Skip to content
Part 33 of 36 in the Series Mutuwar Tsaye by Hadiza Isyaku

Tun bayan da Asma’u ta gaishe shi lokacin da ta shigo motar bata sake cewa komai ba, don ta lura da yadda yake ta son zaƙewa a wurin nuna ita matarsa ce, saboda ba kowa a motar sai su kaɗai. Tsoro cike da ranta ta riƙa sauraron waƙar da ke ta tashi ƙasa-ƙasa a cikin motar, duk da ba fahimtar me suke faɗa take ba, saboda bata cikin nutsuwarta.

Shi kuwa ransa fal da farinciki yake driving motar a hankali, don kuwa baya son su isa da wuri, duk da akwai ƴar tazara kafin a je gidansu Asma’u. Ƙamshin da ke ta fita a jikin Asma’u, da wanda ke fita a jikinsa ne suka taru suka bada ƙamshi na musamman, wanda ko da a cikin kunci mutum ya ke idan ya shaƙe shi sai ƙuncin ya gushe, bare kuma su da suke cikin farincikin kasancewa sababbin ma’aurata. Satar kallon ta ya riƙa yi saboda ya lura da yadda ta sha jinin jikinta, ya kuma yi mamakin haka, don a yadda suka gina soyayyarsu tamkar abokan wasa suke yin ta ba tare da wani noƙe-noƙe ba.

“Asmee”, ya faɗa cikin murya mai nuna tsantsar kulawa ga matarsa ba tare da ya ɗauke idanunsa daga kan tati ba, amsawa ta yi da “Na’am”, sai da ya sauke numfashi sakamakon mutuwar da jikinsa ya yi kafin ya ce “Kin gaji ko?”, ɗan dubansa ta yi sannan ta ɗaga kai “Uhmm”, jinjina kai ya yi kafin ya ce “Oh kay! yana da kyau in miki massage ɗkafin na kai ki gida, ta yadda zaki yi barcinki peacefully”, rufe bakinsa ke da wuya ya faka motar a gefen titi, saboda hanyar ba mutane sosai. Take kuwa tsoron da ke ran Asma’u ya bayyana ƙarara, shashshaɓe fuska ta yi tare da matse ƴan ƙwallan da suka fito a idanunta ba tare da ta sani ba, “Dan Allah mu tafi gida”, ta faɗa hannunta sama kamar mai neman gafara.

Ta cikin ɗan hasken da ya game motar ne ya karanci yanayinta, sosai ta ba shi dariya, amma sai ya gumtse, “Mu tafi ina?”, seriously ya faɗi haka, ta ce “Gida mana, na san Hajja na can tana jira na”,

Baki ya ɗan taɓe “Kina tare da mijinki ne Hajjah zata jira ki?”, shiru ta yi, gabanta na cigaba da faɗuwa, saboda bata da amsar da zata ba shi.

Hannu ya zura ya buɗe motar da ke gefenta, aikuwa kamar Asma’u zata kurma ihu, shi kuwa cewa ya yi “Mu koma baya ki ɗan samu ƙarfi, tunda kin ga ba zan sake zama irin haka da ke ba sai mun isa gidanmu.”

Kuka ta fashe da shi “Don Allah Yaya Bashir ka bari, bana so”, cike da mamakinta ya ce “Bakya so?”, ta ɗaga kai “Eh bana so”, shiru ya yi, duk da dama wasa yake mata, amma sai da ta ba shi tausayi da dariya.

Ɗan langaɓar da kai ya yi “Toh rufe motar”, kasa ko ɗaga hannunta da ke kyarma ta yi bare ta iya rufe murfin motar, lurar da ya yi ne ya ba shi damar miƙa hannunsa ya ja murfin motar kamar yadda ya yi da farko wurin buɗewa.

Ƙuri ya ma fuskarta da ke ta fitar da ƙwalla, hannunta mai taushin gaske ya ruƙo kafin ya ce “Dama tsorona kike?”, lokaci ɗaya kuma yana jin kamar ya maida ita a cikinsa saboda tsananin ƙaunar da yake mata.

Tabbas ba wai tsoronsa Asma’u take ba, tunda ba wani abin da bata sani ba na aure, sanadiyyar karance-karancen litattafai, da kuma kallon films. Kawai wautarta tana faɗa mata zai iya yi mata wani abun da idan ya kai ta gida za’a gane, ga shi mugun kunyar ƴan gidansu take ji.

Har a cikin ranta ta ji daɗin ruƙon da ya yi ma hannunta, tunda ga shi ta nemi kyarmar da take ta rasa, a hankali ta lumshe idanunta lokacin da hucin fuskarsa ya sauka a fuskarta, tare da sakar mata ƴar sumba.

A kunne ya raɗa mata “Ki kwantar da hankalinki, ba abin da zan maki har sai mun je India, amma kuma ina son na ji gumin jikinki sosai a yanzu”, duban sa ta yi a cikin fuskar ban tausayi.

Ido ya kashe mata, haɗe da ɗan lakatar kumcinta ya ce “Idan kika zo hannuna sai na cire miki wannan tsoron, don haka ma ki shirya”, ita dai bata ce komai ba, sai ma wasa da zoben dake hannunta.

Daidaita zamansa ya yi a kan seat, belt ya mayar a jikinsa, sannan ya yi ma motar key suka ta fi. A matsayinta na mai hankali ta fahimci yanayin da ya samu kansa na son raɓar jikinta ko da bai faɗa ba, itama a nata ɓangaren bata ƙi ta ji ta kwance mina-mina a jikinsa ba domin rage gajiyar da ta dame ta, toh amma ba yadda ta iya, dole ta yi haƙuri itama, tunda saura ƴan kwanaki suka rage musu.

Shiru ce ta ratsa motar, har suka isa a ƙofar gidansu Asma’u ba wanda ya sake cewa uffan, tunda dama Bashir ne ke maganar, kuma shi ma abin da ya ishe shi ya ishe shi.

“Toh ƴar gidan Hajjah, mun zo”, ya faɗa yana duban ta, murmushin farinciki ta yi haɗe da ƴar dariya, cewa ya yi “Guduna kike ko?”, Kai ta girgiza “A’ah” ya ce “Toh meye na yi mani kuka a ɗazu?”, musu ta yi ta hanyar faɗin “Ni ba kuka na yi ba”, idanu ya ware “Au! Zan maki ƙarya?”, shiru ta yi saboda ta san ita ke ƙarya ba shi ba.

Sakin fuskar da ta yi ba ƙaramin kyau ta ƙara mashi ba, sassuta murya ya yi sannan ya ce “Asma’u”, da wani irin salo ta dube shi, cigaba ya yi da faɗin “Ina son ki sosai”, Bashir bai taɓa zaton a yanzu zata iya magana ba, sai ji ya yi a cikin muryarta mai taushin gaske ta ce “Nima haka, Allah ya bar mani kai mijina”, mamaki bai ida ƙume shi ba sai lokacin da ya ji ta kwance a jikinsa.

Idanunsa a lumshe ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi, tabbas aure rahama ne, domin da shi ne kaɗai ake samun irin nutsuwar da ma’auratan suke ciki yanzu, zagayo ta ya yi da hannunsa suka yi shiru, ba abin da suke saurare sai bugun zukatan junansu. Sun ɗan ɗauki lokaci a haka, Bashir kuma baya son zargi saboda unguwa ce ta mutane, don ma sanyi ya sa ƙafar mutane ta fara ɗaukewa.

“Asma’u, ki shiga ciki ko?”, idanunsa a lumshe ya furta haka cikin muryar da bata fita sosai, kai ta ɗaga almar “Eh”, sai da suka sumbaci juna sannan suka ware, ƴan maganganu suka yi, sannan ya zura hannu ya buɗe mata mota, fita ta yi ba tare da ta ɗauki jakarta ba, dakatar da ita ya yi “Jakar fa wa zai ɗaukar maki?”, tana dariya ta ce “Kai mana”, ya ce “Ni ɗan ruƙon jakarki ko?”, ta ce “Eh”, ya san wannan ƙarfin halin nata duk don an zo ƙofar gidansu ne, cewa ya yi “Zamu haɗe ne”, duk suka sa dariya.

Fita ya yi shi ma bayan ya ɗauki jakar, bayan sun jera zasu shiga gida ne ta ce “Kawo jakar”, ya ce “Ki bari in riƙe maki”, ta ce “”Ni na isa?”, ya ce “Har kin yi yawa ma”, ta so karɓar jakar amma ya ƙi, tsokanarta ya riƙa yi, har suka shiga gidan tana dariya.

Sosai Hajjah ta yi murna da ganin autar ta tare da mijinta, haka dama kowace uwa take fatar ma ƴarta ko ɗanta. Cike da girmamawa Bashir ya durƙusa har ƙasa ya gaishe da Hajjah da su Hajiya Ummah da suke cike da ɗakin, amsawa ta yi haɗe da sanya musu albarka.

Su Hajiya Ummah ma fatan Alkhairi suka yi mashi, sannan aka nuna mashi dangin su Asma’u na kurkusa da ke cike da ɗakin, wata wadda take matsayin Kaka a wurinsu ce ta tsokane shi da faɗin “Yanzu kai in banda abinka, duk ga irinmu masu jini a jika, shi ne zaka zaɓi wannan ƴar shawai-shawai ɗin”, dariya sosai ya yi, Yaya Asiya ce ta tare mashi ta hanyar faɗin “Hajiya ai yanzu ƴan shawai-shawai ɗin ake so”, hannu riƙe da haɓa ta ce “Iyeee! Ƙanwarki zaki shigar mawa ko?”, Hajjah dai dariya ne nata gami da faɗin “Ah toh!”, bayan duk sun ɗan dara ne Bashir ya miƙe da shirin tafiya, tambaya ya yi “Ina Dr.?”, aka faɗa mashi yana ɗakinsu, don akwai ƴar maganar da yake son yi da shi.

Kan sa a ƙasa ya ce “Bari in je wurinsa”, Hajjah ta dubi Asma’u da ta zo ta lafe a gefenta “Ku je ki raka shi mana”, kafin Asma’u ta yi motsin kirki ya ce “A’a ta bar shi Hajjah, na ga ai ta ɓoye gefenki kamar bata son fita”, Asma’u na ji ta ƙara turo baki. Yaya Salma ta ce “Kya bari ma yarinya”, ita dai bata ce su ci kansu ba.

Deeni na zaune a gefen gado ya ji Sallmar Bashir, amsawa ya yi gami da faɗin “Ango ka sha ƙamshi”, zuciyarsa na kallon Bashir a bakin ƙofa, ƙarasowa Bashir ya yi gami da miƙa masa hannu suka gaisa, zama ya yi a gefensa suka ɗan tattauna maganar tafiya, kana Bashir ya tashi da nufin tafiya. Deeni ya so raka shi, amma Bashir ya hutar da shi.

Asma’u kuwa kowa kanta ya dawo, sosai suka yaba yadda Bashir ke nuna mata kulawa, musamman da ya kawo mata jaka har ɗakin Hajjah ba tare da kunya ba, Gwaggo Salame ta ce “Allah ya sa ya riƙe mana ke da Amana”, duk suka karɓe da “Amiin”, lokaci ɗaya kuma suka ci-gaba da maganar.

Bayan zancen ya ɗan lafa ne Yaya Asiya ta lura da Asma’u bata da niyyar tashi ta chanja kayan jikinta, sai ma ta miƙe ƙafa tana danna waya, da ɗan faɗa-faɗa ta ce mata “Wai Asma’u zaman me kike da ba zaki tashi ki watsa ruwa ki chanja kaya ba, kin wani yi zaune kin dafi waya kina chat.”

Hajiya Ummah ta ce “Haka zata je gidan mijin ta riƙa yi ko? Na daɗe ina faɗa mata duk lokacin da ta fita Unguwa ta dawo ta watsa ruwa ko ta wanke hammatarta, sannan ta nemi kayan da suka dace ta saka gami da fesa turare, amma ban ga alamar wannan maganar ta shiga ranta ba”, Asma’u kuwa kamar an soka mata mashi a zuciya, don ƙaramin aikinsu ne su sa ta gaba su yi ta zaƙulo laifukanta suna faɗa, wanda kuma hakan gyaran rayuwarta ne idan duk ta ɗauka.

Kamar zata yi kuka ta ce “Yanzu fa zan tashi”, A cikin hasken fitilar ɗakin Hajiya Ummah ta galla mata harara, “Toh maza ta shi ki je ki yi wanka”, ta ce “Da wannan sanyin?”, Hajiyarsu ta ce “Ki yi a toilet ɗina, akwai ruwan zafi a can”, ba don ta so ba ta tashi, wardrobe ta nufa ta fiddo zane da hijabi, cire kayan jikinta ta yi tare da shanya rigar a murfin wardrobe, duk da ba wari take ba, sai ma ƙamshi na musamman da ke tashi a jikin rigar. Kawai yana da kyau ne idan mutum ya fita unguwa ya dawo toh kafin ya linke kaya ya maida, ya ɗan shanya su sha iska, idan da hali ma ya wanke, saboda gumin jiki ɓata ƙamshin kaya yake.

Asma’u na fitowa ta shafe jikinta da mai, sannan ta ɗauki doguwar riga mai nauyi ta saka gami da feshe jikinta da turare, bayan ta zauna a gefen Hajiyarsu ne ta ce mata “Don Allah yanzu baki ji daɗin jikinki ba”, sosai kuwa Asma’u ta ji daɗin jikinta, har sanyin ma da take faɗa ta daina ji.

Yadda Hajja ta miƙe kafafu alamun gajiya ne Asma’u ta lura da shi, matsowa ta yi kusa da ƙafafun daga gefen Hajjah, “Da gani waɗannan ƙafafun kwanansu biyu ba massage”, ta faɗa a lokacin da take ɗan daddanna mata ƙafar, cike da jin daɗi Hajjah ta ce “Kamar kin sani auta, shi ya sa zan yi kewar ki”, Asma’u ta ce “Insha Allahu Hajjah ko bana nan zaki ji daɗi”, cewa ta yi “Allah ya sa”, saboda ta san damuwoyinta suna da yawa, Asma’u ce kuma kaɗai zata iya ji da su ba tare da gajiyawa ba, shi ya sa kullum cikin zullumi ta ke.

Asma’u kuwa wani ƙarfi na kula da mahaifiyarta ne ya shige ta, tun a cikin dare take kula da Mahaifiyarta kamar yadda ta saba, idan gari ya waye kuwa kai ka ce ba ita aka ɗaura ma aure ba, hidimarta take kamar kullum, duk da su Yaya Asiya da ke gidan, da an ce ta samu wuri ta zauna sai ta ce musu na bankwana ne, idan ta tafi sai ranar da Allah ya nufa dawo kuma.

Gashi kuma a kwana a tashi har ya rage safiyar gobe ne zasu tafi. Kwana ahalin gidan suka yi a ɗakin Hajjah suna yi ma Asma’u nasiha, Deeni kuma addu’a da neman dacewa suka suka riƙa yi mashi, don shi ne abin tausayi ba kowa ba.

Washegari da ƙarfe tara na safe suka fito, Lalu ne ya kama Hannun Deeni suka nufi ɗakin Hajjah, a gabanta suka zauna da nufin yin bankwana, inda Asma’u tuni ta riga su sai sharɓar kuka take, Deeni da ke ta tausayinta ya ce “Kukan nan ya isa haka mana, rayuwa dama ta gaji haka ai”, Lalu ma tuni tausayin ƙanwarsa ya mamaye shi, ita kuwa Hajjah ƴan ƙwallanta itama take.

Buɗe tafin hannunta ta yi, duban Asma’u da ke kuka ta yi tare da yi mata alamar ta ɗaura tafinta a kai, Lalu ne ya ɗora na shi a kan na Asma’u, sannan Deeni da ke babba shi ma ya ɗora na shi, ɗayan hannunta ta ɗora a kan duka hannayensu ta ce “Allah ya yi maku Albarka, Allah ya tsare mani ku, ya sa yadda zaku tafi lafiya, ku dawo mana lafiya”, kowa da ke ɗakin suka ce “Amiiiin.”

Deeni ta duba sannan ta yi mashi addu’a ta musamman a kan Allah ya sa a yi mashi aikin a Sa’a. Sannan ta ɗora da mishi da nasiha kamar haka “Wannan aikin da za a yi maka ɗayan biyu ne, ko dai a samu nasara, ko kuma akasin ta, don haka duk wadda ta faru, ka karɓa hannu biyu, sannan ka gode ma Allah”, Jinjina kai ya yi “Insha Allahu Hajjah.”,

Juyawa ta yi wurin Lalu “Farouk, ga amanar ɗan uwanka nan a hannunka, ka tabbatar bai shiga wata damuwa ba” shi ma ya ce “Insha Allahu Hajjah”, Albarka ta sanya musu sannan Lalu da Deeni suka janye hannunsu.

Bashir da bai daɗe da shigowa shi da abokinsa ne ta yi ma iznin shi ma ya matso kusa da ita. Cike da yaƙinin zai kula mata da ƴa ta dube shi cikin lafazi mai daɗi “Bashir, ina jin a jikina zaka zama silar farincikin ƴata, don haka don Allah ka riƙe mani ita da Amana, ka ga dai bata da kowa sai Allah da Manzonsa, sai kuma kai, don haka kada ka bari ta yi kuka”, kai jinjina “Insha Allahu Hajjah”, ta ce “Idan ta yi maka ba daidai ba, ka hukunta ta yadda ya kamata, na san Asma’u na da tsiwa, amma ina roƙonka da ka yi adalci a wurin hukuncin”, a wannan gaɓar bai iya cewa komai ba, don shi har yanzu bai ga wani hali da baya so a wurin Asma’u ba, mai yiwuwa sai a nan gaba, tunda ba a sanin asalin halin mutum sai an zauna da shi.

Bayan ta juya wurin Asma’u ne ta yi mata nasihar da ta ji tsoron Allah a gidan aurenta, sannan ta bi mijinta, domin aljannarta tana a ƙarƙashin ƙafarsa, biyayyarta ce zata bata damar samun wannan Aljanna.

Duk nasihohi da fatan Alkhairin da ya kamata ayi, Hajjah da su Hajiya Ummah sun yi ma ƴan’uwansu, lokacin da suka miƙe kuwa ɗaya bayan ɗaya suka yi hugging juna, Asma’u kuwa sai da aka ɓanɓare ta a jikin mahaifiyarta, har waje suka raka su, aikuwa ta sake ƙadaddabe ƴan’uwanta mata, Haƙuri suka bata, sannan Bashir ya kama hannunta suka shiga Mota, a seat ɗin gaba Deeni ya zauna shi da Driver, Su uku kuma suka zauna a baya, Inda suka sa Bashir tsakiya, yadda zai ji daɗin lallashin amaryarsa da ke gefensa.

Hannu suka ɗaga ma juna tare da addu’ar fatan samun Nasara. gidansu Bashir aka biya suka yi bankwana da Amarya, sannan suka nufi Abuja. Da misalin ƙarfe bakwai na yamma kuma jirginsu ya ta shi.

<< Mutuwar Tsaye 32Mutuwar Tsaye 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×