Skip to content
Part 22 of 36 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Tantamar Dr. Safiyya bata ƙarasa sharewa ba sai da su Rahila suka fito mota, dukkansu mamaki ne farkon abin da ya fara ɗarsuwa a zukatansu, ganin sun haɗu wurin da basu da alaƙa ta jini da su, kasantuwar su ɗin ƴan uwan juna ne, don da Babansu Rahila, da Dr. Safiyya uwa ɗaya uba ɗaya suke, asali ma da taimakon Dr. Safiyya ne Rahila ta zama kwararriyar likita a fannin lafiyar idanu.

Cike da farinciki Rahila da Fadila suka haɗa baki “Ammee, me ya kawo ki nan?”, Lokaci ɗaya kuma duk suka yi hugging ɗinta, farinciki fal da ranta ta ce “Abin da ya kawo ku nan shi ya kawo ni”, don ta ji ana faɗin su Deeni zasu yi baƙi, kuma da dukkan alamu su Rahila ne baƙin da zasu zo.

“Lallai dai kam Ammee”, Abdullahi ya faɗa yana dariya, wanda shi ne ya yi driving ɗinsu Rahila, kuma shi ne wanda Rahila take bi mawa.

Lalu da Deeni kuwa tuni sun fara tambayar kansu alaƙar da ke tsakanin wadannan mutane, Dr. Bashir kuwa ya sani, don shi ɗin ɗan mijin Dr. Safiyya ne.

Sannu da zuwa suka yi ma juna, Rahila da hankalinta na wurin Deeni ta ce “Dr ya jikin?”, Ya ce “Alhamdulillah, fatan kun sauka lafiya”, duk suka amsa “Lafiya lau Alhamdulillah.”

Lalu da bai barin magana ta jiƙa a bakinsa ne ya ce “Dr. Ina kuka san juna?”, Dr. Safiyya ta ce “Ƴaƴana ne, Mahaifinsu brother na ne uwa ɗaya Uba ɗaya”, Deeni ya ce “Masha Allah”, Lalu kuwa cewa ya yi “Tabbas kuwa, ga kama nan”, duk suka yi dariya.

Cikin gidan gabaɗaya suka koma, Asma’u na ganin su Rahila ta rungume su da murna tana yi musu sannu da zuwa, sun ji daɗi sosai, domin shimfiɗar fuska ta fi ta tabarma. Hajirsu Deeni kuwa duk da ba lafiyar ƙafafu gare ta ba, amma sai da ta tashi tsaye ta tarbe su lokacin da suka shiga ɗaƙi. Cike da ladabi su Rahila suka duƙa har ƙasa suka gaishe ta, amsawa ta yi tare ɗago da kafaɗar Fadila, yayinda Rahila da Abdullah suka miƙe da kansu.

Bayan sun zauna ne suka ƙara wata gaisuwar, anan ne kuma ta ke jin alaƙar dake tsakanin Dr. Safiyya da kuma su Rahila, ta ce “Allah Sarki, ga kama nan kuwa sosai”, Salma ta ce “Aikuwa dai wlh”, don duk wanda ma ya gansu zai ce Dr. Safiyya ce mahaifiyarsu.

Cike da ƙauna Hajiyarsu Deeni ta riƙa kallon ahalin, lokaci ɗaya kuma ta ce “Amma baki ba zai iya gode muku ma wannan ahali ba, don cikin taka rawar gani kuke wurin Deeni ya fita daga wannan halin da yake ciki”, Deeni ya ce “Gaskiya ne Hajja, Allah ya saka musu da Alkhairi.”

Bashir kuwa tsakar gida ya koma, Asma’u ya ke son ta fito daga kitchen amma ta ƙi, don ta lura da wani mayen kallo da yake mata, Dr. Safiyya kuwa ta yi tsammanin so yake su tafi, daga ɗakin ta ɗan ɗago murya “Bashir na tsaida ka ko?”, Leƙowa ya yi “A’a, ba wani abu Mommy”, ta ce “Yauwa toh, yanzu zan fito”, ya ce “Okay Maa”

Daga ɓangaren Rahila kuwa tana jin Deeni zai fita India ta ce “Amma wallahi na ji daɗi, Insha Allahu da an je can zai samu lafiya”, Dr. Safiyya ta ce “Allah ya sa”, suka ce “Amiiiin”

Sun tattauna maganar da kuma irin yadda Deeni ke ji a idanunsa, amsar dai ita ce “Akwai sauƙi”, amma kam jiya e’ yau, sai dai addu’a kawai.

Shirin tafiya Dr. Safiyya ta yi, inda su Rahila zasu je can gidanta su kwana. Har waje suka raka su, Bashir na tsokanar Fadila ya ce “Wai ina Malik?”, Ta ce “Yana nan garas”, dariya ya yi “Uhmm, ai sai garas ɗin”, ta ce “Toh ya kake so na ce”, ya ce “Ba ni da wani zaɓi”, ta ce “Toh a’a.”

Rahila dai maganarsu mai muhimmanci take da Dr. Safiyya, bayan sun gama ne Bashir ya juyo wurinta “Don Allah ki yi mata faɗa a kan Malik ɗinnan, ta rabu da shi, ga abokina nan mutumin kirki”, Rahila na ƴar dariya ta ce “Ku cire ni a wannan sabgar”, dariya duk suka yi, sannan suka shiga Mota, suka tafi.

Cikin gidan suka dawo, ƴar hira aka ɗan yi, daga bisani Lalu da Abdallah suka tafi masallaci, Deeni kuwa ɗaki ya shiga ya gabar da tashi, bayan ya gama ne ya ɗauki wayarsa, number Deena ya sa sannan ya kira, tana ɗaga kiran ya ce “Ba kya nema na ko?”, Daga can ta ce “Sorry Yaya”, ya ce “Na ƙi”, marairaicewa ta yi “Dan Allah”, ya ce “Na ƙi fa”, ta ce “Toh shikenan”, sai ta yi shiru.

Shirun shi ma ya yi, ƙasan ransa a hargitse, duk kuwa da albishir ɗin da Dr. Safiyya ta zo mashi da shi.

Shi ɗin ne ya katse shirun ta hanyar ambaton sunanta, bayan ta amsa cikin sanyin murya ne ya ce “Kin yi shiru”, kamar zata yi kuka ta ce “Ban san me zan ce maka ba Yaya, na ce sorry, amma ka ƙi”, yadda ta ƙarashe maganar ne ya ba shi tausayi, cewa ya yi “Ayya, toh na yi”, daga can ta ce “Yauwa, thank you”, ya ce “Ina yarona?” ta ce “Gashi a jikinna”, ya ce “Nima ai ya kusa dawowa a jikina ko?”, ta ce “Insha Allah.”

Sai da suka yi ƴar soyayyar su sannan ya faɗa mata albishir ɗin tafiyarsu India.

Deena ta yi farinciki sosai, domin zuwansa India zai iya zama silar rashin mutuwar aure su, cewa ta yi “Wallahi na ji daɗi sosai Yaya, Allah ya sa a dace”, ya ce “Amiiiin”, ta ce “Sai na ji dama da ni za a je”, ya ce “Nima na so haka Dee-Dee, amma ba komai”

Bayan ta gama wannan murnar ne ya shaida mata cewa Dr. Rahila ta zo ita da ƴan gidansu, kuma akwai yiwuwar ta zo ganin Raihan, ya yi haka ne saboda baya son wargaza mata farincikinta.

Aikuwa sai da abin da ya guda ya auku, a hasale ta ce “Me ta zo yi?”, Ya ce “Gani na”, ta ce “Uhmm, gulma dai”, sosai maganar ta bashi dariya, cewa ya yi “Gulma kuma??”, Ta ce “Eh mana”, ya ce “Ke kuma kishi ko?”, Ta ce “Eh, ni bana son ana shige ma mijina”, don ya ja maganar ya ce “Duk da mata huɗun da Allah ya yarje mashi ya aura?”, Ta ce “Eh”, ya ce “Lallai ma, toh ki kwantar da hankalinki ma, ke ɗaya ce ƙwallin ƙwal.”

Wata irin dariyar farin ciki ta ƙyalƙyale da ita, haka dama yake so ya ji ta tana nishaɗi, lallaɓa ta ya yi a kan idan su Rahila sun zo ta yi musu tarba mai kyau, ta ce “Baka da matsala mijina”

Lalu da Abdallah ne suka shigo ɗakin, mafarin ya yi ma Deena sallama. Sabuwar hirar crypto suka buɗe, Deeni na jin su, wani wurin ya sa baki, wani wurin kuma ya yi dariya, domin harka ce mai samatsin gaske.

Rahila kuwa wata irin ƙauna ta musamman take yi ma ahalin Deeni, musamman Hajiyarsu, mafarin ta zauna suka sha hira, a nan taba Hajiyarsu Deeni labarin irin ciwon dake samun Deeni, tare da albishir ɗin Insha Allahu zai samu lafiya, Hajiyarsu Deeni ta ce “Allah ya sa”

Salma da Asma’u kuwa sun zage da aiki, cikin ɗan ƙanƙanen lokaci suka gama tare da zubo shi a warmers masu kyau, sun shigo da shi ne Rahila ta ce “Sannunku da aiki”, da ƴar dariya ta ƙarashe maganar, Salma ta ce “Yauwa Dr.”

Bayan sun gama jera komai a babban carpet ɗin da ke ɗakin ne Salma ta dubi Fadila dake kishingiɗe a kan kujera tana danna waya ta ce “Lunch is ready Sisi”, Fadila na dariya ta ɗago ta dube ta, “Okay, Sannunku da aiki.”

Ba a jima ba sai ga su Lalu sun shigo ɗakin, Inda Abdallah ya yi ma Deeni jagora, wani irin tausayi ne ya cika ma Rahila rai, mutum nagartacce, amma ƙaddara ta naƙasta shi.

Take idanunta suka ciko da ƙwallan so da tausayi, bayan ya zauna ne ta ce “Sannu Dr”, ya ce “Yauwa, nagode”

Zaman cin abincin suka yi, Salma ce ta yi serving ɗinsu, abincin ya musu daɗi sosai, suka yi ta buga santi suna dariya.

Asma’u ba da ita aka yi zaman cin abincin ba, saboda wankan da ta shiga, fitowar ta banɗaki ke da wuya ta ji wayarta da ta manta a kitchen tana ruri, da hanzari ta shiga kitchen ɗin, unknown number ta gani, take ta gane Bashir ne, tana ɗaga kiran da sallama, yana amsawa ya ɗaura da “Miss India”, ta ce “Kuma dai?”, Ya ce “Yeah”, dariya kawai ta yi, don bata da abin faɗa.

Daga can ya ce “Kin gama aikin?”, Ta ce “Yeah”, ya ce “Sannu toh”, ta ce “Yauwa and thanks”, ya ce “U r wlcm”, ɗan shiru ne ya ratsa su, daga bisani ya ce “Ki yi save na number ta, zuwa anjima Insha Allahu zamu yi magana mai muhimmanci da ke”, ta ce “Ok zan yi”, ya ce “Aha! Thank you so much”

Sallama suka yi, ta wuce ɗaki, anan ake faɗa ta yi sauri ta shirya, don zata raka su Rahila gidansu Deena su ga Raihan”, dama ƙafar yawo ce, da hanzari ta ci abinci, sannan ta shirya cikin doguwar rigarta material mai kyau, mayafin da aka yi da yadin cifon mai kalar peach, sai ratsin purple, rigar ta yi mata kyau sosai, kasantuwar ta na farar fata.

Sosai ta birge Rahila, don tana son irin waɗannan rigunan “Wow! Gaskiya kin yi kyau fa”, ta faɗa cikin fatan ina ma zata samu irin wannan yadin itama ta ɗinka shi, Asma’u na dariyar jin daɗi ta ce “Thank you”, Fadila ma sosai ta yaba da kayan.

Bayan Asma’u ta gama shirinta tsaf ne Rahila ta ɗauke su ita da Fadila suka fita, sai da suka je karshen layin ne ta dubi Asma’u dake gaba “Ina zamu fara zuwa?”, don sun shirya hada gidan Yaya Asiya, da kuma Hajiya Ummah zasu je.

“Ai mu fara zuwa gidansu Dee-Dee”, Asma’u ta zaɓi fara zuwa can ne saboda mahaifiyar Deena, don duk shaƙuwarsu, amma bata son zuwa gidan, shi ya sa ko ta kama a je toh sai dai ta je a gagguce. Rahila ma gidan take son a fara zuwa, ita kuma duk don ta ga wacece Deena da son ta ya ƙara ma Deeni makanta zuci, ta yadda baya ganin kowace mace sai ita.

Cewa ta yi “Okay, wace hanya zamu bi toh?”, Hanyar dama ta nuna mata, Fadila dake can baya tana danna waya ta ɗaga kai “Wace unguwa suke?”, sai da Asma’u ta ɗan leƙo kafin ta bata amsa “Suna unguwar dosa”, kai Fadila ta ɗan jinjina “Okay, amma ba nisa ko?”, Rahila ce ta ce “Ke da ba a ƙafa zaki je ba miye na damuwa da nisan wurin”, Asma’u me zata yi idan ba dariya ba.

Da yake abu kaɗan ke motsa mata da miskilamci ta haɗe rai “Kin san bana son doguwar tafiya”, baki Rahila ta taɓe “Ai da kin yi zamanki baki biyo mu ba.”

Baki ta turo “Uhmmm!”, Rahila ta ce “Ke dai kika sani.”

Deena ma tuni ta shirya tarbar su Rahila, girki na musamman aka yi musu, sannan ta buga wanka cikin riga da skirt na atamfa, ƴar sakarta mai kyau ta saka a wuya, sai ƴan hannu marasa nauyi duk da ta saka. A koda yaushe ita mai yawan ado ce, shi ya sa da ta yi yake karɓarta.

A falo ta zauna ta rungume ɗanta, wayarta ta ɗauka, tana shirin kiran Deeni sai gashi ya kira ta, bayan ta ɗaga ne ta ce “Ina shirin kiran ka”, ya ce “Sai ga shi na kira ko?”, Ta ce “Yeah”, ya ce “Su Rahila sun fito fa”, ba yabo ba fallasa ta ce “Allah ya kawo su lafiya”, tambayar ta ya yi “Me kika shirya musu?”, Ta ce “Girki mai daɗi”, ya ce “Yauwa Wifee, na san ke gwana ce wurin karrama baƙi” murmushi mai sauti ta yi, inda ya cigaba da faɗin “Mommah ta dawo?”, ta ce “Nope”, ya ce “Sai yaushe?”, Ta ce “May be gobe ko jibi”, ya ce “Allah ya dawo da su lafiya” ta ce “Amiiin ya Allah.”

Daga can ta jiyo ƙarar buɗe gate, ce mashi ta yi “Da alamar kamar sun shigo”, ya ce “Okay, je ki gani toh”, “Okay”, ta ce sannan ta tsinke kiran.

A nan falo ta bar Raihan, saboda masu aikin gidan na ta kaikawo a falon, burin Deena itama shi ne ta ga wadda alamu ke nuna tana son mijinta, lokacin da ta fita har sun faka motar su, wadda girman motar da kuma kyawunta kaɗai ya bayyana ma Deena su Rahila ba ƙananun mutane bane. A ɓangaren Rahila ma tanƙamemen gidansu Deena ya sa ta gane gida ne na masu ƙumbar susa.

Yanzu abin da ya rage musu shi ne su ga juna, da ɗan sauri Deena ta isa a parking space, isarta kuma ta yi daidai da fitowar Rahila a mota. Lokaci ɗaya gabansu ya yi muguwar faɗuwa sakamakon ƙayatuwar junansu da suka gani.

Cike da basarwa Deena ta rungume Rahila tana faɗin “Oyoyo Sannunku da zuwa”, Rahila na dariyar da zallarta yaƙe ne ta ce “Yauwa Sannunmu”, bayan sun saki juna ne Deena ta koma wurin Fadila ta yi hugging ɗinta tare da sannu kamar yadda ta yi ma Rahila, tana juyawa wurin Asma’u ta yi mata hararar wasa “Fushi nake dake wallahi”, Asma’u da ta san laifinta ta ce “Tuba nake matar Yaya, a yi haƙuri”, baki ta ɗan murguɗa “Na ƙi yin haƙurin”, dariya su duka suka yi, Rahila ta ce “A yi haƙuri don Allah”, wata ƴar harara Deena ta ƙara yi ma Asma’u “Kin ci domin-domin”, Asma’u ta ce “Na gode.”

Cikin gidan suka ƙarasa, a nan ne Rahila ta gamsu cewa duk kuɗinsu basu kai su Deena ba, don duk abin da ke ƙawata gida, kuma na gani na faɗa akwai shi falon, sannan duk inda mace takai, toh Deena ta kai, musamman yadda ta iya tsara kwalliya ba tare da hayaniya ba, a ranta ta ce “No wonder Dr yake rikicewa a kan wannan yarinyar”, a zahiri kuwa murmushi take tana kallon Deena lokacin da take tambayar Asma’u wacece Rahila a tsakanin Rahila da Fadila, duk kuwa da ta gane.

Bayan Asma’u ta nuna mata Rahila ne ta ce “Toh a kusa dake zan zauna, don ke ta musamman ce a wurinmu”, ƙarashe maganar ya yi daidai da zamanta a gefen Rahila, hannunsu cikin na juna suka gaisa tare da yi musu sannu da zuwa.

Yadda Deena ke ta shimfida musu fuska ya masu daɗi sosai, domin hausawa sun ce shimfiɗar fuska ta fi ta tabarma. Dukkansu wayayyu ne, cikin ɗan lokaci suka saki jiki da juna, hatta Fadila da ke miskila gidan ya mata daɗi, musamman da Raihan ya zo hannunta, don burinta kenan idan ta haifi ɗa ta sa mashi Raihan.

A ɓangaren abinci kuwa, sun ɗan ci kaɗan, saboda ba yunwa garesu ba, da Deena ta matsa a kan sai sun ci da yawa Fadila ta ce “In dai ba so kike mu kasa tafiya ba ki barmu a haka”, Deena na dariya ta ce “Toh shikenan.”

Sun sha hira sosai, a nan Deena ta yi ma Rahila godiya a kan ƙoƙarin da suke ta yi wurin ganin Deeni ya samu lafiya, Rahila ta ce “Ai ba komai”, a nan ne kuma ta shiga zayyana ma Deena irin ciwon da yake damun Deeni, da kuma hanyoyin da za a bi wurin ganin ya samu lafiya, wanda kuma dole sai an fita da shi a India ne ake sa ran zai warke, don can ne suke da kayan aiki.

Yadda Rahila ke magana cike da ilimi gami da nutsuwa ne ya tafi da hankalin Deena har ta ji ta birge ta sosai. Toh ita mace kenan Rahila ta birge ta, ina ga namiji kuma? Take a karon farko ta yi murna da rashin lafiyar Deeni, cike da magagin kishi a ranta ta ce “Na gode ma Allah da Yaya baya gani, da ban san ya zan yi ba idan ya ga Rahila…”

 

 

 

 

<< Mutuwar Tsaye 21Mutuwar Tsaye 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×