Skip to content
Part 24 of 31 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

“Ke da wa?”, Hajiyarsu da ke gefenta zaune a kan gado ta tambaye ta, kasantuwar a wuri ɗaya suke kwana, saboda Asma’u na taimaka mata sosai a cikin dare.

Wannan magana bata bukatar ɓoyo, shi ya sa kai tsaye Asma’u ta ce “Ina wanda suka zo da Dr. Safiyya ɗazu?”, Jinjina kai Hajiyarsu ta gami da faɗin “Na gane shi”, Asma’u ta ce “Shi ne, wai gobe zai zo wurina, kuma wai da maganar aure”, tambaya ta maido mata “Dama kin san shi ne?”, Asma’u ta ce “A’a, yau ne na fara sanin shi.”

“Kuma shi ne har zai zo gobe da maganar aure?”, Har ila yau ta sake maido mata tambaya, don bata ɗauki maganar da wani tasiri ba, Asma’u ta ce “Haka ya ce”, ta ce “Toh shikenan, amma dai ki bi a hankali da samarin zamanin nan, don mafi yawansu basu da tabbas”, shiru Asma’u ta yi, don maganar Hajiyarsu gaskiya ce.

Aje wayar ta yi, har zata kwanta Hajiyarsu ta ce “Ɗauko mani ruwa”, sai da Asma’u ta ɗan nisa kafin ta ce “Toh”, dirowa ta yi daga kan gadon ta nufi jug ɗin da ake haɗa mata ruwa mai sirki da addu’io a kan Carpet, tsiyayo ruwan ta yi a cup ta kawo mata. Karɓa ta yi, a ƙasan ranta kuma tana yaba ƙoƙarin da Asma’u ke yi da ita dare da rana ba tare da musu ko nuna gajiyawa ba, “Allah ya baki miji na gari, inda zaki huta”, a cikin ranta ta yi ma ƴar autarta wannan addu’a, tare da tunanin wanda zai cigaba da kulawa da ita idan Asma’un ta yi aure.

Jug ɗin dake kan tray haɗe da cup Asma’u ta aje a kan stool, ko da Hajiyar zata buƙaci ruwan cikin dare. Kan gadon ta dawo ta kwanta, ba tare da ta sake bi ta kan wayarta ba, saboda Bashir ya bar ta da maganar da bata san ta ina zata fara gasgata shi ba.

“Kin yi addu’a ne?”, Hajiyarsu ta katse mata tunanin da take shirin faɗawa, “A’a’, ta faɗa a taƙaice “Toh tashi ki yi”, kamar Asma’u zata yi kuka ta ce “Zan yi daga kwancen”, saboda addu’ar bacci wahala take mata.

Sanin duk wanda ya fara addu’ar bacci da wuya ya ƙarasa ta bacci bai yi awon gaba da shi ba ya sa Hajiyar faɗin “Ki tashi ki yi daga zaune, don barci zai iya ɗauke ki, ƙarshe ki yi ta damuna da mafarkai cikin dare”, Asma’u bata sake musu ba, tashi ta yi zaune, addu’ionta ta yi gami da shafe jikinta, sannan ta kwanta, yayin da ta bar Hajiyarsu zaune tana addu’ar itama.

A ɓangaren Bashir kuwa, washegari wurin ƙarfe goma ya nufi part ɗin Dr. Safiyya, a falo ya tarar da su Rahila da sauran ƙannensa na ɗaikin suna break past, zama ya yi kan kujera suka gaisa da juna.

Duban Fadila ya yi dake ta naɗar tamisa da wake tana kaiwa baki “Hajiya ba tayi?”, a hankali ta ɗago ta kalle shi, hannunta riƙe da cup mai ɗauke da black tea “Ai wannan ba a ba yaro mai ƙuiya”, ta faɗa bayan ta haɗiye wanda ke bakinta, ya ce “Ko?”, Ta ce “Yeah”, ya ce “Amma zaki ba saurayinki ko?”, Harara ta wurga mashi, wadda ta sa kowa dariya.

Plate ɗinshi aka haɗa mashi, tamisa ce manya guda uku, sai dafaffen wake da aka yanka hanta ƙanana a cikinsa, sai kuma black tea da ya ji tea spices sai ƙamshi yake. Ci ya riƙayi yana santi, bayan ya gama ne suka dasa hira mai cike da nishaɗi da su Rahila, a nan ya ji lokacin da zasu koma gidansu Deeni bankwana, Rahila ta ce “Shiryawa zamu yi yanzu, amma da mun je ba zamu daɗe ba.”

Ɗan rausaya kai ya yi “Okay”, lokaci ɗaya kuma yana ƙoƙarin bin umarnin zuciyarshi da ke hana shi faɗa musu son da yake ma Asma’u, duk da wannan ne musababbin shigowashi wurin su, ƴar hira suka taɓa, sannan ya tashi ya fita.

Yana komawa ɗakinsa ya danna ma Asma’u kira, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta ɗaga “Na ɗauka ba zaki amsa kirana ba”, ya faɗa tare da zama gefen gadonsa, daga can cikin murya mai sanyin jiki ta ce “A kan me zan ƙi ɗaga kiran ka?”, Ya ce “Na sani ko ba kya so na?”, murmushi mai sauti kaɗai ya ji ta yi, cike da kulawa ya tambaye ta yadda ta wayi gari, bayan ta amsa da “Lafiya” ne ya ce “Bayan sallar la’asar zan zo, kuma ba ke kaɗai zan gani ba, hada su Yaya, kin amince na zo?”, ɗan shirun da ta yi ne ya ba shi damar cewa “Magana nake Madam, kin amince?” Da sauri-sauri ta amsa mashi da “Na amince”, ransa fari sal ya ce “Good and thanks”, bai wani ja ta da magana ba, saboda ya fahimci jikinta a mace yake.

Kan stool ya aje wayar bayan sun yi sallama, kwantawa ya yi yana mai fuskantar POP ɗin da ya ƙawata rufin ɗakin, “Ya Allah, na ga Asma’u ina so, ka sa ta zama rabona, sannan ka tabbatar mani da Alkhairin da ke tare da ita”, addu’ar da ya yi kenan, saboda komai na rayuwa sai an nemi taimakon Allah, musamman ma shi da ya kasance kamar an yi masa baki, don tun da causin ɗinsa ta yaudare shi, ya haƙura da soyayya, mahaifiyarsa da duk wanda ke da iko a kansa sun yi faɗan ya yi aure har sun gaji, daga ƙarshe suka sa mashi ido, har sai lokacin da shi da kansa ya zo da maganar auren. Toh da alama lokacin aurensa ya zo.

Su Rahila kuwa suna kimtsawa suka ɗunguma hada su Hassana suka nufi gidansu Deeni da nufin yin bankwana. Da mamakin su Hassana sai suka ga ashe gidansu Lalu ne, cike da mamaki Hassana ta ce mashi “Kai, wai nan ne gidanku?”, Ya ce “Ƙwarai kuwa, kwana da yawa.”

Asma’u da ke tsaye a tsakar ɗakin ta ce “Ina kuka san juna?”, Lalu ne ya karɓe da faɗin “Toh zari gwana! Ina ruwanki”, a tsiwace ta ce “Daga tambaya?”, Hussana ta karɓe da “Ke rabu da shi, Abokinmu ne”, ta ƙarashe maganar tana dariya. Duk wanda ya san Lalu ya san shi da jama’a maza da mata, shi ya sa ba wanda ya yi mamaki da ta ce abokinsu ne.

Dosowar Deeni ɗakin ce ta sa duk suka maida hankalinsu a kan ƙofa, in banda Lalu da ya tafi domin ƙarasa shigowa da shi. Sosai ya ba duk wanda ke ɗakin tausayi, musamman su Hassana da yau ne suka fara ganinsa, ga shi dai cikakken namiji, amma jarabawa ta same shi. Kan kujera one seater ya zauna suka gaisa da juna, a cikin zuciyarsa kuma yana kallon kowa na ɗakin ɗaya bayan ɗaya. Ɓangaren da yake jiwo muryar su Hassana ya kalla “Ya Mommy?”, Suka ce “Lafiya lau take, tana gaida ku”, ya ce “Masha Allah, muna amsawa.”

Wayarsa ce ta sa kowa yin tsit, hannu ya zura aljihu ya fiddo tare da amsa kiran da sallama, bayan ta amsa daga can ne ya ce “Ina kika aje phone ɗinki, na kira sau ba adadi?”, Deena ta ce “Na sa chrg ne, kuma ina kitchen wurin yi ma su Mommah girki”, ya ce “Okay, sun dawo kenan?”, ta ce “A’a, sai zuwa anjima.”

Fatan dawowa lafiya ya yi musu, sannan ya ce zasu yi magana anjima saboda suna da baƙi, tambayar shi ta yi “Su waye?”, Ya ce “Su Dr. Rahila ne”, yana jin wata ƴar ƙwafar da ta yi kafin ta ce “Uhmm, ina gaida su”, bata jira ya sake magana ba ta tsinke kiran, a cikin zuciyarshi ya yi murmushi, tare da maida hankalinsa wurin Hajiyarsu lokacin da take magana da Rahila a wace unguwa suke a Kano.?

Rahila ta ce “Muna nan kusa da stadium ɗin Ahamad Musa”, Deeni ne ya ƙarasa ba Hajiyarsu amsa, don bata san inda wani stadium yake ba, inda ya ce “Hotoro kenan Hajiya”, Ta ce “Auho”, saboda ta san unguwar sosai.

Tunda aka barsu su uku a ɗakin wannan ce maganarsa ta biyu, don su Hassana da Fadila suna tsakar gida tare da Lalu da Abdallah ana maida yadda aka yi, Rahila kuma so take ta ji muryarsa, ta rasa ta ina zata sa shi doguwar magana, amfani ta yi da matsayinta na mai kula da lafiyarsa ta ce “Dr. Kamar kana sa damuwa a ranka ko?”, Murmushin yaƙe ya yi, tare da duban saitin da take zaune da zuciya, sai da ya lumshe idanunsa sannan ya ce “A’a”, ta ce “Ga shi kuma kana yawan yin shiru, kamar ba ka son magana?”, ɗan shiru ya yi, daga bisani ya ce “Dr. Ta ya wanda ya rasa idanunsa a ce ba zai yi damuwa ba?, Kwatsam fa ƙaddara ta same ni, na daina ganin duniyar nan mai cike da haske, ga mahaifiyata nan a kusa da ke kan Carpet, ina son in ga fuskarta in ji daɗi, amma ba wannan damar, haka ƴan uwana da nake tsananin so. Ga matata da yarona, ina son in ga fuskar ɗan da na haifa, shi ma ba dama, sai dai ayi ta siffanta mani shi, wai muna kama da ina yaro, shin wannan kaɗai bai isa ya sa ni a damuwa ba.?”

Wani irin tausayinsa ya taso musu ita da Hajiyar, take idanun Rahila suka ciko da ƙwalla, a hankali ta lumshe idanun tare da matse ƙwallan, lokaci ɗaya kuma ta ce “Gaskiya dole ka yi damuwa”, ya ce “You see, abin is not easy, kin ga damuwa dole ce ko?”, kai kawai ta iya jinjinawa “Uhmm.”

Hajiyarsu kuwa cewa ta yi “Allah ya baka mafita ta Alkhairi”, suka ce “Amiiiin”, tabbaci Rahila ta ƙara ba shi na zai samu lafiya idan sun je India, saboda a kwai likitoci ƙwararru a can, ya ji daɗin wannan Albishir sosai.

Sun yi ƴar hira ba laifi, daga bisani suka fara shirin tafiya saboda basu da lokaci. Sha tara ta arziki aka haɗa musu, sun ji daɗi sosai, dukkansu sun gode ma juna bisa ga karamci da suka yi ma juna. Albarka kuwa sun sha ta wurin Hajiyarsu Deeni. Da zasu tafi har waje Deeni shi ma ya raka su. Rahila kuwa kamar kada ta tafi saboda son da take mashi.

Bayan sun tafi ne Lalu ya ce ma Deeni “Mu shiga ciki ko?”, lokaci ɗaya kuma ya ruƙo sandar Deeni da nufin yi masa jagora, “Bari na riƙa kwatantawa Lalu”, bai yi masa musu ba, sai dai ya sanya mashi idanu tare da komawa gefensa.

A hankali Deeni ya riƙa sanya sandarshi a gaba, wadda ita ce ta kai shi har cikin ɗakin Hajiyarsu, a nan ne kuma ta faɗa mashi batun zuwan Dr. Bashir an jima, da kuma manufar da ya ce zata kawo shi, cewa ya yi “Aure da gaugawa haka?”, Hajiyar ta ce “Ni ma shi na gani Deeni, Ni tsoron samarin wannan zamanin nake”, ƴar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce “A bari ya zo mu ga inda ya dosa kawai”, ta ce “Toh shikenan.”

Asma’u kuwa gyara na musamman ta yi ma gidan da jikinta, wanda hakan ke nuna itama tana son Bashir, Lalu na lura da yanayinta ya ce “Wai wannan tsa-tsaf ɗin na miye?”, Amsa ta bashi da “Na idon matambayi ne”, dariya ya yi haɗe da faɗin “Allah dai ya aurar da ke mu huta da jarabarki”, bata ba shi amsa ba ta shigewar ta kitchen.

Wurin ƙarfe huɗu da rabi Dr. Bashir ya zo, kai tsaye kuma cikin gidan aka yi mashi iso a ɗakin Hajiyarsu Deeni, don da magabatan Asma’u yake son fara magana, idan sun amince sai a ɗora magana.

Har ƙasa ya durƙusa ya gaishe da Hajiyarsu Deeni da tafi jin daɗin zama a kan Carpet, cike da kulawa ta amsa mashi, hannu ya miƙa ma Deeni suka gaisa, sannan ya zauna ƙasa, Hajiyarsu Deeni ta ce “Ka koma kan kujera mana”, ya ce “A’a Hajja nan ma ya yi”, Deeni ya ce “A’a Dr. Ka dawo sama don Allah”, bai sake musu ba ya dawo kan kujerar ya zauna.

Ɗan shiru ɗakin ya yi, Hajiya da Deeni suna sauraron Bashir, inda shi kuma duk sun masa kwarjini, ya rasa ta ina zai fara. Deeni na fahimtar shiru ɗin Bashir ya ce “Dr. Ka yi shiru, Asma’u ta ce tafe kake da batu”, Bashir ya ji daɗin wannan damar da ya samu, kai ya jinjina tare da duban Deeni “Batu babba ma kuwa Dr.”, Deeni ya ce “Toh muna sauraren ka”, ya ce “Toh Nagode.”

Kallon da ya ga Hajja na masa ne ya sa shi sauke ganinsa a ƙasa, inda ya fara da “Abin da ke tafe da ni shi ne, na ga Asma’u, kuma ina son ta da aure, idan har ba a yi mata miji ba, toh ina son a ba ni dama, idan har na samu yadda nake so, toh a cikin sati biyun da ya rage za a yi komai a gama, idan zamu tafi India zan tafi da matata, tunda wannan shi ne fatan mahaifana.”

Tunda ya fara magana Deeni ke jinjina kai, Hajiyarsu Deeni kuma bata san lokacin da ta sauke ajiyar zuciya ba sadda ya kai ƙarshen maganar, “Babbar magana ta faɗa”, saboda har a ranta bata shirya rabuwa da Asma’u nan da mako biyu ba, duk da tana mata fatan ta yi aure.

“Aure da wuri haka Dr.?”, Deeni ya faɗa yana mai jinjina al’amarin, Bashir ya ce “Ƙwarai Dr. Indai an bani Asma’u”, Deeni ya ce “Toh Shikenan, Allah ya tabbatar da abin da yake Alkhairi”, da zuciya ya dubi Hajiyarsu da ya fahimci sanyin jikinta.

“Hajiya, me kika ce?”, Ɗan rausaya kai ta yi kafin ta ce “Ai ka gama komai Deeni, amma dai aure ai yana bukatar abu biyu ko? Bincike, da kuma fahimtar juna, idan duk an yi wadannan toh zamu baka Asma’u, duk da Ban shirya rabuwa da ƴar auta a yanzu ba”, dariya maganar ƙarshe ta basu, Deeni ya ce “Toh sai yaushe kika shirya rabuwa da ita Hajja?”, Tana dariyar itama ta ce “Toh Ni ban san lokacin ba, duk da ina son ta yi aure.”

Bashir ya ce “Kada ki damu Hajja, Insha Allahu zan kula maki da ita sosai”, ta ce “Toh Allah ya baka iko”, ya ce “Amiiiiin.”

Sati ɗaya suka ware zasu yi bincike a kansa, idan har sun samu ingantaccen bayanai,, toh magabata zasu haɗu a yi magana, sannan a ɗaura aure. Ya ji daɗin wannan damar da ya samu a wurinsu. Bayan ya keɓe da Asma’u ne ya ce “Autar Hajjah”, cike da salo ta kalle shi tana ƴar dariya, don wata irin kunyar sa take ji.

Faɗa mata yadda suka yi da su Deeni ya yi, daga ƙarshe ya ce “Yanzu ke zaki bada damar cigaban tafiyar, ki faɗa mani kina so na?”

Baki ta zumɓuro tare da shagwaɓe fuska, saboda tambayar ta mata tsauri, sosai salon ya tafi da shi, shima shawaɓewa ya yi “Idan bakya son na sai ne na faɗa musu ba sai sun yi bincike ba.”

“Toh bana son ka ne zan baka damar ka zo gidanmu?”, Ware idanu ya yi yana dariyar jin daɗi, domin ya samu amsar tambayar shi, domin tabbatarwa ne ya ce “Yanzu dai kina so na”, kai ta ɗaga “Uhmm”, ya ce “Alhamdulillah, Allah ya tabbatar mana da Alkhairi Amiin, domin ya ji daɗin yadda bata wahalar da shari’a ba. Zayyana mata irin son da yake mata ya shiga yi, tare da albishir ɗin rayuwa mai cike da farinciki idan sun yi aure. Batun asalinsa kuma cewa ya yi bincike ne zai nuna. Basu bar wurin ba sai da suka gamsar da junansu a kan soyayya.

A gidansu Deena kuwa ana sallar magarib su Hajiya Hadiza suka dawo, don haka a gajiye suke, basu samu damar yin magana ba sai washegari bayan sun gama breakfast ta kira Deena a ɗaki, faɗa mata ta yi cewar ta shirya tsaf zata je gidansu Deeni ta faɗa musu a raba auren kowa ya huta, don haka Deena ta amince? Ta ƙara tambayar Deena ne domin tabbatar da amincewar ta.

<< Mutuwar Tsaye 23Mutuwar Tsaye 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.