Skip to content
Part 32 of 32 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Jikin Asma’u ba ƙwari ta zauna a gefen tare jingina da kan gadon, saboda tsabar ruɗewa bata san lokacin da ta aje wayar ta kan bed side locker ba. Aysha da ke tsaye a gabanta ce ta ɗauki wayar gami da damƙa mata a hannu “Ki adana wayarki tun kafin ayi maki ram da ita”, aikuwa gam Asma’u ta matse wayarta a hannu, saboda yanzu ba a shaidar mutane, don kuwa satar waya ya zama ruwan dare a ko ina, sai dai fatan Allah ya tsare mu Amiiiiin.

Aabubuwa biyu ne suka haifar ma Asma’u da wannan mutuwar jiki. Na farko shi ne farincikin ɗaura aurenta da wanda take so, domin babu abin da ya kai farincikin auren wanda zuciya ke so, musamman da ita kullum addu’arta kenan, saboda ta ga yadda auren dole ya zama silar wargajewar farincikin wata ƙawarsu, shi ya sa ta dage da addu’ar neman tsari a wurin Allah, kuma ga shi ya karɓa mata.

Na biyu kuma, shi ne kewar mahaifiyarta da danginta, tabbas ko a cikin gari za a aje ta, toh ba ƙaramin al’amari bane ta tafi ta bar mahaifiyarta, bare kuma wata uwa duniya har India, wannan kewa ta sa mata mutuwar jiki fiye da ma farincikin. Ɗaya bayan ɗaya ta riƙa kallon ƙawayenta da ke cike da ɗakin suna ta shewa, wasu na zaune a tsakiyar gadon, wasu kuma a gefen gadon, kana ganin fuskokinsu ka san cike suke da farinciki.

“Allah ya sa Alkhairi Asma’u”, in ji ƙawarta mai suna Nafisa, da ta zauna gefenta haɗe da dafa mata kafaɗa, fuskar Asma’u ɗauke da murmushi ta ce “Nagode sosai Nafee, Allah ya bar zumunci.”, Aysha da duk suke zagaye da ita ta ce “Wai ya na ga kamar bakya murna ne, kamar wadda aka yi ma auren dole?”, sai da Asma’u ta sauke murmushi mai sauti kafin ta ce “Aysha ina murna mana”, Aysha ta ce “Toh fuskarki bata nuna ba fa”, Asma’u ta ce “Ko?”

Lokaci ɗaya kuma ta ƙara faɗaɗa fuskarta da murmushin da ta ke jinsa kamar yaƙe.

“Gaskiya dai toh farincikin ne ya yi kaɗan, don haka mu ga fiye da haka”, Asma’u kam a yanzu ba ta san ta yadda zata bayyana abin da ya fi haka ba, ɗan rausaya kai ta yi kafin ta ce

“Aysha kewar Hajiyarmu ba zata bar ni in yi farinciki ba, bana son in tafi in barta, ga shi ba cikakkiyar lafiya ne ita ba”, sosai Aysha ta fahimce ta, cewa a yi “Allah na nan, zai kula maki da ita”, Asma’u ta ce “Allah ya sa.”
Sosai Aysha ta ja hankalinta har ta saki jikinta, su kuwa ƙawaye sun kunna waƙoƙi sai rawarsu suke a ɗakin, ita dariya sai dariya take musu.

Alamar shigowar saƙo ta ji a wayarta, dubawa ta yi, aikuwa ta ga Bashir ne Ya rubuto mata “Alhamdulillah for being my forever Asmee, Allah ya bar mani ke wifeee”, murmushi mai cike da kayatarwa ta yi kamar tana gaban shi, reply ta rubuta mashi kamar haka “Amiiiiin my husband, I love you with all my heart.”

Bayan ta tura mashi ne ta maida hankalinta wurin ƙawayensu da suka sake sabon salon rawa.

Sosai suka shagala da rawar, sun so tilasta ma ta shigo cikinsu itama ta ɗan taka, amma ta ƙi, saboda a yanzu kam daga ɗaura aure ta kama tiƙar rawa bai kamata ba, musamman da ya kasance gidan Kawu Bala take.

“Yanzu duk don aurena ake wannan nishaɗin?” Tambayar da ta jefo ma kanta lokacin da tunani ya fizge ta, gani take kamar mafarki ne ba gaske ba. Yadda hayaniya da kuma kaikawon da ƙawayenta ke yi a ɗakin ne ya bata cikakkiyar amsar tambayar da ta yi ma kanta. “Allah Sarki Hajiyarmu da Yaya, Allah ya baku lafiya”, ta faɗa a ranta cike da kewa da kuma tausayi ɗan’uwanta da kuma mahaifiyarta, domin kula da su a kanta ya ke, kuma bata taɓa nuna gajiyawa ba, don ta san dolen ta ne, kuma sakamakon hakan na wurin Allah.

“Kai-Kai, ku rage sautin nan ga Baba nan ya shigo”, muryar Maryam kenan da ta karaɗe ɗakin lokacin da take tsaye a bakin ƙofa, wadda kuma ta yi sanadin katse ma Asma’u tunani tana duban ta, a cikin ran Asma’u ta ce “Yauwa”, saboda hayaniyar ta fara sha mata kai sosai. Su kuwa ƴan rawa babu wadda ta saurari me Maryam ke faɗa, bare su dakata.

Aikuwa kamar daga sama suka ji Muryar Kawu Bala na faɗin “Wannan kiɗan fa na lafiya ne?” Fancy, wadda matsayin jika take a wurinsa ce ta ce “Murna muke taya Aunty Asma’u”, fuskarsa cike da annuri ya ce “To maimakon ku yi karatu shi ne za ku ɓige da rawa?” sosai ya basu dariya, ku san majority suka haɗa baki suna faɗin “Karatu kuma?”

Ya ce “Eh mana”, Fancy da kanwa bata jiƙa a baki ta ce “Ai mun yi karatunmu jiya, yau kuma ranar farinciki ce, ka kawo mana kuɗin liƙi ma”, juyawa ya yi yana faɗin “Ku sha rawarku lafiya, amma ba zan bada kuɗin liki ba Allah ya kamani”, dariya su ma suka cigaba da yi.

“Lallai a jiƙa ki a sha Asmee”, Fancy ta faɗa tana duban Asma’u, Asma’u ta ce”Wurin me?”, Fancy ta ce “Da Kawu Bala bai hana mu cashewa ba, kun tuna bikin Ummah da ya fafaki mai Dj da ƴan rawa a ƙofar gida?Tunawar da suka yi ce ta sa su kwashewa da dariya.

Maryam na dariya ta ce “Na tuna wannan rana, kai mun ga ikon Allah, sai ga masu Dj sun gudu sun bar speaker na ta ihu ba mai control, ƴan rawa ma ɓat aka neme mu aka rasa.”

Sosai tuna wannan labari ya sa su dariya hada ƙwalla, Fancy ta ce “Kawu Bala ai ikon Allah ne, yanzu ma ƙarfin hali fa ya sa ni magana”, Maryam ta ce “Ai kin yi ƙoƙari ma, amma ƙila don muna cikin gida, kuma mata ne kaɗai shi ya sa bai yi faɗa ba, Asma’u ta ce “Da alama kuwa.”

A can gidansu Asma’u kuwa mutane ne har ba masaka tsinke, ƴan uwa na kusa da na nesa duk sun zo, kuma sun nuna kara da karamci a matsayinsu na ƴan uwa. Hajiyarsu ta samu Alkhairi sosai, wanda tunda take aurar da ƴaƴa bata taɓa samun gudunmawa mai yawa kamar haka ba. Ko da yake kowane ɗa da arzikinsa ake haifo shi, kamar yadda tun Asma’u na jaririya aka fahimci haka.

Hidimar ake, amma ƙasan ran Hajiyarsu itama cike da kewar ƴarta, a zaton ta idan dare ya yi Asma’u zata dawo gida ta kwana, tunda bai kai Amarya za a yi ba, kawai za jira ranar Tuesday su wuce India.

“Amarya tana gidan Alhaji Bala ko?” Ƙanwarta mai suna Hajjah Bintu ta tambaye ta, lokacin da suke zaune a gefen gado suna tattauna magana a matsayinsu na ƴan uwa. Mai saurin kuka ne aka jefe shi da kashin awaki, amsa ta bata da “Aikuwa suna can, na ɗauka zasu bar ta dawo ai”, Hajjah Bintu ta ce “Gaskiya kam, tunda ƴar nan fa barin ƙasar nan zata yi, kin san ni ban cika son al’adun nan na Hausawa ba, lokacin da ƴa ke bankwanar barin mahaifiyarta, lokacin ne kuma za a tura ta wani gidan uban wanka”, Hajja ta ce “Toh ya muka iya.”

Kayan da ke tsube kan gado Hajjah Bintu ta duba “Masha Allah, Asma’u fa ta yi goshi”, Hajiya Ummah da ke gefe ce ta ce “Ai auta ba daga baya ba, kun tuna lokacin da aka haife ta, kayan kamar za a buɗe shago?”, Hajjah Jummai ta ce “Wallahi kuwa, Allah dai ya basu zaman lafiya”, suka ce “Amiin ya Allah.”

Sun so dudduba kayan, waɗanda suka haɗa da zannuwan gado, kayan kitchen, frames, da sauran duk irin gudunmawar da ake ba ma Amarya, sai dai mutanen da ke ta shigowa ɗakin jefi-jefi ne ya hana, kuɗaɗen ma tuni Hajja ta hannanta key da asusun dake cike da cash a wurin Hajiya Ummah, waɗanda Allah ne kaɗai ya san yawan su, sai kuma idan sun ƙirga. Na banki ma lissafinsu sai an zauna, don har yanzu credit alert shigowa yake a wayar Hajjah.

A can wurin Asma’u kuwa itama kamar ta yi kuka, don ta fi son ta kwana wurin mahaifiyarta. Tana kwance a gefen gado tana ta zullumin barin gida wayarta da ke kan stool ta shiga vibration, daga kwancen ta miƙa hannu ta ɗauki wayar, a kunne ta kara ta tare da sallama, daga can yana amsawa ya ɗora da faɗin “Ya na ji muryarki a ƙasa-ƙasa, me ya faru?”, kamar zata yi kuka ta ce “Kaina yake ciwo”, cike da damuwa ya ce “Ayya, sorry! Hada taron jama’a”, ta ce “Uhmm”, tambarta ya yi “Kin ci abinci?”, ta ce “Nope!”, ya ce “Toh me zaki ci, gashi nan Faisal zai fita, ku faɗi abin da kuke so zai kawo muku”, amsa ta ba shi da “Bama buƙatar komai”, aikuwa ba ta ankare ba ta ji tsinkuli a ƙafarta, wanda Maryam ta sauke mata shi, saboda duk suna jin me take faɗa, kuma basa son ta yi musu buƙulu.

Maimakon ta ba shi amsa, sai nishinta ya ji a wayar, tambayarta ya yi “Lafiya kuwa?”, ta ce “Kan ne fa”, lokaci ɗaya kuma ta yunƙura ta tashi zaune.

Duka ta sakar ma Maryam haɗe da harara, Maryam na dariya ta sassuta murya “Toh baƙinciki zaki yi mana ne, sauran ƙawayen duk suka mara ma Maryam baya, don duk ƴan son aci bati ne aka tara wurin.

Asma’u dai basu gama wayar ba sai da Bashir ya tabbatar mata da Faisal zai zo musu da kayan maƙulashe yanzu.

Fancy da yake bata gajiya da abin dariya ta ce “Allah ya sa Faisal ɗin ma ya ce yana so na, don na ga daga abokai har dangin Bashir duk ƴan gayu ne”, Safiyya ta ce “A haka zaki ƙare da kwaɗayi, duk suka kama dariya.

Ba a daɗe ba Sai ga Faisal da wani abokinsa sun faka da motarsu a ƙofar gida, Tabbas suma sun zo da niyyar latsa ƴan matan amarya, amma kawu Bala ya basu mishkila, domin yana ganin mota ta faka ya taso yana tambaryar su wa suke nema, aikuwa kwarjinisa ya sa Faisal ya ce “Saƙo ne Bashir ya bada a kawo ma Asma’u”, kawu Bala ya ce “Okay, toh ku kawo a miƙa mata”, ba don ransu ya so ba suka fiddo manyan ledoji guda biyucike da kaya suka miƙa mashi, bayan ya juya ne abokin Faisal ya ce “Ba dai haka muka so ba”, Faisal na dariyar takaici ya ce “Na rantse kuwa, amma gobe ma rana ce ai, zamu zaɓi na zaɓa, don na ɗaukar ma raina a gobe zan yi matar aure Insha Allah.” Key ya yi ma motar suka bar unguwar suna yi ma kansu dariya.

Kamar haka ne su Safiyya suka sa Fancy gaba suna yi mata dariyar mugunta a lokacin da Aunty amarya ta kawo musu saƙonsu. Fancy na dariya ta ce “Ke! Gobe fa nan, kin san dai gayun da zamu ci har sai mun kori maza.”

Asma’u dai dariya ce tata, Aysha da ke kame a akan Carpet tana ta dariya itama ce ta buɗe ledojin da ke a gabanta tare da faɗin “Me muka samu?” Kaf ƴan matan da ke ɗakin sai da idanunsu suka koma kan ledojin, gasassun kaji ne naɗe, sai kuma Snacks da suka haɗa da shawarma, cupcake da kuma milky donut, sai kuma gullisuwa da tuwon madara da duk aka yi packaging. A ɗayar ledar kuma drinks ne kala-kala, sosai suka yaba ma ƙoƙarin Bashir da abokansa. Ba tare da ɓata lokaci ba suka shiga kaso, inda aka ɗibar ma ƴan waje nasu, su ma suka sha badagonsu a nan, Asma’u kuwa donut kaɗai da ice cream ta sha, saboda bata jin ma yunwar.

Washegari ne suka tsara walima ta gani ta faɗa a babban Events center ɗin da masu ƙumbar susa ne ke iya kama shi. Sosai Amarya da ƙawayenta suka yi shiri na fita tsara, hall ɗin ya cika sosai da jama’a, inda aka cigaba da gabatar da biki cikin farinciki da jin daɗi.

Kamar kullum Deena na zaune a ɗaki tana duba waya, kamar an ce ta shiga WhatsApp, status ɗin Rahila ta gani a farko, kasa haƙuri ta yi har sai da ta buɗe, pictures da vedio na amarya da ango ne ta saka, da kuma nasu ita da su Yaya Asiya suna ta farin ciki, aikuwa tamkar sabo haka ciwon rabuwa da mijinta ya dawo mata a zuciya, domin da yanzu da ita za a sha wannan hidimar.

Kiran Deeni ta yi a waya ta ce “Ya ban gan ka a wurin walima ba?”, saboda ta tuba status ɗin mutane da yawa, amma bata ga inda wani ko wata suka sa hotonsa ba, maido mata tambaya ya yi da “Kin je ne?”, ta ce “Eh”, ya ce “Really?”, ta ce “Yep”, ya ce “Ban yarda ba”, ta ce “Toh shikenan”, ba don ya gamsu sosai da cewar ta je ba ya ce “Ai da na san zaki je, da nima na je ai”, a nan ne Deena ta gane bai je ba, kuma dama damuwarta kada ya je su haɗu da su Rahila, bare har su samu zarafin ɗaukar hotunan da Rahila zata yi terere dasu a kan media.

“Me ya sa baka je ba, kuma na ga duk kowa ya je hada Hajjah?”, amsa mai cike da son sanya mata nutsuwa a zuciya ya bata “Saboda ban san zaki je ba”, cewa ta yi “Ai nima ban je ba, live status na gani Rahila da wasu friends ɗinmu na ta sakawa”, ɗan shiru mai nuna alhini ya yi, kafin daga bisani ya ce “Shi ya sa ban je ba ai, da ace kina gidana ne zan ɗan leƙa saboda ke, duk da a matsayina na Babban Yayan Amarya bai kamata a ce na je ba”, ita dai daɗi ne ya ƙule ta, tunda ko shakka babu idan ya je, toh sai an kalle mata shi, don ko da baya gani, idan ya saka baƙin gilashinsa ɗaga hankalin ƴan mata yake.

Ba zato ta ji an murɗa handle ɗin ɗakinta, wanda ko shakka babu Ummanta ce, saboda ita kaɗai ce ke shigo mata ɗaki kai tsaye, sosai ta kama kanta, a tsorace ta ce “Zan kira ka”, tare da katse kiran.

Sosai Ummanta ta fahimci alamar rashin gaskiyar da ya bayyana a tare da ita, cike da tuhuma ta tambaye ta daga tsayen da take a bakin ƙofa “Ke da wa kuke waya ne?”, a dake Deena ta bata amsa “Ƙawata ce Mommah?”, ƙwafa ta yi wadda ke nuna alamun rashin gasgata zancen Deena, a ranta ta ce “Ko waye ma zan kama ki ai”, saboda ta daɗe da fahimtar kamar suna waya da Deeni.

Umurni ta bata akan ta fito su shiga kitchen, saboda a tsarin gidan ƴan aiki basa girki su kaɗai. Goya Raihan ta yi, sannan ta bi bayan Ummanta da tuni ta sauka ƙasa. A falo suka haɗu da Alhaji Lawan, bayan Deena ta mashi sannu da zuwa ne ya juya wurin Hajiya Hadiza “Wai har kun gama bikin ne?”, sarai ta fahimci bikin da yake nufi, amma sai ta basar ta ce “Wane bikin?”, ya ce “Na su Dr. Safiyya mana”, baki ta taɓe “Biki kam da saura, yau ma suna can suna shagalinsu, amma ni ba zan je ba”, yadda ta ba shi amsa kowa ya san da biyu ne, “Toh da kyau”, ya faɗa tare da wucewa ciki. Deena kuwa tuni ta wuce, don duk abin da zai ɓata mata rai ta daina sauraren sa, fatan zaman lafiya ta yi ma Asma’u, sannan ta cigaba da aikinta.

A wurin walima kuwa an yi mai cike da nutsuwa, duk da abokan ango da na amarya sun nishaɗantar da mutane, sannan waɗanda suka ƙulla soyayya a tsakaninsu tuni sun ƙulle, kamar yadda mafi yawansu suka sha buri. An sha hotuna da vedios kamar me, Amarya ta samu sanya Albarka a wurin mahaifiyarta da sauran dangi. Bayan taro ya tashi ne aka nufi gidansu Ango da Asma’u, domin gabatar da ita a wurin iyayen Ango, saboda ba cikakken time ɗin da za a ce a ware watarana ta buɗar kai, kuma ga Amarya da mahaifiyarta suna son ganawa ta musamman.

Sosai Amarya ta samu albarka ta musamman a wurin surukanta, Baban Ango kuwa ya yi mata kyautar kuɗaɗe masu kaurin gaske. Da ƙarfe tara Ango ya ɗauko matarsa da nufin maido ta gidansu, duk da ba haka ya so ba!

<< Mutuwar Tsaye 31

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.