Shiru Lalu ya yi yana nazarin tazarar dake tsakanin Lagos da Kaduna, ɗan jinjina kai ya yi saboda da ya fahimci tafiyar ba ta wasa ba ce, cewa ya yi “Lallai akwai tafiya ba kaɗan ba”, Bashir ya ce “Toh ka gani, tafiya ce mai nisan gaske, daga nan Indira Gandhi Airport zuwa Kempegowda International Airport a Banglore, estimated time a jirgi 2 hours ne, idan a mota ne kuma 25 hours ne..”, Katse shi Deeni yayi ta hanyar jefo masa tambaya “A train fa?”, saboda ƙagare yake ya ji yadda distance ɗin zai kasance, kasantuwar train duk ya fi su nawa.
Amsa Bashir ya ba shi da “Tafiyar zata kai 30 something hours, toh ta ina zamu fara?”, Deeni da ya tsani tafiyar mota ya ce “Na rantse kuwa, ni ko ina da lafiya bana juriyar zaman mota, bare yanzu da nake Umuyun”, duk don a yi dariya ya yi ma kansa ba’a, amma hasashen yadda makaho zai yi doguwar tafiya irin wannan da irin ƙuncin da ke ciki sai dai suka yi dariyar yaƙe, domin suna ji masa ba daɗi.
“Asmee, ko kin fi son mota ko Train?”, Bashir ya tambaye ta cike da zolaya, maƙe kafaɗa ta yi kamar ƙaramar yarinya “Uhm-uhmm!”, baki Lalu ya taɓe haɗe da ƴar dariya.
Da misalin ƙarfe uku jirginsu ya bar New Delhi, zuwa ƙarfe biyar da rabi sun sauka a Kempegowda International Airport Banglore. Airport ɗin ya ƙayatu sosai, musamman irin decoration na green grasses da aka ƙawata Airport ɗin da shi, su da suke gani sun yaba da wurin ba kaɗan ba, ƙauyanci wurin Asma’u kuwa bata san ma ta yi ba a lokacin da suka fito Airport ɗin, waiwayawa ta yi ta kalle shi, sannan ta juyo “Lalu, kamar stadium ko?”, juyawa duk suka yi, bayan sun kwashe da dariya ne Lalu ya ce “A haka stadium ɗin yake?”, Deeni ne ya tare mata faɗa ta hanyar faɗin “Ita abin da idanunta suka gani kenan”, Bashir ya ce “Lallai kam”, saboda kallo ɗaya yadda aka yi constructing rufin wurin tamkar stadium mutum zai faɗa. Mota suka shiga, tuni dama sun yi booking wani luxury hotel dake nearby Narayana Nethralaya Eye Hospital, inda nan ne za a yi ma Deeni aikin ido.
Kamar yadda suka yi a Riyadh, nan ma haka suka yi a wurin rabon ɗaki. Hannun Lalu cikin na Deeni suka shiga cikin ƙayataccen ɗakinsu mai cike da nutsatstsun kayan alatu, a gefen gado ya taimaka mashi ya zauna lokaci ɗaya kuma bakinsa na faɗin “Alhamdulillah”, zama gefensa Lalu ya yi tare da faɗin “Mun sha tafiya fa”, Deeni ya ce “Kai dai bari, Allah ya sa mun shigo a sa’a”, Lalu ya ce “Amiiiiin ya Allah.”
Shiru suka ɗan yi, Deeni na ta ƙiyasta yadda garin yake a zuciyarsa, hada-hadar mutane kaɗai ta tabbatar mashi da birnin babba ne, ji ya riƙa yi dama a ce Deena na tare da shi, duk da a ba shi da idanu yana ta yaƙinin tafiyar zata fi daɗi a tare da matarsa, kasantuwar idan suna tare da ita mantawa yake da duk wata damuwa da ta sha mashi kai. Kwaɗayin jin muryarta yake, tambayar Lalu ya yi “Deena bata sake magana ba?”, Yadda yake damuwa da ita ba ƙaramin ƙona ran Lalu yake ba, saboda ya lura da yadda yake shiga wani hali na ƙunci wanda ko shakka babu tunaninta ne.
Waya Lalu ya ɗauka, kai tsaye WhatsApp ya shiga, aikuwa saƙon Deena ne ontop, bayan jerin missed calls ɗinta, a daƙile ya ce “Ta yi magana”, cike da son jin saƙon masoyiyarsa ya tambaye shi “Me ta ce?”, Lalu ya ce “Voice ne”, tare da yin playing ɗinsa, hannun Deeni ya kama “Ga wayar”, gam Deeni ya riƙe ta, tare da ɗago da ita a saitin fuskarsa.
Hasken wayar ne Deeni ya ji ya ratsa masa ido, Ras gabansa ya faɗi, domin a karon farko kenan da ya taɓa jin irin haka “Ka san me Lalu?” Girgiza kai ya yi “A’a”, Deeni ya ce “Hasken wayar nan na ji a idanuna?”, Cike da mamaki Lalu ya ce “Da gaske?”, ya ce “Na rantse kuwa”, ɗan jujjuya wayar ya riƙa yi by his left and right side, yana ganin yadda hasken ke matsawa a kowane side.
Lalu ya ce “Insha Allahu warakar ma tana nan tafe”, Deeni ya ce “Allah ya sa, da na yi farinciki sosai Lalu.”
Deena ce a ransa, don haka ya sake playing ɗin voice ɗin, idanunsa a lumshe yake sauraron maganarta kamar haka “Asslm Alkm Ƴayana, fatan kun sauka lafiya, Allah ya huta gajiya Amiiiiin. Ya Uncle Lalu, da su Asma’u. Na yi missing ɗinka mijina, ina jin kamar na buɗe idanu na ganni a kusa da kai.”
Lalu na jin maganarta ransa ya kuma ɓaci, tabbas yana tausayi su, toh amma yadda suke magana kamar ba saki a tsakanin su shi ke damun shi, baya son su cigaba da irin abin da zai hana su zaman lafiya, tunda basu da tabbacin zasu sake rayuwa a tare.
Bai ida ƙuluwa ba sai lokacin da Deeni ya ba shi wayar a kan ya kira mashi ita voice call, tunda ta faɗa mashi ta daina rufe data saboda shi, Lalu bai yi musu ba ya kira mashi ita, yana jin sun fara soyayyarsu ya tashi ya shige banɗaki yana tsaki.
Deeni kuwa farinciki fal da ransa lokacin da suke waya da matarsa, tambayarta ya yi “Ina Mommah”, ta ce “Tana can ɗakinta”, ya ce “Bata gane muna waya ba kuwa”, Deena ta ce “Ta kusa ganewa”, ya ce “Da gaske?” Ta ce “Allah kuwa”, ya ce “Toh ki kula my Deena, da wayar nan ne kaɗai nake samun sauƙin ciwon raba ni da ke, idan da bama waya ƙila da yanzu na mutu ma”, daga can ta ce “Ai ba zaka mutu ba, da kaina zan riƙa zuwa wurinka ko da za a tsire ni kuwa” ƴar dariya ya yi “Ke! Koda wasa kada ki fara, umurnin uwa ya wuce wasa kin ji ko”, cewa ta yi “Toh ai ba zan iya jurar rashin ka ba”, ya ce “Duk da haka dai, don haka ki kula”, ta ce “Insha Allah”, sun sha wayarsu sosai, kafin daga bisani su yi sallama.
Lalu na fitowa ya ga yadda soyayya ta kashe ma Deeni jiki, zama ya yi gefensa bayan ya karɓi wayar, shi baya barin sai ta kwana, don haka ya ce “Yaya, yadda kuke tare da Deena zai iya zame muku matsala fa”, Deeni ya ce “Me yasa ka ce “Haka?”, Lalu ya ce “Ka ga saki ne a tsakaninku wanda sai Allah ne kaɗai zai iya gyara al’amarin, toh me ya sa ba zaku koya ma kanku haƙuri da juna ba? Sai ma kullum kuke ƙara maida kanku a ruwa, wannan zai iya zama silar da zaku shiga wani halin fa.”
Sosai Deeni ya fahimci maganar Lalu, ɗan saurarawa ya yi kafin ya ce “Farouk, nima ina tunanin abin da kake son fahimtar da ni, ton amma, ta ya kake ganin zan iya ɗaukar wannan rashin har guda biyu, ba idanun, ba mata? Akwai sauƙi kuwa?”
Yadda ya ƙarashe maganar kamar zai yi kuka ne ya ba Lalu tausayi, tabbas ko shi ne da wahala ya iya, girgiza kai Lalu ya yi kafin ya ce “A’a”, Deeni ya ce “Ka gani, ƙarfin hali kawai nake, ko da ina da idanu rashin masoyi ba shi da daɗi, wannan wayar da muke domin farincikinta ne, don ta samu sauƙi” Lalu ya ce “Amma kuma zata iya bijire ma mahaifiyarta ai”, Deeni ya ce “Kuma haka ne, zan kiyaye Insha Allahu.”
A ɗakinsu Asma’u kuwa daaga ake ta sha, tunda Bashir ya leƙa banɗakin ya ga ƙayatuwarsa ya fito tare da rantsuwa a kan wannan banɗakin ba na mutum ɗaya bane, da Asma’u ta tambaye shi na mutum nawa ne? Sai ya amsa mata da na amarya da ango ne, sosai ta fahimci inda ya dosa, duban shi ta yi daga zaunen da take a gefen gado ta ce “Ka ga sai ango ya fara shiga, idan ya fito sai amarya itama ta shiga.”
Sam baya son gardama, shi ya sa ya ɓullo mata ta hanyar da baza ta yi gardamar ba, ɗan rage tsawonsa ya yi, lokaci ɗaya kuma ya sassauta murya tare ƙure mata kallo “Asma’u, kina wahalar da ni”, yadda ya ƙarashe maganar ba wasa ne ya sa ta saurin duban sa.
Idanu ta ware “Ni nake wahalar da kai?”, kai ya ɗaga mata “Uhmm”, tunawa ta yi da nasihohin da aka yi mata na ta zama mai biyayya ga mijinta, duk abin da ta san zai faranta ransa, toh ta koya ma kanta shi ko da ba ta so.
“In sha Allahu na gama wahalar da mijina”, ta faɗa tare da miƙewa, shi ma ƙarasa miƙewar ya yi yana mata kallon mamaki, domin itama babu wasa a maganarta.
Hannayenta ta ɗora a kan kafaɗunsa, cikin salo mai cike da jan hankali ta ce “Me kake so?”, zagayo da hannunsa ɗaya ya yi a jikinta ya ce “Mu je banɗaki, ko ba kya iyawa?”, gaban Asma’u na dukan uku-uku ta ce “Zan iya duk abin da mijina yake so”, ya ce “Komai na ce?”, tambaya ta maido mashi “Kana musu ne?”, kai ya girgiza, saboda ta fara nuna mashi idanunta a buɗe suke, cewa ta yi “Toh mu je”, tamkar raƙumi da akala ya bi ta suka nufi ban ɗaki, har sun kai bakin ƙofa ya dakatar da ita “Asma’u, na hutar da ke, koma ki zauna”, wani irin kallo ta jefe shi da shi “Bana son wahalar da kai fa”, ya ce “Ai ni na ce”, cike da ƙarfin hali ta yi ta musun akan sai ta shiga, da ya ga kamar da gaske ta ke, ya yi maza ya shige ban ɗakin ya rufe ƙofar.
Sosai ya bata dariya, don wani abu ya rikayi kamar ba Bashir mai buɗaɗɗen ido ba, jiki ba ƙwari ta koma kan sofa ta zauna jagwab, lokaci ɗaya kuma bakinta na faɗin “Wai ni Allah”, saboda tsoronta kada Bashir ya sanya ta yanayin da zata ji kunya a gaban ƴan’uwanta, sannan ita dai a hanlin yanzu tsoronsa da kuma kunyar sa ma take sosai.
Wankansa ya yi ya fito, daga ita har shi kasa gumtse dariyarsu suka yi, ta nufi ban ɗaki ne ya tambaye ta “Dariyar me kike?”, ta ce “Irin wadda kake yi ce nake”, sai da ya sake wata dariyar kafin ya ce “Zamu sake gamewa ai.”
Wankan ta yi ta fito, bayan ta kimtsa ne suka ɗunguma ɗakinsu Deeni, a can suka ci abinci, sannan suka yi sallolinsu.
Dukkansu a gajiye suke, don haka basu yi wata doguwar hira ba. Ɗaki su Asma’u suka dawo suka yi shirin bacci, kasantuwar gobe tunda safe zasu tafi asibitin bisa ga jagorancin wani Abokin Bashir mai suna Akshay Singh.
Washegari tunda safe suka fara shiri, zuwa ƙarfe goma ne suka nufi Naranaya Nethralaya Eye Hospital dake a nan cikin Bangalore.
Naranayax Eye Hospital na ɗaya daga cikin manyan Hospitals ɗin da ake kula da lafiyar idanu, kuma internationally suke samun Patients kasantuwar sun ƙware a wurin aikinsu.
Tun da suka shigo gate ɗin asibitin Lalu da Asma’u suka baza idanu suna kallon dogon ginin da aka ƙawata da glass, Lalu ya ce “Lallai asibitin nan babba ce”, Ko da Deeni bai gani ba, amma ya ji ajikinsa asibitin babba ne.
A daidai entrance ɗin shiga cikin ginin ne suka tsaya, security ɗin dake wurin suka gaisa da shi, tare da nuna masa alamar samun damar zuwa asibitin.
A daidai entrance ɗin shiga cikin ginin ne suka tsaya, security ɗin dake wurin suka gaisa da shi, tare da nuna masa alamar samun damar zuwa asibitin.
Iznin shiga ya ba su, amma kafin nan sai da ya buƙaci da su karanta ma Deeni rubutun da ke jikin bangon, don da shi ne marar lafiya zai shiga cikin asibitin.
Tambayar su ya yi me aka rubuta, Lalu ya ce “Your Faith shall heal you”, kai Deeni ya jinjina tare da faɗin “Gaskiya ne, shi dama magani ai believe ne haɗe da hope, kuma without these ma da bamu zo ba”, Bashir ya ce “Haka ne.”
A reception Deeni da Asma’u suka zauna, yayin da Lalu da Bashir suka je wurin attendance suka karɓi duk wani abin da ya kamata su karɓa, sannan suka dawo wurinsu Deeni suka zauna domin jiran kiran doctor.
Suna cikin ƴar hira ne sai ga abokin Bashir wato Akshay ya shigo, Bashir na ganin shi ya miƙe tsaye yana murna saboda kaf India ba shi da aboki kamar sa, kasantuwar halinsu na kirki ya zo ɗaya.
“You are highly welcome my friend”, Akshay ya faɗa bayan sun yi hugging juna shi da Bashir, cike da murna Bashir ya ce “Thank you my dosti.”
Su Deeni ma tashi tsaye suka yi domin gaisuwa, abin da ya ba su mamaki shi ne irin gaisuwar girmamawar da Akshay ya yi ma Deeni, domin duƙawa ya yi har ƙasa ya taɓa ƙafafun Deeni irin yadda Indiyawa suke gaishe da manyan su, wani abin ƙayatarwar kuma shi ne yadda Deeni ya ɗago kafaɗun Akshay kamar shi ma ba indiyen ne bakinsa na faɗin “Thank you.”
Cike da tausayi Akshay ya rungume shi, yana faɗin “May God heal you”, Deeni ya ce “Amiin ya Allah.”
Hannu ya ɗaga ma Asma’u bakinsa na faɗin “You are welcome our bride”, Asma’u ta ce “Thank you”, Lalu ma tuni sun gaisa ta hanyar hugging da kuma musabaha.
Bayan sun gama gaisawa ne Bashir ya ce “You imitates African time from your African friends, abi?”, kai Akshay ya girgiza yana dariya “Oh sorry, I knew you are waiting for me since yesterday, it’s sudden excuse please”, ya faɗa tare da ɗaga hannu alamar ban haƙuri.
Sauke mashi hannu Bashir ya yi tare faɗin “Don’t mind”, ƴar hira ta abokai suka riƙa yi.
Deeni shi dai yana jin su kawai, a yanayin jikinsa sai yake ji tamkar mafarki ya ke, wai ashe har akwai ƙaddarar da zata sa ya daina gani, kuma har a dalilin wannan ƙaddara zai zo India “Lallai Allah ne kaɗai masanin ƙaddarar da ke rubuce a rayuwar bawa, da ace kuma bawa ya san da faruwar wasu abubuwan, toh da ya kauce musu, ko kuma ya shirya ma faruwar wasu irin yadda yake so”, a ransa ya faɗi haka cike da miƙa lamuransa ga Allah.
Yana cikin wannan tunanin ne ya ji muryar wata nurse tana faɗin “Nuruddeen, from Nigeria”, a dai-dai inda ya ji muryarta ne ya ɗaga hannu “Ma”, duk da su Lalu sun amsa mata.
“Doctor is waiting for you”, ta faɗa tana duban Deeni, kai ya jinjina mata “Okay”, Bashir ne ya kama shi suka miƙe, Inda ya yi masa jagora har office ɗin doctor, bisa ga jagorancin Nurse ɗin.
Sosai Deeni ya tafi da hankalin mutanen da ke wurin, Akshay kuwa sosai ya bayyana tausayinsa ga Deeni. A nan waɗanda suke yare ɗaya suka riƙa tambayarshi abin da ya samu Deeni da yaransu, bayan ya ba su labari ne suka riƙa yi mashi addu’a.
Dr. Niranjana ita ce wadda Deeni ya yi arba da ita a office ɗin, karon farko da ta ga Patients mai capacity da ya bata tausayi, duk da ta ga Patients ɗin da ta zubar ma hawaye, kasantuwar ta mai tausayin gaske, toh amma tausayin Deeni ya sha banban da na sauran, domin ko shakka babu shi ɗin yana da muhmmiyar rawar da yake takawa ga ahalinsa.
“Welcome to our hospital”, ta faɗa tana kallon Bashir da ke facing Deeni a kan kujerar da ke gaban Table ɗinta, amma kuma zuciyarta Deeni take kallo cike da tausayi.
“Thank you”, suka faɗa gabaɗayansu.
Cigaba da magana ta yi “Before we start, I want informed you that only your faith can heal you not doctos. Our own is to use our knowledge and skills for treating you effectively, hope you get it.”
Wannan maganar da ta yi irinta ce dukkansu suke yi ma Patients ɗinsu, don haka Bashir ne ya tabbatar mata da Deeni ya san haka sosai, domin shi ɗin medical doctor ne a fannin gynecology, tambayar Bashir ta yi “Really?”, Bashir ya ce “Yeah, he still have a patients that are waiting for him to recover.“
Cike da tausayin Deeni ta ba su tabbacin Insha Allahu zai samu lafiya har ya koma bakin aikinsa, a ran Deeni ya ce “Allah Ya sa..”