Skip to content
Part 31 of 34 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

“To idan ka warke fa? Shi ma ɗin ba zaka yi aure ba?”, Deena ta tambaye shi cike da son jin ƙwaƙwaf, ya ce “Idan na warke ke ce matata ai, na san ƙila Mommah ta dawo mani da ke. Idan kuma ban warke ba na gama aure har abada”, ya bata wannan amsa ne don ya kwantar mata da hankali.

Baki ta taɓe “Uhmm, wata na kawo maka harin zaka ce haka?”, ya ce “Waye ke kawo mani hari?”, ta ce “Rahila fa”, dariya ya yi tare da faɗin “Ita ta faɗa maki?”, Ta ce “Na ga alama mana”, ya ce “Toh shikenan, Ni dai ban gani ba”, ta ce “Zaka gani ai”, ya ce “Mu zuba mu gani”, ta ce “Au haka ka ce?”, ya ce “Toh ya kike son na ce? Ke ce fa kika kawo maganar”, shiru ta yi ba tare da ta ce komai ba.

Ya fahimci jikinta ya yi sanyi, musamman da irin amsar da ya bata, mafarin ya buɗe mata abin da ya fahimta dangane da Rahila ta hanyar faɗin “Kin san me?”, ta ce “Sai ka faɗa”, ya ce “Na fahimci abubuwa da yawa dangane da Rahila, amma ko kusa ba ita ne a gabana ba, daga ke an gama Insha Allah Deena.”

Sosai maganar da sanya ma Deena nutsuwa a ranta, ita dama tashin hankalinta kada Rahila ta yi mata kutse a zuciyar miji, cewa ta yi “Ni ma ba zan yi aure ba Yaya”, ya ce “Kada ki sake faɗar haka, ki yi addu’a kin ji tawan”, ta ce “Insha Allahu Yaya.”

Ya ji daɗin yadda bata yi mashi gardama ba, magana mai daɗi suka yi ma juna musaya, daga bisani suka yi sallama.

Wannan kira da Deeni ya yi mata ba ƙaramin daɗi ya yi ma Deena ba, cike da farinciki ta yi addu’a akan Allah ya dawo mata da farin cikinta, domin tabbas Deeni ne farincikin rayuwar ta. Ta yi niyyar zama har ayi sallar asuba, cikinta ta ji ya murɗa, da hanzari ta shiga banɗaki, tana dubawa ta ga period ɗinta ne. Shirya kanta ta yi tsaf sannan ta fito, kwanciya ta yi tunda an ɗauke mata sallah, bacci mai nauyi ne ya yi awon gaba da su ita da ɗanta.

Deeni ma ya yi farincikin da ya daɗe bai yi irinsa ba sakamakon jin muryar Deena, hakan ne ya ankarar da shi wahalar da yake ba kansa ta ƙin kiran ta, ɗaukar ma ransa ya yi na daina yi ma kansa wannan horon. Zuciyarsa fal da farinciki ya cigaba da Salatin Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, domin da shi ne bawa yake samun mafita a wurin Allah.

A bangaren Dr. Bello kuwa, tunda ya ji saura few days Deeni ya bar ƙasar hankalinsa ya mugun tashi, yadda ya ga rana haka ya ga dare saboda muguwar hassada. Washegari da zuwansa wurin aiki ya samu Md a office, kan chair ya zauna yana fuskantar Md, fuska a kicincine ya gaishe da shi “Good Morning Sir”, ta cikin farin gilashi Md ya kalle shi, amsawa ya yi “Morning too, how was the day”, Bello ya ce “Alhamdulillah.”, ɗan shiru ya yi, a ransa yana nazarin ta inda zai fara yi ma Md maganar Deeni, don ko kusa bai san ta ina zai fara ba.

Md ya lura da akwai magana a bakinsa, cewa ya yi “Is their any problem?”, girgiza kai ya yi “No Sir”, tare da ɗan cije lips, Md ya ce “Ok, na ga kamar kana nazari ne ai”, murmushin yaƙe ya yi kafin ya ce “Yallaɓai ai a wannan lokacin kullum cikin nazari ake na tunanin ya za a yi survive”, Md ya ce “Gaskiya ne, Allah ya bamu mafita”, bayan Bello ya ce “Amiiiiin” ne ya ɗaura da faɗin “Sir”, Md ya ce “Ina jinka”, Bello ya ce “Ashe Deeni zai je India”, tuni Md ya fara fahimtar irin tsanar da Bello ke yi ma Deeni, kuma ya ɗaukar ma ransa cusa ma Bello takaici a kan Deeni, cewa ya yi “Haka ne, ranar Tuesday ne Insha Allah”, satar kallon Bello ya yi ta cikin farin gilashinsa don ganin sauyin yanayinsa, aikuwa yana ganin ya firgice a ransa ya ce “Ikon Allah”, saboda bai taɓa tunanin akwai irin wannan tsanar a tsakanin Bello da Deeni ba, kuma tabbas ya san tsanar ta ɓangare ɗaya ce, Bello ne kawai ke ta haukansa, tunda bai taɓa ganin wannan alamar a wurin Deeni ba.

“Ai fita da shi wajen shi ne mafita, muna sa ran in sha Allahu zai samu lafiya a can, saboda hatta Patients sun yi kewar Deeni”, da biyu Md ya faɗi wannan maganar, aikuwa ta soki zuciyar Bello, ƙwafa ya yi kafin ya ce “Haka ne Yallaɓai”, a ransa kuma ya ce “Ai ko da asibitin nan zata tashi Deeni ya gama zamanta, rayuwarma na rantse zan iya raba shi ita”, kamar Md ya san me yake tattaunawa a ransa ya ce “Allah dai ya sa a dace, kuma ya tsare”, ba don Bello ya so ba ya ce “Amiiiiin dai”, rufe bakinsa ya yi daidai da miƙewar sa “Bari na je office”, ya faɗa cike da tsanar Md, don ya fahimci kamar da biyu yake faɗa mashi magana.

Ɗan rausaya kai Md ya yi kafin ya ce “Ok”, da idanu ya raka shi har ya fice, mamaki cike da ransa ya ce “Allah ya kyauta, mutane sai baƙar hassada?”, saboda ya san irin wannan maƙiyan na wurin aiki, shi kanshi ya sha wahala kafin ya kawo wannan matakin, kusan ma har yanzu yana ɗanɗana wahalar, duk da ya rinjayi maƙiyansa, tsakaninsa da su sai kallo.

Dama yana son yin magana da Deeni, wayarsa da ke a gefen system ɗinsa ya ɗauka, number Deeni ya kira, ringing biyu ya ɗaga, daga can cikin girmamawa Deeni ya ce “Barka da Safiya Yallaɓai”, cike da ƙaunar Deeni ya ce “Barka dai Deeni, ya gida da mutanen gida”, Deeni ya ce “Lafiya lau Sir”, Md ya ce “Masha Allah, ya shirye-shiryen tafiya?”, Deeni ya ce “Alhamdulillah, komai ya kammala, rana kawai muke jira Yallaɓai”, Md ya ce “Masha Allah, Allah ya tabbatar da Alkhairi, ya sa a dace”, Deeni ya ce “Amiiiiin Sir, na gode sosai.”

Fatan samun nasara ya yi ma Deeni, tare da yi masa nasiha a kan ya ƙara dagewa da addu’a, saboda ko ba komai maƙiya basa barin mutum ya zauna lafiya. Deeni ya ji daɗin haka sosai, godiya ya yi mashi, daga bisani suka yi sallama.

Dr. Bello kuwa jugum ya yi a office, duk da sanyin gari da kuma na AC da office ɗin amma shi zufa yake, sosai ya fahimci kamar da biyu Md ke bashi amsa, musamman da ya ce Patients ma sun guje su, kuma tabbas haka ne, yanzu da wahala a samu patients a gynea, sai dai wurin family planning kaɗai, su kuma sauran nurses kaɗai suna ji da su.

“Ko da za a rushe hospital ɗin nan na rantse Deeni ya gama zamanta, Ni za a yi ma iskanci da yada magana?”, ya faɗa cikin tsananin ƙunar rai.

Sosai ya yi imani da maganganun malaman sa, waya ya ɗauka ya kira, suna gaisawa da Malam na tudu ya dasa da faɗin “To ya ake ciki ne?”, Kamar Bello zai haɗiye zuciya ya mutu ya ce “A kan wancan ɗan anacen ne mana, wai har ni Md zai riƙa yi wa habaicin Kura a kan Deeni?”, daga can Malamin ya ce “Duk ka fita batun su, na faɗa maka Deeni ba zai warke ba bare har ya ƙara tasiri a rayuwa, don haka ka fita batun kowa”, Bello ya ji daɗin maganar, cewa ya yi “Haka nake son ji, kuma Md ɗin kansa zan iya maganinsa idan ya cigaba da shiga hancina”, daga can ya ce “Na ce ka fita batunsu fa, duk kai ne a gabansu”, haka dama Bello ke son ji, baki a washe ya ce “Yauwa, toh ya batun ƴar gudaliya, so nake fa ta kori kowa, sai Ni”, Malaminsa ya ce “Ita kam ta zama taka, amma batun tsohon mijinta sai an yi da gaske, don na buga na gani shi ma ƙwaro ne, kafin a kar shi sai an shirya”, Bello baya jin ƙyashin kashe ko nawa ne a harkar bin Malamai da bokaye, cewa ya yi “Zan biya ko nawa ne don a raba su”, Malamin na jin haka ya ce “Baka da matsala, idan dama ta samu ka shigo cikin satin nan, zan baka laƙanin da ko uwarta da ubanta ka ce ta rabu da su, toh zata bar su ta bika.”

Wata irin shewa Bello ya yi kafin ya ce “Ina yin ka Malam, anjima after Magrib zan shigo, ƙila da abokina ma”, Malamin ya ce “A’a, ka zo kai kaɗai, laƙanin da zan baka sirri ne namu, sai kuma jama’armu irin ka”, Bello ya ce “An gama, godiya nake.”

Bayan sun gama wayar ne ya aje ta a kan table, lokaci ɗaya kuma bakinsa na faɗin “Mun san maganin kowane shege ai”, cigaba da danna system ɗinsa ya yi, tare da cigaba da saƙa mugun abu a ransa.

Sai kana da maƙiya ne dama zaka gane kai mai nasara ne, kamar haka ne Deeni ke ta samun galaba a kan duk wanda bai ƙaunarsa a rayuwa, ko Umman Deena da ta ƙwace ƴarta, ya san shi ke a sama, tunda Allah bai bar shi ya wulakanta ba. Kamar yadda Md ya bashi shawarar ya cigaba da addu’a, haka kuwa aka yi, domin ya ƙara naci da dagewa a wurin addu’a, musamman da ya kasance saura kwana biyar su tafi.

A shirye-shiryen bikin Asma’u kuwa an ci ƙarfin komai, tun daga ɓangaren amarya da ɓangaren ango kuwa. Tsaye ƴan uwan Asma’u suka yi wurin ganin sun gyara ƙanwarsu ta yadda zata yi daraja a wurin mijinta. Tun da aka sa ranar ɗaurin aure ake ɗura ma Asma’u kayan da zasu gyara ta, batun gyaran fata kuwa an mata gyaran da kai ka ce ba bahausa ɓace, sosai ta sha gyaran da asalin kyawunta ya fito kamar ƴar Ethiopia, sannan ga wani ƙamshi na musamman da ke tashi a jikinta.

Zaune take a ɗakin Hajiyarsu a gefen gado suna magana wayarta ta shiga ruri, sanin Bashir ne ta figi wayar ta bar ɗakin, bayan ta ɗaga ne ya ce “Ina kan hanyar gidanku fa”, ko kusa bata shirya ganinsa yanzu ba, don fita zasu yi, a marairaice ta ce “Fita zamu yi fa”, ya ce “Ai ba daɗewa zan yi ba”, ta ce “Toh Shikenan sai ka zo.”

Cikin shirinta take a cikin maroon ɗin Jalbab, maɗaurin ne kawai ta gyara ta zauna zaman jiransa. Yana zuwa ya kira ta a waya tare da faɗa mata ya iso. Ba ta wani ɓata lokaci ba ta nufi waje. Fitowarta ta yi daidai da fitowar Bashir a mota, su duka sai da gabansu ya faɗi kamar yau ne suka fara ganin juna. Tabbas duk sun ƙara kyau, da ace namiji na gyara jikinsa kafin aure, toh Asma’u zata ce Bashir ya yi gyara sosai, don har kumatu ya ƙara.

Kasa ƙarasawa ta yi a gabansa, ba tare da ta san dalilin hakan ba. “Ya kika tsaya anan? Ki karaso mana”, ya faɗa cikin sanyin murya, bata yi musu ba ta karasa tare da jingina da jikin motarsa, “Sannu da zuwa”, ta faɗa a takaice, ya ce “Yauwa Asmeen Love”, ƙuri ya yi mata da idanunsa masu kashe mata jiki, a daburce ta ce “Ya dai”, ya ce “Haka aka gyara mani ke? Gaskiya kin yi kyau sosai Asmeee, ga wani ƙamshi mai kashe jiki da yake fita a jikinki, kamar na sace ki na gudu”, ƴar rausaya mai cike da kissa ta yi “Da gaske?”, ya ce “Da gaske mana, na rantse kin tafi da dukkan nutsuwata”, ta ce “Ai kaima ka yi kyau sosai, har ƙiba ka ƙara”, ya ce “Ai nutsuwar samunki ce ta sa ni ƙiba, saboda kin iya tattalin masoyi”, Asma’u ta ce “Ai kaima ka iya, gashi ka cusa Mani sonka sosai”, yadda ta ƙarashe maganar kamar ƙaramar yarinya ne ya ba shi dariya, cewa ya yi “Da gaske kina so na?”, ta ce “Uhmm!”, ya ce “I love you toooooo!”, dariya su duka suka yi, daga nan ya faɗa mata maganar Events ne, sun tsara bayan ɗaurin aure za a shirya gagarumar walima a Events center.

Asma’u ta ji daɗi sosai, ya ce “Na san zaki zama bride of the year ko?”, Kai ta ɗaga mashi sannan ta ɗora da kai kuma “Groom of the year ba”, ya ce “Insha Allah my Love”, kasantuwar su duka suna son rayuwar holewa, ƴar soyayyarsu suka sha, sannan ta dawo gida, inda shi kuma ya juya kan motarsa ya koma inda ya fito.

Da komawar Asma’u ta sanar musu da maganar Dinner da Bashir ya zo mata da ita, Hajiyarsu ta ce “Ni fa bana son bidi’ar nan, kawai a yi walima gidansu ango, shi ne za a tsiri wani Party?”

Salma ce ta yi caraf ta ce “A’a Hajiyarmu, don Allah ki barmu mu yi hidimarmu yadda kowa ke yi”, Yaya Asiya ta ce “Wallahi kuwa, yanzu ina ake biki a ƙumshe?”, dariya su duka suka kwashe da ita, Asma’u ta ce “Aikuwa an daina”, haɓa Hajiyar ta riƙe, baki a buɗe ta ce “Asma’u da ke za a juya mani baya?”, cike da shagwaɓa ta zauna tare da zama a gefen Hajiyar, riƙo mata hannu ta yi “A’a Hajjah, wace nii”, ta ce “A’a toh, na ga alama ai.!”

Nan suka taru hada Hajiya Ummah suka lallaɓata a kan komai za a yi shi yadda Shari’a ta tanadar, cike da gamsuwa da su ta ce “Ni dama ba hanawa na yi ba fa”, suka ce “Yauwa Hajjah”, Asma’u kamar zata koma cikin Hajjah ta ce “Ai zaki je ko Hajjah”, ta ce “Ina?”, Salma ta ce “Wurin Dinner mana”, kai ta girgiza “Ba da ni ba”, marairaicewa Asma’u ta yi “Wayyo Hajjah, kin je na bikin Yaya, shi ne ba zaki je na autarki ba?”, duk don zaulaya ne ta ce ba zata je, cewa ta yi “Toh, Allah ya kaimu ranar lafiya.”

Sun ji daɗi sosai, duk da sun san dama zaulayarsu take. Shirin fita suka yi su uku in banda Hajiya Ummah.

Kwanci tashi asarar mai rai, gashi har kwanakin ɗaurin auren Asma’u da Bashir da suka rage sun zo. Gidansu Asma’u ya cika da baƙi maza da mata, wanda suka zo daga kusa da kuma nesa, kasantuwar su ɗin ƴan dangi ne. Rahila ma tuni ita da Fadila sun zo, kuma a ranar suka zo gidansu Deeni, duk da ba nan zasu kwana ba

Washegari Juma’a aka ɗaura auren Asma’u da Bashir a babban masallacin Juma’a, inda ɗaurin auren ya samu halattar manyan mutane hada Alhaji Lawan, saboda Bashir ɗan masu faɗa aji ne.

Asma’u kuwa tuni dama tana gidan Alhaji Bala, tunda shi ne maɗaurin aurensu. Tana zagaye da ƙawayenta kiran Lalu ya shigo wayarta, da hanzari ta ɗaga kiran “Hello Uncle Lalu”, daga can ya ce “Toh yau dai Allah ya kawo mani ƙarshen jarabarki, an ɗaura maki aure”, ras gaban Asma’u ya faɗi “Da gaske kake an ɗaura?”, ya ce “Ina maki ƙarya ne?”, kai ta girgiza tamkar yana gabanta, don kuwa duk faɗan da suke yi Lalu baya yi mata ƙarya.

Ya ce “To ki yi ma kanki fatan Alkhairi, kamar yadda nima na ke ta murnar samun hutun azabarki”, yana faɗin haka ya tsinke kiran.

Kasa motsi ta yi daga inda take tsaye, ɗaya daga cikin ƙawayenta mai suna Aysha na lura ta taso, dafa kafaɗar Asma’u ta yi “Ya dai kika yi shiru?” buɗan bakin Asma’u ta ce mata “Wai an ɗaura”, tambaya Aysha ta sake maido mata “Auren?”, Asma’u ta jinjina kai alamar “Eh”, buɗa Aysha ta rangaɗa tare da faɗin “Alhamdulillah, anɗaura-anɗaura”, aikuwa kaf ƴan matan dake ɗakin suka karɓe da shewa “Yeaaaaaaaaaa! Ta zama matar Baahirirrrrr”

<< Mutuwar Tsaye 30Mutuwar Tsaye 32 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×