Mahaifin Bashir ya bada babbar gudunmawa a wurin tafiyar su Deeni, domin ko a cikin jirgi first class ya biya musu, ta yadda zasu yi tafiya mai cike walwala ba tare da takura ba, wani abin daɗin kuma su huɗu ne kaɗai a wurin, Deeni da Lalu, sai Asma’u da Bashir.
Asma’u kuwa wannan ne karon farko na shigar ta jirgi, Lalu kuma ya sha shiga daga Abuja zuwa Lagos, amma wannan ne karon farko na zamansa a VIP, don haka duk suke jin su tamkar a mafarki, musamman yadda wurin ya ƙayatu kamar suna a falon gidansu.
Lalu kam social person ne, don haka duk abin da ya shige mishi duhu a cikin jirgin sai ya tambayi Bashir ba tare da jin kunya ba, don baya son kansa ya yi murfi. Bashir kuma da yake yana son cigabansu, har abin da Lalu bai tambaya ba yake yi mishi bayani, daga ƙarshe ma sai ya maida dubansa a window yana kallon taurarin da suka ƙawata sararin samaniya, a cikin hasken farin watan da ya zama fitila ga daren.
Asma’u matsoraciyar gaske ce, daga zaunen da take a jikin window itama ta ce mishi “Bari wurin ganin ƙwam ka ga aljannu su biyo ka”, duban ta ya yi haɗe da ƴar harara “Su biyo ki dai”, ba tare da sake kula ta ba ya maida dubansa ga window, cike da nishaɗi yake ta kallon ayoyin Allah da ke cike da sarararin samaniya.
Ɗaya daga cikin hostess ɗin jirgin ce ta shigo domin ganin daidaituwar zamansu, da kuma jin abin da duk suke buƙata, da respect ta ɗan russuna musu kai alamun gaisuwa, bayan sun mayar mata da martanin gaisuwa ne ta tambaye su “Do you have an issues?”, girgiza kai Bashir da Lalu suka yi “Nope”, jinjina kai ta yi tare da duban Asma’u da ta lahe gefen mijinta sai ware ido take “What of you Ma?” Sosai kyawun hostess ɗin da ta yi cikin dressing ɗinsu ne ya yi ma Asma’u kwarjini, kasa bata amsa ta yi, sai dai Bashir ya ba ta amsa da “Nope Ma” murmushi da ke kwance a lips ɗinta ne ta ƙara faɗaɗawa “Okay”. Duban Deeni da fuskarsa ke ɗauke da baƙin gilashi ta yi, a wannan karon ita ce ya yi ma kwarjini, saboda hasken fuskar da Allah ya sa masa, shirun da ya yi kuma sai take ganin kamar Ego ne na masu kuɗi, saboda sun sha haɗuwa da Passengers masu girman kan tsiya, waɗanda ko magana basa son yi, don haka ta sa kai tare da komawa inda ta fito.
Deeni kuwa nutsuwar wurin ce ta jefa shi cikin tunanin matarsa, musamman da kunnuwansa ke ta jiyo mishi yadda Bashir ke ta ririta Asma’u, duk wani motsi na ta sai ya tambaye ta me take so? Ba tare da jin kunyar ƴan’uwanta ba, hakan ya na ma Deeni daɗi, amma kuma yana sanya masa kewar Deena.
Yanzun ma idanunsa da ke a rufe imaginig Deena yake zaune a gefe ta ɗan kwanto jikinsa, inda ɗayan hannun nashi yake ɗauke da Raihan da ke zaune a kan jikinsa, “Kin gaji ko?”, ya tambaye ta cikin kulawa”, sai da ta ƙara narkewa a kafaɗarsa sannan ta ce “Uhmm”, sumbatar kanta ya yi “Sorry, mun kusa sauka ai”, duk a cikin hasashen nasa yana ƙiyasta sun je wata ƙasa ne, suna a hanyarsu ta komawa gida Nigeria.
A irin wannan lokacin ne Deena ma ta kasa barci sai juye-juye kawai ta ke a kan gado, a ƙasan ranta itama tsara tafiyar take ga ta nan an yi ta da ita, kuma wai Deeni na da lafiya, ba wai a makaho ba. Da ta yi tunanin ta gama ne ta ɗauki wayarta, voice ɗin da Deeni ya yi mata ne da wayar Lalu ta kunna, inda ya ke cewa “Saura thirty minutes jirginmu ya tashi, ki mana addu’a kin ji matata?” son jin muryarsa mai sanya mata nutsuwa take, musamman kalmar “Matata” da ya faɗi, don haka ta yi ta maimaita sauraron voice ɗin, daga ƙarshe ne ta yi masa fatan sauka lafiya, da kuma fatan dacewa a wurin aikin, sannan ta rungume ɗanta ta cigaba da tunani, har barci da ke ɓarawo ya zo ya sace ta.
Cikin ikon Allah kuwa ƙarfe biyu saura ne jirginsu ya sauka a Capital City na Saudi Arabia, wato Riyadh, wanda ya kama ɗayan dare a agogon Nigeria. Inda aka ajiye wasu Passengers, yayin da idan jirgin ya huta kuma za a ƙara wasu Passengers ɗin haɗe da su Deeni su wuce India.
Bashir is familiar with these places, shi ya sa baya jin wani abu sabo a tare da shi, amma ba su Asma’u da ke gani ra’ayal aini ba, hatta Deeni dake feelings da imagination, ya ji a jikinsa ya zo wurin da bai taɓa zuwa irinsa ba, hatta weather da kuma mingling ɗin yake ji mutane na yi ya sha ban-ban da na Airport ɗin Nigeria, duk da mu ma a Nigeria ba daga baya ba.
Asma’u da Lalu kuwa baki a sake suke ta kallon Larabawa daga inda suke zaune. Bayan Bashir ya yi magana da attendance ne suka wuce hotel ɗin da ke cikin Airport ɗin. Abinci suka ci, suna gamawa kuma suka samu damar gaisawa da family ɗinsu ta hanyar voice call a WhatsApp, inda Lalu ya kira Hajiyarsu, cike da ƙaunar mahaifiyarsu suka gaisa ɗaya bayan ɗaya, lokacin da wayar na hannun Deeni ne ta ce mashi.
“Da zaku samu dama da ka je Ka’aba ka yi addu’a”, abin da ke ransa kenan shi ma, don dai ba dama tunda garin ma ba ɗaya ba, cewa ya yi “Wallahi kuwa Hajjah, sai dai idan mun dawo ne zamu yi Umara Insha Allahu”, ta ce “Toh Allah ya amince, ya sa a dace”, ya ce “Amiiiiin”, maida ma Asma’u wayar aka yi, tambayarta ta yi “Hajja, yanzu wa ke taya ki kwana?”, ta ce “Ni da Salame ne ai, zata ɗan kwana biyu, sannan ga Yusra itama.” Asma’u ta ji daɗin haka, ta san Gwaggo Salame da son aiki, kuma Hajiyarsu zata ji daɗi.
Ɗunguma suka yi zuwa ɗakunansu, ɗaki ɗaya Lalu da Deeni suka shiga, Asma’u kuma ita da mijinta. A wannan wurin ba gida bane, don haka Lalu ne ya yi ma Deeni jagora zuwa ban ɗakin, wanka da alwala ya yi ya fito, kai tsaye sallar nafila ya gabatar, sannan ya cigaba da addu’oinsa kamar haka “Allah gani a kusa da garin da aka haifi Manzonka Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama, ina roƙon ka don Rahamarka da jin ƙan ka, ka dubi raunina ka ba ni lafiya, domin kai ne mai warkarwa, sannan ka sa ina da rabon sake rayuwa da matata, domin ita ce jigon rayuwata a wannan duniyar”, ya yi addu’aoi sosai, sannan Lalu da ke ta chat ya taimaka masa ya dawo kan gado ya kwanta, zuciyarsa kuwa fal da tunanin matarsa da ɗansa, da a yanzu su ne a gabansa fiye da lalurar da ke damun shi.
A can ɗakin su Asma’u kuwa dukkansu sun yi wanka, sun kuma yi shirin barci, abin da ya ba Bashir dariya da mamaki shi ne yadda ta matsa nesa da shi ta kwanta, bai ce komai ba, don ya san idan ya ce ta dawo kusa da shi wani tashin hankalin ne, don haka da kansa ya matsa kusa da ita, blancket ɗin da take ciki ya ɗaga tare da shigewa ciki ya kwanta.
Barcin gajiya ya fara fizgar Asma’u ta ji shi kwance a bayanta, gashi ta ƙure ma gadon bare ta matsa, yunkurin tashi zaune ta shiga yi ya dakatar da ita ta hanyar ruƙo hannunta”Ina zaki je?”, ta ce “Zan koma can ne?”, ya ce “Can ina?”, ta yi shiru gabanta na faɗuwa, cike da damuwa ya ce “Wai me ya sa kike mani haka ne, Ni ba mijinki ba ne? Haba!”, sosai ta fahimci ya ji haushi, langaɓe kai ta yi, cikin son wanke kanta ta ce “Ka ga ina tsoron wani abu ya faru, ga su Yaya muna tare, zasu gane”, haɗe rai ya yi “Toh sai me idan sun gane, ai sun san dama haka zata faru ko shi ya sa ma suka aura mani ke.”
Bata san yana da fushi haka ba, jikinta a sanyaye ta ce “Ka yi haƙuri”, daga kwancen da yake ya ɗan kalle ta, “Ba komai, yi barcin ki”, matsawa ya yi nesa haɗe da juya mata baya. Aikuwa ƙunci kamar ya kashe ta, har ta kai ga ta nemi barci ta rasa, da abin ya ishe ta ne ta matsa bayansa. Bashir na ta ƙyafta idanun ya ji saukar hannun Asma’u a jikinsa, wata irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, bai san lokacin da ya ɗaura hannunsa a kan nata ba.
“Ba ka yi haƙurin ba?”
A shagwaɓe Asma’u ta tambaye shi, ka sa bata amsa ya yi saboda yanayin da ya samu kansa a ciki, sai bayan da ya juyo suna fuskantar juna ne ya ce “Wane ni da zan ƙi haƙuri da Gimbiya Asma’u” ta ji daɗin hakan sosai, a cikin sabon salon da ƴan’uwanta suka ɗaura ta a kai ne ta sumbaci lips ɗinsa, suma ne kawai Bashir bai yi ba, ɗaurawa ta yi da “Ka ga, ina fashin sallah fa”, idanunsa da ke a lumshe ya ware “Da gaske?”, ta ɗaga kai, ya ce “Kuma a hakan kike gudu na ko?” shiru ta yi tana ƴar dariya, cike da zolaya ya ce “Kin ga ranar da muka haɗu ƙila na baki ajiyar baby da zai taya mu zaman India”, maƙe kafaɗa ya yi “Kam, ba yanzu ba”, ya ce “Sai yaushe?”, ta ce “Lokacin da Allah ya nufa.”, shi ma a yanzu kam baya son daga zuwa ta samu juna biyu, har sai ya ga yadda zamansu a ƙasar ya kasance.
A wannan yanayin kam ya san duk bala’insa ba zai iya yi mata komai ba. A cikin salo na musamman suka faranta ran juna, daga nan suka yi barci.
Da Asuba Bashir ya riga Asma’u farkawa, sanin an ɗauke mata sallah ne sai ya bar ta ta sha barcinta, wanka da sallah ya gabatar, sannan ya zauna ya ɗan yi azkar, daga kan Carpet ɗin yake ya ga tana motsi, tuna farincikin da suka samu a daren jiya ne ya yi saurin tashi, a gefen gado ya zauna tare da faɗin sunanta, a hankali ta buɗe idanunta, cewa ya yi “Ki tashi, safiya ta yi.” Asma’u ta san da sauran tafiyar da ke gabansu, don haka bata ɓata lokaci ba ta tashi, cewa ya yi “Kin ga, gwara mu shirya da wuri, kada jirgi ya tafi ya barmu”, sosai maganar ta bata dariya, cike da zolaya ta ce “Toh ba sai ya jira mu ba”, dariya ya yi “Ai ko a Nigeria jirgi baya jiran kowa, bare kuma ƙasashe irin waɗannan da suka san aikinsu.”
Saukowa ta yi kan gadon haɗe da yin miƙa, lumshe idanunsa ya yi, a ransa ya ce “Masha Allah”, saboda Asma’unsa cikakkiyar mace ce.
“Ko in zo in maki wankan?”, ya faɗa yana dariya, daga bakin toilet ɗin da take ta ɗaga kai “Yeah”, idanu ya ɗan zaro “Da gaske kina so?”, ta ce “Ina so mana”, yadda ta yi maganar kamar da gaske ne ya ba shi ƙwarin guiwar tasowa daga gefen gadon, yana zuwa dab da banɗakin ta yi mashi gwalo tare da banko ƙofar ta sa key tana dariya.
Hannu riƙe da haɓa ya ce”Inyee! Ni zaki boda ko? Na rantse kuwa kin ci bashi yarinya”, komawa ya yi kan sofa ya zauna yana danna waya.
Wanka da kimtsa jiki Asma’u ta yi, sannan ta fito, cikin doguwar riga ta shirya, sannan ta ɗaura sweater a kai ta ɗan roller mayafin a kanta, hannunta ya kama suka shiga ɗakinsu Lalu.
Kwance suka samu Deeni a kan sofa yana fuskantar rufin sama, tashi ya yi zaune lokacin da ya ji muryarsu, zama suka yi a gefen gado, Asma’u ce ta gaishe shi “Yaya barka da safiya”, cike da kulawa ya ce “Barka dai Asma’u, ya gajiya?”, ta ce “Alhamdulillah”, Ya ce “Masha Allah”, hannu ya mika ma Bashir suka gaisa, Lalu na fitowa banɗaki suka gaisa da juna.
A nan suka yi zamansu aka yi ta hira akan doguwar tafiyar da ke gabansu, don Idan jirginsu ya sauka New Delhi a arewacin India, toh zasu sake hawan wani jirgin zuwa Banglore, wato babban birnin Karnataka da ke kudancin India, a can asbitin da za a yi ma Deeni aiki take. Asma’u da mararta ke ta ɗan murɗawa ce ta yi jugum, saboda idan tana period tana fama da ciwon mara, kuma tana tunanin yadda wannan doguwar tafiyar zata kasance.
Breakfast ɗin da aka kawo musu ma bata iya cin wani abin kirki ba, Bashir na lura da haka ya ce “Ki cika cikinki fa, kin ga muna da sauran tafiya a gaba”, ɗan yamutse fuska ta yi “Bana iya ci”, ya ce “Why?”, ta ce “Cikina ke ciwo”, ya fahimci sanadi, “Ayya, bari na sa miki order magani.”
Bayan ya gama break ɗinsa ne ya ɗauki wayarsa, take ya saka order magani a pharmacy ɗin dake cikin airport ɗin, ba a fi minti talatin ba bell ɗin ɗakinsu ya shiga ringing, Lalu ne ya miƙe, maganin ne har an kawo, karɓa Asma’u ta yi ta sha, sannan suka koma ɗakinsu don ƙarasa shiri, saboda jirginsu zai tashi ne da ƙarfe taran safe.
A cikin Airport ɗin suka ƙarasa tun ana saura hour ɗaya jirginsu ya tashi. Ba tare da ɓata lokaci ba aka yi duk abin da ya kamata ayi, ƙarfe tara da minti goma jirginsu na saman iska, zuwa azuhur kuma sun sauka a Indira Gandhi International Airport da ke a birnin New Delhi na ƙasar India.
A India Asma’u da Lalu sun ga mutane kala-kala, Deeni ma a irin wannan lokacin ne yake jin ƙunci a ransa, saboda yana son ganin abubuwan da labarinsu kawai yake ji, amma ba damar hakan.
A nan cikin airport ɗin suka ci abinci, kuma suka yi sallah, saboda jirgin da zai kai su Bangalore ya kusa tashi, Lalu da ya gaji da sa musu dokar lokacin tashin jirgi ya ce “Wai ba ma tafiya a mota ko Train ne?” Idanu Bashir ya zaro “Mota?” Lalu ya ce “Allah kuwa na gaji, sai faman yawo muke a saman iska kamar wasu tsuntsaye”, dariya sosai maganarsa ta sa su, Deeni ne ya ce “Samun wuri fa!”
Duk suka ƙara dariya”, Bashir ya ce “Ka san Distance ɗin da ke tsakanin Kaduna da Lagos?”, Sosai kuwa Lalu ya sani, tunda sun sha zuwa a mota, kan Flight da kuma train “Bashir ya ce “Toh Distance ɗin dake tsakanin New Delhi da Bangalore ya fi haka, sai ka yi estimate ɗin tafiyar idan a mota ko Train ne, ka ga ya distance ɗin zai kasance?”