Skip to content
Part 25 of 36 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Wata irin sarawa kan Deena ya shiga yi sakamakon faduwar gaban da ta mamaye ta, har ta kai ga bata iya tantace sauran maganganun Ummanta, don kuwa tunda aka fara maganar raba su bata taɓa jin tashin hankalin da ya kai irin na yau ba. Toh! Ta ina ma zata fara juriyar rabuwa da Deeni, Anya zata iya?

“Ai yanzu India za’a fita da shi ayi masa aiki, me zai hana a bari ya dawo, idan an ga bai samu lafiya ba shikenan sai mu rabu”, Deena ta faɗa cike ƙasƙantar da kanta.

Daga kan gadon da Hajiya Hadiza ke zaune ta watso mata mugun kallo, don bisa ga dukkan alamu gardama zata yi mata yanzu “India kuma, yaushe za a fita davshi?”, da karfin guiwa Deena ta ce “Nan da two weeks zasu tafi”, ƙwafa kawai ta yi, don bata gamsu ba, kuma ita fa ko Madina za a kai shi, toh bata damu ba, shi ɗin ne bata son haɗa surukuta da shi, don haka ko ya warke ba damuwarta bane, saboda haka dole ma ta kashe mata aure.

“Deena, ana son raba ki da kaya, ke kuma kina naɗa musu gammo ko?”, ta faɗa fuska a murtuke, kai Deena ta girgiza alamun “A’a”, cewa Hajiya Hadiza ta yi “Toh, idan ba haka ba kina da tabbacin zai warke ne? Ita fa irin wannan makancewar ƙaddara ce wadda sai dai a mutu da ita, don haka idan kin zaɓi kashe kanki saboda so, toh ga ki ga Deeni nan, amma ki sani, ba ni, ba ke, sai ki kwashe kayanki ki koma ɗakinki, amma ko da wasa kada ki sake zuwa inda nake, tunda kin zaɓi miji akan uwarki.”

Tunda ta fara magana Deena ta rumtse idanunta gam, saboda ko mashi ne Ummanta take soka mata a zuciya sai haka, “Inna ki Llahi wa inna ilaihi raji’un”, Deena ta riƙa faɗi a zuciyarta, lokaci ɗaya kuma lips ɗinta na ta kyarmar tashin hankali “Me ya sa Mommah ta ke son yi mani haka? Me ya sa ba zata fahimci halin da zan shiga ba?”, tambayar da yi maka kanta a zuci kenan tare da fashewa da kukan tausayin kanta, don kuwa ta san mutuwa ce zata yi, tunda ya zama wajibi a gareta ta bi umurnin mahaifiyarta.

“Na cutar da ke ko? da zaki kama yi mani kukan banza da wofi”, ta faɗa cikin tsananin fushi. Kai Deena ta girgiza, cikin tsarƙewar Muryar kuka ta ce “Ba haka bane Mommah”, katse mata magana ta yi “Rufe mani baki, ni wawiyar yarinya ce irin ki da zaki riƙa yi mani musu? Toh ki sani, dole ki bi umurnina, idan ba haka ba, na rantse da Allah na yafe ki, ki je ki bi mijinki, ni kuma na barki da Allah”, tana rufe baki ta tashi fuu! Zata fita.

Da sauri Deena ta bi bayanta ta riƙe ta tana kuka, “Don Allah Mommah ki saurare ni”, fizge hannunta ta yi “In saurare ki ɗin Ubanki, ni zaki wulaƙanta, to na bar ma Deeni ke.”

“Wayyo Allah, na shiga ukuna Mommah, na rantse ba haka bane”, Deena ta faɗa hannunta a ka tana matsanancin kuka, saboda fushin mahaifiyarta ba ƙaramar barazana yake zame mata ba.

Raɓe Deena ta yi ta nufi ƙofa, bakinta na faɗin “Dubu ma sai kin shiga idan baki bi magana ta ba”, kiciɓus ta yi Alhaji Lawan yayin da ya shigo ɗakin, Deena na ganin shi ta ruƙo mashi hannu tana faɗin “Daddy, don Allah ka ce ma Mommah ta saurare ni”, cike da tausayin Deena ya yi ma Hajiya Hadiza kallon tuhuma, saboda ya lura idan bata tada zaune tsaye ba hankalinta bai taɓa kwanciya.

“Ke me ya sa ba kya son zaman lafiya? Kin ƙi barin yarinya hankalin ta ya kwanta”, ya faɗa cike da nuna mata rashin kyautawarta.

“Alhaji, kada ka shiga wannan faɗan, saboda kai ƴaƴanka mata na can cikin daraja a gidajensu zaka faɗi haka ko.?”

 

Bai taɓa tsammanin zata faɗi haka ba, ɓoye mamakinsa ya yi ta hanyar faɗin “Toh ita Deena ba ƴa ta ce ba ko?”, ta ce “Eh, ubanta ita ya mutu, shi ya sa zan yi abin da zai aikata ko da yana raye.”

Wannan magana ta tsuma shi, ajiyar zuciya ya yi tare da faɗin “Toh Shikenan, amma idan da Ubanta na da rai sai ya yaƙe ki a kan wannan rashin adalcin da zaki yi”, yana kai wa nan ya dubi Deena, “Deena, ke ƴata ce, amma zan bar mamanki ta yi playing wani role wanda ta nuna mani ban isa ba a kanki, don haka ki yi haƙuri, kuma ki bi umurnin mahaifiyarki, ina mai tabbatar maki da ba zaki taɓe ba”, yana kai ƙarshen maganar ya sakar ma Deena da idanunta ke rufe hannu, bai jira jin wata magana daga bakinsu ba ya fice daga ɗakin.

Deena na ganin haka ta durƙushe kan guiyawunta, riƙe ƙafafun mahaifiyarta ta yi tana kuka, lokaci ɗaya kuma ta ce “Don Allah ki gafarce ni Mommah, ki yi duk abin da kike so a aurena, na haƙura da shi tunda ba kya so”

Ware hannayenta ta yi “Ba so ne bana yi ba, cutarwar da ke cikinsa ce nake guje maki, amma ba kya ganewa.”

“Na gane Mommah, na gane”, Deena ta ɗago kanta da ke ta girgizawa ta dube ta.

Maimakon wannan sadudar ta Deena ta sauko mata da girman kanta, sai ma ta ƙara sa mata wata izza, don dama ita haka take “Gafara ki bani wuri”, ta faɗa haɗe da janye ƙafarta ta fice, ɗif wutar Deena ta ɗauke, a hankali ta lumshe idanun ta, hatta sautin kukanta cikin zuciya ya koma, inda ta riƙa gunji.

 

Yanzu ina zata sanya kanta, da baƙincikin rabuwa da mijinta, ko da fushin da mahaifiyarta ta yi? Bata da wani wayau ko dubara yanzu a kan wannan lamarin, don haka dole ta yi kuka ko da zata mutu.

 

Jiri na ɗibarta ta koma ɗakinta, kan gado ta faɗa haɗe da kifa kanta a kan fillow ta cigaba da kukan da bata san ranar tsayawarsa ba, don raba ta da Deeni daidai yake da raba ta da rayuwar ta, a cikin kukan ta riƙa tuno irin tsananin son da Deeni ke yi mata, wanda zata iya rantsewa da son da yake mata ya ɗara wanda take mashi, toh shi ya zai yi idan ya ji wannan batu?

 

A nashi bangaren, tun jiya da Deena ta faɗa mashi mahaifiyarta ta dawo ya shiga tunanin maganar da ta ce sai ta dawo za su yi ta, kuma wannan batu yana ɗan tayar mashi da hankali, duk da tunaninsu bai kai ga saki ba, number Deena ya fara kira, amma ya ji switch off, mafarin yana shiga ɗakin Hajiyarsu ya faɗa mata Maman Deena fa ta dawo, don haka a kira ta waya.

Kamar yadda ya ƙagara ya ji maganar Umman Deena, haka itama Hajiyar ta ƙagara, sai dai kuma yana da kyau a bari ta huta, tunda suna da yaƙinin ba ta manta ba.

 

Cewa ta yi “Me zai hana a bari ta huta tukunna sai a kira?”, ko kusa Deeni bai so haka ba, sai dai ba zai iya fitowa kai tsaye ya nuna mata ba, “A bari ta huta kuma?”, ya faɗa cikin sanyin murya, ta fahimce shi sosai, mafarin ta dube shi da idanunta masu matukar tausayinsa.

 

“Ka san halin shu’umar surukar taka, amma dai bari a kira ta mu ji, ya ji daɗin haka, cewa ya yi “Yauwa toh”, wayarta ta ɗauka ta yi dialing Number Umman Deena, sai dai har ta tsinke bata ɗaga kiran ba, sake kira ta yi, har Hajiyarsu Deeni ta yanke tsammanin da zata amsa kiran ta ji sallama daga cikin wayar.

Gaisawa suka fara yi, daga bisani Hajiyarsu su Deeni ta yi mata sannu da dawowa haɗe faɗin “Kwanaki mun fara magana kika ce a bari ki dawo”, daga can cikin galatsi Umman Deena ta ce “Eh, gashi kuma na dawo Hajiya”, Hajiyarsu Deeni ta ce “Toh muna sauraren ki, so muke idan da hali a tsara yadda Deena zata dawo ɗakinta, kafin Deeni ya tafi, ko kuma sai idan ya dawo daga India?”

 

“Ai Hajiya bana tunanin Deena zata dawo ɗakinta”, sosai amsar ta rikitar da Hajiyarsu Deeni, tare da jefa ta a ruɗani, idanunta na cigaba da kallon Deeni da ya fara bayyana tashin hankalinsa a fuska ta ce “Kamar ya ba zata dawo ɗakinta ba Hajiya Hadiza? Ina ce Deena ta gama wanka ko.?”

 

Ba tare da shakkar komai ba Umman Deena ta ce “Hajiya ina nufin a raba auren, don Deena ta yi ƙarantar da ba zata iya ɗawainiya da Deeni ba.”

 

Maganar ta jijjiga Hajiyarsu Deeni, amma sai ta danne don kada a ga rauninsu ta ce “Hajiya Hadiza kin san me kike faɗa kuwa? Kina faɗin a raba aure sai ka ce auren ƴar tsana?”

 

“Hajiya ni bana ganin wannan abun da wata illah, tunda itama Deenar ta amince”, Hajiyarsu Deena ta ce “Toh Shikenan, sai dai mu ba ƙananun mutane ne da basu san darajar aure ne ba, zamu nemi waliyyanta da suka bamu ita, idan ya so zamu yanke duk hukuncin da ya kamata”, katse kiran ta yi, don ba zata iya jurar maganganun da ƴar cikinta zata riƙa faɗa mata ba, don kawai ƴaƴansu na auren juna, tunda a girme ma ba za a haɗa Hajiya Umma da Umman Deena ba.

 

Deeni da ba abin da kunnensa bai ji ba ya dafe kai tare da sauke numfashi mai bayyana tsantsar tashin hankalin da ya samu kansa a ciki, “Inna li Llahi wa inna ilaihi raji’un”, ya shiga furtawa cikin zuciyarsa, saboda shi ma bai san ta ina zai fara ɗaukar wannan bala’in ba.

 

“Ka ji me ta ce ko?”, Hajiyar ta tambaye shi, ya ce “Na ji, kawai Allah ya kyauta”, Hajja ta ce “Amiin, amma ban san wace irin suruka ce wannan ba, a ce uwa ta kashe auren ƴarta ba dalili?”, cike da ƙarfin hali Deeni ya ce “A’a dalilinta shi ne na makance, kuma ƴarta ba zata iya rayuwa da makaho ba”, Wannan magana ta harzuƙa Hajja, cewa ta yi “Makanta? Akwai ubanda ya wuce ƙaddarar Ubangiji ne?, Ni masifar matar nan ta ishe ni wallahi, tunda aka yi auren nan bata bari an zauna lafiya ba.”

 

Deeni ya ce “Za a samu lafiyarta idan aka bar mata ƴarta, ni ma na gaji Hajja, zan yi abin da take so ko da hakan zai shafi rayuwata.”

 

Yadda ya ƙarashe maganar cikin raunin murya ne ya ƙara ɓata ranta, faɗa ta shiga yi kamar Umman Deena na gabanta, Lalu na shigowa ya tambayi ba’si, ana faɗa mashi ya ɗuro ashar , sannan ya biyo bayan ashar ɗin da faɗin “Don Allah a bar mata ƴarta, ta ga idan Yaya zai fasa rayuwa”, Deeni ya ce bar mata ƴarta za a yi kuwa Lalu, Insha Allahu ba zamu ƙara jayayya da ita ba.”

 

 

Ta wani bangaren Hajiyarsu Deeni ta ji daɗin ƙarfin halin da ya nuna a take, duk da ta san abin dole ya taɓa mashi zuciya.

 

Umman Deena kuwa maganar da ta gaya ma Alhaji Lawan ce ta dawo mata a rai, take ta gane bata kyauta ba, don kuwa ko maƙiyinsu ya san Alhaji Lawan na ƙaunar Deena kamar yadda yake ƙaunar ƴaƴansa, asali ma ya fi fiddo tausayinsa a kanta, fiye da ƴaƴansa, saboda ita marainiya ce, kuma ya ɗaukar ma ransa indai yana da rai ba zata yi kukan maraici ba. Sai dai kuma son zuciya ya sa Umman Deena mantawa da wannan ƙoƙarin nasa har ta furta mashi maganar da bata dace ba, duk da ta fara tuhumar kanta. Ita dama haka take, sai ta yi abin, daga ƙarshe ya dawo yana sha mata kai, musamman da ta je ɗakin Alhaji Lawan, kuma ta ga ya ba banza ajiyarta har ta fito.

 

Da abin ya cigaba da isar ta ne ta sake iske shi a Bedroom ɗinsa yana shirin fita, babbar rigarsa da ke aje kan gado ta kai hannu zata ɗauka, da nufin taimaka mashi ya sa kamar yadda ta saba, “Na hutar dake”, ya faɗa tare da janye rigar, lokaci ɗaya kuma ya yi mata kallon mai cike da tsana, don kuwa ya tsani butulci a rayuwarsa.

 

Murya a kunya ce ta ce “Dama kai kaɗai ke shirya kanka ne?”, tamkar ya mare ta ya ji, don wannan ne karon farko da ta yi mashi abin da ya ji tsanarta a ransa, saboda ainahin rashin wayonta ya bayyana.

 

“Na ce bana so, ki fita ki bar mani ɗaki”, ya faɗa tare da fizge rigar da ta ɗauka ya sanya, sosai hankalinta ya tashi, saboda bai taɓa fushin da ya yi zafi irin haka ba, duk simplicity ɗinsa bai kai na ya ɗauki raini ba, bayansa ta bi lokacin da ya ɗauki waya da agogonsa ya nufi ƙofa, ɗan ruƙo hannunsa ta yi “Alhaji me yas a ba zaka fahimce ni ba”, sheƙeƙe ya dube ta, “Ta ya zan fahimce ki tunda ba ni ne Uban ƴarki ba, don haka ki yi yadda kike so, amma ki sani, ba na rantse ba, amma yanzu na gama shiga batun ƴarki har sai lokacin da kika gane gaskiya kuma kika yi nadama”, yana rufe baki ya fizge hannunsa ya fice, ransa ɓace ya wuce ta ƙofar ɗakin Deena, inda sautin kukanta ya sa shi haɗiye wani gululun baƙinaciki, tabbas yana tausayin Deena, amma da alamar akwai jarabawar da ke shirin samun ta, wadda a yanzu bai da iko a kanta, “Allah ya baki mafita” ya faɗa a ransa, lokaci ɗaya kuma ya wuce ƙasa, kai tsaye wurin motarsa ya nufa, inda driver ya ɗauke sa suka fita.

 

Umman Deena kuwa kasa motsawa ta yi daga inda take, saboda tabbas Alhaji Lawan ya yi fushi, kuma a iya sanin da ta yi mashi duk abin da ya ɗauke kansa a wurinsa, toh ya barshi kenan bari na har abada, ko da kuwa abin ya sake maido kansa wurinsa, “Toh sai me? Tunda Allah ya san mafita nake nema ma ƴata”, abin da wani sashe na zuciyarta ya ruwaita mata kenan, take ta samu ƙwarin guiwar ficewa daga ɗakin.

 

Kukan Raihan ne ta tsinkayo a ɗakin Deena, a hankali ta murɗa handle ɗin ɗakin, kwance ta hango Deena ta kifa kanta tana kuka, yayin da shi ma yake gefenta yana tsandara na sa kukan da ya game upstairs ɗin, “Ba kya jin kukansa ne? Kin wani kife kai kina mana kukan Isakanci.”

Tuni Deena ta yi nisan da bata jin komai sai ƙunar da zuciyarta ke yi, hatta Raihan ɗin sama-sama take jin sa, mafarkin ta kasa motsi bare ta tsinana masa wani abu, kamar daga sama ta ji duka a bayanta, lokaci ɗaya kuma Ummanta na faɗin “Don Ubanki ba magana nake ba”, a firgize ta tashi bakinta na faɗin “Wayyo Allah Mommah, me na yi?”,

 

Saukar marin da ta ji a kumatu tare da faɗin “Ubanki kika yi”, ne ƙara gigita ta, hannunta dafe da kumci ta ci gaba da kallon mahaifiyarta. Ita kam wace irin jarabawa ce wannan? Ga Mari double-double, ga kuma tsinka

jaka, kuma a wurin wadda ya kamata ace ta tausaya mata!

<< Mutuwar Tsaye 24Mutuwar Tsaye 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×