“Me ya faru kake faɗin Allah ya ƙara?”, kamar daga sama Bello ya tsinkayi muryar matarsa tana mashi tambaya, don kuwa saboda muguntar da ta cika masa rai bai san da zuwan ta ba. Murna fal a ransa ya ce “Wancan makahon ne aka ce surukarsa ta ƙwace ƴarta”, jiki a sanyaye ta zauna gefensa tare da faɗin “Kuma shi ne kake faɗin ya Allah ƙara?”, fuskarta bayyane da tausayi ta ƙarashe maganar, domin ita dai Deeni tausayi yake bata.
Ya san halinta sarai bata goyon bayan miyagun halayensa, mafarin ya haɗe rai “Toh me kike so na ce?”, ta ce “Babu daɗi dai, ni wallahi tausayi yake ba ni, ba idanu, kuma ba mata? Haba don Allah”, haushin Deeni ne ya ƙara turnuƙe shi, cewa ya yi, “Tausayi kuma?”, ta ce “Eh”, ya ce “Toh ki daina wahalar da kanki ma, wannan mutumin shi ne ya hana mijinki saƙat a wurin aiki, yanzu da baya nan ke kanki kin ga chanji, tunda ga shi har ƴan kumatu kin ƙara”, cike da salo ya ƙarashe maganar tare da shafar kumcinta da ya ciko saboda jin daɗi, da yake mace ce, cikin ɗan lokaci ya cire mata wannan sanyin jikin, “Allah ya kyauta”, ta faɗa tare da miƙewa ta koma kitchen. Shi kuwa kwanciya ya yi, ya ci gaba da ƙulla makircinsa.
Sai dai wannan makircin bai isa ya yi abin da Allah bai yi ba, domin halin da Deeni yake ciki ya yi Imani da cewa jarabawa ce daga Allah, kuma komin daɗewa zata zama labari da ikon Allah. Amma fa duk da haka yana jin ƙunar rasa Deena da ɗansa a kusa da shi, duk da ya so koya ma ransa haƙuri da juriya, amma ko da ya yunƙura, sai ya ji zai iya mutuwa, mafarin ya saduda. Addu’a ce ta zame mashi abin yi ba dare ba rana, abinci kuwa sam baya iya ci, in banda black tea kaɗai da ya ke ɗan sha.
Lalu na lura da baya cin abinci ya kawo ƙarar shi wurin Hajiyarsu, don da an kawo mashi sai ya ce a kai mashi ɗaki, idan ya shiga zai ci a can, daga ƙarshe ko dai ya ci kaɗan, ko kuma a fito da shi.
Shigowarsa ɗakin Hajiyarsu kenan da safe ta ce mashi “Deeni”, ɗago kansa ya yi, tare da duban inda yake jiyo sautin muryarta da zuciya.
“Lalu ya kawo mani ƙararka baka cin abinci, haka ne?”, bai yi musu ba ya ce “Hajiya bana iya cin abincn”, da ɗan faɗa-faɗa ta ce “So kake ka kashe kanka ko?”, shiru ya yi, wanda ya bata damar ci gaba da faɗin “Ban hana ka yin damuwa ba tunda an jarabe ka, amma ka yi a hankali, kada ka jefa kanka cikin wata masifar ta daban, wadda mu da kai ne kaɗai zata cutar, sai kuma ɗanka da duk rintsi zai ƙaunace ka idan ya girma.”
Kasaƙe Deeni ya yi yana sauraron ta, inda ta cigaba da cewa “Ita jarabawa Mumini take samu, don haka ka daure ka riƙa cin abinci ka ji ko?”, yadda faɗan ya ƙare da lallashi ne ya ƙara narkar mashi da zuciya, cikin raunin murya ya ce “Insha Allahu Hajjah.”
Tabbas idan aka ci gaba da maganar sai kukan da yake haɗewa ya fito fili, mafarin ya yi gaugawar kawar da maganar ta yin batun kuɗin auren Asma’u da za a kawo yau tare da fidda ranar da za a ɗaura musu aure, saboda sun binciki Bashir da ahalinsa sosai, kuma sun gamsu da nagartar su, tunda gashi har yau waliyyansu zasu haɗu a ƙarasa maganar.
“An faɗa ma ƴan Funtua kuwa batun auren Asma’u?”, su ma dangin mahaifinsu ne da ya zama wajibi a faɗa musu domin fita haƙƙi, Hajiyar ta ce “Eh, an faɗa musu, amma sun ce a aiwatar da komai, sai idan bikin ya zo zasu zo”, kai ya ɗan jinjina, lokaci ɗaya kuma gabansa ya girɗe ya faɗi sakamakon kiran da ya shigo wayarsa, wanda ko tantama babu Deena ce, saboda sautin da ya zaɓar ma number ta ne ke tashi.
Hannu ya sa aljihu ya fito da wayar, danna power wayar ya yi, sannan ya maida wayar aljihu, domin bai iya ɗaga kiran, saboda kukanta fama mashi ciwon da ke ranshi yake, ƴan maganganu suka ƙara da Hajiyar sannan ya koma ɗaki ya kwanta.
Tunanin yadda zai cigaba da rayuwa ba tare da Deena da ɗansa ba ya dasa, don yana jin da wahala ya iya. Tabbas Umman Deena ta cutar da shi, cutarwar da yake fatan Allah ya saka mashi, kukan da ya saba duk lokacin da samu kansa shi kaɗai ya cigaba da yi, cikin ransa kuma yana addu’a’ar Allah ya ɗauki ranshi ya huta da wannan bala’in.
Hajiyarsu kuwa jugum ta yi a inda ya barta zaune, baccin damuwar halin da Deeni yake ciki, hada ta kewar rabuwa da Asma’u kuma, tabbas tana son Asma’u ta yi aure, amma ba yanzu da take taimaka mata ba, don ba abin da Asma’u bata yi mata na kyautawa, duk da dolen Asma’u ne. Sallamar Yaya Asiya ce ta katse mata tunanin, don bata ji shigowarta ba, sai dai sallamarta a bakin ƙofa.
“Ku ne tafe?”, ta faɗa idanunta na kallon Yaya Asiya da ke sanye cikin ƙayataccen swiz kace mai ruwan peach, wanda aka ƙawata flowers ɗinsa da purple color. Duk a cikin ƴaƴanta ba wanda ya kai Asiya hutawa, saboda mijinta yana da kuɗi, sannan ita kanta sana’ar siyar da sutura take, shi ya sa take ɗasawa.
Kusa da ita a kan Carpet Asiya ta zauna bakinta na faɗin “Ni kaɗai na zo ko?”, amsa Hajiyar ta bata “Ke kaɗai ce fa, mun yi waya da Salma ta ce suna tafe ita da Asma’u.”
Kai Asiya ta ɗan rausaya tare da gaishe da Hajiyar, bayan ta amsa ne Asiya ta ɗaura da tambayarta “Hajjah, wai jikin ne?”, tambaya ta maido ma Asiya “Me kika gani?”, Asiya ta ce “Duk kin rame sosai”, guntun murmushi ta yi tare da girgiza kai “Asiya idan ban rame ba in yi me? Damuwar raba Deeni da matarshi kaɗai ta ishe ni, ga lalurarsa ta rashin gani, sannan ga auren Asma’u da ya zo a lokacin da ni dai ban shirya ba Asiya”, sosai Asiya ta fahimce ta, cike da tausayin mahaifiyarta ta ce “To ya za a yi Hajja, shi aure lokaci ne da shi, idan ya yi, ba makawa sai an yi, sannan rayuwa ce da shi, idan karshensa ya zo sai ya mutu, kawai a fawwala ma Allah kawai”, Hajiya ta ce “Gaskiya ne, Allah ya bamu mafita baki daya.”
Tattauna tsare-tsaren da suka shirya a kan surukan Asma’u da zasu zo suka shiga yi, suna cikin maganar ne su Hajiya Ummah, Salma da Asma’u suka shigo.
Da mamaki Asiya ta ce “Ina kuka haɗu?”, saboda ba mahaɗa a unguwar da Hajiya Umma da Salma suke, Hajiya Ummah ta ce “Napep ta haɗa mu”, Asiya ta ce “Kamar ya?”, Asma’u ta ce”Mun tsaida Napep kawai muka ga ita ce a ciki”, Hajiyar ta ce “Ka ji wani ikon Allah”, dariya suka yi, Asma’u ta ce “Shi kanshi Mai Napep ɗin sai da ya yi ta mamaki yana dariya, da ya ji yadda muke , Yaya Asiya na dariya ta ce “Ai dole.”
Cike da girmamawa suka gaishe da Hajiyar, Hajiya Ummah ta ce “Ina Deeni?”, don bata ganshi ba”, Asiya ta ce “Yana ɗakinsu”, kai ta rausaya, suka ci-gaba da tsokanar Asma’u, inda Asiya ta ce “Amarya ba kya laifi”, duƙe kai ta yi tana dariya, Hajiyar ta ce “Ai ni wannan amarya, ku dai yi mata faɗan tsiwar nan, ni ita kaɗai ce damuwa ta”, Salma ta ce “Ko yau faɗan da na yi mata kenan Hajjah, wai a waya ma sai da suka kafsa faɗa ita da Lalu, daga ya kira ta zai tambaye ta”, kamar zata yi kuka ta ce “Shi ne fa ya tsokane ni da faɗan”, Hajiya Ummah ta ce “Ko shi ne ya tsokane ki baki san shi yayanki ne ba? Hakan na nufin mijinki ma ba zaki rangwanta masa ba idan saɓani ya haɗa ku ko.”
Yadda Asma’u ke son Bashir bata tunanin zasu yi faɗa da shi, cewa ta yi “Ai Lalu ɗin ne mafaɗaci”, daidai lokacin kuwa ya shigo ɗakin.
“Inyee! Gulma ta ake ko?” Ya faɗa tare da ƙarasowa cikin ɗakin, Asiya ta ce “Faɗa ake mata ta bar tsiwa saboda aure zata yi, shi ne ta maida laifin a kanka”, ƙwafa ya yi kafin ya ce “Allah ya yaye mata, in dai faɗa da ni ne ma ta gama”, aikuwa ta ce “Da dai ya fi”, Hajiya Ummah ta ce “Zan mare ki fa Asma’u, ko an faɗa maki wasa muke da ke, shashasha marar wayau”, tsit Asma’u ta yi tana sauraron faɗan da suka shiga yi mata wanda zai haifar mata da zaman lafiya idan ta yi aure.
Lalu kuwa bar musu ɗakin ya yi, inda ya koma ɗakinsu, yadda ya ga Deeni kwance ya ɗauka bacci yake, mafarin ya raɓa gefen gadon ya zauna tare da cigaba da danna wayarsa.
Ba tare da tsammani ba ya ji Deeni ya ce “Lalu, ɗan rufa mani blancket a jiki, zazzaɓi nake”, ta shi Lalu yayi bakinsa na faɗin “Subhanallah, na ɗauka bacci kake ai” bargon dake gefe ya jawo ya lulluɓa ma Deeni a jiki, lokaci ɗaya kuma yana faɗin “Magani fa? A ɗauko maka?”, daga kwancen Deeni ya girgiza kai “No Lalu, bana iya sha.”
Nannauyar ajiyar zuciya Lalu ya sauke, don ya san wannan zazzaɓin na ƙunci ne kawai, “Allah ya sawaƙe”, ya faɗa tare da ficewa ya koma ɗakin Hajiyarsu, Hajiya Ummah dake zaton fitowarsu tare da Deeni ta ce “Wai ina Deenin?”,
“Yana can zazzaɓi yake?”, Lalu ya faɗa cike da damuwa a fuskarsa, Hajiyarsu ta ce “Zazzaɓi kuma? Yanzu fa ya fita daga ɗakin”, Lalu ya ce “Yana can dai kwance”, Kamar Hajiyarsu zata yi kuka ta ce “Kai..! Allah ya ba shi lafiya.”
“Bari mu ga yanayin da yake ciki?”, Hajiya Ummah ta faɗa tare da miƙewa, bayansa suka bi zuwa ɗakin don ganin halin da ɗan’uwansu yake ciki.
Yadda suka ganshi ƙame a kan gado ne Asiya ta ce “Bacci ma yake ko?”, kai Lalu ya girgiza, inda shi kuma Deeni ya ɗan motsa domin tabbatar musu da idonsa biyu. Hajiya Ummah ce ta ɗan yaye bargon gami da taɓa wuyansa, zafin da ta ji a jikinsa ne ya sa ta saurin janye hannunta bakinta na faɗin “Lallai zazzaɓi yake sosai”, cike da tausayinsa Asiya ta matso “Sannu Yaya”, ɗan ɗaga kai ya yi alamar “Yauwa”, saboda baya iya tashi saboda rikewar da zuciyarsa ta yi.
Salma ce ta ce “Lalu ka ɗauko mashi magani ya sha kafin a kira Doctor, don wannan jikin sai an haɗa da allura”, Asiya ta ce “Gaskiya kam”, don itama ta ji irin zafin da jikinsa ya yi.
Lalu ya ce “Wanda bai ci abinci ba ta ina zai sha magani? Duk yau ko ruwa bai sha ba, ku san kullum da yunwa yake kwana”, Ran Hajiya Ummah a ɓace ta ce “Da sakel kuwa, yanzu Hajiya ke faɗin baya cin abinci, dole kuwa ciwo ya sarƙi mutum”, matsa mashi Hajiya Ummah ta yi a kan ya tashi, duk da rikewar da zuciyarsa ta yi bai yi mata musu ba, tashi ya yi haɗe da jingina bayansa da kan gado yana sauraron Hajiya Ummah dake faɗin “Deeni me ya sa baka son abinci?” cikin raunin murya ya ce “Bana iya ci ne Hajiya”, ta ce “Kamar ya baka iya ci, so kake ka cutar da kanka halan? Idan fa ka mutu mu ke da asara ba Hajiya Hadiza da ƴarta ba, don haka ka bi a sannu.’
Su Asiya da Salma kuwa sai kallon tausayi suke mashi, Asma’u kuwa tuni ta fice ta kwarmata ma Hajiyarsu sosai Deeni ke jin jiki, ba tare da ɓata lokaci ba kuwa ta shigo ɗakin itama.
Sosai yanayinsa ya girgiza ta, amma sai ta danne ma ranta ta shiga yi masa faɗa inda ta ce “Idan ka ja na mutu shikenan, baka san ƙuncin da zuciyata ke ciki ba a kan halin da kake ciki, maimakon ka koyi danne ma ranka, sai kuma ka ƙara mani wata damuwar”, sosai Deeni ya ji ba daɗi a ransa, cikin raunin murya ya ce “Ki yi haƙuri Hajjah.”
Wani irin tausayinsa ne ya kama su, har ta kai ga kaf cikinsu ba wanda bai zubar masa da ƙwalla ba, Asiya ta ce “Ai yana da haƙuri Hajjah, kawai yanzu zazzaɓi ne da ake ta fama da shi”, tuni itama ta sauko , inda ta ce “Toh Allah ya sauwaƙe, amma yana da kyau ya koyi juriya, ba don komai ba ma sai don aikin da za a yi mashi, idan yana da damuwa ta ina aikin zai yi kyau?”, suka ce “Gaskiya ne.”
Nasiha mai ratsa zuciya ta yi musu baki ɗayansu, sannan ta umurci Lalu da ya kira Doctor a yi treating ɗinsa.
Fitowa suka yi daga ɗakin, inda suka cigaba da hidimar tarbar surukan Asma’u. Da yamma kuwa bayan la’asar suka zo, An yi sa’a kuma Deeni ya samu sauƙi, don haka da shi aka tarbi baƙin, sai kuma Khamis da sauran iyayensu.
Cike da farinciki Walliyyan Bashir suka nema mashi auren Asma’u, yayin da waliyyanta suka amince gami da tabbatar da cewar sun ba shi Ita, bisa ga karɓar sadaki da kuɗin lefe 2.5M lakadan.
Bayan tafiyarsu ne Alhaji Bala ya ɗan tangari ƙeyar Asma’u yana dariya “Inye, su Asama an yi goshi”, dariya mai cike da kunya ta ruga kitchen tana yi.
Wayarta da ke ta ruri tun a waje ta ɗauka, “Matata”, Bashir ya faɗa cike da daɗin rai, cewa ta yi “Yaushe na zama matar?”, ya ce “Nan da three days mana, nan da one week kuma muna India”, Ras gabanta ya faɗi, saboda duk kamar wasa take jin labarin, yanzu a wannan lokacin da Hajiyarsu ke tsananin buƙatarta ne zata tafi ta barta? Kai da sakel.!
“Don Allah da gaske kake saura three days?”, ya ce “Sosai ma, ba ki ga su Kawu sun zo ba?”, cikin sanyin murya ta ce “Na gani”, ya ce “Toh sun ƙarƙare magana, ranar Friday za a ɗaura aure, On Tuesday kuma zamu tafi.”
Maimakon ta yi murna, sai ma ta haɗe rai sakamakon fargabar da ke ta ƙara mamaye ta, “Lallai ma”, kaɗai ta iya faɗi, sosai ya fahimce ta, cike da tsokana ya ce “Ko bikin ya yi kusa ne”, da sauri ta ce “Eh, don Allah a ɗaga”, ya ce “Ko?”, ta ce “Allah kuwa, bana son na bar Hajiyarmu, gashi bata da lafiya”, tunda ya ji ta sako batun Hajiyarsu sai ya muhimmantar da maganar ta hanyar faɗin “Toh ki bari idan na zo an jima sai mu ƙarasa maganar”, ta ji daɗi sosai, cewa ta yi “Yauwa Babe”, cike da jin daɗi ya ce “Me ne kika ce?”, ta ce “Sweet Babe”, ya ce “Awwnn”, inda su duka suka yi dariya.
Hirarsu mai cike da zallar ƙauna suka sha, daga bisani suka yi sallama. A take kuma kiran Deena ya shigo wayarta, da farko kamar ba zata ɗaga ba saboda saboda tsaf Deena zata sanya ta kuka, amma da ta tuna su ɗin ƙawaye ne, dole su yi kuka tare sai ta ɗaga, maganar farko da Deena ta fara yi cikin sanyin jike ita ce “Na ɗauka kema ba zaki amsa call ɗina ba”, cike da son kare kai Asma’u ta ce “Haba, a kan me zan ƙi amsa call ɗinki”, daga can Deena ta ce “A kan komai ma”, Asma’u bata bari maganar ta yi tsawo ba ta kwantar mata da hankali a kan duk rintsi ita tana tare da ita, kuma ko Deeni da ya ke ƙin ɗaga kiranta yana yi ne domin su samu zaman lafiya a zukatansu, amma ba don yana fushi da ita ba, daga can Deena ta ce “Uhmm, yanzu ina Yaya?”, Asma’u ta ce “Yana can suna magana, kin sa
n saura one week su tafi..”