Skip to content
Part 30 of 31 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Ba tare da fahimtar manufar bin ƙwaƙawaf ɗin Umman Deena ba Dr. Safiyya ta ce “A gidansu Asma’un, da yake tare muka je da shi a kan batun tafiyar Deeni India, toh anan ya ganta, ya kuma matsa a ɗaura auren su tafi tare da matarshi, saboda da shi za a tafi Indira, kuma zai daɗe can.”

Hannun Umman Deena riƙe da haɓa ta ce “Ikon Allah, Asma’un ce har a India?”, Dr. Safiyya ta ce “Aikuwa dai, kin san rabo”, baki Umman Deena taɓe sakamakon hassada gami da tsanar family ɗinsu Deeni da ke ta azalzalar ma zuciyata, cewa ta yi “Hu’um! Da yake ni na ƙwace ƴata a hannunsu, shi ya sa bamu san komai ba game da auren”, ba tare da fahimtar inda ta dosa ba Dr. Safiyya ta tambaye ta “Kamar ya kin ƙwace ƴarki?”, ta ce “Na raba auren mana Dr.”, take walwalar dake shimfiɗe a fuskar Dr. Safiyya ta gushe, cikin tsananin rashin jin daɗi ta ce “Haba Hajiya Hadiza, me ke damunki ne don Allah”, Umman Deena ta ce “Me fa? Kawai ba zan lamunci a bautar mani ƴa ba, alhalin su nasu ƴaƴan suna can suna jin daɗi”, Dr. Safiyya ta ce “Kamar ya bauta? Akwai kalar jin daɗin da Deena bata ji a gidan aurenta ne? Gaskiya ban ji daɗi ba”, ba tare tunanin ta yi kuskure ba ta ce “Ban ce Deena bata jin daɗi ba, kawai lalaurar nan da ta same shi ne bana son su ɗaura mata jidalin kula da shi”, Kai Dr. Safiyya ta girgiza kafin ta ce “Yanzu ba asibiti zai je ba, ai da kin bari ya dawo tukuna”, Umman Deena ta ce “Koma dai yane ni dai na ƙwace ƴata”, Dr. Safiyya ta fahimci Umman Deena ta yi nisan da bata jin kira, cikin sanyin jiki ta ce “Allah sa haka ya fi Alkhairi”, Umman Deena ta ce “Amiiiiin.”

Kafin a zo maganar Deeni sosai suke hira, amma sai ga shi sun fara yin jugum-jugum, nan ne kuma Umman Deena ta so jawo hirar, inda ta buɗe Card ɗin ta karanta tare da faɗin “Allah ya sa Alkhairi”, Dr. Safiyya ta ce “Amiiiiin.”

Tambayar Umman Deena ta yi “Ina Deena?”, ta ce “Tana ɗakinta”, yunƙurawa ta yi zata tashi “Bari a kira ta ku gaisa”, Dr. Safiyya ta san ko shakka babu Deena na cikin damuwa, kuma da ta ganta akwai yiwuwar har kuka ta yi, cewa ta yi “A’a ƙyale ta”, Umman Deena dama bata son a ga yadda Deena rame, ta san dole sai an zage ta, duk da Dr. Safiyya bata iya ƴan gulmace-gulmace ba.

Hirar duk ta kasance ba daɗi, Dr. Safiyya ta saɓi jakarta “Kin ga tafiya zan yi”, Umman Deena ta ce “Tun yanzu?”, ta ce “Kin ga hidimar da yawa ai”, ta ce “Haka ne”, har bakin ƙofa ta raka ta.

Daki Umman Deena ta dawo ta ɗauki IV ɗin da ta bari kan kujera, sama ta haura, zuciyarta cike da ƙunar da za a iya danganta ta da hassada ta nufi ɗakin Deena, murɗa handle ɗin ta yi ta shiga, lokaci ɗaya bakinta na faɗin “Sannun ku ƴan ɗaka, kin ƙumshe ke da ɗanki, saboda an hana ku abin da kuke so.”

Tun farkon shigowarta gaban Deena ya soma faɗuwa, aje wayar da ke hannunta ta yi akan filon dake gefenta tana duban mahaifiyarta da ta ƙaraso gabanta ta tsaya, bata san me zata ce mata ba, mafarin ta yi shiru tana sauraron da me ta zo.

“Karɓi ki gani da idonki”, Ta miƙa ma Deena IV ɗin, hannun Deena na ƴar kyarmar tsoro ta karɓa, wasancewa ta yi ta tambayi Ummanta “IV ɗin waye”, Amsa ta bata da “Ki karanta mana”, lokaci ɗaya kuma tana jin takaicin yadda Deena ta zuƙe saboda damuwa.

A hankali Deena ta warware, tare da karantawa kamar yadda Ummanta ta umurce ta, bayan ta gama ne ta ɗago ta dube ta “Na gani, katin gayyar bikin Asma’u ne”, Ummanta ta ce “Ita da wa?”, Deena ta ce “Da Bashir”, Kai Ummanta ta jinjina, zama ta yi a kan stool don maganar da ke bakinta mai yawa ce, kuma babban fatanta shi ne Deena ta fahimce ta.

Domin janye ra’ayin Deena ne ta karɓi Raihan da tun tana tsaye ya yi mata ƙuri. Ɗan wasa ta yi mashi, hakan kuwa ya ma Deena daɗi, don rabon da Raihan ya zo hannunta har ta mance.

“Kin san dalilin da ya sa na kawo maki IV ɗinnan?”, kai Deena ta girgiza “A’a”, don kuwa har a ranta bata san manufar hakan ba, tunda yanzu babu sauran alaƙa tsakanin su da su Deeni bare su gayyace ta.

“Don ki ga wane ne Asma’u zata aura”, faɗar Umman Deena, har yanzu dai Deena bata fahimce ta ba, duk da ta san Bashir ne Asma’u zata aura.

Kawai dai ta yi ƙarfin hali ne ta ce “Kamar Bashir ne zata aura ko?”, Umman Deena ta ce “Shi ne, kin ga sun zaɓa ma ƴarsu miji nagartacce ɗan Usuli, amma shi ne suke son kashe ki da yi ma ɗansu jagora a cikin gida. Dududu da fara neman auren ba a yi wata ɗaya ba”, yanzu Deena ta fahimci inda maganar ta dosa, shiru ta yi, don kuwa bata da abin faɗa, kuma har a ranta bata ga inda Bashir ya fi Deeni ba, idan kuma har akwai toh sai dai idan kuɗi aka fi shi, kuma wannan kuɗin ba su ne a gabanta ba. Ita ta soyayyar mijinta take.

Haka Ummanta ta cigaba da zuba a kan son cusa mata tsanar Deeni da ahalinsa, amma ba wanda ta fahimta bare ta iya ɗaukarsa. Sai dai Deena ta riƙa pretending ta hanyar nuna mata ta fahimce ta, daɗin da ta ji ne ya sa ta umurtar Deena ta fito domin shirya ma Alhaji Lawan girki na musamman, kasantuwar yau zai dawo.

Tare suka fita a ɗakin, inda Umman Deena ke saɓe da Raihan tana yi mashi wasa, sai da suka je kitchen ne ta miƙa ma ɗaya daga cikin ƴan aikinta shi “Karɓi wannan ɗan ƙwaƙur ɗin, aiki zamu yi” ta faɗa tana dariya

Salmai ta ce “Hajiya ai da ya taya ku aikin”, Umman Deena ta ce “Ya dai hana mu aiki, kina gani sai ƙura mana ido yake, ta ƙarashe maganar haɗe da lakatar kumcinsa, shi kuwa kamar mai jira, sai ya wangale baki yana dariya.

Salmai ta kuma “Hajiya dariya yake maki fa”, ta ce “Na gani Salmai”, duƙar da fuskarta ta yi tana yi mashi wasa, shi kuwa sai dariya take.

Kowace uwa da ɗanta ake haƙa mata farko, aikuwa Deena bata san lokacin da ta sake jikinta ba. Salmai na goya Raihan suka cigaba da aikinsu. Girki mai rai da lafiya suka shirya, suna gamawa suka haura sama domin kimtsa jikinsu.

Alhaji Lawan bai dawo ba sai gab da magriba. Ya yi mamakin yadda ya ga Deena sake a falon, duk da muguwar ramar da ta yi.

Ita da kanta ta karɓi jakar, bakinta na faɗin “Daddy sannu da zuwa”, cike da tausayinta ya dafa mata kai “Yauwa Deena, na same ku lafiya”, ta ce “Lafiya lau Daddy”, tambayar ta ya sake yi “Abokina fa?”, ta ce “Yana wurin Salmai”, ya ce “Madallah.”

Hamshaƙiya kuwa tana gefe sai murmushi take, sosai ta yi kewar mijinta, don haka ba ƙaramin daɗi ta ji a ranta ba da ta ga babu alamun fushi a fuskarsa ba. Shi ma ya yi kewar ta sosai, wani irin kyau ya ga ta ƙara masa, bai san lokacin da ya mayar mata da murmushi ba tare da raɓawa gefenta ya wuce, karɓar jakar ta yi a hannun Deena, sannan ta bi bayansa.

Deena ta lura da irin farincikin da mahaifiyarta ta shiga sakamakon dawowar mijinta, hakan ne ya fama mata ciwon da ke ta tsuma a ranta na kewar Deeni, ranta ba daɗi ta haura sama da nufin yin Sallah.

Tsaye ta same shi a gaban gado yana cire wristwatch ɗin hannunsa, da hanzari ta ƙarasa cire masa, tare da ajiye ta a bedside locker, babbar rigar da ke jikinsa ta cire mashi tare da ajiye ta a kan gadon. Shi kuwa salo da kyawu gami da ƙamshin da ke fita a jikinta ne ya ƙarasa tafiya da shi. Tabbas idan kana son ka huce bisa ga laifin da matarka ta yi maka, toh ka ɗan yi nisa da ita na wasu ƴan kwanaki, da zaran ka dawo, in dai matar ta amsa sunanta mace, toh zata zo maka salon da zaka yafe mata, kamar dai yadda Umman Deena ta shiga mantar da Alhaji Lawan laifin da ta yi mashi ta hanyar hugging ɗinsa ta yi shiru tana faɗin “I miss You”, a hankali ya ɗaura hannayensa a gadon bayanta yana faɗin “Miss you too tawan”, basu yadda sun jima a haka ba saboda magrib ta kusa.

Banɗaki ya shiga ya yi wanka, yana fitowa ya taras da jallabiya marar nauyi ta ajiye mashi. Sanyawa ya yi, sannan ya fice masallaci ya yi sallah, bai shigo gidan ba sai da aka yi Isha’i. Abincin da aka shirya mashi ya ci ya ƙoshi, sannan ya koma ɗakinshi, saboda a yanzu yana buƙatar ganin matarsa a kusa da shi. Umman Deena kuwa haka take so. Ɗaki ta koma ta canja shiga, sannan ta dawo ɗakinshi. Zaune ya ke a kan kujera tare da ɗan kwantar da bayansa ya lumshe ido, ita kuwa a gabansa ta durƙusa tare da shimfiɗa tafukanta a kan cinyoyinsa, sanyin da ya ratsa shi ne ya sa shi buɗe idanun, ɗagowa ya yi gami da saita zamansa yana dubanta, yadda ta marairaice ne ya ƙara mashi kewarta a ransa, ya san maganar da ke ranta, amma sai ya basar ya ce “Menene?”,

Cike da ƙanƙan da kai ta ce “Yafiyarka nake nema Alhaji, tunda ka fara fushi da ni na nemi kwanciyar hankali na rasa, don Allah ka yafe mani”, sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ɗago da kafaɗunta ta zauna gefensa.

Fuskantar juna suka yi kafin ya ce “A kan me zan yi fushi da ke, bayan mafita ce kika ganin kin nema ma ƴarki?”, Kawai hanyar da kika biyo ce baki kyauta ba, kuma in don ni ne toh ya wuce”, ruƙo hannunsa ta yi sannan ta ce “Alhaji, ban raba Deena da mijinta ba don son zuciyata ba, sai don kawai na nema mata mafita na yi haka”, tambayar ta ya yi “Wace mafita?”, ta ce “Mun yi karatu da wani mai lalurar gani, da mu da shi baka ga irin wahalar da muke sha ba wurin kula da shi, duk inda zamu je ba za a rasa wanda zai yi masa jagora a cikinmu ba, tun muna yi cikin jin daɗi, har muka sare, zan iya ce maka mu ke masa karatun ma, toh shi ne nake ganin kamar irin wannan yanayin ne Deena zata shiga.” Tabbas ya karɓi uzurinta a yanzu, shi kanshi sun taɓa hidima da wani wanda baya gani, kuma ya san ya wahalar take.

“Allah ya kyauta, ya sa kuma haka ya fiye musu Alkhairi”, ta ce “Amiiiin”, shiryawar da suka yi ne ya bata damar cewa “Yanzu ka yafe mani?”, kai ya ɗaga haɗe da ruƙo hannayenta “Na yafe maki, amma da sharaɗin sai kin daina kyarar mani ƴa”, ta ce “Na daina Alhaji, ba zan ƙara ba”, ya ce “Yauwa tawan.” Sosai suka shirya, inda suka dasa hira mai cike da jin daɗi, daga bisani suka yi shirin bacci.

Deena kuwa ta rasa me ya sa damuwar Deeni ta zame mata sabuwa a yau, tun bayan da ta koma ɗakinta take kuka, saboda ta kira Deeni ya ƙi amsa kiranta, Lalu ma da ta kira ya ce baya gida, bai kuma bata courage ɗin ta sake kiranshi ba idan ya koma gidan, hakan ya sa ta rungume ɗanta ta yi lamo a kan gado, har bacci marar daɗin gaske ya zo ɗauke ta.

Tuni dama alarm ɗin wayarta a saite yake, ukun dare na bugawa ta zame jikinta daga na ɗanta ta shiga banɗaki ta yi alwala, tana fitowa ta kabbara sallah, inda a cikin sujudar ta kai ma Allah kukanta akan ya sassauta mata wannan damuwar.

Bayan ta gama sallar ne ta ɗauki wayarta, data ta kunna tare da shiga WhatsApp, status ɗin mutane ta fara view, har ta zo wurin na Rahila, kasantuwar sun yi exchange na contacts ɗin juna.

Invitation card na bikin Asma’u ta saka vedio da kuma Image, jikin caption ɗin ta rubuta “Can’t wait, Allah ya sa Alkhairi ƙanwata.”

Sosai abin ya sosa ran Deena, “Wato har wannan tsintacciyar ta fi ni gata ko? Ba damuwa”, ta faɗa cike da ƙuluwa, don daga family ɗin su Deeni ba wanda ya turo mata invitation, a ganinta duk da ba zata zo ba, amma ta canci su faɗa mata.

Wannan takaicin ne ya sa ta rufe data tare da ficewa WhatsApp ɗin, a kan gado ta aje wayar, sannan ta ɗan kifa kanta still a kan gadon daga zaunen da take a kan Carpet. “Haƙiƙa ina cikin jarabawa, ya Ubangiji ka bani mafita da daga gare ka ba don halina ba”, ta faɗa tare da fashewa da kuka.

A yadda ƙunci ya mamaye ta, ji ta riƙa yi dama ba a haife ta a duniyar ba, bare ta kawo wannan lokacin mai cike da baƙinciki, wanda kuma bata san yaushe ne zata fita ba. Sai dai ta manta da bayin da Allah yake so ne yake jarabta, kuma idan suka yi haƙuri mai cike da tsoron Allah, toh zasu yi farinciki a nan gaba.

Vibration ɗin da wayarta ya shiga yi ne ya sa ta ɗago kanta, cikin ranta tana faɗin “Waye ke kirana haka?”, number Deeni da ta gani ce ta bata amsar tambayarta.

“Yaya?”, ta faɗa a ranta kafin ta ɗaga kiran, murya a dakushe ta yi mashi sallama, daga can ya amsa shi ma a cikin raunin murya. Shiru ne ya ɗaga ratsa su, saboda tamkar strangers haka suka koma ma juna, cewa ya yi “Deedee”, amsawa ta yi “Na’am”, ya ce “Ina cikin matsananciyar kewarki”, sosai ta yarda da maganar shi, amma haushin ƙin amsa kiranta da yake ta ce “Kuma shi ne kake abandoning call ɗina? Ni ban yarda kana missing ɗina ba”, tana jin lokacin da ya sauke numfashi kafin ya ce “Ki gafarce ni, bana son saka ki a damuwa ne shi ya sa”, maganar kwanaki ta sake maimaita mashi, cewar “Har akwai sauran damuwar da ta rage wadda ban shiga ba? Mutuwa kaɗai ta rage ban yi ba Yaya, kuma ina fatan Allah ya ɗauki raina in huta”, da kuka ta ƙarashe maganar, wanda ya yi matuƙar ɗaga hankalin Deeni, lallashinta ya shiga yi, haɗe ta jaddada mata wannan ne ya sa baya amsa kiranta idan ta kira.

Bayan ta tsagaita kukan ne ya cigaba da faɗin “Ki yi haƙuri, kuma da ina da iko ba abin da zai hanani maida ke, toh bana son fitina ne shi ya sa, amma na san lokaci zai zo da zaki sake zama matata”, cike da zaƙuwa ta ce “Allah ya sa, ina matuƙar kewarka mijina”, amsa ya bata da “Ni ma ina kewarki Deedee.” Bai yadda ya kira ta da matarsa ba saboda gudun shiga hurumin Shari’a, tunda yanzu babu tsarin maidata a gabansa, kawai dai yana fatan haka ne.

Maganar bikin Asma’u ta yi mashi, ya ce “Saura kwana uku ai”, ta ce “Na gani a Status ɗin Rahila”, cewa ya yi “Toh fa, ƙila Asma’un ta tura mata”, ta ce “Uhmm! Ni dai ai ba wanda ya gayyace ni”, ya ce “Zaki zo ne?”, ta ce “Ko ban zo ba ai ɗana zai zo bikin Auntinsa ko?”, ya ce “Haka ne, toh ina gayyatar ɗana, kuma na fi son ya zo tare da mamansa”, dariya suka yi, don sun san abin ba mai yiyuwa ne ba.

Hira mai cike da ƙauna suka sha, a nan Deeni ya ƙara kwantar mata da hankali, cewar shi ba zai sake iya aure

ba, ita kaɗai ce zaɓinsa, tunda kuma ya rasa ta toh shikenan.!

 

 

 

<< Mutuwar Tsaye 27Mutuwar Tsaye 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×