Deena ta manta da zuciya na da idanun da ganinsu yake da tasiri fiye da na idanu, domin ita tana tsara abu ne a yadda take so kafin ta karɓe shi, don haka rashin idanu ba zai hana Deeni son Rahila ba madamar zuciyarsa ta amince da ita, domin nagartar Rahila ba wai a idanu kaɗai ta tsaya ba, nagarta ce mai sanya nutsuwa a zuciyar duk wanda mu’amala ta haɗa shi da ita, wanda kuma Deenin da take gode ma Allah da baya gani ya san haka, kawai dai ra’ayinsa a kan soyayya da ita ne ba a sani ba tunda bai faɗa ba.
Rahila ma bayani take ma Deena, amma ƙasan ranta tana jimamin rasa Deeni, wanda ganin Deena ya sa ta yanke ƙauna da samun shi, domin ba inda ta ci karo da makusa a wurin Deena.
Sun sha hira sosai kamar sun daɗe da sanin juna. Lokacin sallar Al’adar na yi suka shiga ɗakin Deena suka gabatar, daga nan kuma suka fara shirin tafiya.
Cike da jin daɗin zamansu a gidan Deena ta ce “Da sauran lokaci fa, don Allah ku bari a ɗan jima mana”, Rahila ma ba don tana son tafiya ba ta ce “Akwai wuraren da zamu je, ko Asma’u?”, Ta ƙarashe maganar da tambayar Asma’u.
“Eh, kin ga zamu je gidan Yaya Asiya da gidan Hajja Ummah”, ɗan rausaya kai Deena ta yi kafin ta ce “Gaskiya kuna da tafiya”, saboda ta san distance ɗin da ke tsakanin gidajensu.
Turaruka masu tsada ta haɗa musu, sannan ta naɗe kuɗi a envelope ta saka a cikin leda, miƙa Asma’u ta yi “Ungo ƙawa, riƙe musu”, Rahila ta ce “A’a, bayan karramawar da aka yi, hada kuma wannan?”, Fadila ta ce “Wallahi fa”, Deena na dariya ta ce “Ai ba yawa, Nagode sosai da kara da karamcinku, Allah ya barmu tare”, duk suka ce “Amiiiin.”
Raihan na hannun Fadila suka fita, sumbatar shi ta yi a kumatu kafin ta dubi Deena “Ina son yaron an, ki bar mani shi mu tafi Kano”, Deena na dariya ta ce “Na bar miki shi Hajiya”, duk suka yi dariya.
Kafin su shiga mota ne ta ce ma Asma’u “Ƙawa, don Allah yaushe zaki dawo?”, Asma’u ta ce “Insha Allahu zan fidda time in zo, idan kuma kin koma gidanki kin ga zai inje can.”,
Deena ta san abu ne mai wahalar gaske ta koma, murmushi kawai ta yi haɗe da faɗin “Toh shikenan.”
Bankwana suka ƙara yi tare da yi ma juna godiya, domin dukkansu sun karrama junansu, bayan Deena ta karɓi Raihan ne suka shiga Mota, maigadi kuma tuni ya buɗe musu gate, har suka fice Deena na ɗaga musu hannu.
Cikin gida ta koma, zuciyarta cike da kewarsu ta yada zangon a falo, alamun ganin Raihan na bukatar abincinshi ne ta bashi, lokaci ɗaya kuma ta ɗauki waya, number Deeni ta kirawo, yana ɗagawa ya ce “Dee-Dee”, bayan ta amsa ne ya tambaye ta “Ina Jama’ar?”, ta ce “Sun tafi”, ya ce “Da wuri haka?”, Ta ce “Sun ce a kawai wuraren zuwa ai”, ya ce “Haka ne.”
A nan ta faɗa mashi kayan da suka kawo ma Raihan, ya ji daɗi sosai, anan kuma suka ƙara jaddada ma juna kirkinsu Rahila, Deena ta ce “Allah ya bamu ikon maida musu muma”, ya ce “Amiiiin.”
Su Rahila kuwa gidan Hajiya Ummah suka fara zuwa, ta ji daɗin sosai saboda wani irin so take yi ma Rahila, duk lokacin da ta ganta sai ta ga kamar ƴarta.
Ta yi musu kara da karamci, har Fadila ta ce ma Asma’u “Ku dai kuna da kirki wallahi”, a daidai lokacin kuma Hajiya Ummah ta shigo.
Asma’u ta ce “Hajjah kin ji me tace?”, Hajiya Umma ta ce “Na ji, ta manta sun fi mu kirki, Allah dai ya saka muku da Alkhairi”, duk suka amsa “Amiiiin.”
Da zasu tafi ta basu kuɗi, Rahila ta ce “A’a don Allah”, Hajiya Umma ta ce “Ai baku isa ba”, suka kama dariya.
Miƙa ma Fadila ta yi, hannu biyu ta karɓa bakinta na faɗin “Allah ya saka da Alkhairi”, har waje ta raka su, tare da yi musu godiya da fatan Allah ya tsare.
Daga nan sai gidan Yaya Asiya, a nan ma kamar Yaya Asiya ta maida su ciki saboda kulawa, da zasu tafi ne ta fiddo riguna masu kyau irin wadda Asma’u ta saka “Kowa ta zaɓi kalar da tafi so”, ta faɗa tana kallon su.
Rahila ta ce “Wow! Bari kuwa na darje”, suka kama dariya, kusan irin ta Asma’u ta ɗauka, don dai flowers ɗin sun sha banban, Fadila kuwa maroon ce ta ɗauka mai kyau.
Bayan duk sun zaɓa ne ta haɗa musu da beads masu kyau. Sun yi godiya ba kaɗan ba, tambayarta Fadila ta yi “Wa ke siyarwa?”, Ta ce “Ni nake siyarawa”, Fadila ta ce “Aikuwa zaki sha ciniki Aunty”, exchange na contacts suka yi, daga nan suka haɗa kayansu suka wuce gidansu Deeni.
A ƙofar gida suka tarar da Lalu da Abdallah suna shirin fita a kan mashin, tun a cikin mota Rahila ta lura da wani kallo da Lalu ke yi mata, amma sai ta basar.
“Fita zaku yi?”, Ta tambaye su cike da tsarguwa da kanta, daburcewa ya yi, sai dai Abdallah ya ce “Ƙwarai, zamu shiga gari”, Fadila ta ce “Yanzu fa zamu wuce gidan Gwaggo”, wani kallo Abdallah ya yi mata kafin ya ce “An faɗa maki ni baƙo ne a Kaduna, mu haɗu a can kawai, idan kuma na dawo shikenan”, Baki Rahila ta taɓe “Toh ɗan gari”, Fadila kuwa sai dai ta ce “Uhmm.”
Sannu da dawowa Lalu ya yi ma Rahila, bayan ta amsa ne ta bi bayan Asma’u da Fadila, wanda tuni sun shige gida. Khamis suka tarar a falon Hajiyarsu Deeni ya zo a kan maganar tafiyar su Deeni a ƙasar India.
“Dr ce a garinmu?”, Ya faɗa yana mai cike da murnar ganinta, fuskar Rahila cike da yalwa ta ce “Aikuwa dai, mun same ku lafiya”, ta ƙarashe maganar tare da zama gefen Hajiyarsu Deeni a kan Carpet.
Asma’u da Fadila ma gaishe shi suka yi inda ya amsa musu gabaɗaya da “Lafiya lau Alhamdulillah”, Asma’u da ta yi mamakin rashin gaini motarsa ta tambaye shi “Yaya, ban ga motarka a waje ba.”
Amsa ya bata “Tana farkon layi a majalissarsu Alhassan”, kai ta jinjina “Auho”, don ba ta nan suka shigo ba.
Sannu da zuwa Deeni ya yi musu, bayan sun amsa ne Fadila ta ce “Dr, na ga Raihan tubarkalla, kamarku ɗaya”, yana dariya ya ce “Ko Fadila?”, Ta ce “Wallahi kuwa, kamar in tafi da shi Kano.”
Hajiyarsu Deeni ta ce “Allah Sarki, watarana zai iske ki har can”, Fadila ta ce “Allah ya sa.”
Kaf Alkhairin da suka samo Rahila ta baje ma Hajiyarsu Deeni shi a kan Carpet, turarukan da Deena ta basu ta ware haɗe da Envelope ɗin “Kin ga wannan, na Aunty Deena ne”, ɗaukar turarukan da suka game wurin da ƙamshi Hajiyarsu Deeni ta yi tare da shaƙar ƙamshinsu “Masha Allah, turare mai kyau”, Khamis ya ce “Wallahi kuwa, ɗakin duk ya ɗauka”, Deeni kuwa ya ji daɗi sosai, musamman da ya ji hada kuɗi, kai ko ba kuɗi tabbas Deena ta fidda shi kunya, saboda ya san kalar turarukan masu kyau ne.
Duban shi Rahila ta yi “Dr ka ji Alkhairin da Madam ta yi mana ko?”, Yana ƴar dariya ya ce “Na ji, Allah ya saka da Alkhairi, itama ta ce kun kai ma ɗanku tsaraba ai, Allah ya ƙara danƙon zumunci”, duk suka ce “Amiiiin.”
Duk abin da suka samo a gidan Hajiya Ummah da Yaya Asiya ma sai da suka nuna musu tare da yin godiya.
Cike da tsokana Khamis ya ce “Ni ba za a kai mani ziyarar ba?”, Rahila ta ce “Baka da case, zamu je, kwana ma zamu yi”, yana ƴar dariya ya ce “Kamar da gaske”, dariyar itama ta yi, don ta san ba da gasken take ba. Haƙuri ta ba shi a kan next time idan suka dawo zasu je gidanshi.
Godiya ta musamman ya yi musu a kan abinda Dr. Safiyya ta yi na fidda Deeni India, Rahila ta ce “Ba komai, Dr ya fi gaban haka ma, fatanmu duka Allah ya ba shi lafiya.”
Deeni da ke ta kallon Rahila da zuciya ne ya lumshe idanu, tabbas Rahila mutum ce, wadda idan har zai iya son wata mace bayan Deena toh ita ce, duk da bai ganta ba, amma ya tabbatar da cika duka qualities ɗin da za a so mace don su.
Rahila ma shirin da ta ɗan yi tunanin ba zata ne ya zo mata, wanda take jin da ace Deeni bai da mata, da ta kawo kanta a wurinshi tana son ya aure ta, toh amma ba komai, bawa bai wuce rabon da Allah ya tsaga masa.
Tashin Khamis ne ya dawo mata da hankalinta inda ya ce “Dr, ni zan wuce”, ta ce “Ayya, A gaida su Madam.”
Miƙewa Deeni ya yi da shirin yi masa Rakiya, ya ce “Ka bari kawai” Deeni ya ce “Ai dama zan fita, ka ga Magrib ta kusa”, Khamis ya ce “Okay”, tashi Deeni ya yi haɗa da sanarsa, a tsakar gida suka yi sallama, Khamis ya fice, shi kuma ya shige ɗaki.
Da mamaki cike da ran Rahila ta dubi Hajiyarsu Deeni “Hajja, ta ya Dr yake gane lokacin sallah ya kusa? Gashi ko kira ba a fara ba”, Hajiyarsu Deeni ta ce “Allah kaɗai ya sani Rahila, mu kanmu idan ya yi wasu abubuwan sai mu yi ta mamaki.”
A nan take ba Rahila labarin yadda har gida marassa lafiya suke iske shi, ya yi musu tambayoyi, kuma ya rubuta musu magunguna, sannan tana jin lokacin da ake kira ana yi mashi godiya.
Rahila ta ce “Ai dama na san zai iya Hajja, yana da ƙokari ai, bai kamata a ce yana zaune ba”, Hajiyarsu Deeni ta ce “Daga can asibitin ne suka ce ya ɗan dakata ya samu lafiya.”
Ƴar hirar da suka yi ce ta sa Rahila ƙara waye Deeni a wurin mahaifiyarsa da irin tsananin son da take mashi, saboda babu irin kyautatawar da baya yi musu. Sannan kuma ta fahimci irin ɗacin da mahaifiyar Deeni ke ji a ranta, wanda har kuka dukansu suka yi.
Rahila ji ta riƙa yi kamar kada ta bar gidan, toh dolenta, tunda sun yi da Dr. Safiyya zasu je can su kwana.
Sallar Magrib da Isha’i suka yi, an so su ƙara cin abinci, amma suka ƙiya saboda ba yunwa suke ji ba. Abdallah na dawowa ya ɗauke su suka tafi Unguwarsu Dr. Safiyya.
Da farinciki Hassana da Hussaina suka tarbe su, su ne kuma First born ɗin Dr. Safiyya, sannan age mate Fadila, Hassana na murna ta ce “Tun ɗazu muke ta jiran zuwanku”, Rahila na dariyar ganin danginta ta ce “Oh sorry, mun ɗan shiga gari ne”, Hussaina ta ce “Au ho! Na ɗauka wancan ne ya tsaida ku”, ta faɗa tana duban Abdallah da ke shirin shigowa falon.”
“Eh, ni ɗin ne na tsaida su, sai aka yi yaya?”, ya faɗa yana ƙarasowa cikin falon haɗe da dariya a bakinsa. Cewa ta yi “Sai in maka bulala”, kaf falon ba wanda maganar bata sa dariya ba.
Kallon Dr. Safiyya da ke zaune kan kujera two seater ya yi, hannunsa na nuni da Hussaina, dariya a bakinsa ya ce “Wai gwaggo ni wannan yarinyar zata daka”, Dr. Safiyya na dariya ta ce “Itama faɗa take”, saboda Abdallah ƙaƙƙarfan namiji ne wanda ko a cikin maza ba kowa ke iya shan gabansa ba.
Zama suka yi, inda aka yi gaisuwar yaushe gamo, duk da sun haɗu da Dr. Safiyya a ɗazu.
Abinci suka ci haɗe da hira, wadda rabinta duk ta Deeni ce, Hassana ta ce “Wai ba picture ɗinsa mu gani?”, saboda ba Rahila kaɗai ba, hatta Dr. Safiyya dake uwa tana kuranta Deeni.
Picture ɗinsa na jikin Dp ta nuna mata, duk da side view ɗinsa ne a photon, amma sai da Hassana ta gane mai kyau ne, kasa ɓoye birge ta da yayi ne har ta ce “Wow! Kalle sa Handsome, amma Deena ta yi sa’ar haɗaɗɗen miji”, ta ƙarashe maganar tana dariya.
Take wani kishi ya taso ma Rahila, dariyar yaƙe ta yi haɗe da faɗin “Aikuwa, itama matar ba laifi tana da kyau.” A nan suke faɗa ma Dr. Safiyya sun je gidansu Deena kuma ta karrama su, Dr. Safiyya ta ce “Ai Deena na da wayau, don ma mamanta na son raba da Deenin”, wannan maganar ba ƙaramin tasiri ta yi a zuciyar Rahila ba, “Dama kun san su?”, ta ce “Sosai ma, mamanta ƙawata ce ai.”
Mamaki ne ya kama Fadila a kan yadda su Hassana basu san mijin Deena ba, ga mahaifansa ƙawaye har sai da ta tambaya, a nan suke faɗa mata duk basa nan aka yi bikin, sannan da suka dawo basu je ba, sai dai Umminsu kaɗai ta je.
Rahila kuwa sai da ta yi ta jan Dr. Safiyya da magana akan batun auren Deena, aikuwa ta faɗa mata su ne ma ke lallaɓa Umman Deena a kan kada ta bari auren Deena ya mutu, saboda kawai Deeni ya makance. Aikuwa take Rahila ta ji wani daɗi a ranta, kuma ta ɗaura ɗamarar in dai auren Deena ya mutu, toh sai ta auri Deeni da taimakon Allah.
Sun sha hira sosai, daga bisani Fadila da Twins suka yi ɗaki, Abdallah ma tuni ya fice saboda yana da aboki a Kaduna, kuma a wurinsa zai kwana. Rahila da Dr. Safiyya kuwa sabuwar hira suka buɗe wadda ta shafi aikin lafiya.
Asma’u kuwa Dr. Bashir ya tarfa ta a WhatsApp, inda yake ta yi mata ruwan maganganu masu ɗauke da zallar son da yake mata. Bai kuma ƙarasa sanya ta a ruɗani ba sai da ya ce mata “Zaki aure Ni?”, mamaki bayyane a fuskarta ta ce “Aure kuma daga haɗuwa?”, Ya ce “Ƙwarai, idan kin amince zan turo magabatana a gidanku, muddin an bani ke, toh zan ɗauke ki mu tafi India nan da sati uku masu zuwa.”
Bayan mamaki hada dariya maganar ta sanya ta, cikin irin rainin hankalin da ta saba yi ma Lalu ne ta ce “Au haba don Allah!”, Saboda gani take kamar ƙarya yake. Bata ankare ba sai gani ta yi kira ya shigo wayarta, ɗagawa ta yi haɗe da sallama, bayan ya amsa ne ya ce “Asma’u”, ta ce “Na’am”, ya ce “Kin ɗauka wasa nake ko?”, Sai da ta ɗaga kai kafin ta ce “Gaskiya fa, saboda aure ba wasa bane”, ya ce “Haka ne, ni ma ba da wasa na zo ba ai, tunda na ganki a ɗazu na ji na samu matar aure. Idan kin amince gobe zan zo in ne mi izni a gidanku, don so nake idan zamu ta fi India in tafi da matata, idan kuma baki aminci ba, toh ki faɗa mani, amma dai na baki damar ki yi nazari”, yana kai ƙarshen doguwar maganarsa ta ji ƙit! Ya tsinke kiran.
Lokaci ɗaya ta sauke waya haɗe da nannauyar ajiyar zuciya, bakinta na faɗin “Wata sabuwa.!”