Skip to content
Part 28 of 36 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Sosai Asma’u ta fahimci ruɗun da Deena ta shiga sakamakon jin Deeni ya kusa barin ƙasar, don kuwa cikin in’ina ta ce “Kekke don Allah, da gaske kike?”, Asma’u ta ce “Allah kuwa”, sai da Deena ta ɗan saurara kafin ta ce “Amma bai faɗa mani ba, ko da yake ya daina kira na, kuma idan na kira baya picking call ɗin”, kamar zata yi kuka ta ƙarashe maganar, hakan ya ne ya ƙara ma Asma’u tausayin ta, domin a yanzu Asma’u ta san menene so, kuma tana fargabar abin da zai shiga tsakaninta da soyayyarta wadda ke shirin kai wa ga aure, shi ya sa take matuƙar tausaya ma Deeni da Deena.

Cike da lallashi ta ce ma Deena “Ki yi haƙuri da rashin kiran ki da Yaya baya yi, ina da yaƙinin yana yin haka ne saboda baya son ƙara maki wata damuwar”, kukan da ke maƙale a ran Deena ne ya suɓuce mata, daga can cikin wayar ta ce “Haba Asma’u, har akwai wata sauran damuwa da ban shiga ba? Kawai Yaya yana fushi da ne a kan laifin da ba ni na aikata ba”, Asma’u ta ce “Shima fa yana cikin damuwar, ko abinci baya iya ci, kuma ko yau bashi da lafiya, kawai ƙarfin hali ne ya sanya shi iya attending baƙin da suka zo.”

Cikin kukan da Deena ke yi ta ce “Toh shikenan, don Allah idan sun tafi zan sake kira, sai ki ba shi wayar”, Asma’u ta ce “Baki da damuwa ƙawata”, kafin Deena ta sake magana ta jiyo muryar Umman Deena na kiran ta a cikin wayar, Deena ta ce ma Asma’u “Ina zuwa, Ummah na kira na”, Asma’u ta ce “Toh, sai na ji ki”, tare da tsinke kiran.

Jugum Asma’u ta yi tare da daidaita jinginar da ta yi da cabinet na kitchen ɗin, cikin ranta tana ƙara jajanta ma Deena a kan halin da take ciki, don ta fi tausayin ta, duk da cewar Deeni ɗan’uwanta ne, kawai ta yi amfani da karin maganar nan da ake cewa “Ciwon ƴa mace na ƴa mace ne”, mafarin ta tambayi kanta “Ya zan yi a ce nice aka raba da Uncle Bash?”, jin da ta yi zata iya mutuwa saboda tsananin son da take mashi ne ta yi saurin girgiza kai, a fili ta ce “Allah kada jarabce ni da rabuwa da Bashir, su da ka ɗaura mawa ka basu mafita ta Alkhairi ya Allah.”

 

Kunyarsu Alhaji Bala ce ta sa ta shigowa kitchen ɗin, don haka tana jin tafiyar su ta fito. Ɗakin Hajiyarsu ta shiga, aikuwa ta ga kuɗi him ƙasan carpet a gabanta, “Hajjah waɗannan kuɗin fa?”, ta tambaya idanunta a warwaje saboda mamakin yawansu, Salma da ke kusa da ita ta bugo mata ƙafa “Ke bama son rashin kunya”, kamar Asma’u zata yi kuka ta ce “Toh daga tambaya?”, Hajiya Ummah ta fahimci da gaske bata san ko na miye ba kuɗin, cewa ta yi “Na Sadakinki ne da kuma lefe.”

 

A wannan karon firgicewa ta yi, ta ce “Har haka?”, lokaci ɗaya kuma ta tuna maganar Alhaji Bala da ya ce ta yi goshi. Yaya Asiya da duk suka zagaye kuɗin ita da Salma ta ce “Ƙwarai kuwa, gasu nan 2.5M ne, nan da three days kin zama amaryar Bashir Insha Allahu”, maimakon su ga murna a tattare da ita, sai suka ga saɓanin haka, don kuwa rashewa ta yi a gaban Hajiyarsu, saboda bata bukatar sake jin tabbacin maganar aurenta nan da kwana uku, tunda ta ji daga bakin Bashir.

Langaɓe kai ta yi kafin ta ce “Hajja, me ya sa ba za a ɗaga auren ba, ya yi kusa sosai”, yadda ta ƙarashe maganar tana shirin fasa musu kuka ne ya tabbatar musu da gaske take. Kaf ɗinsu ba wanda bai maida attention ɗinsa kanta ba, hatta Deeni da baya ganin ta sai da ya ce “Ikon Allah.”

“Kamar ya a ɗage auren Asma’u?”, Hajiyar ta tambaye ta, a mairaice ta ce “Toh idan na tafi wa zai riƙa kula da ke da kuma Yaya?”, sosai suka ji maganar har a ransu, wanda ya zama silar watsar da makaman yaƙin ci mata da suke shirin yi, don a ganinsu duk iya shege ne abin nata.

Dafa kafaɗarta Hajiyar ta yi kafin ta bata amsa da “Allah ne zai kula da mu Asma’u, kuma ai ga Farouk a gidan ko?”, kai Asma’u ta girgiza, saboda akwai kulawar da ita kaɗai ce zata basu, ko a wurin girki ai ba Farouk ne ke shiga kitchen ba, bare kuma idan aka dawo wurin kulawa ta musamman da take yi ma mahaifiyarta, idanunta na fitar da ƙwalla ta girgiza kai “Don Allah ni dai a ɗaga, idan ya dawo daga India sai a yi auren”, Lalu da bai iya fasa shigar mata hanci ya ce “Lallai ma yarinya, kin makaro ai, tunda har kika bari aka kawo sadaki”, ta so yaɓa mashi magana, amma sai ta tuna faɗan da aka yi mata ɗazu, dole ta yi shiru da bakinta.

Nasiha Hajiyarsu ta shiga yi mata ta hanyar faɗin “Kin ga shi aure lokaci ne da shi, idan ya zo ba fashi sai an yi, don haka ki yi haƙuri da hukuncin Allah, sannan duk ƴaƴan dangin da muke da su fa, sai a rasa wadda zata kula da ni? Ki kwantar da hankalinki kin ji ƴar auta”, nasiha sosai suka taru suka yi mata, bayan ta goge ƴan ƙwallanta ne ta bar musu ɗakin.

Itama Hajiyar kamar zata yi kuka ta ce “Ban shirya rabuwa da autata ba”, Salma ta ce “Dan Allah ki bar faɗin haka Hajja, ki yi mata addu’a kawai”, ranta ba daɗi ta ce “Toh Allah ya tabbatar da musu da Alkhairi” suka ce “Amiiiin.”

Bikin ya zo musu a makare, don haka suka shiga tsara yadda bikin zai kasance ba tare da an ji kunya ba. Suna nan zaune aka fara kiran sallar Magrib, haramar Sallah suka fara yi, Deeni na fitowa Asma’u ta faɗa mashi Deena ta kira waya tana son magana da shi, ya ce “Ok, zan kira ta”, ransa fal da kewar matarsa ya dogara sandarsa zuwa ɗaki ya yi sallah, yana gamawa ya kira ta, aikuwa ringing biyu ta ɗaga kiran da sallama, amsawa ya yi cikin sanyin murya, sannan ya katse shirun da ta yi ta hanyar tambayar ta “Ya kike”, ta ce “Ai ka san ba ni da lafiya amma kake tambaya ta”, ya fahimci azancinta, amma sai ya basar ya ce “Subhanallah, ta ina zan san baki da lafiya?”, ta ce “Haka ka ce ko?”, bata jira jin amsarsa ba ta tsinke kiran. Har cikin ransa ya ji ba daɗi saboda fushinta uƙuba ne a gare shi, duk da a yanzu ba matarshi ce ba.

Bai yi wata-wata ba ya kira ta, tana ɗagawa ya ji kuka take, sai da ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin ya ce “Deena, mene kuma?”, daga can tana kukan ta ce “Me ya sa kake son wahalar da ni, ka san tunda aka raba ni da kai ba zan sake lafiya ba, amma kake pretending.”

Yadda take kukan ne ya ji bai kyauta mata ba, ko da bai riƙa sauraron ta kullum ba, bai kuma kamata yana nuna bai fahimce halin da take ciki ba, haƙuri ya bata sosai da maganganu masu sanya nutsuwa, ko da ya ji ta tsagaita kukan ne ya ce “Asma’u ta faɗa mani kin kira ta ɗazu”, ta ce “Eh, a lokacin ta ce kana cikin mutane”, ya ce “Hakane, kin san aurenta za a yi nan da kwana uku masu zuwa”, da mamaki ta ce “Aure zata yi?”, ya ce “Eh, bata faɗa maki ba?” Ta ce “Eh”, ya ce “Toh ya haka?”, ta ce “Bata so in sani ko?, tunda yanzu na fita a cikin ku”, kai ya girgiza kamar tana gabanshi “Nope, bana tunanin haka, na san zaku yi maganar” ƙwafa ta yi kafin ta ce “Uhhm, maganar tafiyarku fa?”, ya ce “Saura one week”, a nan yake faɗa mata tare da Asma’u da mijinta zasu tafi, fatan nasara ta yi mashi a wurin aikin, daga bisani ta yi shiru, wanda ke nuna tana son furzar da damuwarta, amma ta kasa, shi ma yana son jaddada mata ƙuncin da yake ciki, amma baya son karyar mata da zuciya, cewa ya yi “Zan kira ki”, ta ce “Yaushe?”, ya ce “Kawai zaki ga kirana a koda wane lokaci “, bata son jayayya da shi, cewa ta yi “Toh Shikenan”, suka yi sallama.

Idan so samu ne, toh yana bauƙatar ya ɗan yi tunani mai cike da kewar matarsa a yanzu, toh amma ba dama, saboda ya fahimci tunanin ke ƙara zaizayar ciwon da ke cikin zuciyarshi. Jiki a sanyaye ya laluba gefensa a kan Carpet tare da ɗaukar carbi ya cigaba da lazimi, bai fito ba sai da aka yi sallar Isha’i, inda ya tarar ƴan uwansa na shirin tafiya.

Bankwana ya yi musu, bayan sun tafi ne ya dawo ɗakin Hajiyarsu, muryar Asma’u ya ji ta shigo ɗakin, “Au, ba tare da Salma zaku koma ba?”, ya tambaye ta, Hajiyar ta ce “Ta ƙiya”, ya ce “Uhmm, da gani kema ba kya so ai”, ya ƙarashe maganar yana dariya, itama Hajiyar dariya ta yi kafin ta ce “Toh ya na iya Deeni, lamari ne ya zo mana kwatsam”, daga gefen gadon da Asma’u ta zauna ta ce “Na ce a ɗaga bikin, kun ce a’a”, ta ƙarashe maganar tana cire hijabin jikinta

Hajjah ta ce “Tunda bikin ƴar baby ne ba, yadda Allah ya tsara mun karɓa, Allah ya tabbatar da Alkhairi kawai”, Deeni ya ce “Amiiiiin.”

Ɗan shiru yayi yana sauraron maganar da Hajiyar ke yi da Asma’u, duk da ba ya iya tantace me suke faɗa saboda a takure yake, katse musu maganar ya yi ta hanyar umurtar Asma’u ta kawo mashi abinci haɗe da magungunansa. Ta shi Asma’u ta yi, kafin ta fice ya ce “Kaɗan fa”, waigowa ta yi “Toh Yaya”, sannan ta fice.

Ƙuri Hajiyar ta yi mashi, tana kallon yadda yake ta ɗan yamutse fuska alamar ko kaɗan bayan jin daɗin zaman, kawai ƙarfin hali ne ya ke, “Ka kira Farouk ya dawo maka da abin da kake so mana”, ta faɗa cike da kulawa, ita kam ba don girma da ciwo sun cimmata ba, da Deeni ya ga gata.

Kai ya ɗan girgiza “A’a, abincin ma ya isa”, ta ce “Toh”, Taliya ce haɗe da miya Asma’u ta kawo mashi, sannan ta ɗauko mashi magani, bai wani ɓata lokaci ba ya ci da ƙyar, don ji yake taliyar ta ma fi maganin ɗaci, yana gamawa ya ce ma Hajiyar ɗaki zai koma, sai da safe suka yi ma juna, sannan Asma’u ta yi mashi jagora ya koma ɗaki ya kwanta.

Ambaton Allah ya yi ta yi daga kwancen, saboda shi kaɗai ne zai cire mashi damuwar rashin matarsa da gudan jinin ɗansa da ƙaddara ta shiga tsakaninsu.

Deena kuwa wani irin ruɗu na daban ta sake samun kanta na matsanancin kishi da kuma kewar mijinta. Gani take kamar idan ya tafi ba zai dawo ba, idan ya dawo kuma toh aure zai yi, saboda tana ji a jikinta zai warke, kuma zai yi aure, tunda abu ne mai wahalar gaske ta sake zama matarshi.

Wata damuwar kuma batun auren Asma’u, ta ji haushi sosai da Asma’u ta ƙi faɗa mata zata yi aure, wanda take ganin don yanzu ita ba family ɗinsu bace “Ba komai”, ta faɗa cikin muryar kuka.

Zuciya ce ta ingiza ta kiran Asma’u don ta yi mata ƙorafi, sai ta ji ta busy, ta kira ya fi a ƙirga amma still busy. A WhatsApp ta aje mata saƙo “Yanzu Asma’u aure zaki yi, shi ne kika ɓoye mani? Ta tabbata yanzu ni ba ƴar family ɗinku bace”, tana sakar mata saƙon ta rufe data ta kwanta. Raihan da ke gabanta ta jawo ta rungume, a ranta tana ta neman sassauci a wurin Allah.

Vibration na wayarta ne ya sa ta buɗe idanunta da suka yi nauyi, wayar ta jawo da hannu domin ganin mai kiran, Asma’u ce ta kira, da yake sun zame mata ƙahon zuciya sai ta ɗaga, maganar farko da Asma’u ta yi ita ce “Haba ƙawata, na rantse da Allah ba da wata manufa na ƙi faɗa maki aurena ba, auren ne ya zo a lokacin da ba wanda ya yi zato”, daga kwancen da Deena take ta ce “Ko kin ɓoye mani ma baki yi laifi ba, tunda ni ba ƴar family ɗinku bace a yanzu”, cike da damuwa Asma’u ta ce “Don Allah ki daina faɗin haka, tun kafin ki san Yaya muke tare, kuma ba abin da zai raba mu Insha Allah, kuma na ga kina cikin damuwa ne, idan na faɗa maki sai in ga kamar ban damu da damuwarki ba”, Deena ta ce “Idan na ji kin yi aure kuma kin san sai na fi jin haushi ko?”, Asma’u ta ce “Hakane, don Allah ki yi haƙuri.”

Tun daga farkon haɗuwarta da Bashir har kawo yau sai da ba Deena labari, Deena ta ce “Duk Yaya ya faɗa mani ɗazu, Kuma in dai Bashir ne kin yi sa’ar miji”, Asma’u ta ce “Da gaske?”, ta ce “Allah kuwa, kin san Dr. Safiyya ƙawar Mommah ce, kin ga kuwa na san shi sosai”, Asma’u ta ce “Gaskiya ne.”

Hira suka sha sosai ta ƙawaye, a nan Deena ta ce “Kin ga da muna tare da Yaya har India sai na je, kin ga a tare zamu da ke”, cike da son kwantar mata da hankali Asma’u ta ce “Hakane, Insha Allah zaku sake aure ke da Yaya, saboda yana sonki” Deena ta ji daɗin wannan maganar, cewa ta yi “Allah ya sa”, ƴar hira suka ɗan ƙara, sannan suka yi sallama.

Kasaƙe ta yi tana ta tunanin yadda Ummanta ta nisanta ta da farincikinta, wanda ko da ta koma gidan Deeni ba ba zata iya mantawa da wannan yanayin marar daɗi ba.

Sai dai abin da Deena bata sani ba shi ne, tunda Aurenta ya rabu, itama Ummanta ta nemi jin daɗi ta rasa a wurin Alhaji Lawan, saboda ko zaman gidan baya yi bare ta sa ran hira mai daɗi a tare da shi, a ranar girkinta ma yana zuwa ne don kawai fita haƙƙi, ta yi fushin itama, a ganinta zai sauko, amma duk a banza, daga ƙarshe ba shiri ta sauko da kanta ƙasa.

Kasa baccin da ta yi ne ya bata damar tura masa saƙo mai cike da ban haƙuri a WhatsApp, saboda baya gari, tana gani ya buɗe saƙon, amma bai yi reply ba, voice call ta yi mashi, yana ɗagawa ya ce “Kin ga bana gari ko? Don haka ki bari na dawo”, bai jira jin me zata ce ba ya katse kiran.

A hankali ta lumshe idanunta tare da kwantar da kanta a bayan gado “Wannan wace irin masifa ce?”, ta yi ma kanta tambayar da amsarta ita ce karantsaye ga rayuwar bayin Allah, sai dai ba lallai ne ta fahimci haka ba. Haka ta kwana cikin baƙincikin fushin da mijinta ke yi da ita, wanda ya zama silar samun sauƙin Deena, don bata da kuzarin da zata iya ci mata fuska a yanzu.

A bangaren su Dr. Safiyya kuwa suna ta rabon invitation card, Umman Deena kuma na cikin manyan ƙawayenta, don haka har gida ta zo da nufin kawo mata gayyata.

Umman Deena ta yi farinciki da auren Bashir, saboda yana girmama ta, “Wai, wace yarinya ce mai sa’a da ta samu Bashir?”, ta tambayi Dr. Safiyya, lokaci ɗaya kuma tana buɗe IV ɗin.

Ko kusa Dr. Safiyya bata san auren Deena ya mutu ba ta ce “Ƙanwar surukinki ce”, cike da rashin fahimta ta ce “Wa kenan?”, ta ce “Asma’u mana ta gidansu Deeni”, wata irin muguwar faɗuwa gabanta ya yi, saboda ta san waye Bashir da irin qualities ɗinsa, hatta ƴarta Deena sai da ta yi ma fatan ta auri Bashir saboda ɗan babban gida ne.

Kasa karanta IV ɗin ta yi saboda zafin da ya turnuƙe mata zuciya, tambaya mai cike da son jin tabbas ta yi ma Dr. Safiyya “Wai da gaske Asma’un ce zata auri Bashir? Ina ma suka haɗu toh.???”

 

 

 

 

 

 

<< Mutuwar Tsaye 28Mutuwar Tsaye 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×