ta musamman da kuma roƙon iri.

Cike da girmamawa ya gaishe ta, bayan ta amsa ne Md ya ce mata, wannan ne ya yi replacing Deeni a yanzu”, kallon shi ta yi yana ta yaƙe mata haƙora, duk da acikin ransa takaici ne da hassada cike da shi saboda ya ji an ambaci sunan Deeni.

Ɗan jinjina kai ta yi tare da faɗin “Ai Soonest Insha Allahu zai dawo a bakin aikinsa, saboda rasa Deeni ba ƙaramar illa bace ga lafiya”, ba da wata manufa ta faɗi wannan magana ba, saboda bata san waye Bello ba bare mugun halinsa, amma da yake mai kaza aljihu baya jimurin ass sai kawai ya tsargu.

Fuskarsa a kicincine ya dube ta, lokaci ɗaya kuma ya maida duban a wurin Md lokacin da ya ba shi umurnin ya zauna, kai Dr. Safiyya ta girgiza “A’a, two of us ma its okay”, jinjina kai Md ya yi, tare da Faɗin “Sorry Bello, you can go!”

A ƙufule Bello ya ce “Okay Sir!”, Tare da juyawa, har ya kai ƙofa Md ya ce “Wait, Before you go, ai Salary ɗin Deeni na shiga ko?”, Kai ya girgiza “I don’t know Sir”, ya ce “Okay, it is an assignment, ka tabbatar da har na wannan month ɗin ya shiga a hannunsa, saboda a kwai report ɗin da zamu haɗa a kansa”, kai ya ɗaga “Okay Sir”, tare da ficewa ya jawo ƙofar da ƙarfi, wanda shi ke nuna ya ji ƙunar hana shi zama da Dr. Safiyya ta yi.

Basu wani damu da shi ba, kai tsaye Dr. Safiyya ta cigaba da magana, “Dama musababbin zuwan shi ne jin matsayar aikin Deeni a wurinku”, mai son zuwa birni ne kwatsam sai aka aiko masa Sarki na kira, take Md ya gyara zama tare da faɗin “Alhamdulillah, na ji daɗin da na samu supporter a kan lamarin Deeni saboda da shi nake kwana kullum a raina kasantuwarsa na gartaccen staff wanda idan aka rasa shi akwai damuwa”, cike da gamsuwa ta jinjina kai, yayinda shi kuma ya cigaba da faɗin “Har yanzu yana nan a matsayin staff, although ba aiki yake zuwa ba, because he is permitted to neman lafiyarsa, kuma kamar yadda kika ji salary ɗinsa yana shiga every month.”

Ta ji daɗin wannan bayanin sosai, cewa ta yi “Masha Allah, Allah ya bashi lafiya”, Md ya ce “Amiin ya Allah”, cewa ta yi “Yanzu abin da muka yanke shawara shi ne fitar da Deeni abroad, tunda nan an yi ba a dace ba!”

<< Mutuwar Tsaye 18Mutuwar Tsaye 20 >>

1 thought on “Mutuwar Tsaye 19”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×