Skip to content
Part 3 of 34 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Cike da son nutsar mata da zuciya Lalu ya ce “Insha Allah ba abin da zai faru Hajiyarmu, ki kwantar da hankalinki, kin ga likita ya ce ki daina saka damuwa a ranki”, sosai maganarsa ta yi tasiri a ranta, musamman da ya ambaci umarnin likita, murya a raunace ta ce “Toh Allah ya sa.”

Shi ma tashi muryar can ciki ya ce “Amiin”, lokaci ɗaya kuma ya tsunduma tunanin ta wace hanya zasu faɗa mata halin da Deeni yake ciki, tunda ya zama dole a faɗa mata a matsayinta na mahaifiyarsu.

Bai yi nisa da fara wannan tunani ba suka ƙaraso daidai gate ɗin gidansu, dole ya dakata da neman mafitar, domin baya son ta sake ankarewa da tashin hankalin da yake ciki.

Cike da ladabi ya buɗe mata motar ta fito, “Sannu” ya faɗa, sakamakon nishin da ya ji ta yi lokacin da ta yunƙura za ta yi tafiya, amsawa ta yi da “Yauwa Faruƙu”, sannan ta cigaba da dogara sandarta har cikin gida

Kamar zai faɗi ya bi bayanta, sakamakon yunwar da ta yaye kaf energy ɗin jikinsa, a tsakar gida ya ci karo da Asma’u, wadda ita ce ƙanwarsa ta biyu, tambayar ta ya yi “Akwai abinci?”, da yake basu ga maciji sai ta yamutse baki “Komai ya ƙare, in banda baƙin shayi” ba tare da ya damu da yadda ta yi maganar a gadarance ba ya sake cewa “Dan Allah toh dafa mani Indomie, yunwa nake ji sosai.”

A tsiwace ta dube shi “Indomie kuma, kaima ka bari a gama girkin rana mana, ni nan a gajiye nake” tana rufe baki ta nufi kitchen, wanda shi ke nuna ba ta da lokacinsa, kuma da alamun idan ya dame ta sai ran kowa ya ɓaci.

Da a ce ta san tsananin tashin hankalin da yake ciki, da ko bai roƙe ta ba zata girka mashi duk abin da yake so. Bayanta ya bi har kitchen ɗin, ko kusa babu alamun fushi a muryarsa ya ce “Yanzu idan mijinki ne ya dawo da matsananciyar yunwa, kuma ya ce ki yi mashi girki haka zaki yi?”

Wani irin kallon tsiwa ta watsa mashi, lokaci ɗaya kuma ta raɓa gefenshi da cup a hannunta tana faɗin “Ai kai ba mijin bane, bare ka kawo mani wani ƙabli da ba’adi.”

Take wannan magana ta harzuƙa shi, cikin tsananin fushi ya bi bayanta har ɗakin Hajiyarsu yana faɗin “Kidahumar banza da wofi”, da yake kanwa bata jiƙa a bakinta sai ta ce “Can ka ga Kidahumar”, aikuwa ya kai mata duka a baki, ba don zafin naman da ta sa wurin kaucewa ba, da sai ya zubar mata da haƙora.

Hajiyarsu da tun a waje take jiyo su ta ce “Idan kuka ƙarasa kashe ni kun huta ai”, saboda babu ranar da zata zo basu yi faɗa ba, kuma laifin duk na Asma’u ne, don kaf a gidansu babu rasa kunya sai ita, shi kuma Lalu baya ɗaukar raini ko kaɗan.

Kamar zai yi kuka ya dubi Hajiyarsu da ke zaune a gefen gado ya ce “Wannan yarinyar bata da kunya ko kaɗan”, lokaci ɗaya kuma hannunsa na nuni da Asma’u da ke fake a gefen hajiyarsu. Baki Asma’u ta murguɗa “Eh ɗin bani da kunyar”, aikuwa rufe bakin tsiwar ke da wuya zazzafan mari ya sauka a fuskarta.

Zafin marin na ratsa fuskar ta kurma ihu, korar ta Hajiyarsu ta yi a waje, sannan ta ce idan bata rufe masu baki ba Lalu ɗin ya ƙara mata, da yake ta san tsaf zai aika, don dole ta tsagaita kukan, kamar wadda zata haɗiye zuciya ta riƙa shesshekar kuka.

Ba tare da tausayin ta ba Hajiyarsu ta kira ta, tana zuwa ta ce “Maza ki je ki girka mashi abin da yake so”, hannunta dafe da kumci ta ce “Hajiya Mari na fa ya yi”, a ƙufule Hajiyar ta ce “Ko uban me ya yi maki sai kin girka mashi, shashashar banza marar ɗa’a”, da yake tsoron fushin Hajiyar take bata sake magana ba ta fito ɗakin tana kuka.

Duban Lalu Hajiyar ta yi “Dan Allah ku koyi haƙuri Faruƙu”, cike da tausayin mahaifiyarsa ya ce “Hajiya kin san halin yarinyar can fa”, ta ce “Na sani, ka daina biye mata kawai, lokaci zai zo da ko an ce ta yi maka rashin kunya ba zata yi ba”, cikin ruwan sanyi ta yi mashi faɗa, tare da ankarar da shi rayuwar ma baki ɗaya ƴar haƙuri ce, cike da jin daɗi ya bata haƙuri.

Asma’u kuwa na gama girkin ta zo ta dungurar da plate ɗin a gaban shi, ta juya zata fice ne Hajiyar ta dakatar da ita da faɗin “Yanzu idan mijinki ne haka zaki kawo mashi abincin?”, Asma’u ta tsani wannan misalin da ake buga mata mai taken “Idan mijinki ne.”

Kamar zata yi wani kukan ta ce “Wai me ya sa kuke cewa idan mijina ne?”, Hajiyar ta ce “Saboda mu nuna maki illar wannan banzan halin naki, kuma duk rashin kunyar da kike yi anan gidan, toh ki sani irin ta ce zaki yi a gidan aurenki, tunda doka daga gida take farawa, kuma ina mai tabbatar maki da ba kowane namiji ne zai iya ɗaukar halinki ba.”

Sosai maganar ta taɓa mata zuciya, ƙwalla ne suka cika mata idanu, wanda kuma hakan bai hana Hajiyarsu sanya ta dole ta ba Lalu haƙuri ba. Shi kuwa wannan haƙurin da shi da babu duk ɗaya, don kuwa uƙubar da ke ranshi ta fi gaban wannan.

Tamkar magani ya ke jin indomie ɗin, cunkusa ta ya riƙa yi haɗe da ruwan shayin, duk don ya sama ma jikinsa energy. Yana gamawa ya ce ma Hajiyarsu zai kai ma Deeni motarsa, Allah ya kiyaye ta yi mashi. Bayan fitar sa ne Hajiyata ta tusa Asma’u gaba da nasiha, inda ta nuna mata rashin kunya bata da wani alfanu, don haka ta bi duk wani na gaba da ita sau da ƙafa, don tun a yanzu yayyenta su ne iyayenta, saboda babu abin da basa yi mata. 

Deeni kuwa tuni sun koma bedroom, saboda falon ya cika sanyi, magunguna Deena ta taimaka mashi ya yi amfani da su, sannan ta dawo gefensa a kan gado ta zauna. Yadda take komai ba tare da kuzari ne ba ya ankarar da shi yunwa take ji, tambayar ta ya yi “Ki yi breakfast kuwa?”, Kai ta girgiza “A’a”, cike da tausayin ta ya ce “Saboda me?”, amsa ta ba shi da “Bana jin yunwa”, da lalube ya shafo cikinta “Toh baby fa, shi ma baya ji?”, Ya ɓullo mata ta haka ne saboda baya son ya tursasa mata.

Tabbas tana jin yunwar daga ita har ɗan cikinta, sai dai ba zata iya ko da shan ruwa ba saboda tausayin mijinta, hannunta a kan na Deeni ta ce “Nima ban sani ba ko yana ji”, yadda ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka ne ya ƙara mashi tausayin ta, da zuciya ya ke kallon ta a gefensa, maido da ita ya yi akan jikinsa ya rungume, cikin muryar lallashi ya ce “Baby na jin yunwa, ki taima mashi ya ci abinci kin ji.”

Kasa magana ta yi, sai ma ta kwantar da kanta a ƙirjinsa tana fitar da ƙwalla, haɓarsa ya ɗaura a kanta ya yi shiru shi ma, a ransa kuma yana kallon wannan ƙaddara tamkar a mafarki, domin kuwa ga idanunsa buɗe, amma basa iya tantance fari da baƙi, da zuciya ne kaɗai yake ƙaddara abin da ke gabansa. “Rayuwa kenan!”, Ya faɗa cikin sautin da bai san ya fito ba, saboda ya rufe, kuma ya buɗe idanunsa, amma ba wani chanji.

“Allah ga bawanka mai raunin gaske”, ya faɗa cike da ƙasƙantar da kai a wurin Allah, wasu ƙwalla masu zafi ne suka malalo a kumcinsa, Deena na cikin tunanin yadda zata yi da mahaifiyarta ne ta ji ɗumin hawayen a kanta.

Da hanzari ta ɗago ta dube shi, sharkaf ta ga fuskar sa da hawaye, zuciyarta a kiɗime ta sa hannu ta goge mashi, lokaci ɗaya kuma tana faɗin “Allah zai baka lafiya mijina.”, Ƙanƙame juna suka yi suna kuka mai cike da tausayin kansu, domin kuwa suna cikin tsaka mai wuyar gaske.

Suna cikin wannan yanayin ne wayar Deeni ta fara ruri, a daidai inda sautin yake Deeni ya kai hannunsa tare da ɗaukar wayar “Waye?” ya faɗa yana nuna ma Deena wayar, karɓa ta yi tana faɗin “Lalu ne”, ɗaga kiran ta yi, daga can ya tabbatar mata da yana waje.

Hular kanta ta cire ta goge ma Deeni fuskar sa, sannan itama ta goge tata, saboda bata son Lalu ya fahimci kuka suka yi. A hankali ta zame jikinta daga jikin Deeni ta sauka.

Sai da ta sanya hijab, sannan ta fita ta buɗe ma Lalu, da mamaki sai ta gan shi tare da Hajiya Umma, wadda ita ce babbar yayarsu Deeni. Ashe gidanta Lalu ya biya ya faɗa masu halin da ɗan’uwansu yake ciki, shi ne ta shirya suka taho tare.

“Sannu da zuwa Hajiya”, Deena ta faɗa tana son danne kukan dake shirin ƙwace mata, amsawa Hajiya Umma ta yi da “Yauwa Deena”, lokaci ɗaya kuma ta jawo Deena a jikinta, kukan dake cikin ran Deena ne ya fito, cike da lallashi Hajiya Umma ta ce “Ki yi haƙuri kin ji, ina Deenin?”, Lalu ne ya amsa mata da “Yana bedroom”, tura ƙofar ya yi sannan ya bi bayansu suka nufi bedroom.

Kamar daga sama Deeni ya ji muryar Hajiya Umma, da hanzari ya ɗago kansa tare da amsa mata, ita kuwa hankali tashe ta ƙaraso cikin ɗakin, gefen gado ta zauna tana kallon ɗan’uwanta cike tashin hankali, lokaci ɗaya kuma bakinta na sallallami, don yadda ta ga Deeni ya shallake tunaninta.

Deena da Lalu kuwa tsaye suka yi suna kallon kalar na ta firgicin, don kuwa kuka riris ta riƙa yi tana faɗin “Wace irin ƙaddara ce wannan ta same ka Deeni?”, Lalu ya ce “Ke dai bari Hajiya, masifu daga wannan sai wannan.”

Toh su kenan sun shiga wannan tashin hankali, ya batun mahaifiyarsu wadda Allah da Manzonsa ne kaɗai suka fi ta son Deeni? Haƙiƙa idan ta ji wannan labari Allah ne kaɗai ya san ya zata yi.

Lallashin juna suka shiga yi, don ba wanda bai yi kuka ba. Kan kace me kuma Hajiya Umma ta sanar ma duka ƴan’uwansu, in banda Asma’u da ke can gidansu.

Tamkar gidan makoki suka maida gidan, saboda ƙaunar da suke ma Deeni ta daban ce, Deeni ne fitilar da ta haske gidansu, gashi kuma ya samu tangarɗar da basu san ya zasu yi ba.

Babban tashin hankalinsu ɗaya ne, wato batun mahaifiyarsu, sun rasa ma ta ina zasu faɗa mata, wasu suka kawo shawarar a ɗauko ta a kawo ta gidan Deeni, Yaya Asiya, wadda ita ke bi na Deeni ta ce “Ai ana cewa za a ɗauko ta zata gane wani abu ya faru”, Salma da tun da suka fara maganar ta ce “Toh ya zamu yi yanzu?”, Yaya Asiya ta ce “Kawai Deeni ya iske ta har gida, ina ganin hakan shi ne mafita.”

Nazarin shawarar Yaya Asiya suka yi, daga ƙarshe suka amince da ita, sannan suka tsara gobe idan mai duka ya kai mu, zasu haɗu can gidan, inda Lalu kuma zai zo ya tafi da Deeni.

Duk irin kulawar da ta dace sai da ƴan’uwan Deeni suka nuna mashi, Deena ma ta sha lallashi a wurinsu har sai da ta ɗan saki jiki. Batun aikin gidan ma ɗauke mata suka yi saboda samun kwanciyar hankalnta.

Ba su suka bar gidan ba sai ƙarfe goman dare, inda Lalu ya kwashe su a motar Yaya Asiya suka tafi.

Deena kuwa sosai ta yi kewar jikin mijinta, saboda mutane, tafiyarsu ke da wuya ta taimaka ma Deeni suka yi shirin bacci. A kan jikinsa ta zauna tare kwantowa a ƙirjinsa a lokacin da suka dawo kan gadon, a hankali ya rungumo ta shi ma.

Tambayar dake ta yi masa yawo a rai ya yi mata “Deena, yanzu a ce ba zan warke ba, zaki iya rayuwa da ni a haka?”, Ƙanƙame shi ta yi tana faɗin “Idan ka fi haka ma zan iya rayuwa da kai mijina, kuma ai zaka warke ko?”, Ya ce “Insha Allahu, amma sai nake ganin akwai challenges yin rayuwa da ni a haka.”

Tabbas ta san akwai challenges da yawa, amma bata son a fito da su fili, saboda ɓacin rai ne, cike da son kawar da maganar ta ce “Yaya, ni fa ruhinka nake so ba gangar jiki ba, don haka duk wani challenge da zan fuskanta na yi alkawarin haƙuri da shi, madamar ba zai raba ni da kai ba.”

Sosai ya ji daɗin maganar ta, sassauta murya ya yi kafin ya sake tambayar ta “Umma fa, kin faɗa mata?”, Kai ta girgiza “A’a”, ya ce “Saboda me?”, Ta ce “Tsoro nake ji”, sanin dalilin tsoron ya sa shi yin shiru na wuccin gadi, daga bisani ya ce “Ki daina tsoro Deena, babu mai yi sai Allah.”

Suna cikin wannan tattaunawa ne neighbour ɗin su ta kira Deena, wadda ita ce babbar Aminiyarta a estate ɗin, bayan Deena ta ɗaga kiran ne daga can ta ce “Ƙawa, ko kin haihu ne ba a faɗa mana ba”, kasantuwar sun lura da kaikawon jama’a a gidan Deeni.

Deena na kallon bakin Deeni da ke mata nuni da ta faɗa mata gaskiya ta ce “Haba, ya za a yi in haihu baki sani ba, Yaya ne baya da lafiya”, daga can ta ce “Subhallah, Allah ya bashi lafiya”, Deena ta ce “Amiin”, ƴan maganganu suka ƙara daga bisani suka yi sallama.

Kwanciya suka yi, saboda sun tsara dare na rabawa zasu ta shi su cigaba da kai kukansu a wurin Rabbil Izzati.

Washe gari kuwa Khamis (Na littafin Kishiyar Katsina) ya zo tun da farar safiya kasancewar sun zama tamkar ƴan uwa, saboda mahaifansu abokan juna ne tun na yarinta. 

Da kansa ya ɗauki Deeni suka je wurin wani optician domin ya haɗa musu gilashi, sun yi sa’a kuwa an haɗa musu mai kyau, Deeni na gwadawa ya ji idanunsa sun fara nauyi, inda kuma optician ɗin ya tabbatar ma Deeni akwai alamun sauƙi kenan, tunda har idanun zasu iya karɓar sabon abu.

A hanyar dawowarsu ne Khamis ya dubi Deeni, cike da tausayinsa ya ce “Deeni, ya batun aikin ka, sun kuwa san halin da kake ciki?”, Sai da Deeni ya ɗan nisa kafin daga bisani ya ce “Eh sun san bani da lafiya, amma basu san me ke damuna ba.”, Idanun Khamis na a kan tuƙin da yake ya ce “Yana da kyau su sani, na san zasu baka permission har ka samu lafiya”, Deeni da jikinsa ya yi sanyi ya ce Khamis, idan ban warke ba fa, ya kake ganin makomar aikin nawa?”, Cike da tawakkali Khamis ya amsa mashi da “Makomar aikinka na wurin Allah, shi da ya ɗaura maka, shi ne kuma zai baka mafita, sannan ka da ka yanke tsammanin samun lafiya”, jinjina kai Deeni ya yi “Insha Allah, Allah ya sa mu dace”, Khamis ya ce “Amiin.”

Yadda suka tsara sanar ma Hajiyarsu ne Deeni ya faɗa ma Khamis, sosai ya gamsu da tsarin, don kuwa gwara Deeni ya iske ta gida, a kan ita ta iske shi. Maganganu masu kwantar da hankali Khamis ya cigaba da faɗa ma Deeni, sannan ya tabbatar mashi da zasu taya shi neman lafiyarshi da ƙarfinsu da kuma dukiyarsu har Allah ya sa a dace, Deeni ya ji daɗin wannan albishir, godiya mai yawa ya yi ma Khamis lokacin da ya maido shi gida. Har cikin gidan Khamis ya shigo da Deeni sannan ya tafi.

Deena kuwa hannun mijinta ta kama suka nufi bedroom, sosai glass ɗin ya fito mata da kyawunsa, gabansa ta tsaya gami da dafa kafaɗunsa ta ce “Specs ɗin ya maka kyau mijina”, sai da ya zagayo da hannayensa a bayanta kafin ya ce “Da gaske?”, ta ce “Allah kuwa, ko da idonka ya warke zaka cigaba da sanya shi ko?”, murmushin yaƙe ya yi sannan ya ce “Allah ya sa na warke”, ta ce “Amiin.”

Banɗaki ta raka shi ya sake yin wanka, suna fitowa ta taimaka mashi ya zauna a gefen gado, man shafawa ta ɗauko ta fara shafa mashi a ƙafa, ɗan janye ƙafarsa ya yi ya ce “Bari na shafa, je ki shirya, ke ma”, maƙe kafaɗa ta yi duk da baya ganin ta ta ce “Kai fa babyna ne, ka bari in shafa maka mana.”

Bai sake musu ba ya sakar mata da jikinsa, tsaf kuwa shirya mijinta cikin shiga ta manyan kaya, sannan itama ta shirya tsaf cikin doguwar rigar atamfa mai kyau. waya suka yi ma Lalu ya zo suka tafi gidansu Deeeni…

<< Mutuwar Tsaye 2Mutuwar Tsaye 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×